← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa yayi ya kara kallon asma,u sannan yace ki shirya gobe zakiyi bako, ni ba nufina namiki auren dule ba, a'a zaizo ne ya ganki, kema ki ganshi, idan kun daidaita shikenan, idan kuma baku daidaita ba zan sake turo wani, bana bukatar kice wai saikinsa halinshi, duk wandan
kikaga na turo miki na yadda da inganshi tare da mutuncin iyayen sa, dan haka kwana 2 kawai na baku, ganin inda tayi shiru yasa abba fadin kinajina ko ?

Kai kawai ta iya dagawa sannan tasa hannunta ta share hawaye"

Tattaunawa suka fara tsakanin mama da abba tare da yaya usman, haka ne yabata daman tashi tabar musu falon"

****

Washegari ma'u ta tashi da matsanan cin ciwon kai, saka makon rashin baccin da batasamu, taso taki zuwa mkrnt amman kuma tanason taga halin da ummi take ciki, dan haka ta mike tahau shiri"

Drive ne ya kaita har bakin mkrntr sannan ya juya, dan kaka bata samu daman zuwa gidan su deeni ba saida aka tashi break"

Xama sukayi jugum ita da ummi kamar masu zaman makoki"

Bayan antashi makaranta abba da kanshi yazo ya dauketa"

Koda ta shiga gida a kitchen ta samu mama tanata soye2 sai alokacin ta tona da bakon da abba yace zaizo"

Yatsuna baki tayi sannan ta juya ta shige daki, wanka tayi tai sallah sannan ta tsaya tai addu'a sosai Allah ya kubutar da deeni daga hannun Jamal"

Tana zaune kan sallayan mama tashigo tana fadin Asma'u maza ki fito bakonki ya iso"

Gabanta taji ya fadi, kanta ta daga ta kalli mama sannan tace...
Mama dan Allah kice bacci nake, nifa bansan mezance mai ba"

Shiru mamatayi zuwa can tace, kinga, Asma'u banason shirme maza ki fito ko na kira abbanki na gayamai"

Cikin sauri ta mike tana matso hawaye ta nufi hanyan kofa"

Ke !! Zonan mama ta fada tana kare mata kallo"

Bayan ta juyo tace nufinki ahaka zaki tafi fuska saikace tsowar me takaba"

Bakinta agaba tace to ai yanzun nan fah nayi wanka"

Mama batace komai ba ta juya ta fara ciro mata kaya, mika mata tayi ta Saka sannan ta zaunar da ita dakanta ta mata kwalliya bawata me hayaniya ba"

Madaidaicin gyale ta mika mata dasukai matukar dacewa da kayan datasa, kallo ta kare mata sannan tace toh maza ga kayan motsa baki can na hada ki dauka ki tafi dashi"

Jikinta babu kwari ta nufa kitchen tare da nazarin abinda zata ma bakon ta kuntuka mishi haushi"

Ahankali ta tura kofar falon abba tare da sallama cikin siririyar muryanta, cikin ido ta kalli bakon nata farine babu laifi yana da kyau daidai misali, saidai daganin shi yana da iyali, duk da cewa bawani babba bane amman daganin shi yana da iyali, sauke idonta tayi akanshi sannan ta karasa shiga falon tare da neman yadda zata mishi"

Kayan motsa bakin ta ajeye agefen shi sannan ta koma tsakiyan falon ta tsuna, cikin ladabi tace...

Inakwana daddy, ina gajiya, bata jira ya amsa ba taci gaba da cewa gashi kazo kuma abban bayanan ya tafi Office amman idan ya dawo zan fadamishi kazo"

Cikin mamaki yake kallonta aranshi yace lallai wannan yariya da hikima take, idan na fahimceta tana nufin namata tsufa, gyaran murya yayi sannan yayi murmushi yace, toh shikenan asma'u idan ya dawo din ki gaya mishi, amman wa zaki ce masa?

Rasa abun cewa tayi zuwa can tace zance masa bayan fitanshi wani yazo neman shi"

Murmushi ya sake zaiso kasancewa da wannan yariyar, kallonta yayi ya girgiza kai sannan yace kinada abin dariya, ni sunana Jafar inada mata 1 da yara na guda 2 nine bakon da mahaifi ki ya sanar dake zuwan Sa, duk da nasan kinsan koni waye"

Ko kallon gafen shi batayi ba acikin zuciyarta tace wato abba neman kai yake dani, ya rasa wadda zai turomin sai me mata, dumi taji akumatun ta tana shafowa taji hawaye"

Duk abin da take bakonta na kallonta dan haka ya mike yace nizan tafi sai ince ki gaida mutanen gida"

Bata ce komai ba yasa hannu ya ciro kudi aljihu ya aje agefen kujera yayi waje dan yaga bata da niyar kula shi"

Itama ficewa tayi batare da ta dau kudin da ya ajiye mata ba, bare kayan motsa bakin datakai mai"

Afalo ta wuce mama ta shige dakinta, zama tayi tare da addu'a Allah yasa abban ya janye wannan kudirin nashi"

Washegari da safe ta shirya tsaf domin zuwa mkrnt falon abba ta fara shiga, bayan ta gaisheshi ta mike zata wuce abba ya dakatar da ita"

Komawa tayi ta zau tare da sauke kanta akasa"

Kallonta abba yayi sosai sannan yace bakon ki yazo jiya ko?

Kanta akasa tace eh"

Shiru ne ya ziyarci falon zuwa can abba ya sake cewa...
To me kika ce ? Ya miki ?

Shiru tayi bata ce komai ba, zuwa can abba ya sake cewa....

Karmuyi haka dake mamana, banason na takuraki saboda kin min biyayya saboda haka nakeson na saka miki, wadda kike so shi zan baki bazan miki auren dole ba da iznin Allah, inason nasan meye azuciyar ki game da jafar ?

Motsa baki tai tayi daker ta iya bude baki tace Abba ni banason shi"

Saboda me ? abba ya tambaya

Abba tsoho ne fah kuma yana da mata"

Murmushi Abba yayi kadan sannan yace ashe jafar ya cinka daidai, toh bakomai amman nayi miki sha,wan shi, dan yaro ne me mutunci da sanin ya kamata, haka iyayen shi mutane ne masu karamci, kuma bawani babba bane mamana, ko zai girmin usman bazai wuce shekara daya ba, amman ba komai tunda kince haka, gabe wani zaizo ki ganshi, kinji ko?

Saida gabanta ya fadi wato abba bazai bar mgn haka ba, da wannan tunanin ta tafi mkrnt ko wa Abba zai sake turo mata oho?

***

Akofar gidan su deeni ta hango samari cike, da alama yaran duna ne kome suke agurin oho, acikin su caka kawai ta sheda yanata fada yana daga hannu saidai har motan su ta wuce bata tsinci abinda suke cewa ba"

Ko a aji batai karatun kirki ba Allah2 take atashi break taje taga me akeyi"

Kawayen ta kallonta kawai sukeyi, domin sun kula akwai abun da ke damunta"

Ana buga kararrawa ta fito ta nufi gidan su deeni saidai yazun babu kowa akofar gidan"

Cikin gidan ta nufa tana tura kofar sukayi ido 4 da deeni, zaune yake kan kujera ummi tsugune agefen shi tana tsuma tsunma aruwa zafi tana dannan me ajikin shi"

Hunnu tasa ta mumtsuke idonta sannan ta sake sauke shi akan deeni, aguje tayi kansu, jinta kawai tayi jikin deeni ya rungume ta yana sumbatan ta"

Cikin sauri ummi ta dauke bokitin ruwan zafinta ta basu guri, jefe2 tana satan kallon su"

Sun dan juma ahaka ahankali asma'u ta zame ta koma gefe sannan ta zubawa deeni ido"

Shedan bulala ne ajikin shi rudu2 wasu guraren hadda ciwo, hawaye taji ya cika mata ido, nan danan suka fara zubowa acikin kuka tace nina jawo maka nasan bakowa bane yayi maka haka sai Jamal dan Allah ka yafe min"

Hannuta ya jawo ya riketa dakyau sannan yace....

Shine Asma'u amman karki damu yanaso ne wai ya nunamin shi Soja ne amman ba jarumi ba, wanna abin daya aikata ya nunamin be kai ba"

Kara karkace baki yayi sama sannan yace.....
Ai nagaya masa dan *uwas* data haife shi, idan yana jin yakai shege, ya goyo *uwassa* abaya, ya fadi ina zamu hadu, daban daban zasu koma gida"

Heart beat
*Mmn Yazeed*



Heart Beat
*Mmn Yazeed*鈥�
[22:51, 12/19/2017] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: 馃挆馃挐馃挐馃挆
鈥�*BUGUN ZUCIYA*鈥�
( 鈥婬eartbeat鈥�)

馃挀馃挐馃挆
馃挆

馃挀馃挐馃挆
鈥婤y鈥�
馃挆
鈥嬧€�*Fadeela Lamido*

*@AM拢拢NCI WRITER'S ASSOCIATION馃*

Dedicated 馃憞馃徎
*Sa'adatu Lamido馃憣馃徎*

3鈨�1鈨� to 3鈨�2鈨�

馃檳馃檳 Hannu shi yasa yana share mata hawaye, yana cigaba da fadin.....
Ki daina zubar da hawayen Ki abanza ni be tsoratani ba kuma banyi nadamar hadashi da duna ba, kisan menene, tuhumata yakeyi akan ki"

Ido ta zare akaina kuma?

Eh dan ya nemi nabashi takardan da kika wurgu min da ita"

Tashin hankali bai yane afuskan ta tace... Kabashi ne?

A'a na nunamai bansan wannan zancen ba, amman sai naga yayi dariya, na lura kanshi na aiki sosai, murmushi deeni yayi kadan sannan yace.....
Asma'u da kika samu lbrn Sojoji sun tafi dani ya kikaji?

Wani sabo hawaye ne ya fara zobo mata cikin kuka tace....
Komawa nayi tamkar marainiya, kullum cikin kuka nake, gashi ranan na taho da matsalata, domin mune mi mafuta, wlh ranan jinayi kaman bani da lfy, kuma bansan abinda kemin ciwo ba, tun daga ranan hankali na bekara kwanciya ba, kum.....

Deeni ne ya matse hannun ta, dan haka ta kasa karasa abin da tayi niyya, sannan ta daga ido ta kalleshi"

Shima ita yake kallo sannan yace.....
Inason nasan wacce matsala ce kikazo da ita ranan?

Shiru tayi zuwa can tace abbana ne yace.....
Inayin sauka zai min aure, kuma gashi saura sati 6, yace bazan wuce wata 3 agida ba, shine hankali na ya tashi sosai"

Hannunta ya kara runtsewa sannan yace.....

Toh menene abin damuwa anan Asma'u ?, ko bakison muyi aure ne ?

Shiru tayi tana kallon kasa, zuwacan taji ya sake cewa....

Gayamin meye matsalan ?

Kanta akasa tace inajin tsoron gayawa abbana kai nake so"

Matse hannunta yayi da karfi harsai da tayi kara, cikin yanayi irin na mejin zafi tace.....
Wayyo, hannuna dan Allah kabari da
Zafi fah"

Me yasa kike tsoro? taji ya fadi fuskan shi murtuk"

Saboda ina tunanin bazai yadda ba"

Bangane bazai yadda ba, shi zai zauna miki da miji ?

A'a ba haka bane, ta fada tare da kautar da idanta gefe, haka nan taji bata ji dadin furucin ba, sai take ga kamar da raini aciki"

Shiko ido ya kura mata zuwa can yace.... Inajin ki"

Idan ta kwal2 yayi kaman zatai kuka tace....
Yaya deeni ni. nasan waye abba na, mawuyacin abu ne ya amince dakai, ko hankan zata kasan ce ko, to saida sa hannun kakata, kuma nafara mata zancen duk tabi ta firgice, saboda ta tsorata dakai, gashi abbana jiya ya turo min wani mutumi wai mu daidaita, karashe mgnr tayi tana zubar da hawaye"
Chapter 14 · 0% Book details