← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 47

Sashe 36

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Deeni najin haka yaja jiki yana matsanancin haki yabi ta wani logu yabar gidan dan ya tabbarar idan aka gwadashi za,ace zuciyar shi ta wargatse"

Koda suka dawo babu kowa gurin dan haka daddy yace yaje zai kawo sa"

****

Tsayon kwana 3 ma'u ta fara motsawa, amman babu baki kuma hawayen nan makale agefen idonta bata rabo dashi"

Haka kuma batacin abinci koda yaushe ruwa, dan haka momy take dama mata koko datace ruwa saita zuba ruwa akai ta mika mata"

Aranan su abba suka tafi gaba daya bayam sun mata nasiha sosai, sunso su tafi da ita amma ta nuna bazata ba"

Deeni ko kokari boye damuwan shi yake amman ji yake zuciyar shi tafi garwashi zafi"

Tsayon sati daya da tafiyan su abba amman bar yanzun ma'u bata magana ta rame ko cikakiyar mikewa bata iyawa, farau faraun ma yanzun sai anyi da gaske takesha wanna wadda tarage shi momy ke kurbewa"

Damisalin 12:31am kowa ya kwanta ammam babu wadda ya runtsa"

Dagacan suka farajin kara motaci tare da hayaniya"

Cikin sauri daddy ya tashi ya zauna yana tunanin anguwar lfy kuwa? yana yinkurin sauka agadon wayar sa tai kara, be duba no ba ya dauka tare da mikewa tsaye"

Muryan usman yaji yana fadin daddy abude mana Get"

Fitowa daddy yayi yana tsakiyar falon ya daga murya yace usman kana nufin kana kofar Gidan nan?

Wannan mgn ta daddy babu wada bejitaba dan duk Gidan basu runta ba"

Daidai lokacin da daddy ke fadin baba megadi bude get, a guje ma'u ta duro daga gado, tana fitowa falo ta fadi kasa......

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
.💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*

8⃣7⃣to8⃣9⃣

Ma'u na kwance akasa taga wucewan momy da nafisa aguje dan haka tafara kokarin mikewa amman jiri sai maita yake"

Daga can ta farajin karan momtoci suna shigowa gidan tare da hayaniyan mutane"

Ai ganinta kawai tayi ta mike, tana daf da isa gurin taji momy na fadin....

Usman ?, ansame Jamal din ne?

Bataji amsan da usman yaba momy ba tasakejin daddy yace yana raye?

Aguje ta kwasa ganinta kawai tayi atsakiyan sojoji, kutsawa taitayi har ta isa gaban motar da taga sunzagaye"

Anan taga suna ciki cikin fito da Jamal daga cikin motar"

Daga momy har abba rigegen kallon Jamal suke, dan haka gaba daya sunkewaye gurin"

Momy fadi take Jamal? Kaine Jamal?

Ahakali yace nine momy"

Ina ka shiga jamal kabarmu cikin wani hali?

Cikin yanayi irin na mejin jiki yace kuyi hakuri"

Itako ma'u har yanzun raba ido take takalli deeni, domin kafarshi kawai take iya gani mutane duk suntare mata ganin sa"

Wani daga cikin sojojin ne yace.....

Alhaji yakamata akaishi ciki domin yana bugatan hutu"

Cak suka daukeshi suka nufi part din daddy, kan gadon daddy suka kwantar dashi, sannan suka juya usman kadai ya zauna"

Duk suna tsaye akan jamal daddy Momy, nafisa ma tana tsaye agefe"

Jamal suke kare ma kallo yadda aka daure cinyan shi duk biyun, gashi yayi wani irin baki ya rame, tare da tarin uban kasunba"

Bayan daddy ya gama karewa Jamal kallo ya kalli usman yace"

Wai karayace har cinya biyu?

Girgiza kai Jamal yayi tare da fadin harbi ne aduk kafa fuwan, kuma ya shiga naman sa sosai, dan haka akace karya taka kafan harsai wajen ya warke"

Jimami sukaitayi akan jamal, shidai yana kwance idonshi rufe shi kadai yasan me yakeji"

Sai lokacin Momy ta juya ta kalli dakin tare da fadin a'a ina asma'u?

Gaba dayansu waigowa sukayi suna kallon dakin arude sukayo waje"

Itako ma'u kunya ce ta kamata tana kutsawa momy da abba suna kutsawa dan haka ta zauna afalo tare da hada kai da guiwa domin ta kusa tasa Jamal a idon ta, amman saidai shi kanshima Jamal din kunyan hada ido take dashi"

Suna fitowa suka ganta zaune tayi tagumi"

Daddy ne yace ke meyasa zaki zauna Anan ?, tashi maza"

Kanta akasa ta fara kokarin mikewa Momy ce ta taimaka mata ta mike sannan ta riketa har suka shiga dakin"

Abakin gadon ta zaunar da ita sannan ta juya ta fita badan tagaji da kallon Jamal ba saidan ta kula kamar kunya ma'u takeji"

Shima Jamal din yanajin fitan momy ya bude ido da sauri ya sauke kan ma'u, cikin sauri ya fara kokarin jawo jikin shi kusa da ita tare da miko hannu"

Usman deke zaune agefe ya dago kai ya kalli ma'u gani yayi har yanzun bata daga kai ta kalli Jamal ba, dan haka ya mike ya fice"

Kaman jira ma'u take ta juya ta kalli Jamal tare da fadawa kan kirjin shi, fashewa tayi da wani irin kuka har su momyn dake falo suna jinta"

Hannun shi yasa guda daya ya kara danna kanta akirjin shi, ji yayi zuciyar shi fari kar domin kukan ma'u ya tabbatar mai tayi missing dinshi"

Dan kwalin dake kanta ya zame sannan ya tura hannun shi cikin gashin kanta, zuwa can ya fara sunbatanta tun daga gashin kanta har zuwa wuyanta"

Kara karfin kukanta tayi tare dasa hannunta tana cakumo mai gaban riga kamadai me shirin fada"

Tsayawa yayi cak yan kallonta zuwa can ya rike hannunta muryan shi can kasa yace husna menene haka?

abin kuma fada ne?

Tsayawa tayi cak tana sauraran muryan shi, jin abin take kamar mafarki Dan haka ta dago kai ta kalleshi, kur sukawa juna, zuwa can ta bude baki cikin kuka tace

Yaya Jamal kai ne???

Nine husna"

Hannun ta kara kaiwa kan kirjin shi tare da fadin, Allah yasa ba gizo idona kemin ba"

Kara shafu gashinta yayi tare da kura mata ido, muyar kasa kasa yace.....

Husna ba gizo idonki ke miki ba nine da kaina"

Kusan minti 5 suna kallon junan su zuwa can ma'u ta cire idonta tare da wasa da yatsanta"

Jamal ko ci gaba yayi da kallonta tundaga fuska har zuwa hannun da take wasa dashi"

Kara jawoyo jiki yayi ya rike hannun"

Cikin sauri tayi yinkurin kwace hannunta tare da matsawa can bakin gadon"

Jamal ma kara jawo jiki yayi ya iso bakin gado yana kokarin mika hannun shi ya kamo na ma'u ta mike da sauri ta fita"

Lebe Jamal ya cija sannan ya fara kwalawa usman kira"

Daman usman naganin wucewan ma'u ya mike tare da bin bayan ta da kallo, acikin zuciyar shi yace munafukar yariya"

Yanajin muyar Jamal ya nufi dakin da sauri"

Samunshi yayi ya dawo bakin gado dan haka yace menene haka Jamal?, yaya akayi ka dawo nan?

Kawar da zancen yayi da fadin wai husna tayi ciwo ne naga duk ta rame?

Bazan usman yayi dashi sannan ya gyara mai kwanciya, juyawa yayi yana fadin duk dai abinda zakayi kayi ahankali, kasan dai abinda likita yace"

Shima share zancen yayi bece komai ba"

Washegari gidan cika yayi da baki, cikin harda abba da mama"

Ma'u kasa hada ido tayi dasu abba wani irin kunya takeji idan ta tuna yadda taita kuka akan Jamal"

Tun daren da Jamal ya dawo deeni ya sani Amman yanata kaucewa haduwa dashi"

Kwanan su Abba 1 suka koma, kuma aranan ne alhaji bashir ya kawo ummi deeni"

Bayan tayiwa momy Allah ya kyauta gaba, suka rankaya harda dakin Jamal"

Jamal naganin ummi gaban sa ya fadi domin bazai taba manta wannan fuskar ba"

Saidai abin da ya basa mamaki menene ya kawota gidan su"

Adaddafe suka gaisa, sannan Jamal ya kureta da ido"

Bayan tafiyanta Jamal
yasa usman
ya kira masa momy"

Zama momy tayi kusa da Jamal sannan tace gani yaya akayi?

Idonshi kur awaje daya yace, momy wannan matar da kuka shigo tare wacece?

Kanta tsaye tace matar babanka ce alhaji bashir, itace babar shamsuddeen"

Shamsuddeeni ? Jamal ya maimaita sannan yayi shiru, zuwa can yace Momy kina nufin itace mahaifiyar shamsuddenin da daddy yake gayamin?

Cikin fara'a momy tace itace, ai shamsuddeenin ma yana nan gidan, kasan wani irine shi shiyasa baku haduba, saidai mutaro mumai addu'a Allah ya shirye shi"

Gaban Jamal sake bugawa yayi, Allah Allah yake Momy ta fita ya kira ma'u dan ita kadai take da amsan tambayen shi"

Ji yayi hankalin shi ya tashi idonshi ya rufe mamaki ne yasa ya rasa mezai yi yaji daddi, gashi babu damar tafiya"

Bayan momy ta fita usman ya dawo tun kafin ya zauna jamal yace....

Usman dan Allah kiramin Husna"

Wani irin kollo usman ya masa sannan yace wannan ne kuma baka isa ba wlh, komenene xanyi maka amman ka daina min zancen asma'u bare ma har kace nakira maka ita"

Shiru yayi zuwa can yace toh bani aron wayarka nakira"

Mikamai yayi sannan ya mike ya fita, yana zaune afalo ma'u tazo tashiga dakin da Jamal yake"

Acikin zuciyar shi

Yace wannan ba girmana bane, ya kamata nabar gidan nan"

Ma'u nashiga Jamal ya mata wani irin kallo, tunda take bata taba ganin ya mata irin kallon ba"

Tsayawa tayi tana kallon shi"

Fuskanshi dauke da bacin rai yace"

Husna ke munafuka ce ko? Dake da deeni kuka kulla wannan munafuncin ko, tayaya za,ace deeni dan uwanane? Sai yanzun nasan kunnen kashi gareki, wato kin kawoshi har cikin gidan ubana kuci amanata?

Tuni ma'u fara kuka tare da fadin yaya Jamal bari kaji, dan Allah ka tsaya kaji"

Be saurareta ba daga murya yake cikin fada yana cewa.....

Husna ni kika munafunta ashe duk kukan da akace kinyi na rashina muna funcin ne? shikenan nagaji da halin ki hakurina ya kare, husna inada tsananin kishi akan abin da nake so, zan hakura dake dan nasan yanzun kinbashi kanki"

Cikin kuka take girgiza kai tare da fadin wlh a'a yaya Jamal ka tsaya kaji, wlh bansan komai ba game da zuwan deeni gidan nan, nikaina dana ganshi nayi mamaki, wlh yaya Jamal ban kulashi ba, kuma babu wani abu daya shiga tsakanina dashi"

Cikin tsawa yace karya ne, karya kikeyi, tun kina gidan iyayenki kikai niyar basa kanki, nasan komai"

Dam taji gabanta ya buga take hawaye suka fara zubowa kamar anbude famfo"
Chapter 36 · 0% Book details