← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 47

Sashe 29

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jamal na fita hawayen da take makalewa suka zubu, tashi tayi ta daga labulen window har ya shiga part din momy tana kallon shi tana hawaye"

Duk da cewa jira take Jamal yabar kasan takira deeni awaya amman yanzun sai taji kwata2 batason tafiyan shi, ko banza yanzun Jamal ya zama dan uwanta batajin kin shi kaman da"

Bayan yayi sallama da iyayen sa aka fitarmai da akwatin shi"

Harya mike Momy tace toh ina asma'u fa, nafisa jeki kirata"

Sai da ta goge fuskanta sosai sannan ta fito, duk afalo ta same su"

Momy da daddy fita sukayi suka tsaya agaban motar suna kallon yadda ake zuba kayan Jamal aciki"

Jamal ma hannu ma'u ya roko suna daf da fita ya lura kuka takeyi, ajikin bango ya mannata sannan ya fara share mata hawaye rungumeta yayi tsam ajikin shi, tare da zura bakin shi cikin nata"

Angama loda kayan Jamal amman har yanzun basu fito ba, dan haka momy ta nufi komawa ta dubo su"

Tana tura kofar tasakai, juyowa naga Momy tayi da sauri har tana tuntube"

Karan kofar ne yasa Jamal ya saki ma'u, cikin sauri ya fito daga falon ya nufi mota yayin da ma'u kebin bayan shi, tana tafiya ahankali tare da kallon kasa"

Tana zuwa gurin da momy take ta tsaya har yanzun idonta na kasa"

Cikin motar ya shiga ya zauna daddy ne zaija motar yayin da Jamal ke zaune agefen sa"

Har daddy ya tada motar Momy ta daga hannu tanawa jamal bye bye, idonta cike da kalla, juyawa tayi takali asma'u hawaye tagani yana malaluwa daga idonta"

Hannun asma'u ta jawo takaita saiti window da Jamal ke zaune"

Ido ya zuba mata sannan ya girgiza mata kai, wani hawayen ne ya sake zubowa wadda ita kanta tarasa na menene"

Hannun shi ya miko ya rike nata sannan yasa dayan hannun ya share mata hawaye, fuskan shi dauke da murmushi"

Daddy ne yayi gyaran murya sannan yace, asma'u koma gida kiji ko"

Ahankali jamal ya saketa tajuya ta nufi gida"

Daddy ne yakalli momy sannan yace toh kema wuce kuje Ku daura wa shamsudeen girki, yan zunan zan dawo"

Karfe 11:30am jirgin su jamal ya lula sararin samaniya"✋🏻

Gidan Alhaji bashir daddy ya nufa"

Aharaban Gidan yaga wani gafjejen saurayi, cikin kananan kaya masu tsadan gasky, takalmin dake kafar sa ma abin kallo ne, yana ganin shi ya shai da shine shamsudeen, idon shi sanyi da bakin Glass kwaftarere"

Alama yamai da hannu yazo cikin sauri ya bude motar ya shiga, har suka kusa gidan deeni be juya ya gaida daddy ba, bare ya gaida shi"

Dan haka daddy jefi jefi yake juyawa ya kalli deeni yayi mormushi"

Shiko deeni yama manta inda yake yayi nesa atunanin asma'u ji yake yanzun Jamal babu abin da zai nuna mishi, ko yaki ko yaso dole ya bashi ma'u, jira yake kawai ya huta yaje nemanta"

Suna isa suka sakko sannan daddy ya rike hannun deeni suka nufi cikin gida"

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


*SADAUKARWA👇🏻*
*AMINCI WRITER'S*👍🏻💋💋

*GAISUWA TA MUSAMMAN GARE KU👇🏻*

*Fadeela Lamido Fans group*
*Bugun Zuciya fans 1 2 & 3*

6⃣7⃣to7⃣0⃣

🤳🏻 Ma'u na kwance dakin nafisa taji uhun nafisan tana murnan ganin shamsudeeni"

Tsaki taja sannan ta dada gyara kwanciyarta dan yau jinta take kamar wata mara lfy, ga waya ahannunta amman ta kasa kiran deeni"

Momy ko tunda taga shamsudeen ya shiga ranta, sai dai ta kula akwai karancin tarbiya atare dashi, dan tunda ya shigo babu wadda ya gaida, kujera ya samu ya daura kafa daya kan daya"

Nafisa ko kur tamai da ido, hakanan taji yana birgeta"

Bayan sun hallara akan tebirin cin abici suna tsaka da cin abincin, daddy ya kalli deeni yace" shamsudeen baka iya gaisuwa bane?

'Dagowa yayi ya kalli daddy sanna ya maida kansa kasa yace"

Sassanun ku, ya gari yajin dadi?

Mormushi daddy yayi tare da bin deeni da kallo, zuwa can yace"

Shamsudeeni haka ake gaisuwa? Karna karajin kayi irin wannan gaisuwan bata mutanen kirki bace kaji ko?, yana da kyau idan ka samu dan uwanka musulmi kamai sallama, sannan ka gaida shi inakwana ina gajiya"

Ahankali deeni yace toh"

Daddy yaci gaba da cewa kuma irin wannan kayan dake jikin ka karka kara saka su, gobe zan baka kudi ka shiga kasuwa ka samo kaya na mutunci, gashi jamaludeen baya gari da kunje tare amman ba komai saina hadaka da drive"

Tsagal nafisa tace daddy zan rakashi"

Wani harara deeni ya waigo ya zafga mata, wadda saida yasa nafisa ta dukar dakai"

Shiko daddy fadi yake yauwa ga kanwar ka nan zata raka ka"

Bayan sun kammala ne, momy tasa Nafisa ta nunawa deeni dakin da zai zauna, tana gaba deeni nabinta abaya"

Koda suka shiga dakin wuceta yayi tare da fadin fice kiban guri shegiya munafuka"

Da mamaki ta kalleshi sannan ta juya ta fice guiwanta babu kwari"

Itako ma'u duk abinda ake tanaji, jin muryan bakon take kamar na deeni dan haka taji tunanin shi ya bijiru mata kewanshi ya dameta"

Tashi tayi ta zauna sannan tace afili Allah meyasa ka dauramin son abin da bazan samu ba, ina tsananin son deeni, inason nayi rayuwata dashi, nakuma kare dashi, bana gajiya da kallon sa, bana gajiya da sauraron muryan Sa, hawaye ne sosai yake zubowa a idon ta"

Nafisa ce ta shigo da gudu ta fada gado, tare da fashewa da kuka"

Hannu ma'u tasa ta goge hawayen dake fuskanta sannan ta juya ta kalli nafisa tace"

Nafisa menene?

Kaman jira take ta juyo ta kalli ma,u tace"

Anty Asma'u kina ganin waccan bakon daga zuwan shi ya fara duramin zagi"

Zagi? Kuma kika tsaya kina kallon shi?

Toh yazanyi babba ne fah"

Tabe baki ma'u tayi sannan tace hakane fah babu inda zakiyi nima da haka yaya Jamal yamin idan yaje gidan mu har bulala yake sawa ya dakeni"

Da gaske? Nafisa ta tambaya"

Kai ma'u ta gyada mata kawai domin kiran sunan jamal yasa tunanin sa ya dawo mata"

Har dare ma'u ta kasa kiran deeni, ga waya ahannunta amman zuciyarta babu sukuni, tunin jamal kawai take, lallai mutum rahama ne, Ashe ko gilmawan shi ma arziki ne"

Haka ta kwana da tunanin mutun 2 azuciyarta deeni da Jamal"

Washegari ma kasa kiran deenin tayi, ta rasa menene dalili, gashi dai azuciyarta tana masifan son jin muryan sa kuma tanason tasa wani hali yake ciki"

Tana daga cikin Daki taji fitan nafisa da bakon su, dan haka ta mike ta fito falo"

Kallon ta Momy tayi sannan tayi murmushi kadan tace"

Ai na dauka bacci kike, yanzun su nafisa suka fita, dakin bisu kema kiga gari"

Yake tayi kadan sannan ta dukar da kanta kasa"

Ganin haka yasa momy ta sake cewa ko Jamal yace karkije ko ina ne?

Kai ta girgiza tare da fadin a'a"

Shiru sukayi na d'an wani lokaci zuwa can, momy ta sake cewa"

Kunyi waya da jamal kuwa?

A'a ta fada tare da dago kai ta kalli momy, tambayan ta take son yi ita ya kirata ne, amman ta kasa"

Jugum sukayi kowanne da tunanin sa, Nafisa ce ta katsa musu tunanin da tashigo cikin kuka"

Jikin momy ta fada tare da fasa wani sabon kuka, arude momy ke tambayanta lfy ?

Cikin kuka tace yaya shamsudeen ne yaita zagina ahanya sannan yacewa drive ya tsaya na sauka"

Tabe baki momy tayi sannan tace toh yanzun ina samsudeen din?

Saukeni sukayi suka wuce, da kafa na dawo, kuma saida ya bari anyi nisa"

Hararanta momy tayi tare da fadi, maganin Ki kenan, daga ganin mutum sai shigemai kike, yanzun ai kya kiyaye shi"

***

Kwanan deeni uku agidan suka tafi kano shida alhaji bashir domin dauko ummi"

Bayan sun iso sun sameta jiki ya dada rikecewa, ko hutawa basuyi ba suka nufi asibiti da ita, kwananta uku sa samu sauki dan haka suka koma gida"

Washegari Alhaji bashir yace ta hada kayanta dan tafiya zasuyi da ita amman tace sam bazata ba, dagewa yayi itama ta dage, dole ya hakura, juyawa yayi yacewa deeni tashi mutafi"

Nan fah hankalin alhaji bashir ya Kara tashi domin cewa deeni yayi jeka kawai ina gurin ummina"

Shiru Alhaji bashir yayi zuwa can alhaji bashir ya kalli deeni tare da fadin bamu guri muyi mgn"

Mikewa yayi yana waiwayen ummi sa"

Ya kwashe kusan minti 30 sannan yaji Alhaji bashir ya kirashi"

Yi alwala muje masallaci, alhaji bashir ya fada tare da kwance agogon hannun shi"

Bata rai deeni yayi sannan yace"

Nifah banazuwa masallaci ad'aki nakeyin kayana, dan 'yan unguwar nan gaba dayan su munafukai ne"

Daker suka shawo kanshi ya yadda zashi masallaci, bayan ankidar ne yaji ance kowa ya zauna akwai daurin aure"

Mamaki ne ya kamashi lokacin dayaji ana daura auren ummin sa da alhaji bashir, ji yayi kaman acire masa wani gungumemen dutse ajikin sa"

Suna komawa gidan ummi suka hau shiri, duk da cewa alhaji bashir yace karsu dauki komai amman deeni saida ya kwashe wukaken shi tas"

Cikin takaice tare da dana sani alhaji bashir ya kalli deeni sannan yace"

Me kuma zakayi da wukake haka, bafa nason wannan dabi'ar yanzun ba da bane"

Ummi ce tace auta kabarsu anan karka tafi dashi"

A'a ummi akwai abin da zanyi dashi ummi, kisan zama be ganni ba, bazan barwa Jamal asma'u ba, dole zan nemesa duk inda yake, yabani kayata, wlh wlh ummi matsawar inna nunfashi bazan barwa Jamal asma'u ba' daga
ranan da nasamu nasara asma'u ta dawo gareni zan aje makami na"

Sakatoto Alhaji Bashir yayi da baki yana kallon deeni zuwa can yace"

Saratu wacece Asma'u?

Ahankali ummi ta warwarewa masa komai"

Shiru yayi na wasu lokaci zuwa can ya dafa deeni tare da fadin"

Ka kwantar da hankalin ka, indai kudi na magani zaka Aure asma'u ka neme shi, ko nawa yake so zan bashi, bukatata kawai ya saketa"

Take wani dadi ya ziyarci zuciyan deeni, bakin abban sa dayake gani ya goge tas"

Karfe goma da rabi na dare suka isa Abuja, saida suka sauke deeni agidan daddy sannan suka wuce giida"

Tunda deeni ya dawo kullum saiya fita neman ma'u, yayi dakon jiran kiranta harya gaji"
Chapter 29 · 0% Book details