← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 47

Sashe 46

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mamaki Jamal yace momy waya gaya miki?

Uwarka ce, akace maka bansani bane?, ai ina lissafi, ko ta haihu ne ma?

Sosa keya yayi tare da fadin a'a munan isowa yau"

Yauwa Jamal Allah ya maku albarka dan Allah kutaho da wuri"

Toh momy amman kafin mu tahu inason zan shiga kasuwa"

Me zaka saya indai kayan haihuwa ne nariga dana hada komai"

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


*Sadaukarwa ga duk me karata BUGUN ZUCIYA, nagode da irin soyayyar da kuka nuna min tare da wannan lbr BUGUN HEAT, Allah yabar kyauna💋*

*Sakon gaisuwa da fatan alheri ga marubutan mu, wad'an da suka karamin karfin guiwa wajen rubuta wannan lbr, bani da bakin mgn, hakika kun nunamin kyauna, sai dai nace Allah yabar xumunci🙏🏻*

1⃣0⃣5⃣

✋🏻✋🏻✍🏻 Karfe 3:15pm suka shiga gidan momy murna momy take sosai tana rike da hannun ma'u tare da tsareta da ido, nandan lbrin dawowan su ya zaga ko ina, tsilum saika Nafisa aguje ta shigo da cikinta daya fara tasowa manne ajikinta"

Jikin ma'u taso fadawa, momy ta tareta tare da fadin nafisa lfyr ki lau kuwa? Kewai bakijin nauyin jikin ki ?

Komawa tayi kusa da ma'u ta xauna, sannan ta shiga gaida Jamal wani irin amsawa ya mata batare daya kalleta ba,

'Daga ma'u nafisa tayi sannan ta suka nufi daki, kallon nafisa ma'u take tana mamaki wai yanzun cikin deeni ne jikin nafisa?, Ikon Allah kenan"

Hira suka barke dashi daga falo su momy sunajin dariyar su"

Sai dare deeni yazo daukan nafisa be shigo ba, waya ya mata tafito sutafi sannan tace yana gaida momy"

Daddare momy so tayi ma'u ta kwana gurinta amman taga Jamal sai zarya yake yafita yadawo dan haka tace tashi su tafi"

Dukda kwaciya kawai zasuyi tare yafison haka akan ace sunyi nesa da juna,

Washegari da safe sukaje gaida daddy abinda ya bawa Jamal mamaki daddy be nunafushi ba, sosai farin ciki ya bayyana afuskar shi, koda zasu tashi yaga ma'u na kici kicin tashi, cikin fada daddy yace haba Jamal taimaka mata mana, kunya ce ta kamashi daker ya iya mika hannu ya dagata Albarka daddy yaita samusu tare da addu'ar Allah ya sauketa lfy"

Adaren ranan ciwon nakuda ya tayarwa ma'u tunda momy taga inda take cije baki ta kira jamal, daki ta shiga ta dauko kayan haihuwa tace asibiti zamu"

Karfe 10:39pm ma'u ta haifo zarkada zarkadan 'ya'yanta guda biyu dukkan su maza ne masu kama da Jamal"

Bakaramin maki Jamal yayi ba, tunda suke zuwa asbiti babu wadda yataba cewa yan biyune acikin husnan shi"

Momy ko farin ciki ya hata mgn, adaren suka dawo gida domin ma'u lafiya lau take"

Tun asuba momy ta fara gayawa yan uwa da abokan arziki dan haka tunda safe gidan ya fara cika da baki"

Nafisa ma murna ba'a magana tare da deeni sukazo fuskanshi dauke da murmushi nafisace ta kwaso yaran ta mika mishi kallon yaran yayi gwanin ban sha'awa nan danan idonshi yacika da kwallah yasa hannu ya share tare da fadin nafisa yaran nan sun bani sha'wa inason yara sosai sunbatan yaran yayi tare da fadin Allah yayi muku albarka ya karawa mahaifiyar ku lafy shekara me zuwa ta sake haifo mana kalan ku, yakuma bawa mahaifin ku abinda zai ciyar daku"

Amsawa nafisa tayi da ameen, sannan tace ka manta addu'a daya da bakiyi ba"

Dagowa yayi
ya kalleta, idontshi da ragowan hawaye ga kuma murmushi akan bakin shi yace....

Wacce kenan?

Cikin murmushi tace......

Bakace muma Allah ya bamu irinsu ba"

Murmushi yayi tare da cewa a'a nafisa muruke me albarka kawai, ko mace kona miji ke duk abinda Allah yabani zan karba nayi godiya lokuta da dama abinda mukeso ba alheri bane agare mu"

Dahaka ya mikawa nafisa yaran sanan yace ta gaida asma'u"

Aranan momyn usman ta iso tare da dada"

Tunkafin ta shiga gidan take fadin you alkawari ya cika gani agidan takwara"

Koda suka shiga dakin ma'u daure fuska tayi, tare da kyauda kai, itama dada daure fuska tayi tare da fadin nima ba gurinki nazo ba"

Aranar da daddare hajiya asabe tazo ganin jarirai, farin ciki sosai ta nuna"

Acikin zuciyan Momy tace inma bakin ciki kike ke kika sani, ni baki gabana mantawa ma nake inada kishiya idan yana gidan ki gani nake kamar tafiya yayi"

Awaya deeni ya kira Jamal yamai barka, ana gobe suna ya dauki nafisa suka shiga kasuwa kayan yara yaita kwasa kala kala tare da kayan wasa kai harda keke komai iri daya ne kuma bibbiyu, mota sukaita lodawa, Wata sarka nafisa tagani tace ka saiwa asma'u"

Wani kallo ya watsamata tare da fadin awani dalilin zan saimata ?, kinason mijinta yakaini kutu ko?

Turo baki tayi sannan tace wato ka maida yaya mafadaci ko?

A'a nafisa aiko nine sai inda karfina ya kare"

Washegari akwai suna, anci ansha jama'a ba masaka tsinke da sunan su aka barsu *Hassan da Hussain* aciki waddan da sukazo suna harda zainab kawar ma'u"

Lokacin da yan waliman Jamal suka cika gidan da hayani ma'u ta jawo zainab bakin window da hannu ta mata nuni da deeni"

Tabassa deeni yayi kyau babu wadda zaice yayi rin
rayuwar da yayi abaya, Saika ma zaci yafi su Jamal roko da addini domin su dikine na zamani sanye ajikin su, yayin da deeni yake cikin jallabiya fara karrr hannun sa rike da carbi, gefenshi Faisal ne zaune"

Washegshegari duk yan suna suka watse, sai dada kadai ta rage"

Kulum abba ke kiran dada awaya tare da tambayan jikokin shi, wata rana abba ya kira dada suna cikin mgn ma'u ta kwace wayar tasa akunne tare da fadin abba kulum ni baka tambayata"

Dariya yayi sannan yace......
Asma'u ai muna waya da mijin Ki, nasan lfy lau kike, ya mutanen gidan naku?

Lfy lau"

Toh madallah, Allah ya miki albarka, yadda kika min biyya kema Allah yaba ki masu miki, akullum ina miki addu,a zama lfy tare kwanciyar hankali"

Ameen abba, idon ma'u cika yayi da kwallah, sallama sukayi da abba, hawaye kawai ma'u taji suna Zubo mata daman haka iyaye sukeji idan dan su yai masu biyyaya, lallai naso nayi kuskuren nabi son zuciyata, kome nayiwa iyya na bazan biyasu ba, addu'a ta shiga ma iyayenta Allah ya saka musu da alheri"

Haka dada taciga da kula da yaran ma'u Hassan da Hussain har sukayi arba'in aranan Jamal yakaisu Kano, bayan sati 2 ya koma ya dauko su"

Bayan wata 5

Nafisa ta haifi katon danta, murna gurin deeni ba'a mgn, ya dade rungume da yaron, yana kwalla tare da tufa mishi addu'oi"

Ma'u ma bakinta ya kasa rufuwa, shiryawa sukayi ita da momy zasu tafi, momy na rike da hassan, hussaini a hannun ma'u har sun fito harabar gidan, motan Jamal ya shigo"

Tunkafin ya fito ya daure fuska"

Ma'u ko fara'a take tare da zumudin fadamai nafisa ta haihu"

Cikin basarwa yace naji ai, ina zaki?

Sanyi jikin ma'u yayi, tare da rasa abincewa"

Momy ce ta kalleshi tace.....

Zamuje gano jariri ne"

Da sauri yace amman bada Husna ba"

Daure fuska Momy tayi tare da fadin da Husna kuwa, Jamal wai me kake nufi ne?, kiri kiri ka hana Asma'u zuwa gidan Nafisa, bata taba zuwaba, watanta 6 da haihuwa amman ka hanasu suyi zumunci, wanne irin bakin kishine wannan?

Shiru Jamal yayi tare dasa idon shi akasa"

Cigaba momy tayi da cewa toh abin ya fara damun nafisa, dan harta fara korafi akai, abinda kake nufi baxai yuwuba gara ka canza tunani, jayawa tayi ta kalli asma'u tace wace mutafi"

Acike suka samu falon, ummi na zaune rungume da d'an deeni ahannunta, bayan gaishe gaishe ma'u ta amsa yaron, dakin nafisa ta nufa, tana kokarin shiga dakin sukai karo da deeni yana fitowa"

Cikin sauri ya matsa gefe tare da fadin Ya subuhananlah"

Dago ido ma'u tayi ta kalkeshi, shima idosa nakanta"

Tafiya ta fara tare da gaidashi bayan ya amsa tamai barka sannan ta shiga dakin jikinta asanyaye"

Saida yamma suka koma gida tundaga ranan Jamal be sake barin ma'u tajeba, har ana gobe suna"

Ran momy ya baci sosai dan haka dayazo sallama zai tafi aiki ta rufeshi da fada"

Fadan momy yasa hankalin jamal ya tashi har ya yanke shawaran zuwa ya gano nafisa tare da jaririn da ta haifa"

***

Yana shiga gidan deeni na kokarin fita amman ganin jamal yasa yai saurin fitowa"

Hannu ya bashi suka gaisa fuskan deeni asake yayin da ta jamal take daure"

Har dakin baccin nafisa ya kai Jamal sannan ya juya ya fita"

Bayan sun gaisa ya rungume jaririn ya koma gefe"

Gunshekan kukan nafisa yaji, cikin sauri ya daga kai ya kalleta, sannan yace.....

Ya da kuka kuma?

Yaya Anty asma'u fah bata taba zuwa ba, gashi yanzun ma tunda tazo so daya bata sake zuwa ba"

Shiru yayi yana kallon yadda take share hawaye, zuwa can yace.....

Au saboda haka kike kuka, lallai shagwaba ta miki yawa dallah zoki amsa yaron Ki"

Juyawayi yai ficewan shi"

Daddare nafisa na zaune taji muryan asma'u kasa jira tayi ta shigo"

Cikin fara suka kalli juna sannan nafisa ta karbi yan biyu ahannun ma'u

Bayan sun zauna nafisa take tambayanta halan keda momy?

A'a yaya ne ya saukeni wlh abin yaban mamaki ina zaune yace wai nashirya yakaini Gidan Ki na kwana tunda gobe suna, wlh na dauka sunan ma bazai barni zuwa ba"

Wani farin ciki ne ya kama nafisa, mara misalantuwa"

Washegari yaro yaci suna Mashkur, aranan sunan Faisal yazo, walima sosai deeni yayi"

Washegarin sunan ne daddy ya hada Jamal da deeni, fada ya musu sosai tare da nasiha me shiga ciki, bayan ya gama ne yayiwa deeni albishirin ya budemai manyan rumfuna dazai yi kasunci aciki"

Godiya yayi sosai, nan danan deeni ya zama shararran dan kasuwa"

Tare da faisal suke gudanar da komai cikin Ikon Allah kasuwa saikara burun kasa take"

****

Jamal da deeni zuwan su baguma 3 tare dakai musu niki2 abun arziki"

Yan biyu nada shekara daya ma'u ta sake samun ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji wadda aka sawa Aliyu, sosai yan biyu sukayi wayau tafiya suke gwanin sha'awa"
Chapter 46 · 0% Book details