← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 47

Sashe 12

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta gani zaune ita da wata mata sai kuka take matan na lallashin ta"

Arude tace ummi lafiya ?

Ummi tana kuka tace Asma'u ankama auta, suntafi dashi"

Ankama deeni ? Ummi waye ya kamashi? kuma me yayi?

Share hawaye ummi tayi sannan tace"

Asma,u bansan me yayi musu ba, muna cikin bacci mukaji sojoji cike da gida, kafin infito ma sunsa deeni amota, wasun su suna kaimai duka"

Tsugunawa ma'u tayi ta fara kuka saida tayi me isarta sannan tace ummi babu wadda yabi bayan su?

Sojuji ne fa asmau, kisan ba hankali suka cika ba kuma da alama badaga nan garin suke ba"

Zama tayi dirshen taita kuka ranan bata iya zuwa makaranta ba, tana ganin lokacin tashi yayi ta wuce gida tana tafe tana kuka,

Akofar gida sukaci karo da abba kallonta yayi yaga idonta jawur yace lfy?

Abba cikina ne yake min ciwo"

Cikin tausayawa Abba yace toh sannu maza ki shiga gida"

Kaitsaye dakin mama ta shiga domin yau ta rasa inda zata tsoma ranta jikin mama ta fada sannan ta saki kuka meban tausayi"

Jikin mama sanyi yayi dan bata taba ganin ma'u nayin irin wannan kukan ba, cike da damuwa tace asmau daina kuka ki gayamin me yayi zafi ?

Cikin muryan kukan tace mama bani da lfy"

Jawota mama tayi ta rungume dan yanayinta ya fara bawa mama tsoro, tana kwance ajikin ta tace menene yake miki ciwo?

Bansani ba mama, wlh bansan abinda ke min ciwo ba"

Shiru mama tayi tana kallon ma'u zuwa can tace"

Asma'u idan akwai abinda ke damun ki kifada karkice zaki boye mana damuwar ki"

Shiru tayi bata sake cewa komai ba tai kwance jikin mama jefi2 kana jin ajiyan zuciyarta"

Ganin ta samu natsuwa yasa mama ta kalleta sannan ta jawo Wata leda akusa da ita ta daura mata ajiki"

Duk da tana cikin damuwa da zumudin ta ta fara bude ledan, da kwalin waya ta faracin karo, jikinta babu kwari ta bude kwalin sannan ta ciro wayar, waya ce lafiyayya dadi taji sosai ajiye wayan tayi ta kara leka ledan takalma ne kafa 3 masu kyan gaske tare da turare masu tsada"

Kallon mama tayi tace mama wannan kayan fah ?

Naki ne yayanki ne ya kawo miki, yace agaidaki sauri yake aiki ne yakawoshi

Yayana ? Mama wanene yaya na?

鈥�

💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*

Na sadaukar da wannan shafin ga masoya *BUGUN ZUCIYA* aduk inda suke 👌🏻💝😘

2⃣8⃣ to 3⃣0⃣

🏀 Yayan ki *Jamal*

Mikewa ma'u tayi da sauri sannan tayi jifa da ledan " bantawa tayi tacire wayar acikin kwali dan haka ta dauki kwalin ta buga da kasa" sai lokacin ta kula dan haka ta dauki wayar ta makawa bango"

Ji kake tassss"

Da gudu ta fita ta nufi dakinta ta fada gado tare da saka sabon kuka"

Wato Jamal ne yaje har gida ya kama deeni ? Ko tantama batayi Jamal ne wani sabon tsanan shi taji axuciyarta ji take kamar ta kashe shi"

Tashi tayi ta zauna yanzun meye abinyi ?

Yaya zanyi inkubutar da deeni daga hannun Jamal

Mama ko mamakin hali irin na ma'u tayi sannan ta juya ta kalli bannan da tayi ta girgiza kai, cike da takaici ta fita adakin"

Da misalin karfe biyu da rabi ma'u ta fito cikin shirin tafiya mkrnt yamma, kallonta mama tayi taga idonta duk sun kumbura cikin idonta jawur sun kankance, da alamar ma ko cire kayan makaratar batayi ba tunsafe, dauke idol tayi akanta domin al'amarinta ya fara bawa mama haushi"

Saida ta turu baki tace natafi"

Ko kallonta mama batayi ba tace adawo lfy"

Kaitsaye gidan su deeni ta shiga, ummi nazaune ta tasa abinci agaba ta kasa ci"

Gabata ma'u ta zauna ta bude sabon kuka, hankalin ummi kara tashi yayi, rufe abincin tayi sannan tace ki daina kuka Asma'u bakiga inda fuskan ki ta kunbure ba, mutaru miyi hakuri inada tabbacin auta na zai dawo gida domin nasan shiba rago bane, wannan tashin hakalin da kika ganni ci narashin tabbacin inda yake ne da rashin sanin halin dayake ciki amman da yardan Allah auta zai dawo"

Dahaka ummi ta samu ta shawo kan ma'u, ta wuce makaranta"

Da daddare Asma'u na kwance afalo tana cigaba da tunanin deeni badan tana tunanin kar asirinta ya tonu ba data ansa no Jamal agun yaya usman ta bashi hakuri ya sakar mata deeni"

Tana cikin wannan tunanin taji sallaman yaya usman rufe ido tayi kaman me bacci, Allah2 take ya wuce amman saitaji ya zauna akujeran dake kallon nata"

Zuwacan mama ta fito tana fadin ka iso?

Eh naje gidan momy yanzun tacemin kina nema"

Zama tayi sannan tace eh Daman Asma'u ce gatanan narasa gane mata, kwashe duk yadda akayi tayi ta gaya masa"

Sannan ta nuna masa yadda tayiwa wayar da Jamal ya kawo mata"

Cike da baccin rai yace mama bawani abinda yake damunta banda iskanci da sangarta, bataga ba,a dukanta ba kuma ai ba wuce dukan tayi ba, dan ubanta Jamal din sa'anta ne

Usman na tsaka da fada Abba ya shigo, daga mama har usman sannu suke mai" amman abban yaki amsawa fadin yake ina Asma'u

Toh fah mama ta fada azuciyarta domin indai taji alhaji ya kira ma'u da sunan ta toh akwai mgn"

Itako ma,u tanaji Abba ya kira sunanta ta bude ido tare da sakkowa akan kujeran azuciyarta tace shikenan dada ta fadawa abba"

Kusa da ita abba ya zauna sannan ya rike hannunta guda daya"

Jikinta gaba daya rawa yakeyi"

Abba ko ido ya kureta dashi zuwa can yace, yau naje gidan malam idris na tuntubeshi game dake, ya nunamin komai lfy kuma kina karatu sosai yadda ya kamata, amman abinda ya bani mama cewa da yayi wai baki zuwa makaranta akan lokaci, bayan nikuma nasan kina fita gida da wuri"

Shiru Abba yayi yana jiran yaji me zata ce"

Jita shiru yasa yace badake nake mgn ba"

Kanta akasa tace Abba wlh ni babu inda nake zuwa"

Amman kinsan malam idris bazaimin karya ba ko?

Nasani abba, amman ni daga nafita wlh tallahi banazuwa ko ina sai makaranta, sai dai idan kafin naje lokaci yake kure ....

Cikin ido abba ya kalleta sannan yace bari rantsuwa, ai bacewa nayi ki rantse ba, bakomai daga yau drive zai dinga kaiki makaranta, idan lokacin tashi yayi zai dawa ya daukeki, haka yayi ko ?

Daga kai tayi badan ranta yaso ba"

Juyawa abba yayi ya kalli usman sannan yace kaikuma me kazoyi da daddaren nan ?

Cikin natsuwa ya fara fada mishi komai kamar yadda mama tafada mai, sannan ya kara da cewa abba ya kamata adauki mataki akanta be kamata azuba mata ido tanayin abinda taga dama ba"

Shiru falon yayi zuwa can abba ya nisa sannan yace...

Ke !! Asma'u wani abu na damun ki ne?

Cikin sauri ta girgiza kai tare da fadin a'a"

Akwai wani abunda kikeson ne ko kike son a saya miki ?

Nan ma a,a ta sake cewa"

Shiru abba yayi sannan yace....

Ninasan abinda ke damun ki, Aure ne baki so, kuma bazai yiyoba, tun ranan dana miki mgnr aure kika fara koke2 ita kuma dada ta biye miki har tana taya Ki, bazan kara kaiki gidan ba bare ki kara sata kuka"

Juyawa yayi ya kalli mama sannan yace wlh tun ranan danakaita gidan, dada na nan babu lfy, yanzun jiya nakaita asibiti sunce jininta ya fara hawa"

Juyawa yayi ya kara kallon asma,u sannan yace ki shirya gobe zakiyi bako, ni ba nufina namiki auren dule ba, a'a zaizo ne ya ganki, kema ki ganshi, idan kun daidaita shikenan, idan kuma baku daidaita ba zan sake turo wani, bana bukatar kice wai saikinsa halinshi, duk wandan
kikaga na turo miki na yadda da inganshi tare da mutuncin iyayen sa, dan haka kwana 2 kawai na baku, ganin inda tayi shiru yasa abba fadin kinajina ko ?

Kai kawai ta iya dagawa sannan tasa hannunta ta share hawaye"

Tattaunawa suka fara tsakanin mama da abba tare da yaya usman, haka ne yabata daman tashi tabar musu falon"

****

Washegari ma'u ta tashi da matsanan cin ciwon kai, saka makon rashin baccin da batasamu, taso taki zuwa mkrnt amman kuma tanason taga halin da ummi take ciki, dan haka ta mike tahau shiri"

Drive ne ya kaita har bakin mkrntr sannan ya juya, dan kaka bata samu daman zuwa gidan su deeni ba saida aka tashi break"

Xama sukayi jugum ita da ummi kamar masu zaman makoki"

Bayan antashi makaranta abba da kanshi yazo ya dauketa"

Koda ta shiga gida a kitchen ta samu mama tanata soye2 sai alokacin ta tona da bakon da abba yace zaizo"

Yatsuna baki tayi sannan ta juya ta shige daki, wanka tayi tai sallah sannan ta tsaya tai addu'a sosai Allah ya kubutar da deeni daga hannun Jamal"

Tana zaune kan sallayan mama tashigo tana fadin Asma'u maza ki fito bakonki ya iso"

Gabanta taji ya fadi, kanta ta daga ta kalli mama sannan tace...
Mama dan Allah kice bacci nake, nifa bansan mezance mai ba"

Shiru mamatayi zuwa can tace, kinga, Asma'u banason shirme maza ki fito ko na kira abbanki na gayamai"

Cikin sauri ta mike tana matso hawaye ta nufi hanyan kofa"

Ke !! Zonan mama ta fada tana kare mata kallo"

Bayan ta juyo tace nufinki ahaka zaki tafi fuska saikace tsowar me takaba"

Bakinta agaba tace to ai yanzun nan fah nayi wanka"

Mama batace komai ba ta juya ta fara ciro mata kaya, mika mata tayi ta Saka sannan ta zaunar da ita dakanta ta mata kwalliya bawata me hayaniya ba"

Madaidaicin gyale ta mika mata dasukai matukar dacewa da kayan datasa, kallo ta kare mata sannan tace toh maza ga kayan motsa baki can na hada ki dauka ki tafi dashi"

Jikinta babu kwari ta nufa kitchen tare da nazarin abinda zata ma bakon ta kuntuka mishi haushi"
Chapter 12 · 0% Book details