← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 47

Sashe 24

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haba tayaya zan kwana afalo bayan tunda uwata ta haifeni bantaba kwana afalo ba, wannan wanni irin wulakacin ne zaice wani wai na kwana afalo, aiko bako ne yazo aka barshi, ya kwana afalo an wulakanta shi"

Tunanin da taitayi kenan har gurin 12 tana xaune, zuwa can ta mike ta nufi bishi, dan ita bazata iya bacci afalo ba, kofar da taga yabi, ta tura, kofufi guda uku ta gani ajere, na farkon ta tura"

Daki ne lafiyayya babu Kowa aciki, yana zuba uban kamshi"

Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta shiga, nan taga jirin akwatunan ta dasuka taho dasu dazon, watoh jamal saboda tsabar mugunta ya barni na kwana afalo, dayake beda imani ko tausayi na, bayaji"

Washegari da safe ta fitoh da nufin zuwa part din momy"

Ta kusa isa ta hango megadin gidan yana zaune da redio sa ahannu, azuciyarta tace"

Barinje in tambaye shi, wacce unguwa muke, karasawa tayi tanayi tana wai wayen bayanta"

Takusa isa taji muryan jamal, Ke Husna"

Afirgice ta waigo tana kallon shi"

Ina zaki ?

Dawowa tayi da baya tana kokarin shga part din Momy, amman saitaji jamal yace karki shiga, wa kika tambaya kafin kiki fito?

Ahankali ta dawo baya, tana zuwa daidai gurin shi, yasa hannu ya matse kunneta tare da fadin, ke wai wacce irin yariya ce? me kikaje yi kuma gurin me gadi? sai kace wata ballah gaza"

Zafin da taji shi yasata ta fitar da Wata yar kara, tare da kama hannun nashi tana kokarin cirewa akunneta"

Yarrrr yaji ajikin shi, sanadiyan kama mai hannu da tayi, nan danan jikin shi ya mace, daker ya iya bude baki yace"

Kina ganin kaman zaki iya kwatan kanki ahannu nane?, ko wannan dan iskan saurayin naki idan na rikeshi bazai iya kwatan kashi ahannuna ba, bare ke, kuma bazan sake ki ba harsai kin gaya min me kikaje yi agurin"

Saboda tsananin azaban da take ji batasan sanda tace, rake fah nake son sha, shine naje na bashi ya sayo min"

Tirrrrr, rake? natsani naga mace nashan rake, amman nasan..... Kome ya tuna kuma sai yayi mormushi sannan yace, ina kudin ?

Tsuro tsuro tayi ganin haka ya sake yin murmushi, sannan ya saki kunnen ta yace"

OK, rake zakisha ko? barin naje na nemo miki"

Juyawa yayi ya fita, zuwa can ya dawo ya mika mata ledan hannun shi, tare da fadin daga yanzun duk abin da kike so, kimin mgn zan kawo miki"

Gefe ya koma ya zauna, duk da cewa bawai son raken take ba, amman da ta tuna yace beson yaga mace nashan rake, yasa ta dauko ta fara sha"

Shiko jamal yadda ta daddage take shan raken abin yaso bashi dariya, hakanan yaji tana burge shi"

Tas ta shanye raken, sannan ta mike tana kwashe bawon"

Cikin shi cike da dariya yake satan kallonta, harta shige daki yana bin bayanta da kallo"

11:41pm Jamal kwace akan gado, bacci yaki zuwa duk inda ya juya Husna yake gani lokacin da take shan rake, dariya yayi kadan, sannan ya dada gyara kwanciyan shi, ji yayi kaman gadon yamai fadi dan haka ya jawo folo ya rungu me

Itako ma'u ganin Jamal be nuna fushin shi ba, yasa ta daukan alkawarin sashi yin fushi, dan haka ta tashi ta nufi dakin jamal"

Kayan bacci ne ajikinta dan haka ta dauki hijjabi ta daura kai"

Ahakali take buga kofan"

Waye ? taji ya fada"

Murya kasa kasa tace nice"

Saukowa ya fara yi, tare da fadin menene ?

Daidai lokacin daya bude kofar ya kura mata ido"

Turu baki tayi kadan tare dayin kwalkwal da ido, sannan tace"

Rake zan sha"

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[22:19, 12/15/2017] ‪+234 813 272 6929‬: 💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


5⃣1⃣to5⃣3⃣

Rake ? Banda wadda kikasha d'azon?

Kai ta daga tare da sunkuyar da kanta kasa"

Kallonta yayi daga sama har kasa sannan yace"

Da tsakar daren nan ne zakice min zaki sha rake, banson iskancin banza fah"

Duk da cewa yadda yayi mgnr ya firgitata amman saita dake ta turo baki, cikin shagwaba tace toh ai kaine kace duk abin da nake so nagaya maka"

Yana binta da idon yace, dan nace miki haka kuma sai kizo ki hanani bacci, da daddren nan, ina zan samo rake yanzun"

Hawaye ta matso ya zobo akan kuma tunta"

Ganin haka jamal ya fara fadin kin fara ko?, to yanzun me kike nufi?

kukanta kawai take yi, batare da ta sake kallon sa ba, zuwa can yace"

Duba, husna yi hakuri kije ki kwanta, gobe da safe zanje in nemo miki, kinji"

Wani haushi ne ya kamata, dan ba haka ranta yaso ba, dan haka taki wucewa"

Kallonta kawai yake yana rike da kofar, yana karewa santalin kafa fuwanta kallo, dan rigar bata kai mata kasa ba, zuwa can yayi ajiyan zuciya sannan yace"

Kisan Allah, idan baki wuce ba ranki zai bacci, karki nemi ki raina ni, idan baki hankali ba cikin daren nan saina tayar miki da jiki, karki wuce kiban guri ki gani, kofar ya maida ya rufe sannan ya koma gado ya kwanta"

Itama ma'u karamin tsaki taja tare da fadin maye kawai, juyawa tayi ta shige daki zuciyarta cike da haushin shi"

Hijjabinta ta cire sannan ta haye gado, karaman jakanta ta rarumo ta rungume babu dadewa bacci ya dauketa"

Shiko Jamal bacci gagaran shi yayi, ji yake da akwai inda zaisamo ya bata adaren daya je, ko dan ta daina kukan"

Kasa hakuri yayi dan haka wata zuciyan tace je ka duba mana ko tayi shiru"

Tashi yayi ya nufi dakin ma'u ahankali ya tura kofar, hangota yayi tayi daidai agado tana bacci, haka ne ya bashi daman karasawa ciki"

Ahakali yake tafiya dan beson tasan da shigowan shi"

Tsaye yayi akanta yana karewa ahalitta ta kallo, karo na farko a rayuwan shi dayaji yana son ya kai hannushi jikin mace, saidai bazaitaba bari hankan ta kasance ba"

Ganin kanta babu dan kwali yasa ya tsuna agaban gadon, wani karamin gyale ya gani agefe, ahankali ya dauko ya nannade kan dashi sannan ya kawoshi gaban kan ya daure, shida kanshi daya kalla yasan ba haka ake ba, dan ya tabbarar har gari ya waye bazai kwance ba"

Addu'oi ya tofah mata sannan ya jayo bargo ya rufeta, kula yayi da jakar dake hannunta, ahankali yasa hannun shi ya zare jakan, mikewa yayi ya fara tafi, har yakai tsakiyan falon ya tsaya tare da waiwayawa ya kalle ta, wata zuciyan ce tace danje ka sunbaceta, afilin yace tirrr Allah ya kiyaye"

Dakinsa ya koma ya zauna abakin gado sannan ya bude jakar"

Da sarkan deeni ya fara cin karo, hannu yasa ya zarota, dogowa ce sosai, ga uban nauyi, agefe ya ajiyeta, sannan ya kara saka hannun shi, wani dan dogon Abu yaji me karfi, fitowa yayi dashi, nan ya fahimci wuka ce"

Zarota yayi acikin dan gidanta sannan ya kureta da ido"

Babu abinda wukar take banda sheki dagani bakaramin kaifi gareta ba"

Mamaki ne ya kama jamal, nan take ya shaida daga inda suka fito"

Amman meyasa deeni zaibawa Husna waka? me zatayi dashi? Idan ya bata sarka saboda soyayya ? Toh wukar ta menene?

Take Wata zuciyan tace soka maka za,ayi?

Mikewa tsaye yayi tare da fadin lallai akwai aiki agabana dan husna nema take ta zama yar daba"

Afili yace waishin soyayya hauka ce? Yar karamar yariya duk tabi ta haukace a soyayya ? Idonta ya rufe babu gani babu ji?

Tunanin abban asma,u ne ya fado mai arai, hakika yana tsananin tausayin Sa, yanzun inda wani guri tayi aure za a iya sakin ta ayau, dan babu wadda zayi aure yaga matar da wuka beji tsoron zama da itaba, kuma za,azagi iyayenta"

Dan haka yaci alwashin shima bazai gayawa iyayen saba, dan yasan idan suka sani duk yadda suke Santa saita sure musu"

Ranan Jamal be iya runtsawa ba, tunani kawai yake tare da tsananin mamaki dan abin ya wuce tunanin shi"

Yasan cewa babanta yayi iya kukarin shi akanta, amman shi yana gani akwa wani abu da iyaye basa bashi mahimman ci"

Idan kakai danka makaranta, ba komawa zakayi ka nade hannu ba, yana da kyau ka dinga kai mishi ziyaran bazata, akai akai, kaman duk kwana 3 ko 4, sanan jawo yaro ajiki yana da matukar mahimman ci, dan zai saki jiki dakai, bazai dinga boye maka abuba, haka zai baka daman dakatar da abin tunkan yayi nisa"

Tunanin da Jamal yaitayi kenan, be fargaba saijin kiran sallah yayi"

Boye jakar yayi da kyau, sannan ya shige toilet ya dauro alwala ya wuce masallaci"

Itako ma'u tana tashi taji kanta daure tamau"

Hannu tasa ta shafa cike da mamaki tace menene kuma haka? Kokarin kwancewa take ta kasa, gaban madubi taje ta kallah"

Afirgice ta cire hannuta kai, dan ganin tayi kaman andaure kaya"

Toh waye yamin wannan daurin? Wata zuciyar tace jamal, da sauri ta girgiza kai tare da fadin yaya jamal bazai dauramin dan kwali ba, kodai aljanune, wannan tunanin yasa ta firgice, tayi dakin Jamal aguje, saidai tana shiga taga babu kowa dan lokacin Jamal yana masallaci"

Kara firgicewa tayi ta ranta aguje,ta nufi fita daga bangaren su...

Heart Beat
*Mmn Yazeed*

💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


5⃣4⃣to5⃣6⃣

Jin tayi tayi karo da wani abu, gamshin turaren da taji shiya tabbatar mata Jamal ne, hannu yasa ya dogota daga jikin shi tare da daure fuska yace"

Menene haka, ina zaki ahaka?

Adaburce tace gurin momy zani"

Me zakije yi gurinta?

Tana waiwayen bayanta take fadin nifah wlh tsoro nakeji bazan iya zaman nan ba"

Tsaki yaja tare da kokarin tafiya, afirgice ta kama rigarshi, kallon da ya watsa mata yasa ta sake shi da sauri tare da fadin yaya wlh tsoro nakeji, karka tafi kabarni

Tsaki ya sake ja yayi gaba abinshi, aguje tabi bayan shi tsagal tsagal daga ita sai rigan bacci"

Yana kokarin shiga dakin itama tana kokarin shiga tare da zare ido, ganin tana kokarin bangaje shi yasa ya matsa ya bata guri ta shige"

Kan kujera taje ta rakube, Jamal ko ido ya zuba mata yana kallo kaman ya samu TV"
Chapter 24 · 0% Book details