← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 47

Sashe 31

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma'u ki kwantar da hankalin ki kamar yau ne zakigan shi ya dawo, kodan kinga har yanzun be kira bane hankalin ki ya tashi?, nima da hankali na ya tashi amman daga baya daddyn ku yaje Office dinsu dakenan Abuja antabatar mai suna nan lfy gurin da suke ne babu service"

Duk da ba haka bane azuciyar ma'u taji daddin jin lbrn Jamal yana lfy"

Haka momy taita lallashin ma'u hartaga kaman hankalinta ya kwanta sannan ta tafi"

Momy na fita nafisa ta fara dariya saida tayi me isarta sannan tace"

Ashe dai yaya jamal nada matsaye, amman kuke nuna kamar baku damu da junan ku ba"

Mikewa ma'u tayi ta nufi toilet batare da ta kalli inda Nafisa take ba"

Wunin ranan ma'u ta kasa fita falo, dan gudun kar wani ya fahinta dan tasan halin deeni"

Shiko deeni afalo ya yuwuni, sallah kadai ke fiddashi, har momy ta fahinci kamar akwai abin da yake jira dan motsi kadan yake jan tsaki tare da kallon hanya"

7:30pm ma'u na zaune daki ta takure guri guda, ga abinci da nafisa ta kawo mata agefe ta kasa ci, hawaye ne yake zubo mata ta gefen idonta, bakomai ke tada mata hankali ba illah gudun bacin sunanta ta tabbata deeni zai iya dawowa adaren yau, dan haka dole ta nemi mafita"

Nafisa ce ta shigo ta tabi ma'u da kallo tare da fadin"

Lallai abin naki babba ne, saboda tunanin yaya kike kin cin abinci"

Tsaki taja kadan sannan tace"

Wai nafisa meyasa ba'a rufe dakin nan?, nifa gaskiya tsoro nakeji"

Mikewa nafisa tayi tare da fashewa da dariya sannan tace"

Bana kullewa, kuma ni ba yaya bane bare kimin shagwaba"

Fita tayi tabar ma'u dabin bayanta da kallo, sanna ta share hawayen da ya gangaro ma"

Nisa tayi da tunani zuwa can ta yake shawaran kiran deeni domin tasan indai bata kirashi ba, babu abinda zai hanashi dawowa yau"

Bugu 2 ya dauka tare da fadin"

Asma'u sai yanzun kikaga damar kira na?

Cikin sanyin jiki tace yau banajin dadi ne"

Meke damunki? Koda yake ma barshi Anjima zanzo indubaki tunda kinki zuwa na ganki.....

A,a deeni dan Allah karkazo, koma meye kabari sai yaya jamal ya dawo, tunda yace bazai zauna dani ba, dan Allah deeni kayi hakuri nasan bakaji dadin mgnta ba, kafin yaya Jamal ya tafi yamin gargadi sosai tare da nunamin karnamai wasa da Aure"

Wani kara ma'u taji alamun deeni ya daki wani abu, cikin fada yace"

Ni kike gayawa Jamal ya baki umarni?, atunanin ki ni zan saurari umarnin sa ? Yaci uwassa dan uban sa, me kike nufi kina nufin kinason Jamal yanzun kuma zakibi umarnin sa?

Hawaye ta share sannan tace"

Bahaka bane deeni, narasa inda zansa kaina, inajin tsoron fushin uban gijina, wannan mgnr da mukeyi yanzun haramun ne, deeni kar akamani da wani laifi ayanzun abba zai tsine min duniya zata kalleni abaibai, dan Allah kayi hakuri mubi komai ahankali"

Asma'u kin daina sona ne?

A'a haryanzu kana nan inda kake amman kabari mubi komai ahankali"

Ajiyan zuciya yayi sannan yace"

Asma'u dan Allah karki gujeni idan kika gujeni bansan inda zan saka kaina ba, sonki acikin jinina yake, daga ranan da kika gujeni zuciyata zata iya bugawa, wata kila na rasa rayuwata, asma'u duk abinda kikaga nayi ba laifina bane laifin son da nake miki ne, sonki ya shigeni batare da yayi shawara dani ba"

Ahankali tace deeni?

Na'am asma'u

Nace mezai hana muruki Allah idan alheri ne atsakanin mu ya kawo mana mafuta, idan ba alheri ya canza mana da mafi alheri"

Jiya yayi gaban shi ya buga, cikin fada yace karke sake min irin wannan mgnr, ya zaki dinga mana muguwar addu'a idan bazaki iya furta alheri ba kiyi shiru kawai, kuma bari kiji ni bazanbi umarnin Jamal ba, idan har bakison nabiyoki dakin Nafisa to ki koma part din Jamal gobe"

Amsawa kawai tayi batare da tayi tunanin komai ba, da haka sukayi sallama"

Kara kudundune manta tayi, tana zubar da hawaye tare da rokon Allah ya kawo mata agaji"

Kira ta sakeji ya shigo cikin waryarta azabure ta mike dan atunaninta deeni ne"

Bakuwar no ta gani cikin sauri ta dauka tare da sallama"

Muyar Jamal taji cikin sanyi murya yana amsawa"

Shiru sukayi gaba dayan su, zuwa can Jamal yayi ajiyan zuciya sannan yace"

*Husna* ya gida?

Lfy lau ta fada ahanlkali"

Shiru ya sakeyi hartayi tunanin koya kashene"

Gyaran murya yayi sannan yace"

Momy tacemin kin bige baki, garin yaya?

Shiru tayi harya gaji da jira, jiyayi shirun yayi yawa dan haka yace"

Bazakiyi mgn ba?, to shigenan ki dinga tafiya ahankali Allah ya sauwake, kuma ki daina yawan tunani, muyi waya da usman yanan zuwa acikin satin nan shida dada"

Dadi taji ba kadan ba cikin murna tace Allah ya kawo su lfy"

Shiru suka sakeyi zuwa can Jamal yace"

*Husna* kinajin sanyi kuwa?

Da saurinta tace a'a"

Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace"

Niko sanyi na yawan damuna kibani shawara ya zanyi ne?

Rasa inda mgnr shi ta nufa tayi dan haka tamai shiru"

*Husna* ya kikayi shiru?

Ahankali tace toh ka rufa mana....

*Husna* kona rufa jinake kamar ana karamin, tunda nake bantajin abin da nakeji yanzon ba"

Toh kaje asubiti abaka magani mana"

Ganin bata gane inda ya nufaba yasashi fadin to shikena zanje idan bemin ba saiki bani wata shawaran sallam sukayi harta kashe ta sake ganin wani kiran ya shigo"

Dauka tayi taji Jamal na fadin mantawa nayi bacce kimana addu,ar samun nasara ba, kuma idan namiki wani abu ki yafimin"

Tabude baki zatayi mgn taji ya kashewayar hakanan taji gabanta ya fadi, sake kiran no tayi amman yaki tafiya, tsin tan kanta tayi da addu'an Allah ya dawo dasu cikin kushin lfy"

******

Washegari da yamma deeni ya sake kiran ma'u tare da jajjada mata idan bata koma part din Jamal ba babu abinda zai hanashi zuwa anjima"

Cikin kuka take cemai Jamal ne yace ta zauna anan
gurin momy"

Dagewa yayi tare da nuna mata akwai mgnr da zasu yi me mahim manci, kuma aranan ne zasu nema ma kansu mafuta"

Hankalin ma'u rabuwa yayi kashi biyu, wata zuciyar na cewa taje wata na cewa a'a" kai wata ma zuciyar cewa take kodai zaki gaya momy ne"

Mikewa tayi ta fito falo, momy ta gani zaune tare da deeni, wani irin kallo ya mata, sannan ya mata alama ta gyawa momy zata koma part din Jamal"

Babu abunda gabanta keyi sai duka tara tara ahakali ta bude baki tace......

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*

​7⃣4⃣to7⃣7⃣

💐💐💐 Momy ni yau adakin ki zan kwana"

Da mamaki momy ta kalleta sannan ta danyi murmushi kadan tace"

Halan Nafisa na takura miki da shegen surutunta?

Kin kallon inda deeni yake tayi tace a'a bahaka bane, akwana biyu inayin mafarkai idan na farka ina kasa bacci tare da tsoron dakin"

Shiru momy tayi zuwa can tace"

Asma'u kinayin addu'oi kuwa?

Inayi momy"

Tsakin da deen yaja ne yasa duk suka kalleshi"

Momy ce ta lura harara yake zafgawa ma'u, dan haka ta kira sunan shi sannan ta nuna ma'u tare da fadi"

Wannan itace Asma'u matar jamaludeen dan uwan ka, nasan baku san juna ba ko?

Wani haushi ne ya kama Jamal wadda yasashi mikewa batare da yasan lokacin ba"

Kallon shi momy tayi tace wani abu ne? Naga inakan maka mgn ka mike"

Daker ya iya sarrafa kanshi ya koma ya zauna sannan ya hura iskan dake bakin sa yace"

Naganta momy gsky yayi dacen mata kuma sunan ya dace da ita"

Murmushi momy tayi tare da fadin wlh kuwa nima ina farin ciki da kasancewan ta matar jamal, kaima Allah ya baka yariya me hankali kamarta"

Ma'u banda dukan uku uku babu abunda kirjinta kemata, duk atsorace take, kin yadda tayi su hada ido da deeni duk da ta lura abun da yake so kenan"

Muryan shi taji yana cewa ameen momy amman nima inada yariyar da nakeso itama sonanta Asma'u tana da kyau sosai kamar waccen Asma'u"

Ma'u jitayi hanjin cikinta na tsintsinkewa addu'oi take karantowa acikin zuciyarta, tare da kerman jiki"

Itama momy haka kawai taji bataji dadin zancen deeni ba, amman dama tuni ta lura lamarin shi akwai gyra, juyawa tayi tace asma'u shiga dakina ina zuwa"

Mikewa tayi badan ranta yaso ba dan batason tabar deeni da momy dan tana gudun karyaje ya fadi wata mgnr da zata jawo illah arayuwarta"

Tana daf dashiga dakin taji muryan deeni yana cewa"

Allah yasa yadda kuke sonta itama tana sonku haka"

Wani irin kallo momy ta masa sannan tace"

Meyasa kace haka?

A'a na fadane kawai momy, momy kinsan menene?

Saika fada"

Kwantar da kanshi yayi ajikin kujera sannan yace"

Yariyar da nakesonta take sona babanta baya kyaunata yaki bani ita sannan ya gayamin wasu kalamai da suka girgizani, duk da cewa duk abin da ya fadin haka ne, amman naji zafin sa sosai soboda kalmar da yayi ammafani da ita wajen mgnr sa"

Nisawa yayi kadan Momy na sauraron sa, sannan yace gaba da cewa"

Wlh tsohon nan kawai yaci darajan son 'yarsa da nake amman wlh dasai na zubar masa da hakora"

Baki momy ta rike tare da fadin shamsudeen abin naka har yakai haka"

Wani irin bazawaran murmushi deeni yayi sannan yace Momy kenan, wlh ina tsananin son 'yarsa banajin zan iya barinta jinina da nata gauraye yake, banzan iya barinta ba momy rasata na nufin tsayawar numfashina

Duk abinda deeni ke fada ma'u na makale tanaji innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai take ambata tare da fadin wacce irin masifa ce wannan Allah ka kawo min mafuta"

Muyar Momy ta tsinkaya tana cewa Shamsundeen inason na fahimtar dakai wani abu guda daya, ka dauka kamar kana mgn ne da mahaifiyar ka wacce ta tsuna ta haifeka"

Maida hankali deeni yayi gurin Momy"

Tana kallon cikin idon shi tace Shamsudeen waye ya gaya maka anaja da iyaye? tunda mahaifinta yace bazai bakaba toh kayi hakuri kabar masa 'yarsa"

Cikin sauri yace momy bashi da wani dalili, bakinciki kawai yake min, ya dauki laifin da banawa ba ya daura min, momy daman laifin wani nashafar wani?
Chapter 31 · 0% Book details