← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 47

Sashe 34

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana dannan no aka dauka kamar daman jira ake Asma'u? Taji yaya usman ya fada"

Cikin dakushshayar muyar ta amsa"

Shiru yayi kaman ruwa yacishi, zuwa can yace Asma'u me kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?

Kuka ne ya kubuce mata cikin kukan tace bakomai"

Shiru ya sakeyi sarai ya gane kuka take dan haka ya rasa mezaice mata"

Itama rasa ta ina zata fara tayi, zuwa can yaya usman yace"

Duba asma'u ki kwanta kiyi bacci da safe zan kiraki"

Haka ta hakura badan ranta yasoba, alwala taje tayi sannan tazo ta tada sallah, tanayi kwalla nasauka idonta"

Har aka kira sallahn asuba tana azaune bayan ta ida sallah tasake kiran no yaya usman, tare da alwashin zata cire kunya ta tambaye shi Jamal"

Yana dauka yace Asma'u kinyi bacci kuwa?

Rasa abincewa tayi tare da rikecewa"

Shiru na wani lokaci sannan yaya usman yace"

Menene ke damunki ?

Tsintan kanta tayi da fadin babu komai inason ne nayi mgn da anty fa'iza"

Toh ina zuwa, ya fada sannan ya kashe wayar"

Ba adaukin lokaci ba kiran yaya ya shigo cikin sauri ta dauka"

Gaisawa sukayi a gajarce sannan ma'u ta fara kuka"

Shiru fa,iza tayi tana sauraranta domin kota bude baki batasan me zatace ba"

Zuwa can ma'u ta tsagaita da kukan sanan tace"

Anty fa'iza meye nufin ku na boyemin halin da ake ciki, sabo dame za'a boye min, idan wani abu ne ya sameshi ku gayamin, kara tsananta kukanta yayi amman a haka tace anty ko ya mutu ne?

Muryan usman taji yana fadin"

Ke, be mutuba yanan da ransa, menene kikeyi haka? tun dare kike faman koke koke, Ku daman mata haka Kuke duk kubi ku dama mutum lissafi, yanzun ki bari yau zanshigo Abuja"

Babu laifi ta dan samu natsuwa, saidai yau ta lura gidan yafi kullum rikecewa dan yau ko abun kare ba'adaura ba domin babu masuci"

Da misalin karfe 2 Usman ya iso"

Asma'u na zaune idonta duk sun kode sunyi suntum nafisa ta shigo tace tazo daddy na kira"

Afalon ta same yaya usman da alhaji bashir, momy ma na zaune agefe"

Karasawa tayi ta zauna akasa, acikin dashshiyar muryanta ta gaida su"

Fuskan daddy atunkushe ya kira sunanta, sannan yaci gaba dacewa"

Akwai abun da banso ki sani ba, Amman ba yadda zanyi, ya zama dole kisani, domin abun ya wuce tunanina, tunda jamal ya tafi yau wata uku kenan babu lbr, tun bayan ta fiyanshi da wata daya be sake kiran kowaba kuma ko ankira ba'a samunshi"

Wannan dalili yasa muka fara tsorata kuma tundaga lokaci muke zuwa ofishin su, saidai suma Kansu basu da wani lbr akansu, kullum hakuri suke bamu, tare da nuna mana sunakan meman inda suke ne, amman yanzun mun yanke shawara Usman da shamsudeen zasubi bayan sa"

Tukafin daddy ya karasa ma'u ta fashe da kuka, sai yanzo ne takeji son Jamal me tsanani azuciyarta, fuskan shi ta hango a idonta tare da dogon hancin sa, baya murmushi amman duk sanda yayi abin sha'wa ne, cikin kuka tare da jan majina tace daddy zan bisu"

Kafin daddy yayi mgn deeni ya shigo cikin shirin tafiya tare da wata jaka rataye abayan sa....

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[22:52, 1/2/2018] ‪+234 806 744 6138‬: 💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


8⃣1⃣to8⃣3⃣

Wani kallo deeni ya watsa mata sannan ya dauke kanshi"

Cikin tausayawa daddy ya kalli ma'u sannan yace,....

Ki kwantar da hankalin ki asma'u ke macece babu abin da zaki iya illa ki kara musu aiki"

Zaman ki agida shi yafi ki zauna kiyiwa mijin ki addu'a"

Kuka ta kara fashewa dashi, Usman ne yacire tagumin sa yace....

Ke karki kawo mana hauka, yaza tasa mutane agaba keta mana kuka, meye amfanin kukan?

Tsagaitawa tayi da kukan tare da to she bakinta"

Ciga usman yayi da fada har sai da daddy yace ya isa haka usman ka mata ahankali, kasan mata da miji sai Allah

Wani haushi ne ya sake kama deeni, cikin shi yaji yayi sanyi aranshi yace wannan kukan da asma'u keyi na meye, anya ba babu soyayyar Jamal azuciyarta, dan yaga ko kallon inda yake batayi"

Ji yayi kamar yace bazashi ba ya zauna yaga iya gudun ruwanta amman bazai iya ba soboda ayanzun yana Ganin Momy ne tamkar ummin Sa dan haka bazai zauna ba agidaba bayan yana Ganin hankalin ta atashe"

Shiko usma sosai asma'u take bashi mamaki wai ita da take ikirarin zata kashe jamal saigata wujuga wujuga tana kukan rashin sa, kara kallonta yayi yaga idonta duk sun kunbura"

Juyawa Usman yayi ya kalli daddy yace"

Daddy ni zan wuce basai natafi da wani ba, nikadai ma zan iya"

A'a usman zanfi son ku tafi ku biyu zaifi"

Ba yadda usman ya iya dole tasa zai tafi da deeni badan ransa yaso ba"

Koda suka mike suna sallama ma'u kuka kawai take"

Bayan fitan su momy taita lallashim ma'u, tare da nuna mata ta rage damuwa karya jawo mata ciyo"

Bayan tafiyan su da kwana biyu usman yayiwa daddy waya amman batasan abinda suka tattauna ba, dan haka da daddare tacewa momy abata no da yaya usman ya kira dashi"

Momy bata mata musuba dakanta tasa mata no din"

Acikin daren ma'u takira no saidai usman naji muryanta ya kashe"

Washegari duk suna zaune afalo, kowa babu bakin mgn, zuwa wannan lokacin kuka ya daina zuwa ma'u saidai kunan zuciya wani irin zafi takeji akirjinta ji take kamar tayi tsuntsu ta ganta agaban Jamal, idan ma mutuwan ne ta daukesu tare"

Mikewa tayi ta fita daga falon"

Momy da nafisa ne suka bita da kallo"

Ankwashi kusan minti 15 ma'u bata dawoba dan haka Momy ta kalli kofar tace"

Nafisa dobumin Asma'u kigani waje ta zauna?

Dasauri nafisa ta fita zuwa can ta dawo tace momy bafata waje"

Bata waje ? Amman nan naga tayi, kota dawo ne ta wuce ne bamu kulaba, duba ciki"

Dawowa nafisa tayi tace momy saidai ko toilet ta Shiga amman bata daki"

Zama sukayi suna jiran fitowanta, har aka kwashe minti 30 dan haka momy ta mike gaba daya part din saida ta duba toilet din amman babu ma'u dan haka ta fito afirgice tana fadin nafisa asma'u fa bata gidan nan"

Gaba dayan su waje suka nufu, suna isa gurin me gadin suka hada baki wajen fadi"

Asma'u ta fita ne?

Gargiza kai megadin yayi tare da aje radion shi agefe sannan yace tun fitan Alhaji nake zaune gurin nan banga fitan kowa ba"

Shiru momy tayi zuwa can tace anya baba kodai bacci ya debeka ta wuce baka gantaba"

Girgiza kai yayi tare da fadin idona biyu hajiya babu wadda ya wuce"

Cikin sauri momy ta nufi part din Jamal nafisa nabinta abaya, tun kafin ta karasa tahango alamar kofar abude take"

Da saurinta tashiga cikin falan babu kowa dan haka kai tsaye ta nufi dakin ma'u, saidai abinda ya bata mamaki ma'u bata dakin, dan haka arude momy ta fito tana fadin nagaya muku asma'u bata gidan nan, har momy ta kama kofa zata fita Wata zuciyar tace baki duba dakin Jamal ba"

Cikin sauri ta juya hartana hadawa da gudu nafisa ma ba'abarta abaya ba"

Suna shiga dakin suka hango ma'u kwance akan gadon Jamal"

Bacci take idon ta duk shedan hawaye ya bushe, hannunta daya dauke da glass din Jamal yayin da dayan yake rike da jaridan Sa"

Kara matsawa momy tayi har bakin gadon ta kurawa ma'u ido, bacci take sosai, hannuwan ma'u tasake kallo take taji kwallah tacika mata ido, domin ita kanta hango Jamal tayi zaune sanye da gilashin sa, hannun shi dauke da jarida kamar yadda ya saba"

Kuka ne ya kubuce mata cikin sauri tasa hannunta ta toshe bakinta dan karta tashi ma'u

Nafisa ma kuka take tare dabin dakin da kallo"

Ahankali momy tace Allah ina rokonka dan tsarkin mulkin ka Kadawo da jamalumdeen gurin iyalan sa, muna tsananin bukatar sa"

Haka momy taita addu'oi me kama da sambatu, daga karshe ta jawowa ma'u kofar suka fita"

Sai yamma likis ma'u ta shigo, babu wadda yace mata kalla harta nemi guri ta zauna"

Zuwa can momy ta kalleta tace kinyi sallah?

Eh kawai tace sannan tasa kanta akasa"

Abinci nafisa ta dauko ta aje agaban ma'u sannan ta zauna tace muci"

Wani haushi ne ya kama ma'u dan haka tasa hannu ta ture abinci tare da fadin banci "

Momy ce ta kalle su sannan tace wanni irin bakici ina kula dake yau kusan kwana nawa? bakicin abinci, kina nufin rayuwa zata yiwo ahaka?

Kamar me shirin kuka tace momy konaci awuya yake tsayamin wlh baya wucewa"

Haka nan zaki daure Asma'u nikaina idan inacin abinci ji nake kamar inacin magani"

Momy wlh bazan iya ba yanzun ma kirjina zafi yake min ji nake kamar nufashina zai dauke"

🙆🏼Kinga?, Asma'u ki rage tunani karki jawowa kanki ciyo"

Washegari da safe ma'u taji wayarta na kara, tana dubawa taga Abba ne, duk da tana cikin wani hali saida taji farinci, dan ta dade tanason kiran Abba da mama tsoro ne yake hanata"

Cikin siriyar muryarta tayi sallama, Abba ya amsa sannan ta gaida shi"

Ya amsa babu yabo babu fallasa, nasiha ya shiga mata tare da nuna mata komai mukkadari ne daga Allah kuma babu wadda ya isa ya canja yin Allah"

Wanna mgn ta Abba ya kara tayarwa ma'u hankali saitake ganin kamar Jamal ya mutu ne, dan haka ta kara rikicewa da kuka tare da fadin abba ya mutu ne?

A'a waye yace miki ya mutu?

Toh abba naji kana min nasiha ne"

Jim, yayi zuwa can yace yanzun asma'u sai jamal ya mutune zanmiki nasiha?, toh yanzun wannan kuka da kikeyi meye amfanin sa?, kinfi iyayensa son sa ne?

ance baki cin abinci, rashin cin abincin shine zai dawo dashi?, ki natsu kimai addu'a shi yafi bukata ayanzun, kuka da rashin cin abinci bazaiyi magani ba, irin wannan nasiha daddy yaita mata harta sarara da kukan sannan yaba momy wayar, itama nasiha taita mata daga karshe sukayi sallama"
Chapter 34 · 0% Book details