Sashe 11
Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itako Asamau fuskan nan murtuk ta tsaya agefen da jamal ke ciki sannan ta turo baki tace gani "
Daure fuska yayi murtuk kaman be taba dariya ba sannan yace ni sa'an wasanki ne zaki tsaya daga nesa kina cemin wani gaki ?
Bata rai tayi kamar zatai kuka sanna ta matsa kusa da widow motar tana cigaba da turo baki"
Fuskar shi adaurai yace nayi ciwo harman warke bakizo kika duba ni ba, yanzun gashi zan tafi bakizo muyi sallama ba ko?
Rasa inda mgnr shi ta nufa tayi dan haka tamai shiru tana wasa da hannunta"
Ajikinta taji kallonta yake cikin sauri ta dago ta kalle shi"
Sauri yayi ya dauke idon shi sannan yace *Husna* bazaki min mgn ba ?
Batace kala ba , ganin lokaci na tafiya Yasa Jamal yace shikenan nizan tafi gida ki kula da kanki, kuma ki rage son wasa, kinji ko?
Kai kawai ta daga mai"
Hannu yasa aljihun gaban rikar shi ya Ciro kudi ya kirga 20k ya mika mata"
Hannu buyu tasa ta karba dan ta kosa tabar wajen, juyawa tayi da nufin tafiya taji yace *Husna* nacewa Momy na kina gaisheta ?
Kaita sake dagawa sannan ta juya da sauri dan ta kosa ta daina jin muryan shi"
Usman na Ganin wucewan asmau yatashi ya koma, aguje ya tashi motar yabar gidan"
Asmau ko tana shiga gida ta mikawa mama kudin tace gashi nan yace nakawo miki"
Tunkafin ta rufe baki mama tace karya kikeyi aini yabani nawa".
Mama to nima na baki, ni banason komai nashi wlh yadda na tsaneshi haka na tsani duk wani abu daya shafe shi"
Kai asmau nikam al'amarin ki yana bani tsoro, kin fiye naci da mitan tsiya, dan Allah kiyi hakuri kibar mgn yanzun dauki kudinki ki wuce ina ce dazun kikace nabaki 3k ?
Em mama kibani amman ni wlh bazan bazanyi amfani da kudin shi ba"
Mikewa mama tayi tare da fadin Allah ya shirye ki"
***
Tunda Jamal ya tafi ma'u ta saki jikinta kulum da wuri take zuwa mkrnt , sai ta fara biyawa gidan su deeni sannan ta wuce makaranta"
Kuma da antashi break take kumawa sai kuma taji anbuga kararrawa sannan ta koma mkrnt"
Shakuwa sosai sukayi da deeni, baya zuwa ko ina sai ya jira anta she su akamakarata, zuwa wannan lokacin kawayen ta rahama da zainab sun fahimci halin da suke ciki tsakaninta da deeni, dan haka dukkan su tsoron mu'ammala suke da ita, duk da cewa basu taba taranta akan mgnr ba amman sun san soyayya suke yi"
Ahaka har suka kwashe tsoyon wata 8 zuwa wannan lokacin ma'u ta fahimci son deeni,
Take Dan haka shima deeni soyayyan asma'u yakeji sosai azuciyar shi, saidai babu fargaban komai azuciyan shi dan gani yake ko za azubar da jini saiya Aure asmau"
Itako asmau anata bangaren tana fargaban kaimai deeni a matsayin mijin da zata aure domin tasan mawuyacin Abu ne Abba ya yadda da zabin ta, dan haka ta fara shiga damuwa"
**
Abba ne zaune cikin mota akan hanyar su ta zuwa gidan dada"
Kallon asma' u yayi sosai yace mamana wai meke damunki kwana 2 ?
Karya ta shirya ahankali tace babu komai abba kawai karatu nake dan munkusa fara jarabawa ga kuma saukan mu na tahowa"
Har cikin zuciyan shi yaji dadi, fuskan shi dauke da murmushi yace"
Allah ya taimaka mamana, saura wata 2 ko?
Eh abba"
Murmushi yayi sannan yace kinga dakin gama sai Aure ko ??
Zuciyarta taji ta bugu cikin sanyin jiki tace um um Abba ba yanzun ba"
Kul mamana kar muyi haka dake, isha Allahu bazaki kara wata uku agida ba, Aure zakiyi mamana, meye amfanin zaman"
Nan danan idonta ya ciko da ruwa bawai auren bane bataso deeni ne bata shirya kaishi gida ba"
Baitai aune ba taji hawaye na zubu mata, hannu tasa ta sharewa Abba ne ya juyo ya kalleta sannan yace"
Mamana kina kuka ne ?
Shiru tayi tare da daura hannuwanta dukka biyu afuskanta"
Kallonta abba ya sake yi sannan yace Asmau Ki kwantar da hankalin ki, karkiga wai dan har yanzun baki kawo kowa amatsayi wadda zaki aura ba, zaisa namiki auren dole, bani da niyar na aurar dake ga wadda bakiso, dan haka Ki kwantar da hankalin ki kinji ko?
Sosai taji dadin mgnr Abba acikin zuciyarta tace haka na nufin duk wanda nake so Abba zai amince dashi, yanzun idan nakai mai deeni zai barni na Aure shi?
Dahaka suka isa gidan dada, harta sauka ta shiga ciki Abba sai kallonta yake yana murmushi tare da godewa Allah da bashi yariya kimtsatsiya"
***
Jikinta babu kwari ta shiga gidan dada, idonta har sun fara tasawa almar tayi koka"
Atsakar gida ta samu dada tana shara kai tsaye ta wuce daki"
Bayanta dada tabi da kallo daidai lokaci da Abba ya shigo dada take fadin ita kuma wannan meya same ta"?
Abba ne yace rabu da ita dada shirman miyace"
Tabarma ya nufa ya zauna sannan suka shiga gaisawa da Dada, sun dan taba hira har ya bada lbrn yadda sukayi da Asmau "
Cikin dariya ta mike tace inazuwa barin ganta"
Kan gado ta sameta ta kwanta ta kifa ciki' ahankali dada ta Saka hannunta ta dagota sannan tace ke kanki daya kuwa ?
Shiru tayi dan haka dada tace" to shike nan tashi Ki gayamin meye matsalan ?
Tashi tayi da sauri ta zauna sannan tace dada idan na gaya miki zaki tai make ni?
Me zai hana takwara?
Dada ?, idan na fada miki bazaki fadawa Abba ba?
Nan danan jikin dada ya haurawa ba komai ta tuna ba , sai Firdausi mgn da ma' u tayi yasa ta fara tunani ko itama ta kwaso abin mgn ne, dan haka batasan lokacin da tace babu meji takwara ina jinki"
Hawaye ne ya zubo mata tasa hannu ta share sannan tace"
Dada dan Allah ko abinda zan fada be miki ba, ki tai make ni kirufa min asiri"
Naji naji Asma'u menene kike ta maimaita zance daya"
Dada nifa deeni nake so"
Tsaki dada taja sannan tace to dan wanan kiketa kunbiya2, wanene deeni?
Dada baki ganeshi ba ? Shamsu fah na kayin makarantar m...
Zaro ido dada ta yi tare da dafa kirji arikece tace kar dai kice min wannan tambadaden yaron?
Cikin sauri Asma'u ta diro ta Saka hannuta duk biyun ta rufe bakin dada"
Dada ko banda rawa babu abinda jikinta keyi salati take kokarin yi amman saboda rawan jiki fadi take"
Kalu lahaula innalillahi La,ila ha'illahu......
Asmau kara rudewa tayi ta manta tsoron dada shiya harta fada mata"
Tsugunawa tayi ta rike hannu dada tace dada dan Allah kiyi shiru haka ya isa"
Ina rawa kawai jikin dada yake gaf2 idonta na kifkifyawa"
Cikin matsan cin kuka tace dada yau dan nagaya miki damuwata shine kika rikece, dada idan ban gaya miki ba wa zan gayawa, kefa kika ce duk abinda ya dame ni na fada miki"
Arikece Dada ta bige hannun asma'u tare da fadi ke dallah can rabo dani neman tsari nake"
Toh dada ai ba daidai kikeyi ba kibari karkizo kiyi sabo"
Kallonta dada tayi sannan ta saki salatin ta fara fadin"
Summassabila yassara....
Kara danne bakin dada asmau tayi cikin rude tace dada dan Allah kiyi hakuri kar Abba yaji"
Ina dada bata san tanayi ba cigaba tayi da addu,ai ta batare da tasan metake fada ba"
Itama asmau rudewa tayi tare da kirgixa dada daker ta samu dada ta dawo cikin hayyacin ta"
Kallo dada ta bita dashi tana share zufa zuwa can dada ta dage ta kwasa mata mari"
Hannu tasa ta dafe gurin tare da runtse ido"
Mikewa dada tayi sannan tace duk yadda akayi kinada wani ciwo acikin kanki, idan ma mafarki kike to maza ki farka, dan bazai taba tabbata ba"
Cikin kuka asma'u takalli kofa sannan tace dada to kiyi shiru kar abbba yaji"
Dallah can rufemin baki fitsarariya tir da halin ki, waye zaiso ya hada zuriya da irin jaraba inbada ke shasha"
Ta inda dada take shiga batanan take fita ba, ma'u ko kuka take yi, tare da data sanin fadinwa dada"
Dada ko rufe ido tayi taita masifa daga karshe ta kara fasa kuka"
Saida sukayi me isan su sannan dada tace Asma,u kiyiwa girman Allah ki fita harkan Yaron nan, ni daman tunda na ganku tare kwanaki hankali na be kwanta ba, na firgita da ganin ku tare, wlh takwara ina gargadin ki karki yadda abbanki yaji wannan mgnr, kisan ba lafiyayye bane tun tuni akace zuciyar shi tana daf da bugawa"
Kudundune kai asma,u tayi tana kuka ciki2, zuwa can ta dago kai tace shikenan dada naji nahakura, idan Allah yaso zan cireshi azuciyata, sannan dada dan Allah karki gayawa kowa"
Cikin fada dada tace bazanyi shiruba asmau , idan nayi shiru na zuba ido wani abu kuma ya faru fah"
Dada babu abinda zai faru namiki alkawari dada daga yau bazan sake kulashi ba"
Yadda asmau ta marairaice ne tabawa dada tausayi, dan haka ta shiga mata nasiha"
Da gsk jikin ma'u yayi sanyi dada ta kula da haka, dan haka bayan ta gama ita da kanta ta daga ma'u sannan ta share mata hawaye tace muje kar abban Ki ya gaji da jira"
Tsaye suka samu Abba ganin fitowan su yasa shi fadin da zanje na dawo ne"
A'a karka batta tasata agaba ku tafi gida"
Sallama yayi ya fice ma'u nabin shi abaya"
Har suka isa gida tana share hawaye abba na kula da ita amman yayi kaman be ganta ba, a tunanin shi mgnr auren da yayi mata ne"
Ranan ma'u bata runtsaba tunani yadda zatayi ta rabo da deeni take, amman duk inda ta juya saitaga bazata iya rabuwa dashi ba"
Washegari ma babu mkrnt wuni tayi da tunanin deeni acikin zuciyan ta ta yanke shawaran gayawa deeni ya nemo masu mafita"
Washegari ta kama asabar dan haka karfe 7:30 tayi sallama ta wuce mkrnt"
Tundaga nesa take kallon gurin zaman deeni abin mamaki yau babushi aguri, mamaki abin ya bata dan kullum gurin take samun shi"
Koda takai kofar gidan gurin ta tsaya ta kallah sosai sannan ta shiga cikin gidan"