← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa can ya sake jan tsaki tare da dauke kanshi daga kallon ta, sannan ya wuceta yana kokari balle botirin hannun rigar sa"

Waigowa yayi ya kalleta sannan ya daure fuska tare da fadi.....

Toh yanzun yaya zamuyi?, inason zanyi wanka"

Idonta tsuru2 tace toh dan Allah karaka ni gurin nafisa, nibazan iya xama anan ni kadai ba"

Dauke kai yayi sannan yace ai ko zaki iya ma bazan barki ba, dan inason na sake adaki na, maza ki tashi ki wuce naki dakin"

Dan Allah kayi hakuri wlh tsoro nakeji, aljanu ne adakin"

Aljanu?, baki yi addu'a idan zaki kwanta ko?

Cikin sanyi murya tace inayi jiyane na manta banyi ba"

Toh yayi miki kyau gare da suka firgita Ki, gobe kya kuma"

Hawaye ta matsu sannan tace nifah ba firgita ni sukai ba, jifah inda aka daure min kai kuma na kasa kwancewa"

Akaikai ce ya kalleta sannan yace waya ya daure miki kan ?

Nima ban sani ba kawai bacci nayi, ina tashi naga kaina a haka"

Dariya taso bashi dan haka yai kasa dakai, saida ya saita kanshi sannan ya dago kanshi ya kalleta tare da fadin ai kice bakijin mgn gashi suma mutanen boye hankalin su ya dawo gareki, kinatsu kinki natsuwa, saikace me kunnen kashi toh aigashi nan kinsamu daidai dake"

Kuka ma,u ta fara harga Allah ta yadda da mgnn Jamal, hango Jamal na shirin shiga toilet yasa ma'u mikewa tayi kan Jamal cikuikuye shi tayi sosai ta shige jikinshi

Cikin sauri ya dage hannuwan shi sama tare da fadin tsaya2, sakeni inkwance miki dan kwalin, daker ya samo ya rabata da jikin shi, sannan ya mika hannu ya fara kwance mata, daf da juna suke dan haka kowanne najin domin daya, Jamal ji yayi yanayin jikinshi ya fara canzawa, duk lokaci daya da canzawan tunanin shi, Kai *Husna* ta hadu komai nata me kyau ne, lebenta ya kallah sannan ya sakko kan kirjinta, cikin sauri ya runtse ido dan kawar da tunanin, itako ma'u idonta na kasa dan haka batasan bakin daya yake ba"

Shima ganin idonta akasa yasashi maida idon shi kan kirjinta, kasa dauke ido yayi, ya dauki tsayon lokaci ahaka, zuwa can ma'u ta dago kai, cikin sauri ya kawar da kansa gefe, daker ya iya hada kalman zomoje narakaki gurin momy"

Lokacin da suka isa part din momy tana daki bata fito ba, kai tsaye dakin ya shiga ma'u nabinsa abaya"

Ganin momy kwance tana bacci yasadhi juyawa dakin nafisa ya nufah, itama kwace take tana bacci' juyawa yayi ya kalli ma'u yace toh matsoraciya saikije ki kwanta"

Juyawa yayi ya fice har ya gota dakin momy ya ja yatsaya, juyawa yayi ya koma dakin, tananan kwance inda take"

Ahankali ya karasa gaban gadon ya zauna sannan ya mika hannu ya fara tashin momy"

Ganin Jamal adakinta da safen nan abin ya bata mamaki dan haka ta tashi atsora ce ta zauna tare da fadin Jamal lfy ?

Kasa yayi dakai sannan ya karyar Sakai kaman karamin yaro yace"

Momy daman ...... Shiru yayi ya kasa karasawa"

Kallo Momy ta bishi dashi ahankali tace"

Jamal gaya min menene ya faru? Ko wani abo na damun ka ne?

Cije lebe yayi kadan sannan yace momy daman inaso ne nayi Aure"

Aure kuma? Wanne irin aurene kuma Jamal? Duka2 kwanan ka nawa dayin auren?

Kasa ya karayi da idonshi sannan yace momy ai wannan ba Aure bane, *Husna* fa kanwata ce, nida usman duk daya ne, babu wani babbaci, daukata nake kaman nafisa, dan haka Momy ni inason nai aure yanzun"

Wani kallo Momy tamai mekama da harara sannan tace"

Amman dai Jamal wautanka yawa gareta, inna fahimceka kana nufin bazaka iya rayuwan Aure da Asma'u ba"

Shiru yayi bece komai ba, dan haka Momy ta sake cewa toh shikenan Jamal tunda bazaka iya zama da itaba ai saika sallameta, dan za man beda amfani"

Shiru yayi zuwa can ya daga jajayen idon shi yace"

Momy nifa cewa nayi zan kara aure bawai wani abuba"

Eh ainaji zaka iyayin aurenka ammafa idan ka sallameta, dan baza,a tauyewa yariya rayuwa ba"

Mikewa yayi fuuuu ya fice"

Binshi da kallo Momy tayi afili tace wawa kawai, yana girma yana cin kasa"

*****

Allah sarki deeni bawan Allah,

Deeni ne zaune atsakar gida, ya rame yayi duhu, gefen shi ummi ce kwance kan tabarma, tun daga ranan dauren auren ma'u bata sake samun lfy ba, deeni ko baya iya tabuka mata komai, shima kaman mara lfy yake domin yau sati kenan, beji muryan ma'u ba"

Zaune kawai yake hawaye na zobo mai, hannu yake sawa yana sharewa, jifi jifi yanawa ummi kallon tsana"

Suna haka suka farajin haushin duna, cikin sauri deeni yayi waje"

Caka ya samu tsaye akofar gida, cikin fada yace"

Caka me yasa zaka kawo min shi, ayanzun bani da bukatan duna, katafi dashi bana son ganin kowa, idona asma'u kawai yake son gani, caka bani da kowa, kuma bani da gata, duk abin da ya sameni laifin ummi ne, itace tajamin narasa asma'u, inaji ajikina indan bansamu asma'u ba zuciyata zata Buga, wlh ina masifar son asma'u, hannun caka ya kama ya daura akan kirjishi tare da fadin taba kaji inda zuciyata take yi inaji kaman numfashina zai dauke"

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


*Slm inaba masoya BUGUN ZUCIYA hakuri sakamakon jina shiru kwana 2 da kuka yi, haka ya faru sakamakon wani uzuri nawa, ifatan zaku fahimce ni, kumin uzuri, insha Allahu zan dinga yi, ko babu yawa, wadanda sukamin mgn prvt sukaji shiru suyi hakuri pls🙏🏻 sakon yamin yawa sosai, masu son group ma suyi hakuri pls🙏🏻 insha Allahu page nagaba zan bada no dazuyi mgn asaka Ku*

5⃣7⃣to5⃣9⃣

Haka deeni yaita sambatu, batare daya san me yake cewa ba"

Sosai caka ya tausayawa deeni, bayan ta fiyan caka deeni ya shige gida, samun ummi yayi tanata nunfarfashi, kallonta yayi, kamar bazaije ba, sai kuma ya fara takawa harya je gabanta saida ya share hawayen fuskan sa sannan yace"

Ummi jikin ne?

Hannu ta fara miko mishi dan haka ya tsuna agabata tare da mika mata hannun shi"

Rike hannun tayi da kyau, hawaye na zuba a idonta cikin murya irinta wadda take jin jiki tace"

Auta dan Allah kayi hakuri naga har yanzun fushi kake dani, inacikin wani hali auta, zuciya namin kuna ina takaicin rayuwata, har inajin inama ba,a halittoni ba, duk bawani abu bane ya jawo min illah bin zuciya, gashi yanzun nazo ina dana sani, babu wadda yafi bani mamaki irin baban ka, tunda yasa kafa yabar gari har yau ban sakijin duriyar saba, juyawa tayi ta kalli deeni dayai kasake yana yana sauraronta tace auta kana jina?

Kai ya gyada mata sannan ya kauda kansa gefe"

Ummi taci gaba da cewa, auta babban burina ayanzun shine inga mahaifin ka, inason inganshi kafin ta Allah ta kasance akai na" banason na mutu nabarka babu dangin uwa babu na uba, auta nasan cewa ka girma amman nasan baka iya zama da mutane ba, sai yanzun nake wani tunani, auta da ace kai natsatsene ko na mutu nabarka makota zasu taimake ka, kuma zasu tausaya maka"

Hawaye deeni ya share sannan ya Kali ummi, tausayinta yaji ya kamashi, hawaye ya fara share mata yana fadin bayanzun zaki mutuba ummi, kuma kicire tunanin wannan tsohon a zuciyan ki, ni banason ganin shi natsane shi, kuma duk ranan dana ganshi idona dana shi, wlh wlh na rantse da sarkin dake busan numfashi sai yayi daya sanin kawoni duniya, bana sonshi sam, kuma duk randa na ganshi idona dashi saina mai SAKK"

Girgixamai kai ummi take ahankali take cewa karkayi haka auta"

Cikin sauri ya mike tsaye haba ummi ina tsananin son asma'u Amman gashi tana neman tseremin yau kusan sati 2 kenan banji muryanta ba, ummi inason asma'u kuma inason na aureta, dan haka nifah saina aureta, kuma wlh idan jamal ya kuskura ya tabamin kayana sai na masa CAN CANTA

Hmmm auta taya zaka aureta bayan tana gidan wani, zansu ka cireta azuciyar ka, ka daina kiran matar wani da kayan ka, dan musamu mu fuskanci gaba"

A,a ummi saina aureta, daga baya ma fuskanci gaban"

Toh auta karinka hadawa da insha Allahu, kuma kayi addu'a Allah ya baiyana Mahaifin ka"

Girgiza kai yayi tare da mikewa tsaye, kallon ummi ya sakeyi sannan ya kada kai yayi waje"

****

Shiko Jamal bayan yabar part din momy bangaren su ya koma, afalo ya zauna sannan yasa hannun shi duk 2 ya dafe kai, zuwa can ya cire hannun nashi sannan ya daura tagumi, neman hanyan dazai bi yake, dan gaskiya ayanzun yana bukatar mace akusa dashi, amman fa yana son wadda zai aura ta kasan ce ta girme shi, ko kuma suzo sa annan juna, daker ya iya tashi ya shirya cikin kakin Sa ya fice"

Momy ko batasan da shigowan ma'u sai kusan 12 na rana"

Dakin nafisa ta shi tana fadin nafisa zoki kiramin asma'u"

Turusss tayi ganin asma'u kwance ta kifa kanta akan gado"

A,a ke kuma yaushe kika shigo?

Nafisa ce tace momy ai tunda asuba, yaya Jamal ya rakota, kuma tun lokacin take kuka"

Tahowa Momy tayi tare da fadin kukan lfy, zama tayi abakin gadon sannan ta daga hannu ta jawota tare da halan wani abu Jamal din ya miki?

Shiru batace komai ba, dan haka Momy ta sake cewa asma'u waini me kika daukeni?, nace miki idan kina da matsala ki dinga samu na kina gayamin, ko menene kiji ko"

Murya kasa kasa tace momy inaso nakoma gida bazan iya za agarin nan b....

Sabo da me? Cewar momy tana tsare ma'u da ido"

Tsoro nakeji momy bazan iya zama abangaren yaya ba akwai aljanu aciki"

Aljanu? Inji Jamal din ne ya fada miki?

A,a momy jiya ne na kwanta bacci ban daura dan kwali ba amman dana tashi sai naga andaura min dan kwali"

Murmushi momy tayi kadan sannan ta kauda kanta gefe tare da fadin to banda abin ki, Asma,u ai bake kadai bace adaki, yanzun haka Jamal ne"

Jin ta kawai tayi tace bashi bane momy, shi ai baya ma shigowa dakina"
Chapter 25 · 0% Book details