← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 47

Sashe 40

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hirar tasu bata kare bace, dan haka sukayi shirin zuwa gidan dada"

Tafe suke suna cigaba da hirarsu, acikin su babu wadda ta tambayi mijinta"

Sun kusa isa gidan ma'u ta tsaya tana waige"

Kallonta fa'iza tayi tare da fadin menene?

Ma'u na wage2 take fadin akwai abinda dada tamin kwanaki dan haka wlh yau saina tsoratata"

Tsaki fa'iza taja sannan taja hannun ma'u suka nufi gidan"

*****

*Abuja*

Momy zaune ita da deeni jefi2 suna hira"

Zuwa can deeni ya kalli momy yace momy yau ke kadaice agidan naji shiru ne?

Murmushi tayi sanna tace wlh dagani sai jamal Nafisa sun fita ita da usman, Asma'u kuma tana Kano"

Kano? Kano kuma? Meyasa zata tafi gano bayan mijinta bashi da lafiya"

Cikin takaici Momy tace, to ai ita ba jinyarshi zata iya ba, itama yanzun tana neman me kula da itane tunda karamin jiki gareta"

Cikin sauri ya runtse ido tare da fadin.......

Ciki? Ciki kuma? Haba wannan ma ai ba mgnr dazata sabo bane"

Kallonshi momy tayi da sauri, tare da fadin meka ce?

Mikewa yayi tare da fadin babu komai' ina zuwa"

Wucewa yayi cikin sauri yana shiga dakinsa ya dungule hannun ya Saki wani kara, jikin bango ya manne sannan ya zame kasa tare da fashewa da kuka, kuka yake kaman karamin yaro, hawaye ne shame2 a idonshi, yanzun asma'un shi tabari Jamal kusanceta anya kuwa zai iya rayuwa, fashewa yasa keyi da kura tare da gwara kansa da bango, wani irin tsananin kishine ya taso masa wadda yakeji bashi iya sarrafa kansa wani irin hawaye ne masu danko suke zubo masa, tare dajin kirjin shi kamar ana sukamai kibiya.......

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*

Dedicated
*Meelat Musa*

​9⃣9⃣to 1⃣0⃣0⃣

Kwanciya yayi akasa banda numfarfashi babu abin da yake"

Haka ya kwana cikin tsananin damuwa da bacin rai, wadda tunda yazo duniya be taba jin irinsa ba"

Kwace kawai yake hawaye na malalowa ta gefen idon shi"

Babu wadda yasan halin da yake ciki, acikin zuciyar shi yake addu'an Allah ya dauki ranshi, domin yana bakin cikin yaga ma'u da cikin wani bashi ba"

****

Itako ma'u azauren gidan dada ta tsaida anty fa'iza daker ta yadda ta tsaya, cikin gidan ta leka ta hango dada na wanke kayan miya"

Kara lekawa tayi sannan ta gyara murya tare da magewa tace......

Wai ana sallama da Dada"

Batare da dada ta waigo ba tace....

Kaji wata fitina da yamman nan, koma wanene ce mishi ya shigo"

Murmushi ma'u tayi sannan ta kara make murya tace......

Tsohuwa shamsun duna ne fah, kuma tare yake da gayyan kar......

Ai dada bata bari taji karshen zancen ba ta tuntsurar da kayan miyar, ya watse akasa sannan tabi takai a guje"

Dakinta ta shige ta maida sakata"

Fitowa ma'u tayi tana tuntsira dariya, fa'izama dariyar take, tare da nuna ma'u da yatsa tana fadin ke ko?

Abakin kofar suka tsaya fa'iza ce taita kwalawa dada kira tare da fadin kibude dada nice Fa'iza"

Ta fadi haka,yakai so uku dada bata amsa ba"

Zuwacan fa'iza ta sake cewa dada?

Na'am ta fada ahankali"

Nace ki bude"

Ahankali tace bakiga wani dan daba anan gidan ba?

Babu kowa dada Asma'u ce fah take tsorata ki"

Ahankali ta sake cewa ina asma'un take?

Gatanan muna tare"

Bude kofar dada tayi ahankali ta leko da idonta guda daya, ganin su tsaye yasa ta karasa bude kofar tare da fadin......

Kinci jakar ubanki, kinga min fitsararriyar yarinya, shikenan kuma na zama matoni"

Wuceta ma'u tayi ta shige dakin ta haye gadon dada me runfa ta kwanta"

Suma shigowa sukayi dada nacigaba da fada"

Baza ma'u tayi da ita hartayi ta gama sannan ta leko da kanta ta kalli dada tace.......

Ai ni munsa kafar wando daya dake dada tunda kikace wai idan kikazo gurina zamu hada baki dame kare mu kashe ki"

Murmushi dada tayi kadan, sannan ta nemi guri ta zauna tare da fadin"

Aini zolayarki nake takwara mutuwa ai ita muke jira, ina me gidan naki tare kuke?

Me kare?, ma'u ta tambaya idonta kan dada"

Kai, kai, asma'u
wai meyasa kike fadar min da gaba ne?,

Sanin kankine bana sonjin sunan wannan ibilishin yaron, wlh kika sake zan kira ubanki nagaya mai"

Daga ma'u har fa'iza dariya suka Saka, ganin inda idon dada yayi wuki2

Tare da fa'iza suka karasa aikin gidan yayin da ma'u ke kwance tana kwasan bacci"

Sai kusan sallar mangariba ta tashi lokaci sungama hada abincin dare"

Tuwon shin kafa ne miyar ganye, kallon miyar kawai ma'u tayi ta fara sheka amai"

Bayan ya lafa mata Anty fa'iza ta dawo da ita dakin dada, ma'u rike hancinta tayi da hannunta guda 2

kukarin kuka ta fara tare da fadin anty ni kizo muje gida wlh gidan wani iri wari yake yi mara dadi"

Wani irin kallo dada tawa ma'u sannan ta kalli fa'iza tace......

Wannan yariyar ko ita kadai ce?

Cikin sauri asma'u ta mike ta figi gyalenta tayi waje"

Dadama tashi tayi tana fadin ke takwara dawo kici tuwo"

Ina lokacin ma'u harta bar kofar gidan"

Gidan abbanta ta nufa tana tafe tana hada hanya"

Afalo ta samu daddy sunacin abinci shida mama"

Zama tayi fuskarta dauke da fara'a, nan ta shiga gaida abba"

Wani irin fara'a tagani kwace afuskan abba rabon da taga irinsa afuskar abba ta dade"

Amsawa yayi sannan ya tambayeta jikinta tare da jikin yaya jamal"

Cikin jin kunya ta amsa sannan yashiga samata albarka"

Dadi taji sosai ganin abba yabar fushi da ita"

Zuwa can taji yace matso muci abinci"

Karasawa tayi ta dauki cukali ta faraci, badan ranta nasoba saidan tayin da abba ya mata"

Sosai taci abincin jifi jefi abba najanta da hira, zuwa can taji amai na taso mata daurewa taso yi saidai hakan ya gagara, ji tayi zai kwace mata dan haka ta tashi aguje ta nufi toilet"

Kallonta abba yayi itama mama cikin sauri ta aje cukalin dake hannunta tare dabin bayan ma'u"

Sousai ma'u tabawa mama tausayi, wani irin wunkuri take kamar hanjinta zai fita"

Daker aman ya tsaya sannan mama ta wanke mata jiki ta fito da ita"

Daki taso wucewa da ita amman abba yace abarta afalo tasha iska"

Wani irin kunya ma'u takeji, takasa hada ido da abba, sun sunne kai take taki yadda su hada ido da abba"

Tana cikin wannan halin taji muryan abba yana cewa.....

Mamana me kike son ci?

Bakomai abba banjin yinwa"

Mikewa Abba yayi tare da fadin a'a mamana kiyi tunani bazaki rasa abinda kike so ba"

Shiru tayi tana dad'a boye fuska"

Ganin haka Abba yayi murmushi ya juya ya fita"

Bayan fitan abba ma'u ta mike ta shige daki ta kwanta, ba dadewa bacci ya dauketa"

Cikin baccinta taji wani irin kamshi na addabarta, jitayi koma menene tana sonci, dan haka ta tashi da sauri tana baza hanci taji ta ina kamshin ke tasowa"

Daga can gefe ta hango wasu manyan ledoji sunkai 4, saukowa tayi ta fara budewa"

Kayan kwalama ne cike adayan ledan, dayan ko kajine manya manya guda 2, nan ma'u ta shaida sune suke wannan kamshin, bata tsaya duba sauran ba tahau ci"

Ci tayi tai kat, nan bacci ya sureta"

Misalin 11:00pm mama tashigo, bakaramin dadi tajiba dataga ma'u taci naman sosai"

Kwashe sauran kayan tayi ko wanne ta ajeshi a inda ya dace sannan ta tashi asma'u tace tashi Ki koma gado"

*****

Jamal ne kwance agado sai juyi yake ma'u yake son agani, raboshi da ita tun shekaran jiya da suka fita tare da momy"

Yana cikin wannan tunani usman ya shigo, cikin fara ya zauna akusa da Jamal tare da fadin.....

Yazun muka rabo da bello, yashigo gari jiya da daddare"

Tsaki Jamal yaja, sannan yace, wai yaushe zaka wuce ne?, nifa ka takuramin wlh"

Wata yar karamar dariya usman yayi tare da daukan wayarsa yana dannawa"

Tsaki Jamal ya sake ja sannan yace.....

Haka kurum mutum da matar sa ahanashi ganinta"

Eh kuma dole mutum ya hakura ko yaki ko yaso nima matata nabaro da tsohon ciki"

Gyara kwanciya Jamal yayi sannan yace.....

Nina kiraka?, kaikaga zaka iya, ni da karfina babu abin da bazan iyaba wlh, dan Allah ka tafi wajen matar ka, banason jiyar na warke"

Wani irin kallo usman yayiwa Jamal sannan yace waikai wani irin mutum ne?, nifa sirikin ka ne amman kake gayamin irin wannan mgnr"

Jan jiki Jamal yayi ya zauna sannan ya kalli usman yace......
.

Nufin ka naji kunyan ka?, aini bansan kai sirikina bane, da kanayin sirikuta dani da bakazo jinyata ba, har yanzun kai abokina ne"

Mikewa usman yayi tare da fadin shikenan zantafi, tunda kace na takura maka"

Kauda kai yayi usman na daf da fita jamal yace.....

Ka rokar min momy dan Allah ta turomin Husna mugaisa amman dan Allah karka ce injini, cewa zaka yi ya kamata ne"

Waigowa usman yayi yamai wani irin kallo sannan yace......

Wacce Husnar?

Guda nawa ka sani?

Murmushi usman yayi sannan yace ai tunjiya tana Kano"

Azabure yace kano?, mgnr momy ne ya fadomai, jawo kafafuwan shi yayi ya ajiye akasa sannan yace......

Taya momy zatamin haka sabo da Allah?, harta tura Husna Kano batare da amincewata ba"

Jim usman yayi zuwa can yace, to ai laifin ka ne Jamal"

Tayaya ya zama laifina usman? Me nayi? Da sanda naki auren surutu akaita min, yanzun kuma dayin ba'a kyaleni ba, sai surutu akemin salon kananan yara su raina mutum"

Yazun da aka turata kano, can ma yayatani za'yi kenan"

Kalaman jamal basuwa usman dadi ba, cikin bacin rai yace......

Wai meyasa idan ranka ya baci baka tauna lafazin bakin kane?, waye kake cewa wai ana yayata ka, kadai san bani bace na turata ko?

Jamal kasa mgn yayi bayan wasu mintina ya sake cewa......

Toh naji, yanzun abin da za'ayi kaje ka samu momy kawai atura drive ya dawo da ita"

Usman be juyo ba, yace ai kana da kafa kuma kana da baki, ko ba yanzun ka gama cewa babu abin da baza ka iya ba?

Eh amman kasa mgnr da nauyi, bazan iya taren idon momy na fada mata haka ba"
Chapter 40 · 0% Book details