← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 47

Sashe 42

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaisar dashi Jamal yayi sannan ya tambaye shi jikin shi"

Shiru dakin yayi zuwa can daddy yace......

Jamal nazo ne muyi wata mgn, kasan cewa dan uwanka yana asibiti ko?

Eh Jamal ya fada ahankali"

Toh abinda nake so dakai, akoda yaushe mutum ya zama me karban kaddara yadda tazo mai, wani alfarma nakeson kamin"

Tashi jamal yayi ya zauna tare da jingina bayanshi da bango"

Daddy yaciga da cewa nasan kana son dan uwanka, dan haka inason ka tausaya masa ka duba halin da yake ciki, ka sakar masa asma'u bayan ta haihu shi ya aureta"

Wani irin firgita Jamal yayi tare da sauke ida nuwan shi akan daddy hannu Yasa ya mustsuke ido sannan yace daddy kaine ko mafarki nake"?

Ba mafarki bane Jamal zahiri ne, inason shamsu yaji daddi rayuwa bana so rayuwar shi ta kare ahaka, rayuwar shi abaibai take"

Jim, Jamal yayi sannan yace daddy ai wannan ba kaddarata bace tashi ce, shiya kamata ya karbeta bani ba"

Cikin ido daddy ya kalli Jamal sannan yace nasan haka Jamal amman ai lalurace ta kawo haka"

Shiru dakin yayi Jamal ji yake kaman anamai daka akirji, daddy ne yagaji da shirun yace.....

Jamal inasauraron ka"

Murya kasa kasa yace banzan iyaba daddy, dan Allah kayi hakuri"

Cikin fusata daddy yace nina rokeka alfarma kace min bazaka iyaba, to bari kaji wannan karon umarni zan baka, kafin nan da wayewar gari ka rubuta ma Asma'u sake"

Afusace ya Mike ya fita, wani irin zugi zuciyar jamal kemai tare da tukukin baccin rai wacce irin rayuwa ce wannan yaushe daddy ya sauya hali da zai zabi deeni akaina"

Inason asma'u banga dalilin dazan saketaba, zanyi koma menene dan nakare martaban aurena, shi wanene dabazaiyi hakuri da kandara ba

Irin tunanin da Jamal ya kwana yi kenan washegari dasafe daddy ya sake duruwa dakin"

Jamal naganin shi gabashi ya fadi, hannu ya mika mishi tare da fadin bani"

Sunkuyar dakai yayi batare dayace komai ba"

Cikin fada daddy yace karka maidani dan iska kanaji ko?

Wani irin mummunan tashin hankali Jamal yaji, tunda yake betaba jayayya da iyayenshi ba, kuma baya so ya fara, aman bazai iya aiwatar da abin da daddy yake soba"

Ahankali Jamal yace daddy dan Allah kayi hakuri wlh baxan iyaba, ba nason jayayya dakai, dan gaskiya inason asma'u bazan iya rabuwa da itaba......

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*

1⃣0⃣2⃣

Jamal bana wasa dakai, karkace zakayi jayaya dani, kuma wannan mgnr bana son wani yajita tsakanina ne ni dakai"

Daddy dan Allah ka jayen wannan mgnr, wlh daddy bazan iyaba, bazan iya rabuwa da Husna ba, daddy idan nabarta zan shiga wani hali"

Jamal koma waning hali zaka shiga baxai kai wadda shamsu yake ciki ayanzun ba, bana son nakarajin komai daga gare ka, takarda na nema kuma ita nake son kabani"

Kara dukar dakai Jamal yayi, sun dauki lokaci ahaka sannan daddy yace......

Jamal wlh zan bata maka ranka"

Cikin zuciyar shi yace.....

Raina ya dade da bacci daddy"

Cigaba daddy yayi da cewa, zakai abin da nagaya maka ko kuwa?

Murya kasa kasa yace daddy kayi hakuri🙏🏻

Wlh Jamal zan iya tsine maka"

Kallon daddy yayi da sauri sannan ya maida kanshi kasa yace......

A'a daddy kar kamin haka, dole ce tasa na maka musu daddy ba'a son raina bane, daddy idan na saketa rayuwata zata zama cikin hadari, dan gaskiya inasonta sosai babu rabuwa atsari na, kuma itama tana sona"

Cikin daure fuska daddy yace bantabaye ka wannan ba, kaida shamsu nasan kuna da babbanci kai mutum ne me tawakali da kaddara mekyau ko mara kyau, shamsu bayi dashi, ba'a daura shi akan wannan tarbiyan ba, banaso ya mutu, inaso yayi rayuwa kamar kowa"

Kunya ce ta fita a idon Jamal kwata kwata, tsintan kanshi yayi yana fadin daddy wannan ba kaddarata bace, bazan iya kashe kaina na raya wani ba, Allah ne ya bani Husna, batare da naje neman aurenta ba, duk da cewa na dade ina sonta bantaba nunawa kowaba har usman, kuma ni na sani deeni bawani sonta yake ba, wlh nafishi sonta, yana ikirarin yana sonta ne saboda besan menene so ba"

Itama kanta taso deeni ne cikin yarinta alokacin da batasan me take ba, na tabbata ayanzun Husna bazata so deeni ba"

Daddy idan kace lallai saina saketa bakamin adalci ba, Allah ne ya bani ita batare da yayi shawara da kowa ba, haka kuma Allah ne ya kaddara asma'u ba matar sa bace, dame bazai yi hakuri da hukuncin Allah ba, lallai ne abin da yake so saiya samu?, daddy karku shiga hurumin daba nakuba, deeni ba mutuwa zaiyi ba, darasi ne Allah yake nuna mishi, daddy idan ma muwa zaiyi sakin husnan dakace nayi zai kara mai kwanaki ne? Dan Allah daddy munar Allah yayi hukuncin shi, munemin zabin alheri agurin shi kawai"
Jikin daddy sanyi yayi sosai, shiru yayi na dan wani lokaci zuwa can ya sake cewa.....

Jamal nasani duk abin da ka fada haka ne, shiyasa ako ina nake alfahari dakai, amman kayi yadda nace d'in"

Wani irin yar fa hannun Jamal yayi, sannan ya rungumi hannuwan shi akirji"

Ganin haka daddy yace nakara ma lokaci nanda zuwa gobe ka yanke shawaran, zakamin biyayya ko kuma bijirewa umarni na"

Juyawa daddy yayi da sauri yabar dakin"

Yana fita momy ta fito daga dakin ta bayan daddy tabi da harara sannan taja tsaki ta nufi dakin Jamal"

Tana tura kofar ta hango fuskan Jamal hawaye shabe shabe"

Yana ganinta ya fara sharewa tare da boye idon shi"

Kusa dashi ta zauna sannan ta dago kanshi tace......

Jamal karka tada hankalin ka, bare har ka biyewa zancen mahaifin ka, idan har ka saketa bazan taba yafe maka ba, karka manta, nima ina da hakki akan ka"

Cikin rawar murya yace toh momy ni yanzun yaya zanyi?

Ka dage mishi akan kana son matar ka, ni bantajin inda akayi haka ba, alhaji yana da wani irin son 'yan uwan shi, wadda ya wuce misali"

Jamal be sake cewa komai ba, idonshi ya dauke daga gurin momy ya juyar dashi can gefe, cikin tsananin damuwa"

Momy kokarin kwantar mai da hankali take, amman ta kula hankalinta baya gurin ta, yayi nisa cikin tunani"

Mikewa tayi tai waje tare da fadin Allah ya kyauta"

Jamal naganin fitan ta ya kira wayar ma'u, yauma kashe take kamar kullum, tsaki yaja gashi bashi da no mama"

Wata zuciyar ce tace, ka kira usman, wannan tunani yasashi ya kira layin usman

Zuwa can aka daga usman ne yace gauro ya gari?

Cikin rashin kwarin jiki Jamal yace babban yaya ka huce kenan?

Dariya usman yayi tare da fadin aini daman ba zafi nayi ba"

Kayi fushi mana tinda ka tafi babu sallama, ya gida ya iyali?

Lfy lau suke, karkace min asma'u bata gaya maka fa'iza ta haihu ba"

Yake Jamal yayi kamar yana gaban usman yace da gaske?, me muka samu?

Nana Firdausi, usman ya fada cike da murna"

Allah ubangiji ya albarkanceta acikin addinin musulinci, kace inanan nasake baki nayi 'ya ban sani ba"

Dariya usman yayi tare da fadin wlh jiya da dare ta sauka, na dauka Asma'u zata gayama ne"

Karka karamin haka, ko Husna zata fadamin yana da kyau kaima naji daga gareka, amman bakomai tunda Husna taganta kamar nine"

Hmmm wlh Jamal kana min rashin kunya fah, ya jikinka najika wani iri ne"

Eh wlh bana jin dadi ne, dan hadani da husna mana"

Tsaki usman yaja sannan yace batanan gidan kuma basu dade da tafiya ba ita da mama"

Shiru Jamal yayi zuwacan yace toh sai an jima"

Kashe wayar yayi tare da binta da kallo, lallai yanason suyi waya da husna ayau, dan haka ya yanke shawaran kiran daddy"

Bayan sun gaisa da abba yamai barka samun karuwar da akayi"

Dariya abba yayi tare da fadin toh ai Jamal ku za'aiwa barka, kunji kunya tika tika daku sai yanxun kuka aje daya, daker"

Guntuwar dariya Jamal yayi tare da shafu keyarshi kamar yana gaban abba, acikin zuciyar shi fadi yake abba me kakeci nabaka na zuba"

Jim, sukayi zuwa can Jamal yace.........

Amm abba nakira wayan ta ne akashe, ban saniba ko wayar ta samu matsala ne"

Wai asma'u ?

Eh Jamal ya fada ahankali"

Toh, toh, ina zuwa"

Kashe wayar yaji anyi zuwa can yaji wayar na kara"

No Abba yagani, jikin shi har rawa yakeyi wajen daukan wayan"

Muryan ma'u yaji cikin murna da dauki tana rangada sallama"

Tsintan kanshi yayi da lumshe ido sannan ya amsa mata tare da fadin Husna shine kika yadda kika tafi ko sallama babu ko?

Toh ai momy ce tace haka"

Hmmm Husna toh ya kwana 2?

Lfy lau, ya jiki?

Yayi sauki Husna, yasu mama?

Suna lfy"

Yayi kyau"

Cikin siririyar murya asma'u tace....

Yaya Jamal albishirin ka"

Goro ya fada cike da zumudi dan tunda yake da ma'u bata taba sakar mai jiki kamar yauba"

Yar dariya tayi sannan tace.....

Fari ko jah?

Dariricewa yayi domin bazai ce ga takameme abin da ake cewa ba, tsintan kanshi yayi yana cewa jah"

Kukan shagwaba tasa kamar tana gaban shi, tare da fadin fari fa zakace"

OK toh ya isa kisan ban iya irin wad'an nan abubuwan ba, inajiki toh nace fari"

Cikin murna tace....

Na samu d'iya anty fa'iza ta haihu jiya da dare"

Yi yayi kamar be sani ba, ya lankwasa murya yace......

Dan Allah?

Wlh, yaya bakaga yariyar ba, kamarmu daya"

Har cikin jinin jikin shi yake jin muryanta dan haka ya kara kashe murya yace....

Da gaske?

Hmmm kai dai sai ganta da idon ka, wlh har giran mu iri daya ne"

Zanso inganta kuwa, kishafa min kanta, kice wani babanta na mata barka da zuwa"

Shiru sukayi nadan wani lokaci, zuwa can Jamal yace.....

Husna kina inane yanzun ?

Ina dakina"

Ke dawa?

Ni daya"

OK akwai mgnr da zan gaya miki, akwai wata babban matsala da ta tunkaro mu, daddy ya gindaya min umarni, wadda bazan iya biba, kinsan menene?

Girgiza kai tayi tare da fadin a'a

Ahankali ya fara warware mata abin da ke faruwa"

Kafin ya gama hawaye ya gama wanke mata fuska, cikin kukan tace........
Chapter 42 · 0% Book details