← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 47

Sashe 22

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komai girman Mutun baya kada ka afada, idai da wuka ne saidai ayanke juna, akarshe kuma kaine me nasara"

Duk abinda kayi daidai ne awajan bashir, nikaina bani da bakin mgn"

Har zuwa lokacin da kacika shekara 25, lokacin ne duk ka addabi mutanen garin"

Nasan yana nan a idon ka, baka manta ba, kuma alukacin ne aka nemin baban ka aka rasa, wanda hakan yayi sanadiyan dawowan mu nan"

Kuka deeni Yake sosai, take yaji ya tsani ummi, yana kukan yake fadin gsky kuncuce ni Ashe duk abinda ya faru dani kune sila, ku kuka jefani cikin halin da nake ciki, Ashe shiyasa danaje daukan Asma'u mu gudu abbanta yace tarihi zai maimaita kanshi?

Tuni idon ummi suka kankance saboda tsabar kuka, auta karka sake ka raba asma'u da gidan iyayenta, dan shine abun daya zama min babban kuskure arayuwa ta, naiwa iyayena laifi babba, lokacin dana dawo na neme gafaran su, akace min shekaran su 2 da rasuwa, sai filin gidan gashi kana gani, da hannuta take nunamai tsakar gidan da suke zaune aciki, tare da kara rushewa da kuka"

Shima deeni kai ya hade da guiwa yayi kuka me isar Sa"

Rawan sanyi ummi ta fara deeni na kallo amman saboda tsabar jin zafita daya ke, yaki kulata"

Zuwacan ya miki tsaye ya daga kanshi kasama tare da karkace baki, dan ya riga ya zaman mai jiki, guri daya ya kurawa ido sannan yace"

Na rantse da sarkin dake busan numfashi saina auri Asma'u, babu uban da zambarwa, inanan inakan bakata, ko ana muxuru ana shaho saita dawo gareni"

****

Ma'u ko sanda ta shiga gida samu tayi kowa yana tsaye duk suntashi, kallonta kowa keyi dan haka ta gane sunji abin da yake faruwa"

Koda ta shiga daki babu wadda ya biyuta, har misalin 12 na rana tana kwance"

Haniyan mutanen da taji ya kara yawa haka ya tabbatar mata zancen auren nanan babu fashi"

Zuwa can ta farajin karan motoci, mikewa tayi ta kama labulen window ta leka"

Manyan mutane taga suna futowa mahaifin Jamal kawai ta shaida"

Komawa tayi ta zauna ta daura tagumi, zuwacan ta sakejin wasu motocin nashigowa tare da hayaniya"

Agogo ta kallah 2:30pm arikice ta miki afili tace yanzun dan Allah har 2 tayi, nashiga uku na"

Gaban window ta tafi ta leka, Sojoji ne gungu2 hannun su rike da manyan bindigogi, wurin yacika makil da jama'a daga can ta hango Jamal sanye cikin shadda fara karrr, atsakiyan abukan shi yake, kowanne fuskan shi dauke da murmushi amman tashi kamar amai mutuwa"

Bakin gadon ta koma ta zauna, zuwa can taji maruki na fadin Alhamdulillahi andaura auren *Jamaludeeni* da *Asma'u*

Jitayi kaman ansoka mata kibiya akirji, hawaye taso matsowa Amman sunki zobuwa, gefen gadon ta koma ta makure"

Zuwa can taji anbude kofar ahankali ta dago kanta, momyn yaya usman ce, hannuta rike da kaya, abakin gadon ta ajiye kayan, sannan ta shiga toilet, zuwa can ta fito tace to taso maza yamma nayi"

Kaman za'a kamata haka take tafiya' bayan tayi wanka ta fito momy ta mika mata kayan ta sanya zuruf suka shige, saboda tsabar raman da tayi"

Komawa tayi ta zauna, tana haki, gyale momy ta yafa mata sannan tace tashi muje ke kadai ake jira"

Wayyo momy馃檰馃徏 wlh nagaji, waida zan dan huta ne"

Me kika yi? Maza taso muje"

Haka taitabin bayan Momy kaman me koyon tafiya, har suka isa falon Abba"

Zaunar da ita tayi sanna itama ta zauna tace toh Alhaji ga Asma'u nakawota tayi sallama, tare da neman gafarar ka zamu rakata dakin mijinta"

Dauke kai abba yayi can gefe sannan yace kuje kawai Amina"

Mutumin dake gefesa ne yace a,a bazayi haka ba, ya kamata kace wani abu"

Kwantawa Abba yayi ajikin kujera ya rufe ido, dan haka mutumin yajuya ya kalli Asma'u

Yace barin ara bakinsa naci masa albasa, Allah yasa kije asa'a kinji ko?, Allah ya miki Albarka"

Kuma Dan Allah kiyiwa mijinki biyayya, yi nayi bari na bari"

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace"

Da zan umarci wani da ya yi wa wani sujada, da na umarci mace tayima mujinta sujada"

Manzon Allah ya kara cewa"

Baya halatta ga matar aure tayi azumi kuma mujinta bayayi, face sai da izininsa, ba tada ikon zartar da wani Abu sai da izinin sa"

Haka yaita mata nasiha amman agurin ma'u shiga yake yana fita domin ku fadi take azuciyata, Allah ya kyauta nawa Jamal biyayya"

Har akasata amota kuka take, tare da kankame karamar jakanta ahannu"

Ahaka suka nufi Abuja, gabanta na dukan uku uku, tare da addu,a insha Allahu jibi iwar haka zata sake biyo wannan hanyan"

*Abuja*

Sun shigo karfe tara da rabi na dare kai tsaye gidan Jamal suka nufa"

Agaban wani tankasheshen gida sukaga drive ya tsaya, gida ne me dan karan kyau get din aka bude musu dan haka drive yasaka hancin motan cikin gidan, tun acikin mayafi ma'u ta hango haske kaman rana, ahankali ta dan daga gyalen ta tana kallon Gidan, amma me? Wasu sojoji tahango sunfi 10 suna shawagi haraban agidan tare da manyan bindigogi, kuma da alma agidan suke, cikinta taji ya karta, cikin sauri ta rike momy tare da fadi Momy wadannan agidan suke?

Kallo momy tabi gurin da ma'u take kallo dashi sannan tace"

Eh masu gadi ne?

Innalillahi wa inna laihir raju,un nashiga uku na"

Momy na kokarin lallashin ma'u wayarta tai kara, dauka tayi tasa akunneta batace komai ba ta cire wayar akunneta ta mikawa ma'u tanacewa ansa Jamal zaiyi mgn dake"

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[20:21, 12/14/2017] ‪+234 813 679 9888‬: 💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


4⃣7⃣ to 5⃣0⃣

🐕🐕🐕

Amsa wayar tayi badan ranta yaso ba, daga cikin wayar taji muryan Jamal yana cewa"

Kafin ki shiga gidana ki ajiye Duk wani iskanci naki, akofar gida, karki shigan min dashi gida, dan bazan dauki rashin kunyar ki ba,"

Bejara mezata ce ba ya kashe wayar"

Guntun tsaki ma'u taja sannan ta mikawa momy wayarta, sake gyara mata gyale Momy tayi, sannan taja hannunta suka shi cikin Gidan, tare da ayarin mutanen da sukazo dasu"

Suna shiga falon tasa hannunta ta bude idonta, dan ita bataga dalilin daza'a rufe mata ido ba"

Idonta kiri kiri take kallon gidan, eh Gidan ya had'u kuma anzuba kayan daya dace aciki, amman ita basu bane agabanta, Allah ya sani tana masifar son deeni"

Haka nan taji damuwan ta ya ragu sosai, dan haka ta shiga cikin su Anty fa'iza da Khadija da suke hira adakin daya ke matsayin dakin baccin ma,u"

Su uku ne kadai adakin, manya suna falo suna kallo, dan haka anty fa'iza tayi amfani da daman tana bata shawara"

Asma'u kinga jamal yana da kirki sosai, dan Allah ki bishi sauda kafa, ku zauna lfy, kuma ki guje duk abinda baya so"

Toh kawai asma'u take cewa, Ganin haka Anty fa'iza ta ciro wani littafi ajakarta ta mika mata"

Ranan kusan kwanan zaune sukayi, sunsha fira ammam hirar tafi karkata tsakanin Anty da khadija"

Washegari suka tashi da shirin komawa gida dan haka hankalin ma'u ya tashi "

Damisalin karfe 2 na rana suka fito domin kai asma'u gida momyn Jamal, su kuma su wuce gida"

Motoci aka kawo wadatattu"

Bayan sun isa a gaban momy suka ajeta"
.
Momy da yau ne ganin ma'u nafarko, ta taso da sauri ta kamata, kan cinyan ta, tasata tare da leka fuskan ma'u"

Masha Allah, ta fada afili, sannan taci gaba da cewa Allah ya zaunar daku lfy"

Daga nan su Momy suka yi sallama suka fice da nufin daddare Jamal zai mayar da ma'u

Tun da suka fita ma'u najikin momy tana kuka, Nafisa ko na zaune agefe fuskan ta dauke da dariya"

Bakomai ke bata dariyan ba kuwa illa, tunawa da tayi yaya Jamal baya son ahau gadon sa, kuma yau gashi da mata"

Har gurin karfe Goma, ma'u na gidan Momy, tana jaran Jamal har bacci ya fara deeban ta"

Ganin ma'u na bacci Momy ta shiga kiran jamal awaya yana dauka tace"

Jamal kana ina ?

Ina gida mana momy"

Gida ? toh ina Asma'un ?

Cike da kwarin guiwa yace gata akusa dani"

Mamaki ne, ya kama momy, juyawa tayi ta kalli inda ma'u ke kwance sannan ta maida hankalin ta cikin wayar tare da fadin, kaniyar ka Jamal, abinda zakayi kenan?

Me kuma nayi momy?

Takaici ne ya kama momy harta rasa abin cewa, zuwa can tace kazo yanzun nan inason ganin ka"

Cikin kankanin lokaci ya iso kai tsaye dakin momy ya shiga"

Yan mata guda 2 ya gani suna bacci dan haka ya bisu sa Ido, ya shaida nafisa amman dayar ya kasa tantaceta"

Damamaki yace momy wacce wacece ?

Uwarka ce, waikai sai yaushe zakai hankali, kirikiri ince maka ina Asma'u kace min wai gata, bayan tun da 'yan uwata zasu tafi suka kawo ta, toh inason insan abin da kake nufi?

Jikin shi asanyaye yace toh momy Allah ya huci zuciyar ki"

Mikewa momy tayi tana kokarin fita adakin take fadin, gatanan ta riga tayi bacci, sai kasan yadda zakayi, ficewa tayi abinta"

Bin bayan momy yayi da kallo sannan ya juya ya kalli inda ma'u ke kwance ahankali ya matsa gurin cikin siririyar muryan shi yace ke, *Husna*, Husna, ganin ya kirata su biyu bata tashi ba, yasa ya tsaya yana tunanin yadda zaiyi"

Zuwa can ya matsa kusa da nafisa, hannu yasa yadan dake kafanta nan danan ta mike, sannan yace zoki tasa min Husna"

Da saurinta ta taso, tana tashin asma'u, tashi tayi ta zauna tana mutsutsu ke ido"

Lallan hannunta yabi da kallo, har ya kasa dauke idon sa ahankali yace tashi muje"

Kuka ma'u ta fara tare da fadin nidai aban ni anan dan Allah"

Harga Allah tabashi tausayi amman saiya mika hannu yana fadin zo muje dare yayi fah"

Ganin bata da niyar tashi, yasa ya fita, afalo ya samu Momy dan haka yace,

Momy taki zowa fah"
Chapter 22 · 0% Book details