← Book details Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 47

Sashe 41

Bugun Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa usman yayi ya fice abinshi yayin da Jamal yaita sauke ajiyan zuciyan bacin rai"

****

Sai dare momy ta fito falo, zaune tayi tana jiran shigowan Usman tare da deeni, tun safe yau bataji motsin su ba, garama usman dasafe kan ya fita ya shigo har daki sun gaisa"

Amman deeni rabon da ta ganshi tun taren da ta dawo raka ma'u kano"

Shirun taji yayi yawa dan haka ta mike ta nufi dakin Jamal"

Yana zaune ya hada kai da guiwa"

Kai Jamal yau Usman lfy kuwa har yanzun be dawo ba?

Dago jajayen idon sa yayi ya sauke akan momy, tare da fadin nima shinake jira kuma nakira no dinshi kusan so 10 amman be daga ba"

Atsorace momy tafara dannan wayarta tare da fadin to lfy kuwa?

Bata rufe baki ba taji andauki wayar dan haka ta fara fadin usman ina ka shige gashi har dare yayi?

Momy wlh tafiya ce ta taso min dan haka na wuce, yanzun haka ina kano, gobe zamu wuce Sokwato"

Cikin baccin rai momy tace wanni irin tafiya ne zai taso dahar zaka kasa mana sallama haba usman gaskiya baka kyauta ba"

Hakuri yaitaba momy sannan ta mikawa jamal tana fadin ga Jamal"

Saidai usman najin Muryan Jamal ya kashe wayyar"

Juyawa momy tayi hankalinta atashe tana fadin saura deeni barinje na duba ko shima garin ya bari beyi sallama ba"

Wani Irin abu Jamal yaji yana mai yawo akai, wani mummunan tunan tunanni ya ziyarci zuciyar shi, Husna na kano, Deeni ma yabi bayanta......

Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*


Dedicated
*Rukayya Hassan Osman*😘

1⃣0⃣1⃣

💝💝💝 Cikin tsananin fargaba momy ta tura dakin deeni"

Abude yake saidai babu kowa afalon, cikin dakin ta nufa tana Raba ido"

Akasa ta hango deeni yana numfashi daker, da gudunta ta karasa tace shamsundeeni meya sameka?, baka da lfy ne"

Be iya amsawa ba, kokarin dagashi ta fara amman ta kasa juyawa tayi waje tana kururuwa"

Daddy ne ya fara fitowa sannan nafisa, ganin inda momy tabi yasa sukabi bayanta"

Shima daddy ganin jikin deeni hankalin daddy ya tashi sosai, me gadi yahau kira, juyawa yayi yakalli nafisa da tunda taga deeni ta fara kuka yace"

Kiramin me gadi"

Nafisa ta juya zata fita sukaci karo da Jamal yana dingisa kafa"

Kaikuma meka fito yi ? Ina zaka?

Kallon deeni yayi tare da fadin bakomai"

Toh maza ka koma daki"

Daidai lokacin me gadin ya shigo, acikin kankanin lokaci suka isa asibiti"

Kan gado suka daura deeni sannan suka fara duba shi"

Daga momy har daddy hankalin su atashe yake"

Ba'a dauki lokaci ba likitan ya fito ya nufi office dinshi"

Daddy ne yabi bayan shi

Cikin natsuwa likitan ya gayawa daddy deeni yana dauke da mummunan ciyon zuciya, wadda yayi karfi ajikin shi sosai"

Sannan ya shiga bashi shawaran cewa adaina bata masa rai, ayi kokarin duk abinda ya nuna yana so anemar mai"

Sannan ya kara da cewa zaman shi cikin damuwa na sati biyu zuciyar shi na iya bugawa"

Bayan daddy ya fito ya samu Momy da nafisa tsaye akan deeni, nafisa kuka kawai take"

Cikin tausayawa daddy ya kalli deeni bacci yake daman likitan yace sai safe zai tashi"

Washegari daddy yayiwa alhaji bashir waya ya sanar mai suna asibiti deeni babu lfy"

Cikin kankanin lokaci alhaji bashir ya iso tare da ummi"

Sosai hankalin ummi ya tashi domin ita tasan ciwon deeni be rasa nasaba da asma'u"

Har yanzun bacci yake be tashi ba, dan haka daddy ya kalli alhaji bashir yace.....

Muje gida akwai mgnr da zamuyi"

Nafisa kawai akabari agurin deeni"

****

Bayan sun isa gida afalon daddy suka zauna yayin da Jamal yake daya daga cikin dakunan dan haka duk abin da suke cewa yana jin su"

Daddy ne ya shiga gaya musu abun da likitan yace, sannan ya kara da cewa ya zamar mana dole mu nema mai lfy be kamata mubarshi ya kare rayuwa awahala ba, ina tsananin tausayawa rayuwar Shamsudeen inason ya zama mutum managarci banaso rayuwar shi ta kare ahaka, kuma insha Allahu zanyi korin nema masa abin da ransa ke so"

Cikin kuka ummi tace ninasan abinda yake damun auta, ya dauki son duniya ya daura akan wata yariya, nayi nayi yai hakuri yabar musu Amman yakiji, ubata yai mata aure tuntuni yakuma ce tirrr yaba shi aureta'
Bantaba ganin auta yaso wani Abu aduniya ba kamar yadda yaso asma'u"

Bacin raine kwance akan fuskan alhaji bashir daddy da momy ko hankalin su tashi yayi domin Susan cewa asma'un deeni itace matar jamal

Mikewa alhaji bashir yayi tare da fadin waye uban yariyar"

Shima daddy mikewa yayi tare da goya hannun shi abaya yace zancen waye mahaifin yariyar ai be taso ba, dafa alhaji bashir daddy yayi sannan yaci gaba da cewa....

Bashir kabarmin komai ahannuna nima ai shamsudeen d'ana ne dashi da Jamal duk daya ne, insha Allahu zan nemo mafita"

Duk waddan magan ganun Jamal naji Dan haka hankalin shi ya tashi, kasa zama yayi ya mike tsaye zufa yaji yana karyo mai, tunanin shi yaya zaiyi yaga Husna kusa dashi beso Husna tayi nisa dashi"

Yana cikin wannan tunanin yaji alhaji nashir na fadi"

Inda ace akwai yadda za'ayi musame ita yariyar asma'u ta zauna kusa dashi kona sati 1 ne wata kila ya dawo cikin haiyacin shi"

Cikin sauri momy ta mike tsaye fuskokin su ta kallah sannan ta fita afalon"

Shiko Jamal jiyayi kirjin shi ya buga daramm afili yace matar tawa?

Bazan yadda da wannan shawarar ba, bazata taba yuwuba"

Daha suka tashi kowa zuciyar shi da abinda yake sakawa"

Daddy da alhaji bashir ne suka koma asibiti amman tare da ummi, momy ko cewa tayi anjima zata zo"

Daker momy ta iyayin abinci akakai asibitin, Sanan ta zauna ta rafka tagumi"

Jamal ko ya kasa zaune ya kasa tsaye kano yake son zuwa amman yadda yakejin jikin shi bazai iya fitaba ji yake kamar yana tsami domin rabon shi da wanka tun ana gobe usman zai tafi"

Mikewa yayi ya nufi toilet cikin dibara yayi wankan ya fito"

Gyara jikin shi yaye tare da fesa turare sannan ya dauko manyan kaya ya saka tare da daura hula"

Tafe yake yana dingishi har ya isa dakin momy, ahankali ya tura kofar tare da sallama"

Cire tagumin momy tayi, sannan ta dago ta kalli Jamal"

Kyau taga yayi sosai, mikewa tayi tare da fadi Jamal wanka kayi ne?, meyasa bakajin mgn?

Momy jinayi ina tsami, dama usman ne kemin tun tafiyan shi kwana 2 kenan banyi wanka ba"

Ai da ka kirani namaka, Jamal ka daina wasa da lfyr ka, yanzun kuma da ka kaso kafa ka taho ina zaka"

Kai ya sosa sannan yace, fita zanyi momy, akwai wani aiki ne zan duba ko yana tafiya daidai, yau zan dawo insha Allahu"

Hmmm Jamal wanne aikine? Inace manyan ku sunsan halin da kake ciki?

Eh sun sani momy, wannan aikin idan ban duba ba za'a iya samun matsala ne"

Shiru momy tayi kamar baxatayi mgn ba zuwa can tace.......

Toh shi kenan Allah ya tsare ya dawo dakai lfy"

Ameen yace sannan ya mike ya fara tafiya, harya kai tsakiyan falon Momy tace......

Jamal wanne garine zaka?

Jam yayi kamar bazai yi mgn ba zuwa can yace Kano"

Kano momy ta tambaya sannan tace zonan Jamal"

Cikin sanyin jiki ya dawo ya zauna tare da sauke kansa kasa"

Saida momy ta gama kare mai kallo sannan tace.....

Jamal kace min kawai zaka wajen matar ka, ai bawai rabaku nayi ba, amman tunda hakane ka koma daki zansa dawo da ita"

Jikin shi sanyi yayi bazai iya musawa momy ba, amman hankalin shi nagun husna"

Har daki momy ta raka shi sannan tamai gargadi karya ya sake fitowa"

Momy bata koma asibitiba har dare, tunanin mgnr bashir take, tayaya matar da tai aure za'ace ta zauna gurin balagaggen namiji, hakika tana taya Jamal kishin matar Sa, kuma tana tausawa deeni"

Daddre ma kasa bacci tayi damuwa yayi mata yawa"

10:30pm daddy ya shigo har cikin dakin Momy, nafisa na biye dashi"

Guri ya samu ya zauna nafisa ko gaida Momy tayi sannan ta wuce dakin ta, tare da fadin bari naje nayi wanka"

Amsa mata momy tayi sannan ta maida hankalinta kan daddy"

Hularshi yacire ya aje agefe, sannan ya kalli Momy"

Kauda idonta tayi tare da fadin ya me jikin?

Yaji sauki, ya farka tunda rana, sai dai har yanzun kuka yake yi, kuma ya fada ma abinda ke damun sa yaki fada"

Shiru daddy yayi momy ma mikewa tayi tafara hada kayanta"

Muryan daddy taji yace......

Zauna mana akwai mgnr da zamuyi"

Cikin sauri momy ta aje kayan ta koma ta zauna"

Gyaran murya daddy yayi sannan yace......

Inason ki saurareni da kyau kuma ki fahimceni"

Wani irin kallo momy tamai sannan tace inajin ka"

Akan mgnr shamsudeen ne, nasani kin san cewa asma'u itace yariyar da shamsudeeni ke matukar so"

Cikin ido momy takalli daddy tace....

Ina jinka"

Cigaba daddy yayi da fadin dan haka nake ganin mezai hana shi Jamal ya hakura ya saketa.......

Mikewa momy tayi da sauri tare da fadin Alhaji kasan abin da kake fada kuwa, Asma'u fah matar Jamal ce, kuma ciki gareta, tayaya za'ace ya saketa shamsu ya aura, antaba haka"

Dakewa daddy yayi tare da fadin idan ma ba'ataba za'a fara akan su, dan hakan ne kadai mafita idan ba hakaba za'a iya rasa shamsundeen"

Alhaji wannan mgnr bazai yiwuba sam, dan Jamal nason matar shi, tunda nake da Jamal banta tunanin zaiso wani abuba kamar yadda yake son matar shi"

Gutun murmushi yayi sannan yace nidai abinda nake so dake kiyi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alheri"

Nifah alhaji sam ban amince ba, kama aje wanan zancen wlh bazai taba yiyuwa ba"

Daure fuska daddy yayi sannan yace....

Karki nemi yin jayayya dani, daga ke har Jamal akarkashina kuke, babu wadda ya isa nace ga abinda zaiyi yacemin ba haka ba, Jamal dana ne be isa yayi jayayya dani ba"

Mikewa momy tayi tare da ficewa tana fadin wannan ai zalinci ne"

Girgiza kai daddy yayi sannan ya mike ya nufi dakin Jamal"
Chapter 41 · 0% Book details