← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 44

Sashe 6

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shekara daya ta wuce da faruwar hakan, tun ana maganar ana kwashewa Hamisu albarka har aka manta, kunsan Haka Rai yake da mantuwa, itama Kuma se tayi aure nan a Kano shikenan se maganar ta sake mutuwa. Yayinda Kawu ke ta Fadi tashi wajen ganin ya nema na Kan shi, da adduar iyaye da yake yawan ziyarta Yana musu alkhairi dan ya goge laifin shi, ya kammalla karatun shi tas a BUK, ko aiki Bai tsaya nema ba ya cigaba da zuwa kasuwa, Allah ya nufe shi da siyar rumfa cikin kwari, ya Kuma Fara sayo Kaya Yana siyarwa, kwatsam se alkhairi da budi Suka ta ninkuwa se Kawu ya Zama Alhaji.

Da fari ya saya fili da ake yankawa anan Yan kaba Dake Kan babban titin Hadejia road dake cikin Kano, a ganin shi nan din zaiyi kusa da daukar Hanya zuwa Hadejia, Ashe akwai ranar da zaa wayi gari a samu su sauna, dakata and the rest! A hankali yake ginin saboda shi mutum ne da ku kunsan Yana da high taste, komai Yana son ace nashi yafi na kowa, komai so yake ace nashi is outstanding. Karku manta fa da halayen shi nasan farar mace, Yana nan ba Wai ya canja bane ba, shi ne dalilin da ya Hana shi aure, Yana ta zuba idanu yaga kyakyawa Kuma Fara sannan siririya. Haka abokan da makwabtan shi na Rumfa a kasuwa zasui ta tsokanar shi Fara ko mayya ce! Sede yayi dariya kawai yace musu shi fa Abu me kyau yake so Bai wani zurfafa ba.

Akwai wadanda ko me suke so se kaga Allah ya Basu akasin hakan, akwai Kuma wadanda Allah ke Basu dukkan abin da zuciyar su ta kwadaita masu. In that case Kawu na daya daga ciki, shiyasa yake ganin shi Mai sa'a ne shi. To mahaifiya mutuniyar jahar katsina ce, Amma idan Kika zauna da ita Zaki fahimci ba Yan asalin katsinar bane ba, in fact bama asalin Yan Nigeria bane ba, kawai dai sun hauro Kuma sun Jima har suka Fara aure da hayyayafa.

Haduwar Kawu da Adda kamar yadda muke Kiran ta, a kasuwa ne, Bayan an idar da sallar azahar ya dawo shago, Yana fadawa daya daga cikin yaran sun je su siya Masa abinci gidan abincin da yake ci yunwa yake ji, Dan shi baya ma cin abincin da ake kawowa kasuwa, standard din shi ya wuce haka. Yana nan zaune kamar ance ya dago idanun shi, Yana daga idanu se cikin na Adda wadda take tare da iyayenta da Kuma kanwar ta Anty hajara, ganin Yana kallon ta ya Kuma ki dauke idanun shi se ta dauke Kan ta tana nunawa Anty hajara shi da Baki tana Mata kus din se kallon ta yake, shi kuwa a lokacin ganin ta ya tafi da komai na shi, Jin shi, ganin shi hatta da sense of stimuli din shi Adda tayi nasarar tafiya da shi!

" Kai halilu"

Wanda ya Kira da halilu ya dube shi Yana amsawa tare da jiran umarni, ya nuna masa inda su Adda suke yace Masa ya tabbatar da ya dakko hankalin su sun shigo shagon nan siyayya! Aikuwa halilu yayi nasara, ku kunsan bakin Yan kasuwa, kusan sun iya kalami, Haka kuwa Suka shiga ya tarbe su cikin mutunci da Kuma girmamawa, aka nuna musu kaya, ita dai Adda se Bata Rai take, saboda idan zata dago idanun ta sau Gama kuwa zata Kama Kawu Yana satar kallon ta, hakan yasa ta takurawa su Alhajin KT akan suje wani shagon su duba, su kuwa sun ga kaya, unique ga Kuma shimfidar fuska har da ta tabarma, Dan kafin su Fara saya ya bayar an sayowa kowanne zundumemen lemon kwalba 50cl dinnan. Bayan sun Gama ciniki yayi musu massive discount suka Masa sallama dan tafiya, hade da sake mishi godiya bisa karamcin shi, tare Kuma da Yi masa alkawarin dawowa wani lokacin idan bukatar hakan ta tashi! Ita dai Adda Babu bakin magana, daga harara se cone baki.

Kawu yaga da gaske tafiya zasuyi, Kuma tafiyar su na nufin sede yayi tunanin wannan kyakyawar budurwa dukda ma yasan sunan ta, yaji Maman ta na fadin

" Asiya ga shadda irin wadda Kika ce kina so, ba Zaki dauka ba?"

"Kalla kiga lace dinnan yayi kyau Asiya?"

A Haka ya fahimci sunan ta, Dan Haka yayi ta maza ya tari Alhajin KT ya durkusa har kasa tare da fada Masa abinda yake zuciyar shi

" Baba Naga daya daga cikin yaran ka,  Asiya Kuma naji Ina son ta, idan ka amince ka bani dama Ina son na aureta idan ta amince idan Kuma bakai Mata miji ba"

Kafin wani a cikin su yayi magana tuni Adda tace

"Ni gaskiya a'a, bana son shi!"

Aikuwa iyayen duka biyu sukai kanta da fada, Ina ruwanta zata saka Baki a maganar manya, waye waye! Haka dai tayi shiru tana Kara hade fuska,  Anty hajara nata murmushi a gefe. Alhajin KT ya dubi Kawu yace

" Zan Yi shawara duk yadda ake ciki zaka ji aike na!"

Idan Allah yayi wannan da wannan zasu kasance karkashin Inuwar aure to lallai lallai, duk kiyayya, duk tashin hankali sannan duk wani abu se wannan auren anyi! Haka suka tafi bayan yayi kokarin sake musu alkhairi Amma Alhajin KT ya dakatar da shi, a'a ranar yaran shagon Suka ta Masa tsiya suna zolayar shi, tare da zuzuta how much ya iya zabe, fada suke suna karawa Adda fa tayi karshe ce, shi Kuma Yana murmushi Yana Jin Babu ya shi.

A bangaren su Adda sun koma katsina lafiya, mahaifin ta bayan kwana biyu ya tada mutane har biyu daya yaje Hadejia ya gano Masa su waye dangin da Yar shi zata shiga, dayan Kuma ya tsaya a Kano cikin kasuwa Dan kuwa anan Kawu yafi Zama Kuma nan ce Hulda da mutane. Sede mu ce madalla da iyaye na gari, Allahu ya saka musu da mafificin alkhairi!

Sati daya ya samu kyakyawan feedback Akan komai da ya danganci Kawu, hakan yasa yayi naam da shi ya Kuma samu babbar diyar ta shi da mahaifiyar ta, bayan addu'oi yace

" Kisa a ran ki bazan Miki Dole ba, Amma musulinci ya bani damar Yi Miki zabi, to Ni na zaba Miki Hamisu ki aure shi, idan Kuma baiyi Miki ba har bayan Kun Yi magana, ko ki fahimci wani nakasu a addinin shi ko zamantakewar shi, Ina fata ki sanar Dani se a fasa..."

Wannan fasawar da yace ta dadawa Adda, zuciyar ta tayi haske Dan a ganin ta so ake a cusa Mata auren da Bata so. Haka Alhajin KT ya sake aike ma Kawu sakon Fara nema through wani abokin shi dake nan sabon gari market. Zuwan farko yadda ta tarbe shi duk se yaji Babu dadi, Amma yadda yake son ta se ya kasa hakura, zuwa biyu, zuwa uku zuwa hudu, Adda se ta amince saboda yadda ya damu da ita, yadda yake kuka da ita, yawan kyauta da nagartattun halayen shi yasa ta amince. Wata bakwai daga lokacin se ga Adda a dakin Kawu. Anyi sure cikin mutunci da kyautata wa juna.

Dukda Kawu ya kasance Dan kasuwa ne, to Amma wannan bokon da yayi har zuwa master's level ya saka yake shaawar ganin mace tayi Boko. Shiyasa bayan auren Adda da wata biyar wani abokin kasuwancin shi Dake matsayin Nurse a asibitin murtala yake fada masa, ai school of nursing Kano sun Fara Saida form, idan Yana da candidate ya kawo, bayan dogon tunani kawu ya samu Adda ya fada Mata ta kawo ssce din ta zai nema Mata makaranta. Lokacin da ta san school of nursing ne kamar zata maida Kawu ciki saboda murna, ita dai suna birgeta idan ta gan su a asibiti, wannan abun da Kawu yayi Mata ya sake zurfafa son shi cikin zuciyar ta.

Ko da ta Fara zuwa makaranta, Bayan wata shida akai intro cikin hukuncin Allah ta samu nasara, lokacin da Suka Zama cikakkun student nurses se ta Fara wani tunani cikin zuciyar ta, school of nursing ba wajen wasan yaro bace ba, idan tayi Wasa ta samu ciki shikenan zaa kore ta, Dan Haka a boye da little knowledge din ta na family health ta saya pills take Sha, kusan shi ne kuskuren farko da tayi, Amma wani lokacin ta kance hakan ba kuskure bane ba.

Babu haihuwa Babu labarin ta, shi Kuma Kawu Yana son Yara, lokacin ta Yi shekara uku suna Shirin yin hospital final, a wannan lokacin ya hadu da Mama! Idan aka hada maka Mama da Kuma Adda you'll be confused to who's more beautiful, dukkan su farare ne Kuma kyawawa, sirara masu diri me kyau. Mama Yar Yola ce, ita din I'm not sure of yadda Suka hadu da Kawu Amma dai yazo yace da Adda zaiyi aure, lokacin tana Shirin yin final nursing qualifying exams.

BINTUN BATUUL na kudi me...
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_

Ayshatuuu

Top-notch season 3

007

Da farko dai bansan me mutane suke ji ba idan sun tanka hallitar ka, bansan pleasure din da suke driving ko kuma wani satisfaction da suke samu daga hakan ba, na Kan Dade Ina tunanin Ina ruwan mutane da hallitar mu, those shape, complexion, figure matters? Akwai wani alfarma da kyawawa suke samu a rayuwa? Akwai wani favor ko afuwa da rayuwa take bawa kyakyawawa? Nayi tunanin Allah cewa yayi Yana amfani da zuciya da Kuma ayyuka, Amma baya la'akari da suffar bawan shi! To me yasa mutane Basu iya dauke idanun su akan hakan? Me yasa se sunce Kinga yadda kikai kiba? Kai wannan kiba ce da ita! Wannan siririya ce! Tab Kinga kumatun ki? Ina ruwan ku? Meye matsalar ku? Jikin ku ne? Kunsan yadda muke ji kuwa?

Nasan zuwa yanzun Kun fahimci wacece ni ko da kuwa kadan ne daga ciki, na rayu cikin tsoro, fargaba da kuma tantama da kokonto Haka na rayu, nasan da dama akwai Wanda suke fuskantar abun da nake fuskanta ko Wanda ya fi hakan
.

Bayan haihuwar mu, jikin Adda yayi sauki aka sallamo mu, kamar kowa Nima aka rada min Fatima Amma ana Kira na da Bintu, sati daya da haihuwar mu Adda ta dubi Mamaa dake min wanka tace
Chapter 6 · 0% Book details