← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 44

Sashe 16

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Haka ta sauke wayar ta nufi sauran directors din ta fada musu zataj canceling flight din ta zuwa Kano saboda rashin lafiya ta, dukkan su sukai Mata addua tare da tambayar ta ko tana bukatar taimakon su, ta girgiza Kai tare da musu sallama ta tafi yankan ticket, Allah ya taimaka ta samu, bayan ta zauna a lounge ta Fara Kiran Kawu amma bai dauka ba, se ta Kira Yaya Auwal da suke tare da kawu a kasuwa, shi ya kaiwa kawu wayar bayan sun gaida ya tambaye ta lafiya? Saboda yadda yaji muryar ta, cikin rashin Jin Dadi tace

" Bintu ba tada lafiya sun Kira Ni daga makaranta, yanzun Haka ma can Zan wuce!"

"Me ya same ta?"

Ya tambaya Haka kurum yaji gaban shi ya fada

"Ban sani ba yallabai, Amma dai jiki na na bani she's definitely in critical condition! Daga yadda vice din su ke magana!"

Ya Kara sakin salati Yana tambayar ta ko ta samu tickets din? Tace ta samu amma duk yadda suke ciki zata Kira shi a waya!

I was so busy wallahi yau dinnan, so nace Bari dai muyi taba ka lashe!
[1/3, 20:28] Maman: 017

Tunda Adda take bata taba ganin doguwar tafiya irij daga Abuja zuwa Niger ba, duk da a zahiri tafiyar ba wata bace ba Amma saboda how anxious and eager she was taje taga halin da Bintu ke ciki yasa duk ta gaji ta koma kosa tare da ganin kamar a mota take tafe ba jirgi ba. Addua kala kala Babu wadda batai ba akan Allah yasa Bintu kada ta mutu, Allah Kuma yasa ba wani mummunan abun bane ba ya samu diyar tata ba, tayi hasashen duk wani possible rashin lafiya da Bintu zata iya Yi cikin kankanin lokaci, Amma ko kadan Bata kawo Bintu zata iya Shan Dettol ba Dan ta dauki rayuwar ta.

Ko da ta isa cab ta samu Wanda ya Kai ya har asibitin bayan tayi communicating da vice ya bata address din asibitin da suke. Tana sauka gaban katon building din da aka rubuta Accident and emergency department! Ta sake Kiran shi tare da sanar Masa isowar ta, Babu jimawa se ga shi yazo, ba wani gaisawar kirki sukai sosae ba, saboda kana kallon ta kasan ba a nutse take ba. Suna shiga an fita da ni zuwa hoton makogaro da Kuma na ciki saboda a duba ko an samu chemical erosion a wuraren da Dettol din ya taba. Kafin na dawo Suka samu Zama ita da principal din

" Mun taso ki ko?"

Adda ta girgiza Kai cikin damuwa tace

" Ai ba yadda zaayi, Amma me ya same ta"

Principal ta gyara zaman ta, ta Fara ma Adda bayanin dukkan abin da ya faru, Adda tayi shiru in a total and complete shock. Se da tayi wajen minti na hudu bakin ta a rufe da hannun ta sannan ta sauke hannun tace da principal

" How's she? Ya jikin nata?"

Kafin ma principal din ta Bata amsa aka sake turo ni akan wannan gadon na asibiti Mai Kama da stretcher, tayi saurin mikewa tare da nufo ni, tana zuwa ta rike hannaye na, lokaci daya fuskata ta zabge nayi wani kuyas da Ni. A hankali na bude Baki nace

" Adda sannu da zuwa!"

Ta kasa magana kawai Naga tana kuka, se na lumshe idanu na Ina Jin wani irin radadi cikin zuciya ta, ya akai ban samu na mutu ba, ya akai Haka? Hawaye ya gangaro min daga rufaffun idanu na zuwa kunci na, abun bakin cikin bayan ban mutu ba, ban Kuma Yi nasarar cutar da ki na ba, Dan tun a radiology department din, radiographer yace da Doctor di na babu matsala, Dan mild erosion ne Wanda in no time zai warke da magunguna. Bayan na koma gado ya rage daga ni se Adda a daki, wadda ta Gama waya da kawu tana fada Masa jikin nawa da sauki

" Bintu fada min me ya ke damun ki da har kikai kokarin kashe Kan ki"

Nayi shiru bance komai ba, why is she even asking Bayan Bata taba tambayata ko Ina lafiya ba, ko Kuma tace min kibar dake jiki na ba komai bace ba, it's Allah's way of making me unique and different, Amma se ta Bari ake musguna min akan laifin da bani da shi, laifin da ba nawa ba, tana kallo Bata Hana ba, in fact kamar kunyar nuna ni take matsayin diyar ta.

"Bintu talk to me! Kina da uwar da ta wuce ni? Ki fada min abin da yake damun ki"

Nanma ko bude idanu na banyi ba, zuciya ta tayi nisa wajen hasaso min wata rayuwa ta daban, da duk bani da kiba, da duk ba mummuna bace ba da BashPrince00 Bai guje ni ba, da Samiha batayi betraying di na ba. Har Adda ta Gama zamanta likitan ya shigo, Ina Jin shi Yana Mata bayanin depression ke damu na, ya Kuma kamata su nema min therapy session idan ba Haka ba to watarana zasu ga na kashe Kai na tun da na Fara gwadawa kuwa! Hankalin Adda ya sake tashi, tayi ta kuka kunsan dama nace muku ita saurin kuka ne da ita, Amma kunsan menene, zuciya ta ko gezau na tausayin Adda ba tai ba, Ni buri na ma ta fita a dakin na hango wani syringe da Zan bula jijiya ta da shi, nasan da zarar jini ya fita da yawa a jiki na to Zan mutu kowa ya huta, Nima na huta da bakin cikin da nake ciki.

Zuwa la'asar kawu ya karaso, anyi anyi na karba ruwa ko wani Abu Amma fur naki, bana ma magana balle wani ya saka ran Zan saurare shi, tun Adda na lallaba ni har katsinancin nata ya Mike ta Fara min masifa, nan ma dai Babu mafita, se kawai ta samu guri can gefe ta zauna ta zubawa sarautar Allah idanu, ta barni nayi duk abin da nake ganin daidai ne. Zuwan kawu ya saka ta Jin dadi a zuciyar ta, tare da ganin idan ita na Raina ta ai shi zanyi magana. Amma shima shiru me da ya takura ni kawai se na Fara kuka. Duk me ya janyo hakan? Duk me yasa na Zama hakan saboda bakin mutane, saboda mutane Basu gajiya da fadar abin da Bai kamata su fada ba, saboda mutane suna Shiga sabgar da Bata su ba!

A Haka nayi kwana biyu, cikin hukuncin Allah na samu sauki, Kuma a ranar na ke paper ta ta karshe ta waec, Dan Haka daga asibiti naje na rubuta, na koma hostel hada Kaya na. Babu Wanda na kula se de amsa da sauki, Ina Gama hada Kaya ko graduation ban tsaya ba muka tafi Kano. Muna zuwa na yiwa Adda da kawu sannu sannan na shige daki na kulle!

***

Komai da ya daganci Zainab se da ya kasance a tafin hannun Imam, Yana da network of information a cikin campus yadda Baku tunani, Amma saa daya da akai shi ne Yana da kokari, a ajin su bashi da na biyu, shiyasa ake overlooking rashin Jin shi.

Zainab ta tashi da wurwuri saboda tana son wucewa school, tayi wanka ta samu noodle da tea taci sannan ta shirya cikin olive green Abaya me adon Baki a jiki, ta hada books din ta tsaf sannan ta dauki Jakar ta fito, tana tafe tana waya da jaddar ta wadda ke fada Mata yadda tayi kewar ta, da Kuma tambayar ta har wani lokaci ta dauka Zama a wannan kasar turawan. Zuciyar ta fes saboda a watan da ya gaba ta ba karamin takura Mata Imam yayi ba, har karamin hauka ta so tayi Amma shi ko a jikin shi, jiya dai tayi Masa warning akan idan ya sake biyo ta zata Kai shi Kara student affairs, to a tunanin ta yau ba zata gan shi ba.

Zainab tayi murmushi daidai fitowar ta da ta daga gate din apartment din nasu, wannan murmushin da tayi a daidai Kan idanun Imam dake zaune cikin mota Yana kallon kofar da zata shigar da Kai in anticipation of her. Yayi saurin balle murfin motar ya fito, lokacin ta Fara takowa Dan fita Amma Kuma hankalin ta baya Kan shi, Bata ma lura da wanzuwar wani bawa a wajen ba, magana kawai take da jaddar ta wadda ke saka ta dariya da ba kasafai take ba se idan suna wayar da jadda. Dariyar da take ya saka shi shagala Yana kallon ta tare da kiyasto abubuwan da dama Wanda Baki ba zai iya fada ba se zuciya. Tana sauke wayar ta Fara kokarin tafiya, anan be yayi saurin Shan gaban ta Yana sakar Mata wani killer smile, ta dauke kan ta, tare da kokarin rabewa ta gefen shi ta wuce Amma Bai Bata wannan damar ba yace

" Haba Zainab, tun 6am nake zaune Ina jiran ki sannan kizo ki wuce. At least ko hi Kya cemin"

Ta kalle shi ya girgiza Kai tana kokarin sake wucewa Amma Dake Imam Imam ne se da yasan yadda akai yayi Mata magana har Kuma karshe ta shiga motar shi. Har department din ta, Kai har lecture hall ya Kai ta, se da ta zauna gurin ta ya samu wani yaron shi ya bashi Amana kafin ya tafi bayan ya Gaya Mata zaiyi missing din ta sosae. Kawai se ta samu kanta da dariya, saboda da gaske kawai kallon me tabin hankali take mishi. Tana Gama lecture ta fita Dan zuwa library kamar yadda ta saba Amma ga tsananin mamakin Zainab, Imam na kofar aji Yana jiran ta, wani irin yanayi taji har tace Masa

" Baka da lecture ne?"

Ya girgiza Kai yace

" Ina da akwai of course.."

"Then why are you here?"

Ta tambaya curiously tare da kallon shi da idanun ta masu sheki. Se kawai ya duburburce ya fara stammering. Ganin Haka ta wuce abin ta ta bar shi tsaye, Amma kafin ta karasa ya samu shortcut ya karasa Yana tsaye kofar library Yana jiran karasowar ta, tana isowa taja ta tsaya tace

" Kai aljani ne? You're stalking me I'll report you!"
Chapter 16 · 0% Book details