← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi musu fada sosae sannan ta bar su ba tare da ta tilasta musu su maida auren su ba, hakan da tayi musu tana son taga gudun ruwan su ne. Bayan fitar ta ya dube Samiha da tayi shiru maganganun sirikar tata na sinking cikin Kanta, itama ba Haka taso ba, ba Haka ta tsara rayuwar auren ta ya kasance ba, sede Bata da tsimi balle Kuma dubara. A hankali ta Mike Dan tafiya dakin ta, Bashir yayi saurin bin Bayan ta yace

"Na janye sakin da nayi Miki! Ina fatan mu zauna lafiya!"

Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba tare da ta juyo ba ta wuce dakin ta. Wayar ta ta dauka ta Kira aminiyar ta Hafsatou Bala, Bayan sun gaisa Hafsatou tace

" Me ya samu muryar ki naji duk a shake?"

"Hafsatou could you believe Bashir yau ya bude bakin shi yace Wai naje gidan mu ya sake bi!"

"Ke Bari Dan Allah Samiha! Wannan tatsuniya kike karanta min ba dai Bashir ba"

Hafsatou mamakin wannan magana take har cikin ranta

" Nima da ya fada Hafsatou ban yadda ba Amma wallahi da gaske ne!"

Se ta Fara salati kafin Kuma ta nutsu tace

"Kina Ina yanzun? Kada dai har kin tafi gidan Mami?"

Ta girgiza Kai tana kallon suitcase din ta wadda tayi dam da kaya, tace

" Ammin shi tazo, Bayan ta tafi ya dawo Dani. Amma nasan tunda aka Fara haka wata Rana zaa sake yi. So ya zanyi? Ki bani shawara"

Tayi shiru tana tunani kullum tana so tayi Mata magana Amma ta rasa ta inda zata Fara , Amma yau tace to bari ta gwada saar ta

"Ki saurare ni Samiha, nasan kina tunanin why is your matrimonial home always in dispute. Baki tunanin hakkin Bintu Ginsau ne?"

Samiha tayi shiru tana son ta tuna wacece Bintu Ginsau ma? Se kuwan ta tuna a take komai da ya faru yayi clicking kanta tace

" Sure BinGin! To Amma Hafsatou nayi Mata laifi ne?"

"Kinyi mana, Zaki ga kamar ba laifi kikai ba but morally abin da kike Bai kamata ba"

***

A tare suka tafi asibiti shi da Safiyya da Kuma Iman ita zeeyzeey tana makaranta. Tunda suka dauki hanya yake bawa Ummaah labarin Bintu, tunda take da shi, Bai taba ko da Wasa ya Bata labarin wata mace ba, Wai da sunan kawa ko wani abu se yau. Hakan yasa ta bashi dukkan hankalin ta tana sauraren shi

" Ummaah ta Yaya kawai Dan danka Yana da kiba, body figure din shi ko Kuma yayi Baki se ka tsane Shi Ummaah, what's beauty idan ba trial ba"

Safiyya na murmushi tace

" Amma banji Dadi ba, a Ina ka santa? What's her name?"

Ba tare da ya fahimci yanayin yadda uwar tashi ta fassara zancen shi ba yace

" Student di na ce, sunan ta Fatima Bintu!"

Ta gyada Kai tace

" Allah sarki!"

Haka ya cigaba da bata labarin Bintu ba tare da ya ma fahimci yanayin hakan ba. A zuciyar Safiyya tamkar an haska saboda dadi, yau danta ne take zancen wata yarinya.

Alhaji Gidado na kwance a gadon da aka bashi na asibiti, Dan ma ance a Dan fita a bashi waje Amma yadda yaran shi da Kuma yaran Yan uwan shi Suka cika gurin. A hankali Suka tako Yana rike da Jakar mahaifiyar ta shi, dayan hannun shi Kuma Iman ta kankame hannun. Kowa da ke asibitin yasan tabbas an kwantar da babban mutum saboda yadda wannan family din suka taru Babu kakkautawa.

Aunties din shi ya gaggaisar sannan ya wuce can inda mazan suke ya zauna suka gagaggaisa, Bayan wajen awa Suka shiga suka duba shi sannan suka fito. Zasu tafi Minal wata cousin din shi ta karaso da sauri tana fadin

" Hamma Akram Dan Allah nazo mu tafi ka sauke ni zanyi shopping!"

Ya tsaya sannan ya dube ta yace

" Bata nan zamu wuce ba!"

Daga Haka ya cigaba da tafiya shi da Iman da ke tsalle tsalle, yayin da ita kuma Safiyya se lokacin zata taho ta tsaya gaisawa da wadanda suka kwana biyu Basu gaisa ba. Suna zuwa gida abinci ya Fara ci sannan yayi sallah, kamar kullum ya Yi dukkan routine din Shi kafin kwanciya sannan ya zo kwanciyar. Se Kuma Bintu ta Fado masa, ko me take Yi a yanzun?ya ayyana cikin ran shi, ya cigaba da Dan tunanin how much of pains da yake tunanin tayi enduring ita kadai cikin rayuwar ta.

A bangaren na nayi karatu sosae, dukda na kasance Haka nake Amma wannan karatun se nake ji kamar I owe it to someone, naji Ina son na fidda shi kunya ta hanyar cinye test dinnan. Dan Haka babu Wasa na dukufa ni ce har dayan dare kafin na je kitchen na tafasa slimming tea di na na zubo cikin mug, Ina karatu Ina Sha har na shanye tas kafin na kuskuro Baki na sannan na kwanta, Babu jimawa Bayan na Gama duk tunanin peace din da ya Fara ziyartar rayuwa ta kwana biyu, Ina ayyana dalilin hakan se Kuma na tuna irin gudunmawar da Akram ya bawa rayuwa ta, for unknown reason se kawai na Fara murmushi Ina Jin wani nishadi me dadi Yana shiga ta. Mamaki sosae ya Kama ni na yadda lokaci daya nake Jin kamar rayuwa ta tana canjawa. A hankali dai bacci ya tafi dani.

Washegari na tashi da wani irin kuzari, for the first time naji na tashi da annashuwa da Kuma walwalar. What has gotten into you Bintu? Haka na dinga tambayar Kai na lokacin da nake kitchen Ina hada meaty spaghetti da akai order. Bayan na kammalla nayi wanka naci abinci kamar kullum na Sha abubuwan da nake ganin zasu saka kiba ta ta ragu na Zama yadda nake so. Bayan na shirya na sako wani atamfa me kyau da Mamaa ta Dinka Mana, normally duk kayan zuwa makaranta ta materials ne Amma yau se naji Ina son na saka wani kayan daban. Bayan na saka na Fara kokarin daura Dan kwali se na kasa, Batuul dake shafa Mai akan gado tace

" Haka saurayi kikai Naga har wani rawar Kai kike"

Ban ce Mata komai ba balle na Bata amsa, a karshe na samu na daura dankwalin na dakko wani veil da ya shiga da atamfar na yafa se naji dukka I'm uncomfortable. Nan ma Batuul ta Fara dariya tana fadin

" Wallahi gwara ki saka hijabin ki kinfi kyau, Kinga yadda tumbin ki ya fito kuwa?"

Na juya a fusace Ina kallon ta, ta karasa yafa karamin veil din ta ta fice ta barni tsaye Ina harar ta, se Kuma naji I'm demoralized bani da confidence din fita da shi, kilan idan na fita da shi mutane suyi tayi min dariya nayi wani irin, cikin sauri na maida shi wardrobe sannan na dauki hijab na saka na dauki jaka ta na fita, dakin Mamaa naje nayi Mata sallama sannan naje dakin Adda wadda ta Gama shiryawa alamar fita zatai, tace

" Muje na sauke ki. Kin dai ki Suleiman ko? Naga Wanda Zaki aura ai. Har ni zance Miki kiyi Abu ki kiyi"

Wani irin yanayi naji marar Dadi nace

" Adda ya zanyi? Kema kin San Suleiman baya so na, so kike na dinga cusa Kai na wajen shi?"

Ta fusata zata Kai min hannu nayi saurin matsawa Wai na Yi Mata rashin kunya, har Ina mayar Mata magana. Na Bata hakuri sannan nabi Bayan ta zuciya ta kamar zata fito. Batuul na gaba ni Kuma Ina baya muna tafe suna Hira wadda kusan dukka labarin saurayin ta take bawa Addar ita Kuma tana ta saurare tare da murmushi.

A school suka sauke ni, na Mata godiya sannan na tafi class, gaba daya mood di na ya baci, yadda na tashi da safe cikin farin ciki ne da zumudin zuaa makaranta amma a yanzun se naji duk Raina ya baci. Bayan zuhr aka zo yin test din, yau Bai zo inda nake ba Wanda yasa naji rashin Dadi, bai Kuma tambaye nu ko naci abinci ba kamar yadda ya saba, duk se naji kamar an kukkunce min knots din Kai na. Fuskar shi Babu annuri ko kadan ni Kuma saboda zakewa Wai se nake Jin Babu dadi, guys imagine my audacity! Haka ya rarraba question papers din ko kallo na baiyi ba da yazo wajen bani, duk se naji idanuna sun cicciko da kwalla, ko dai shima ya gaji Dani he find me boring and unattractive again? Me yasa bani da sa'a ne cikin rayuwa ta? BashPrince00 ma da ya Fara so na he chose Samiha over me! Kuma a take se na tuna samihan, I'm sure tana can tana farin ciki a rayuwar ta, wannan tunanin sun da nayi se kawai na Fara kuka a hankali Wanda ko mutum na kusa dani ba lallai ya fahimci hakan ba.

Duk abinda nake Ashe Yana kallona, ban gaya muku how observant gayen nan yake ba ko? To shi mutum ne me kula da Kuma lura. Har aka kammalla test dinnan banyi cikin dadin Rai ba Bai Kuma kula ni ba, sannan na kasa fahimtar ma abin da yake tunani daga fuskar shi, Dan kuwa expression din shi was very blank!

Ayi hakuri a Kuma Kara hakuri... we're almost there. Thank you for hanging around 😊❤️😘

Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 036

Ko da Muka kammalla test din nayi tunanin kamar yadda aka Saba zai bimu ne one on one ya karba, Amma se yace Mana duk wanda ya Gama kawai ya kife sheet din ya fita, the class is over. Haka kuwan nayi na goge fuska ta sannan na sake dage hijab di na ya rufe kusan rabin fuskata kafin na fita, duk tunani na zaice na tsaya Amma shiru kake ji baice min ba, hakan ya sake tunzura ni naji kamar irin I'm worthless dinnan, na Fara tunanin ko dai shima he finds me boring kamar yadda kowa yake gani.
Chapter 34 · 0% Book details