← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 44

Sashe 5

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da zaa yiwa Adda Sajida kishiya, akwai wani Abu da ta yiwa mijin ta Wanda se da ta dawo gida tayi zaman wata data, daga yace zaiyi aure Adda aka Fara throwing tantrums, zagi ta uwa ta uba, kishi dai na hauka, mutuminnan ya dauke idanun shi, lokacin harvest yayi ya kawo amfanin gona gida, mutuniyar ku tace to ita fa anan zatai ramuwa, ta dauki dawa ta hada da alkama, ridi da shinkafa, Kai Adda Sajida Bata da kirki, Dole se da ta dawo gida Amma Kuma mijin Bai sake ta ba, cewa yayi ta fitar Masa a gida ya daina ganin ta har se ya huce, to se da akai biki da sati uku amaryar har ta Zama Yar gari kafin uwargida Adda Sajida ta koma. To kunga hakan Bai Hana shi auren ba, se ma darajar ta da ya rage, Saboda maza basa uzuri akan kishi ko kada.

Abin da ya karya lagon Adda shi ne zuwan Alhajin KT da Kuma Iya wato mahaifiyar ta, kunsan yadda iyayen da suke, mutane ne masu Kara da Kuma dattako, dukda a yanzun Ina ganin abin odd na goyawa mijin yata baya bayan nasan shi ne bashi da gaskiya, gaskiya bazan iya ba, dukda ance Wai hakan shi ne siya ma Dan naka daraja a gidan aure, this is all by the way!

Alhajin KT da Iya sun Yi kokari matuka wajen tausar Adda, har ta samu ta Dan dangana Amma cikin zuciyar ta Bata tunanin rift din da aka samu tsakanin ta da Kawu Abu ne da zai cike, dadin dadawar bacin ran ta se Alhajin KT yayi uwa ya Kuma Yi makarbiya wajen ganin aurennan ya tafi, a karshe ma dai Wai shi ne walliyin Mamaa, ciwo goma da ashirin kenan!

Aka kawo amarya dakin ta, kowa tausar Adda yake, tare da nuna Mata yadda zatai ta kwaci Kan ta, Amma da se idan ta rike wannan girman nata, idan ta Bari kuwa to zata kwace ita Kuma ta Zama Yar kallo, wasu Suka ce Mata duk namiji se yayi daukin amarya, se yayi rawar Kai se Kuma yayi falli, Amma idan uwargida tayi hakuri da zarar gishiri ya ishi Kan kaza to fa ungulu zata koma gidan ta na tsamiya, ai dama ance tsohuwar Zuma ita ke magani. (A soothing message to uwargidas' I'm rooting for you!)

Dama bacci Kam dai rabi da rabi akai, kusan kwana tayi tana karatu Dan ya debe Mata kewa, Amma dukda haka amidst karatun zata kwanta tayi kuka ta godewa Allah, a Haka safiya tayi ta Mike jiki a sanyaye tayi wanka tayi sallah sannan kuma ta wuce kitchen ta daura sassaukan abinci kamar yadda Iya ta Nanata mata, tace Mata lallai lallai ta daure tayi girki ta Bata, shi ne girman, tana kammallawa ta koma daki ta zura fararen uniform din ta da suka Sha guga suka daukar idanu, a karshen hannun akwai lanyard na nuna ita din student ce, ta daura katon hijab akai da ya rufe Mata uniform din sannan ta dauki jakar ta Dan ficewa, sede tana kokarin kulle kofar parlon ta se ga Kawu ya nufo ta, da ta kalle shi se taga kamar Yana murmushi, kamar wani annuri ne ke exuding daga fuskar ta shi, taji kamar ta shake wuyan shi kowa ya huta, Amma se ta Fara Nanata auziyya Dan korar shaidan, ya karaso tare da karbar makullin da kulle Mata saboda battling da take tayi da shi ta kasa kullewa, saboda hankalin ta da Kuma tunanin ta dukka baya gurin, bayan ya rufe dakin ya Mika Mata makullin tare da amsa gaisuwar da ta Masa ciki ciki. Duk yadda Taki se da ya Kai ta har makaranta kamar yadda ya saba, sannan da ta tashi yaje ya dakko ta, lokacin da ta dawo Mamaa ta kammalla abinci, ta gyare gidan tsaf, tana daki tana sake sake. Se dare suka hadu yayi musu nasiha sosae tare da Yi musu alkawarin adalci. Da farko Adda Bata Shiga harkar Mamaa, ko abinci tayi se taki ci, Amma hakan Bai Hana Mamaa cigaba da kyautata Mata ba, a Haka har Adda bayan wajen watanni hudu ta fahimci sincerity din ta Kuma ga laulayi da ta Fara me ban wahala, Haka Adda ta yada makaman ta ta rungume ta, shikenan zaman lafiya se ya wanzu a gidan. Bayan watanni Adda ta Gama makaranta ta Kuma samu aiki cikin asibitin murtala Muhammad dake cikin kano, Fara zuwan ta Babu jimawa itama se ga ciki ya bayyana a jikin ta, lokacin na Mamaa wata wajen takwas. Kawu yayi murna kamar zai zauce, Mamaa ta Haifa mace aka saka Mata suna Fatima ana Kiran ta Haka, Bayan watanni Adda ma ta haihu aka saka Mata Fadima.

Kunsan yadda Kawu ya dinga saka Mana suna Fatima se Dana Fara tunanin Anya kuwa bamu Hadi da shi'a? Yo Ina dalili mu kusan takwas suna daya, Fatima, Fadima, Sajida, Adawiyya, Zuhriyya, Zuhra, Zahra, Batuul da Kuma ni Bintu! Mu Tara kenan fa! To Haka sunan mu suke se maza guda uku Wanda yasa Auwal, Sani da Kuma Salis. Gidan mu kamar su kusan daya, farare Kuma kyawawa, sirara, dogaye. Yadda iyayen su Mata suke Haka Suma suke, kunsan it can't be a coincidence Dan akwai gidan da zakaje kaga kowa ya nada kyau, to gidan mu kenan, har alfahari suke da wannan kyan nasu!

Bayan set din su Fatima da Fadima, se Kuma Mamaa ta Haifa Adda Sajida ita Kuma Adda ta haifa Yaya wato Auwal, tana aikin ta yayinda Mamaa ita ke zaune a gida, tamkar ministan cikin gida, komai indai na cikin gida ne to kada ma kaje wajen Adda kawai Mamaa ce komai. Mamaa ta sake haifan Yaya Adawiyya, ta sake haifan Yaya Zuhriyya se lokacin ita Kuma Adda ta haifa Yaya Sani, Mamaa ta haifi Zuhra, se Kuma sukai goyon Yaya Salis Wanda shi ne namiji kadai wajen Mamaa, Adda Kuma ta Haifa Zahra. Shikenan se haihuwan ya tsaya kamar daukewar ruwa, har su Yaya Zahra sukai shekara biyar abin da baa taba Yi ba a gidan, a yi shekara biyar Babu sabon jariri gidan. Lokacin Adda ta Gama BNSc din ta tana kokarin Fara masters se kawai ciki ya bullo a jikin ta, ta kance wannan cikin ba karamin katsalandan yayi Mata ba, saboda tana kokarin pursuing dream din ta se ga ciki ya fito, to ya zatayi? Haka ta hakura ta jira zuwa lokacin da zata haife abin da ke ciki.

Ita Bata faye Shan wuya idan tana da ciki ba, Amma wannan karon Kam se cikin yazo da sabon salo, tun kafin first trimester ya wuce se ga bump ya fito Dan Haka kowa ya Fara tunanin kilan twin gestation ne, wato Yan biyu amma duk lokacin da taje hoton cikin se ya nuna guda daya ake gani, Dan Haka komai da aka siya na Batuul ne, Babu Wanda yasan da zuwa na saboda tun a ciki Batuul ta danne ni, ita kadai ake iya visualizing. Se da ta Fara nakuda aka kaita asibiti, tuntuni sunyi da Kawu wannan karon ma Fatima ce Babu fashi, se Yaya Fatima ta ce to dama bamu da Batuul Dan Haka se ace Mata Batuul. Wannan shi ne Shirin su, Bayan an haife ta Kuma se wani ciwo ya turnuke, ko da aka zo examination se akaji alamar wani Babyn Amma Kuma presenting part din ba Kai bane ba, maimakon a barta ta haihu se aka bada shawarar kawai ayi CS, Har a yanzun akwai Wanda suke ganin CS mutuwa ce balle a shekaru da dama da Suka gabata, hankulan kowa a tashe yake, Danna ita din nurse ce Amma Kuma family din ta fa? Haihuwa hudu kayi su lafiya har da wannan ta biyar Amma se a ta shida Abu ya gagara! Haka aka tafi da ita, Babu jimawa aka fito da ni sede baa Basu ba saboda Wai na sha ruwa banyi kuka ba, I've to go for another resuscitation, cikin hukuncin Allah kuwa se gashi Ina jin zafin heater na Fara kuka, Kuma jiki na ya koma pink yadda ake so.

Su 'Yan biyu farin jini ne dasu sosae, musamman idan ba Kai ka Haifa ba, se kaji sun burge ka kana son ace naka ne, to Haka muma muke da wannan farin jinin, Amma yawanci Batuul ke da shi bani ba, Ni na kasance kamar wata shadow din ta!
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_

005

Top-notch season 3

Ayshatuuu

Gaba daya sukai shiru suna jin abinda dan na su yake Yi, a ganin su diban albarka ce kawai wannan, a ganin su bokon da yake yi ita ce ta saka yake dukkan wannan abun, Amma a ciki Kawu Mamman ya fahimce shi, har ran shi ya Kuma ji Dadi,ban sani ba ko Dan kasancewar shi mahaifi ne ga Salamatu? Allah masani

"Nagode sosae Hamisu, nagode da baka wulakanta min Diya ba ka dawo da ita da martabar ta, Ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwar ka!"

Kun fahimci abin da nake so ku fahimta? Shi Kawu Mamman he's grateful saboda lokacin da Kawu yaji Bai son Salamatu baiyi kasa a gwiwa ba yazo ya sanar musu, Bai wulakanta ta ba balle cutar da ita ba, da yake Yana da wayayyen Kai se gashi Bai ja maganar ba yazo ya dawo da auren. To bashi kadai bane ba, hatta malam mahaifin shi ya fahimce shi, Kawu Sabaru ne dai yake ta banbanmi, har da fada Masa kada ya sake taka kafar shi zuwa gidan shi, Wanda dama ko Bai fada ba Kawu Kam ya bar wannan dakin zauren.

Bayam duk sun tafi, Malam yayi Masa fada sosae da sosae, ya nuna masa rashin dacewar abin da yayi, ya nuna masa illar rashin hakuri, a karshe ya Masa fatan alkhairi tare da bashi shawara akan rayuwa, ba tare da ko Innar shi yayiwa sallama ba, kawai ya dauki hanya ya koma Kano, Yana zuwa yayi sallama da Inna talatu ya tafi Dan Kama haya da Fara sabuwar rayuwa! Salamatu taji dacin mutuwar auren ta, tayi kuka marar iyaka Amma da taji zata cigaba da Zama Kano se hankalin ta ya kwanta, saboda tsoron komawa Hadejia ayi ta Yayata maganar.
Chapter 5 · 0% Book details