← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 44

Sashe 17

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maimamkon ya Bata amsa ko ya Bata hakuri se gani kawai tayi ya tsugunna ya Kuma Ciro wani Dan karamin box ya bude a take wani glittering ring ya bayyana a ciki, zainab ta bude idanun ta tana Jin wani tingles a cikin zuciyar ta, ya Kuma Miki Mata bunch of white roses tare da fadin

" Zainab, please be my life partner! Marry me zainab!"

Aka Fara ihu saboda taruwar student a wajen, se tafi suke suna hailing Imam, wasu Kuma na fada Mata tace yes! Ta kalle shi, ta Kuma kalli abubuwan dake hannun shi, he looks so sincere and cute. Tana murmushi a hankali Wanda Imam ke matukar kauna tace kamar whisper

"Yes!"

Bintun Batuul is not free! Contact me for payments.
[1/3, 20:28] Maman: 018

Wani lokacin bamu Sanin yadda ake zuciyar mu Kan Fara son mutum, wani lokacin se mun gama cika Baki akan " Ni kike tunanin zanyi soyayya da wane? Allah ya kiyaye, Allah ya rufa min asiri" wannan shi ne yawancin abin da muke fada, Bayan min Mata Allah yake controlling zukatan mu, shike saka so a lokacin da yayi niyya. Beside wannan ita zuciya wata shu'umar halitta ce, munsan kwakwalwa ke controlling duk wani sassa na jikin Dan Adam, kowanne organ na functioning ne da izinin brain, Amma akan soyayya se kuga zuciya ta aiwatar da Abu ba tare da kwakwalwa ta ankare ba.

Wani lokacin kiyayya ta Kan rikide ta koma kiyayya, yayin da mafi Muni shi ne ganin masoya sun Zama Makita, wannan Abu ba karamin tada hankalin mutane yake Yi ba. Zainab ta kasance Bata fiye kaunar duk wani Abu da ya shafa Imam ba, saboda yadda yake rayuwa ya banbanta da yadda take tata, Amma ku kalla how much yadda ya dinga kula da ita yasa ta karkato har ta bashi damar Shiga cikin zuciyar ta. She was so excited da ganin wannan zoben, ga roses, gashi Kuma a tsugunne a gaban ta Yana tambayar ta ko zata iya auren shi? Ta kalla fuskar shi me dauke da wani irin kasaitaccen murmushi da zaiyi wahala ka kalla baka ji zuciyar ka ta narke ba, Abu ne me wahalar gaske. A take taji ko Ina na zuciyar ta ya amsa, taji wani irin blood rush cikin jikin ta Baki daya, har Bata san ta Fara yelling

" Yes! Yes!!"

Ba, a take kowa dake gurin suka Soma tafi, da yawa abun ya burge su, yayin da ya Zama akasin Haka ga wasu,, suna ganin how foolish she's ta Fara kula wannan spoilt and rotten brat din! koma dai menene zainab bata damu ba, abin da ya dame ta shi ne Allah ya amince tayi rayuwa tare da Imam. Kowanne labari akwai farkon shi Kuma da karshen shi, karshen labari farkon wani labarin ne. Haka yake a dukkan rayuwar mu.

Fatin ciki marar misaltuwa ne ya bayyana a Kan fuskar Imam, duk irin kyautatawa da stalking din ta da komai da yayi gani yake she's too good and too decent for him, Amma ga mamakin shi se Allah cikin sauki ya karkato Masa da zuciyar ta har ta karba soyayyar shi, mikewa yayi tare da kokarin Kama slender but long fingers din ta Dan zura Mata ring din dake hannun shi Amma Taki hakan tare da karba daga hannun shi tana murmushi ta zura a index finger din ta tana sakin kayataccen murmushi me kwantar da hankalin Wanda ake yiwa. Daga Haka ta fasa Shiga library din sannan tabi Bayan shi kamar yadda ya bukata, Suka cigaba da tafiya zukatan su fari Kal Babu wani diso na bacin Rai, se da suka samu wani shade sannan suka zauna, bayan sun zauna ya dube ta har lokacin ya kasa cewa komai, he's so short of words!

"Zainab! Ina son ki, bansan wanne irin so nake Miki ba, Amma zuciya ta yearns for you!"

Tana murmushi cike da Jin kunya ta fur ta a hankali kasan numfashi tace

" I love you too!"

Hakan ba karamin Dadi yayi masa ba, anan ya dube ta Yana tambayar asalin labarin ta, duk da yasan da yawa daga cikin labarin daga bakin Murad, Amma dai zai so ace yaji daga bakin ta. Cikin nutsuwar ta ta Fara fada masa labarin ta kaf da dalilin zuwan ta kasar nan Dan karatu. Se da ta gama sannan yace

" Kina ganin Zaki iya convincing jadda har muyi aure?"

Se ta Ciro wayar ta ba tare da ta amsa ba, bugu biyu jadda ta dauka tana amsa gaisuwar ta cikin larabci, ta danyi shiru tana Wasa da yatsun ta kafin can dai saboda tambayar da jadda take Mata na fatan dai lafiya take, ta amsa eh Amma tana son gabatar Mata da wani, Jin wanin da ta fada jadda ta saki murmushi tana godewa Allah wannan kyakyawan labarin da taji daga bakin jikar tata. Ta so kwarai ta dawo gida ta samu wani Dan Qatar tayi aure, ba Wai ta samu a UK ba, but does that even matters? It doesn't as far as ita din tana son shi to magana Kam ta Kare.

A wannan lokacin Bata kashe wayar ba se da sukai magana da Imam duk da an samu tangarda sosae, wato communication barrier. Shi Yana Jin turanci Amma babu larabci yayin da take jin larabci Babu turanci, karshe dai se zainab ce ta zame musu interpreter! Suka gausa tayi Masa tambaya sosae akan shi da kasar shi, Jin shi Dan Nigeria yasa ta Fara tambayar shi ko iyayen shi zasu amince ya aura zainab din? Se ya nuna Mata bashi da matsala da parent din shi,duk da a kasan ran shi yasan ba Haka bane ba, yasan iyayen shi mutane ne masu kabilanci, mahaifin shi ya fada Masa duk lokacin da zaiyi aure zai Nemo bafulatana yar uwar shi ya aura, to fa se gashi balarabiya ya samu wadda ba Yar kasar su ba, ba Kuma yaren su daya ba.

Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya gwanin ban shaawa, soyayyar su zata saka kaji kaina kana son ka samu me son ka, yadda yake Mata yadda yake kula da ita da yadda kokarin canja salon rayuwar shi duk saboda ita, Abu ne da kowa ke fatan samu Kuma zainab ta samu. Shudewar wasu watanni, jadda ta sake tuntubar su ko suna tare har lokacin zainab ta tabbatar Mata se abun da yayi gaba ma, wannan yasa jadda tace Mata

" Na yarda Dake zainab, na Kuna yarda da tarbiyyar da mukai Miki, sede baka shaidar zuciyar da ta Fara soyayya, Ina ganin idan iyayen shi sun yadda ko zakuyi aure kawai, hankali na zaifi kwamciya"

Imam Dake karanta translation din wayar da zainab ke yi, ya saki murmushi tare da mikewa ya daka tsalle, zainab ta Harare shi tana fadawa jadda zata ji daga bakin shi. Ko kunsan a yammacin wannan rana Suka Isa masallaci aka daura musu aure? Shike nan Imam ya Zama miji ga zainab, zainab ta Zama matar Imam! Sede duk wannan abun da sukai Babu wani mutum daya daga bangaren Imam da yasan abin da yake faruwa!!!

***

Yadda daga Adda har Bintu, har Kawu kowa ya shige dakun shi ba tare da ya ce wani Abu ba ya bawa Mamaa tsoro, saboda ya kamata suyi bayani akan abin da ya faru, ta fito saboda tasan hankalin ta a tashe yake, ta shiga dakin Adda ta samu tana kokarin Shiga wanka, tana ganin ta ta Dan saki fuska tace

" Sannu da gida Mamaa, na shigo a gajiye zanyi wanka ne!"

Yadda Addan ke dauke yasa Mamaa Sanin tana bukatar kadaici se tayi Mata sannu da zuwa kawai ta wuce wajen Kawu, tana fita Adda ta kulle dakin tare da komawa ta zauna ta dakko wayar ta, ta Fara Kiran Fadima, kamar yadda kuka sani Yaya Fadima ita ce babba a wajen Adda, Kuma tana aure a sokoto da yaranta. Bayan ta dauka suka gaisa da Adda wadda muryar ta har rawa take Yi, tace

" Adda Abu ya same ki ne? Ko wani abun ke faruwa a gidan bani da masaniya?"

Adda se ta Fara kuka tana fadin

" Fadima Bintu ce! Bintu..."

Hankalin Yaya Fadima ya tashi, duk da tana kokarin dannar kanta Dan ta samu ta kwantarwa da Adda hankali

" Me ya faru da BINTUN? Ina ce tana makaranta"

Wannan karon kukan na Adda karuwa yake tace

" Bansan me ya faru ba a makaranta, har ta Sha Dettol zata kashe kanta, se da ta..."

" Ita BINTUN? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun! Ya rabbul alamin"

"Ita dai fa Fadima, ya zanyi yanzun anyi ruling depression!"

Shiru ya biyo baya saboda Tsabar yadda Yaya Fadima ta kadu, se Kuma tace

" Ki daina kuka Adda, Amma kiyi hakuri laifin ki ne! Tun farko Baki dauki Bintu kamar Yar ki ba, kin Bari kowa Yana cin Kashi a kanta ko wannan kadai ya Isa Bintu ta samu depression har ta Kuma samu suicidal thoughts!"

"Na sani, nasan nayi kuskure Fadima amma bansan ya zanyi na gyara ba, bansan yadda Zan Fara shawo Kan matsalar Bintu ba!"

Cikin rashin Jin dadi yaya Fadima tace

" ki nutsu tukunna, sannan ki huta, zuwa dare ko safe se muyi magana, Amma kiyi ta Mata addua"

Daga Haka sukai sallama sannan ta Shiga wankan saboda kanta Dake ciwo.

Kawu Yana kwance can cikin bedroom lokacin da Mamaa ta shig, ya juyawa kofa baya tare da yin likimo tamkar me yin bacci, Amma ba baccin yake ba ko kadan tunanin Bintu kawai yake, tausayin ta da Kuma Jin haushin Kan shi Akan halin da yarinyar take ciki, wanne irin sakaci yayi har yarinyar ta Shiga mawuyacin Hali take Kuma kokarin saukar rayuwar ta? Haka ta fito jikin ta a mugun sanyeye, se ta wuce waje na. Ina zaune akan gado da wata sabuwar Reza a hannu na Ina kallon hannu na ta wajen da na San radial artery di ta na nan!

Ta-kwalam

BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI is not free, do contact us for payment details!
[1/3, 20:28] Maman: 020

BAYAN WATANNI UKU!
Chapter 17 · 0% Book details