← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 44

Sashe 15

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya naji am humiliated, naji na kasakanta na Kuma wulakanta. Nayi shiru rooted to the ground na kasa moving an inch, suka cigaba da hirar su Akan kiba da yadda Basu son ko kadan suyi gaining weight. Kun San ranar wallahi Hadejia da banje ba kenan. Kuma tun daga wannan ranar ban sake ko da wasa shafa powder ba, ko da kuskure in fact wallahi make up stuffs di na dukka na tattara na bayar da su!

A ranar saboda rashin confidence, kasa kallon madubi nayi, saboda kada Naga abin da zai saka na wanke fuska ta. Ina nan tsaye Samiha ta shigo da gogaggen house wears din ta, ba wani Abu ta shafa ba Amma tayi kyau sosae, se naji Ina tsoron kada muje fa ta kwace min habiebie. Se Kuma na kawar da wannan tunanin daga Rai na, a duk duniya Samiha ita ce wadda na Fara trusting, nake Kuma tsamannin ba zata taba ha'inta ta taba, aikuwa muka fita tare Bayan ta Gama

"Ma shaaa Allah! Whoa! Wow! Kin gan ki kuwa BinGin, shiyasa nake cewa kiyi kwalliyya, Baki ga yadda fuskar ki tayi ba"

Nayi murmushi Ina Jin Dadi tare da Jin wani nervousness na yadda haduwa ta da BashPrince00 zai kasance. A Haka dai muka tafi bayan ya Kira ya tabbatar min da zuwan shi. Muna tafe Ina haduwa da colleagues di na suna fada min nayi kyau ko dai BashPrince00 zai zo ne. Duk da ban Faye magana ba, ban Kuma faye shiga mutane ba Amma Ina yawan maganar shi har ta kasance Yan class din mu sun San shi, sun Kuma San yadda nake ji a tattare da shi.

Visiting din mu a katon visiting hall ne wan da school ta ware domin hakan. Na Shiga ciki tare da Samiha Ina Jin wani irin yanayi saboda cikar mutane a gurin. Amma da ke kusa da Samiha nake I felt a lot relieved. Na wuce ciki Ina wuwwula idanun Inga ta inda Zan hango shi, ku kwace na San shi, wayar dake hannu na ta Fara vib, Cikin salo yadda wani ba zai gani ba na Kara a kunne na nace

"Ban ganka ba"

A hankali na hango wani can extreme a zaune, Yana waving hannun shi. A take naji dukkan jiki na yayi sanyi kamar an datse min gwiwoyi na Haka naji. Kunsan kalmar "elite?" Kunsan kalmar "butter?" To wadannan biyun su ne kawai kalmomi da zaa iya describing BashPrince00. Samiha ta saki murmushi tana rada min

" Kai ba dai wancan shi ne BashPrince00 din ba?"

Ni dai na kasa magana, har Muka karasa in da yake zaune, fuskar shi dauke da wani murmushi da kullum nake mafarkin gani, Ni kuwa na taba ganin namiji me dimple a rayuwa ta? Kai Anya kuwa? Inaga ban taba gani ba se Akan shi. Dimple din fa sosae fa Kuma both side, ba fari bane ba Amma kunsan caramel? Kunsan abin da ake cewa wancan caramel skin ne da shi? To Bari na fada muku caramel consist of butter, honey and sugar! Ku tuna irin sheki da shining din da caramel zaiyi, to kamar Haka skin din guy dinnan yake, ga wata gargasa da ta kayata wannan shiny skin din, ya zanyi na kwatanta muku BashPrince00 ni kuwa? Kawai jikin shi, kayan shi da komai nashi speaks of handsomeness, he's beautiful jama'a, ku manta ance beautiful is meant for girls, a'a fa yau fa shi ne kadai word din da zanyi muku kwatancen BashPrince00 da shi. Se murmushi yake da nake kallowa kasa kasa yayin da yake narkar min da zuciya ta.

To Bari kuji kamannin Samiha, a'a ai na tuna na fada muku kammanin ta ai a other chapters, ta tunkuda ni Wanda yasa na Isa gaban shi babu shiri, na tsaya gaban shi Amma to my utmost disappointment hankalin shi da wannan murmushin Yana Kan Samiha... Wayyo ni BinGin!

Kamar kullum kada ki Bari labarin BINTUN BATUUL, NAZNEEN da kuma GENERAL NASEER ZAKI ya wuce ki, kunsan dai tafiyar ba yau aka Fara ba, wannan season 3 ne!
[1/3, 20:28] Maman: 016

Amma Kun San da gaske idan zaka aikata babban zunubi da gaske imanin ka tafiya yake, a lokacin da nake zaune gaban locker da Kuma kwalbar Dettol a hannu na, gaba daya bana ji bana Kuma gani, kawai abin da subconscious mind di na ke fada min, Bintu Ginsau kisha, kada ki tsaya, gwara ki kashe Kan ki ki huta da wannan bakin cikin, idan kin mutu ma Babu Wanda zai damu, Babu wan da zaiji wani Abu. Wannan zuga da zuciyata tayi min yasa hannu na na rawa na balle murfin, without any second thought na bude Baki na na Fara kwankwada, se da na Sha wajen rabi sannan na Fara Jin wani hautsinawa da ciki na ya Fara, na yarda kwalbar a kasa na sulale Ina wani Abu kamar me fitting. Ban San minti na nawa na dauka Ina Jin wannan azabar da Kuma ciwo ba, Amma saboda yadda zuciya ta tayi tauri ko neman taimako banyi ba, cikin hukuncin Allah se ga lubna wato roommate Dita ta shigo daga dakin kawar ta in da take zuwa kwana, wani irin salati ta saki lokacin idanuna rufewa suke Amma Ina kokarin bude su, ta karaso waje na tana fadin

" Bintu! Bintu!! Bintu!!!"

Ina Jin ta Amma na kasa dagowa balle na amsa, ta fita da gudu, only God knows minti na nawa ta dauka suka dawo ita da Senior prefect, house captain, Matron da Kuma Hall admin da ta shigo coincidentally. Ni dai bana ce ga abin da ya faru ba, Ashe suna.zuwa Hall admin ta Kira senior master Akan lallai a turo bus akwai emergency a hostel, Suka kalla kwalbar Dettol din dake gefe na anan suka tabbatar abin da na Sha kenan. Lubna ta dakko cup ta zazzago madara ta kada ta taho Dan bani, Amma se aka hanata akace ta Bari asibiti zaa je Dan na Riga da nayi loosing consciousness di na. Haka muka tafi asibit ko sick bay baa tsaya ba, cikin gaggawa aka karbe ni a emergency unit din su, cikin lokaci principal da vice suka karaso asibitin lokacin har an saka min tube ta hanci na zuwa Baki na zaayi draining Dettol Dake barazanar dauke min rauyuwa, se da aka kwashe tsaf kafin akai min abin da ake cewa daurayar ciki, Bayan an Gama sannan suka zauna da principal wadda hankalin ta a mugun tashe yake har lokacin.

" Wannan ya nuna she wanted to commit suicide!"

"Suicide doctor?! Suicide fa? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!"

Ta fada hankalin ta a mugun tashe, Doctor din yace

" So Kun fahimci ko tana da wani problem mentally? We need to invite her parents"

Principal tayi shiru tana kallon Doctor din, ku kwayi tunanin amsar tambayar akan fuskar shi take a rubuce, se can tace

" Ban San ta sosae ba, Amma room mate din ta tace dama Bata Shiga mutane since js1, she's always alone and lonely!'

Doctor din ya sake rubutu sannan ya kalla principal yace

" Ya kamata tuntuni ki gane me yake damun ta da har Bata shiga mutane, dukda banyi concluding ba tun da banyi magana da ita ba, Amma Ina tunanin yarinyar nan na fama da depression"

"Depression again? To Doctor aside this. Tambayar da nake so batu maka shi ne ya jikin nata, Dettol din Bai bar Mata matsala ba?"

Yayi dogon numfashi sannan yace

" Eh daga yadda kukai saurin kawo ta, bana tunanin complications din me yawa ne, zamu jira zuwa ta farka sannan tayi hoto mu gani"

Haka Suka Jima suna tattaunawa kafin principal ta fito ta samu vice tare da ce Masa ya Kira guardians di na da sauri. Haka ya koma school lokacin kusan kowa yasan abin da ya faru, Samiha dake bacci tashin ta akai aka fada Mata, wani irin zabura tayi tace

"Dettol? Dettol fa? Bintun?"

Ba karamin tsorata tayi ba, da Kuma gigita ba, tayi shiru tana pouncing akan gadon ta, tare da tunanin possible abin da zai saka ni Nasha Dettol, ita Baki daya ma ta manta what transpired tsakanin ni da ita da Kuma Bashir. Amma ni ta Ina Zan taba manta abin da sukai min.

Kira sosae akai yiwa Kawu amma bai dauka ba, se kawai suka samu contact din Adda, suna Kira Babu jimawa ta dauka, a lokacin tana garin Abuja tazo wani conference da Nursing and midwifery council of Nigeria ta hada musu a matsayin ta na director school of nursing Kano. Sun Gama suna kokarin tafiya airport zuwa Kano, wayarta dake cikin jaka ta Fara kara, dole ta tsaya ta fito da ita tare da karawa a kunnen ta, bayan sun gaida tayi inquiring me magana, yayi saurin bata hakurin rashin gabatar da Kan shi da yayi tun farko kafin yayi Mata bayani hadi da cewa

"Daga school din su Fatima Bintu Ginsau ne, Bata da lafiya sosae, Muna bukatar one of her Guardian to be in school please!"

" Me ya samu Bintu? Me yake damun ta? Is she conscious? Subhannallah!!!"

Ta fada ta Fara rikicewa, ni ba mutum bace ba me jinya, Dan Ni kowa yasan bana rashin lafiya, ko nayi ma sede ka gani Amma ba Zan fada ba, so Adda tasan duk abin da ya kayar da Ni lallai abun kallo ne.

" Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, tana da Rai Amma dai ya kamata ki samu kizo ko zuwa gobe ne!"

Ta duba golden wrist watch din da ke daure a hannun ta na dama, se lokacin ma goma na safe tayi, Dan Haka tace

" Yanzunnan Zan Yi catching next flight to Niger"
Chapter 15 · 0% Book details