← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 44

Sashe 25

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da na kalle ta ba mace

" SCENTMANIA nake amfani da shi"

Se ta Mike tana fadin

" A Ina Zan samu? Turaren nan duniya ne wallahi saboda yayi kamshi me kwantar da zuciya."

Daga zaune na Fara Mata bayanin su, nace

" Ai matar ta san lakanin turare Batuul, oils ta ke yi Kuma tana iya maida maka oil zuwa spray, Kuma idan Zaki siya, se kinyi Mata bayanin yadda kike son turare kafin tayi Miki recommending. Batuul ki gwada shi kawai..."

Shigowar habiba ta dakatar da Ni daga bayanin SCENTMANIA, Nima bansan yadda akai na San shi ba, ba Zan iya tunawa ba, Amma fa yanzun bana tunanin akwai turaren da Zan iya amfani da shi Bayan SCENTMANIA.

" Adda Bintu kizo in ji Mamaa"

Na Mike Bayan na.amsa ta nabi Bayan ta zuwa dakin Mamaa, tana zaune da bowl a hannun ta na kwadon salad a ciki, na zauna bayan ta yimin tayi nayi murmushi nace

" Pizza akai order, nayi ta Dan so tayi.yawa shi ne na cinye aba ta"

"Ke dai Bintu ba Zaki rabu da wadannan fast food din ba, ke ba exercise kike ba, shiyasa jikin ki jiya I yau"

Na tabbatar Mamaa ba zata taba fadar Haka ba, Amma Adda ai ba zata fasa ba, Koda kuwa zata ga na rataye Kai na ne Dan takaici. Bance komai ba se kicin kicin da fuska ta da nayi, shikenan saboda kana da kiba you can't eat abin da kake so? Ni dai Ina Zan saka Rai na ne naji Dadi?

" Kinsan an kawo kudin Batuul ko?"

Na gayda Mata Kai na Ina fadin

" En! Allah ya Sanya alkhairi

Suka amsa Amin baki dayan su, kafin Adda tace

"Kawun ku ya tambayi ko kina da saurayi a hannu, mun fada Masa Babu kowa dake zuwa wajen ki, ya yanke hukuncin zai aura Miki Suleiman tun da,.."

Ai ban Gama saurara ba, tunda sunan Suleiman da Kuma nawa hade da kalmar aure suka shigo sentence daya naji na daina gane me ake fada tukunna!

Ta_kwalam
[1/3, 20:28] Maman: 026

"Did I heard you well? Aure Kuma?"

Ta fada da wata irin murya da zata tabbatar maka a raunane  take, ya sake ruko ta zuwa jikin shi saboda Yana iya ganin kishi karara akan fuskar ta, kafin yayi magana ta Fara kuka a hankali tana fadin

" Tsoro nake ji, tsoron family din ka nake, you already have a wife how will they accept me Chum Chum?"

Yayi shiru Yana Jin tashin hankali hade da tsoro Yana shigar shi, duk wata hanya da yake ganin lallashin ta zaiyi sauki yabi Amma se yaga abin na zainab kamar gaba yake sakewa. Kuka take sosae kamar yau aka sanar mata mutuwar Fahad, ya duba agogon dake kafe a hotel room din yaga karfe takwas da mintina goma , ya Kamata yayi haramar komawa amma Kuma idan ya kalle ta se yaji ta Ina zai bar ta a halin da take ciki, duk yadda Imam take sahibul Kalam yau gashi kalamai sun gagari bakin shi, abin da kawai yayi was hugged her and patted her back. Anan suke ta zaune har yaji alamar tayi bacci, cikin sauri ya kwantar da ita ba tare da yayi wani abu ba ya fice daga dakin.

Dakin shi ya koma baifi minti na goma ya rage Tara tayi ba jikin shi ya gyara ya canja zuwa manyan Kaya da Bilal ya kawo masa, da saura mintina biyar ya Shiga wajen Ummiey, ya gaishe ta a gaggauce kafin ya wuce inda yake da tabbacin anan zaayi taron. Yana tafe Yana kallon gidajen da ke mallakin su, kowanne da idan aka haife shi ya isa sure anan zaa Gina Masa gida ayi Masa sure, a tarihin Gidado close Babu wani bare a cikin wannan waje, Haka zalika bai taba Jin labarin in da akace Wai yau a tarihin dangin su dake nan wani ya taba auren bare, shi ne na farko shiyasa yake Jin tension Yana building a jikin shi.

Alhaji Gidado na zaune ya mikar da kafafun shi akan tumtum, dalilin hakan kuwa saboda kumburin kafafun da yake fama da shi kwana biyunnan. In dai taro zaayi to Alhaji Gidado yakan kasance mutum na farko da yake fara zuwa wajen taron, ba dai ka Riga shi ba sede ya jiraka. Gefen shi Amarya Safiyya ce wadda tun tana yarinya ita ke serving din shi tea, to ko jiya bayan anyi auren ma yau seda ta dafa Masa tea ta kawo Masa, tana zubawa taji deep voice din da tayi shekara takwas ba taji ba yayi sallama, a hankali ta juyo da wide grin saman fuskar ta, tace

"Hamma Imam! Ashe ka dawo? Ashe da gaske ne!"

Shima Yana murmushi Wanda kowa yasan Safiyya da Imam yadda suke, tun tana yarinya mutuniyar shi ce, saboda a cewar ta shi ya Fara kawo Mata cartoon din Sofia the first, wannan shi ne dalilin da yake ce Mata Sofia. Bayan ya zauna yace

"Sofia the first!"

Ya fada da murmushi saman fuskar shi, ta gyara Zama Bayan ta jira ya gaida Alhaji Gidado, sannan Suka gaisa tayi Masa murnar Gama makaranta da Kuma dawowa gidan cikin aminci da alkhairi, yayi murmushi Yana Mata godiya, a hankali daya biyu Kuma se ga iyayen su suna zuwa, dukka Suka gaishe su, Amma ganin Safiyya bata tafi ba se ya tabbatar wa da Kan shi taron har da ita, shi Bai maga tashi matar ba, tun da yazo Bai ga Rukayya ba, baisan Rukayya na dakin Mujahid ba, shi ta aura ba shi ba. Ganin lokaci ya cika se kawai akai proceeding da tattaunawar da zaayi, anan ya gabatar musu sabon construction company da ya bude Wanda ya damka shi kacokam hannun Imam, sannan ya tabbatar wa Imam Safiyya ce matar shi, a hankali ya dago Yana kallon ta Haka itama tana tayi Masa murmushin nan Mata me kwantar da hankalin, Haka kawai se yaji kaso me tsoka na damuwar da take ciki ta tafi, idan har Safiyya ce then komai zai zo da sauki.

Bayan an Gama suka fito Bayan dogayen adduoi da Kuma nasiha da akai musu, suna tafe kowannen su yayi shiru zukatan su na tunani mabanbanta. A Haka Suka karasa wajen Ummiey shi, ta saka musu albarka, a ranar Bai samu damar komawa wajen zainab ba, se ya zauna a dakin shi yana tattaro bakin zaren, Yana ayyana yadda zai Fara, saboda kukan da zainab tayi yau da safe ba zai iya cigaba da ganin shi ba, ba zai iya boyewa ba saboda shi din ba Haka yake ba.

Da daddare aka raka shi well furnished gidan shi, gidan da akai Masa shi da Safiyya, Bayan dukkan abin da sunna ta tanada se Suka Fara Hira like the old friends they were. Ya tambaye ta dalilin fasa bikin shi da Rukayya? Se ta fada Masa ai ganewa akai suna soyayya ita da Mujahid shi ne yasa aka fasa akace gwara ta aura Mujahid tun da dai har sun Riga da sun shirya Kan su. A bangaren shi se yace

" Safiyya! Ban taba kawowa cewar Zan aure ki ba, though I've been eyeing you akan auren Ashe ke rabo na ce"

Tayi murmushi tana sunkuyar da kanta kasa irin kunyar fulanin nan, yace

"Ina son ki saurare ni, Ina son ki nutsu nayi Miki bayani Safiyya"

Ta dago ta kalle shi taga fuskar shi Babu alamar Wasa, hakan ya tabbatar Mata da gaske yake maganar me muhimmanci ce,

"Ina da aure Sofia! Yes da gaske nake nayi aure shekaru wajen hudu Sofia, I can't tell anyone Sofia, kinsan yadda muke rayuwa a gidannan, I'm scared!"

Tabbas tayi mamaki, matuka ma kuwa Amma Kuma ba abin mamaki bane ba Dan dama kowa yasan Hamma Imam daban yake tun Yana yaro, duk wani abun Jan magana to ya iya dakko shi. Tasan tana son shi, tana son shi sosae, ko ranar da aka ce Mata zata aure shi, kusan murna hanata bacci tayi, har se da Dada wato mahaifiyar ta ta fahimta, anan ta Fara Bata dabarun yadda zata karkato hankalin shi gare ta tun kafin ma ya dawo, Kuma ko Ummiey ma Haka tayi ta Zama da ita tana nusar da ita dabarun sace zuciya tun da suka Haka akai musu aure ba tare da son rayukan su ba. Dole ka danne halin da kake ciki Dan ka faranta Masa Rai.

"Tana Ina? A Ina ka barta? Tana can UK din?"

Ya Kama hannun ta for the first time saboda abin da yake gani cikin idanun ta, she's trying hard to suppress kishin dake taso Mata, yace

" Nazo da ita..."

A hankali ya kwashe komai da komai ya fada Mata, tun daga soyayyar su day komai da komai, labarin soyayyar tasu se ta kayatar da ita ta Fara murmushi tana Jin Bai kamata su rabu ba, se da ya Gama yace

" Bansan ya zanyi ba Sofia, Kai na ya kulle na Rasa yadda Zan fadawa wani cewar bake kadai bace Mata ta ba!"

Ta saki nannauyar ajiyar zuciya tace

"Ina son na ganta please, zaka kaini?"

Yayi murmushi Yana matsa hannun ta yace

" Of course Dear! Ya zanyi? Ki bani shawara"

"Take it easy and slow, kasan gidannan ko bango na da idanu da kunnuwa!"
Chapter 25 · 0% Book details