← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 44

Sashe 23

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramadan Kam rungume shi kawai yayi Yana Masa barka da zuwa, shi dai tun da yaji zancen ango a bakin Sadiq, se ya ji kamar an watsa masa ruwan sanyi, shifa a wani dangin ana ganin nothing is possible ko, to ban da a Basu dangin, matsawar numfashim Alhaji Gidado ba ceasing yayi ba, Kuma kannen shi biyu da manyan yayan suna raye, to zasu cigaba da upholding duk wani policies din shi. Kafin wani lokaci Kam sauran cousins din shi dake kusa da Kuma Suka San shi duk sun yanyanbe shi, ga iyayen su acan Suma da abokan shi, mahaifin shi ya hango Yana murmushi, a take yaji duk wata nutsuwa ta sake shigar shi, da kyar ya samu suka sake shi ya tafi wajen baffanin na shi, kafin ya karasa wajen na su ya hango kakan shi da abokan shi shima, mahaifin shi da idanun shi yayi Masa alamar ya Fara zuwa wajen Alhaji Gidado, Babu shiri ya juya wajen Alhaji Gidadon dake kwasar gaisuwar mutane dake Masa Allah ya Sanya alkhairi, wani katon carpet ne da Kuma tumtum da ya samu ya shigida da shi, tamkar basarake Haka mutumin yake, Yana ji da kudi, mulki da Kuma izza. Yana hada idanu da jikan nashi se ya muke Yana bude hakoran shi alamar farin cikin isowar shi, ya cire sneakers din kafafun shi tare da karasawa ya rusuna cikin girmamawa Yana gaishe da kakan, Amma se ya rungume shi Yana jadadda Masa farin cikin ganin shi, anan ya umarci Sadiq da ya karbo Masa abinci a cikin gida, sannan ya dubi mujahid yace ya raka Imam ya gaida baffanin shi sannan su dawo , Yana jiran su suci abinci, Haka yaje cikin su ya gaishe su, suna ta murnar dawowar shi, mahaifin shi yayi Masa murmushin Yana shafa Kan shi kafin Suka koma wajen Alhaji Gidado, anan suka ci abinci kafin yace

" Ango se kaje kayi wanka ka canja Kaya, ka dawo ku gaisa da mutane!"

Haka ya mike jikin shi a matukar sanyaye Yana tunanin makomar shi shi da zainab, ko me take yanzun? Shi ne abin da ya Zama Yana Masa yawo cikin ran shi. Duk yadda su Sadiq suke zuzuta Masa amaryar ta shi da ya riga yasan Rukayya wadda ya San da alkawarin auren ta a kanshi tun kafin ya tafi UK, se Suka ga he's not excited at all, Sadiq cikin zolaya yace

" Wai Imam baka murnar dawowar ka ne da Kuma sabuwar amrya da zaka hadu da ita?"

Ya kalli Sadiq Yana wani fake smile Amma shi dai zuciyar shi ko kadan ba a nutse take ba. Se yanzun yake sake ganin wani tashin hankalin dake jiran shi.

A gidan Baffa lamido Suma amaren dukka suna zazzaune da kawayen su, wasu kana kallon su zaka fahimci suna cikin farin ciki kada Rukayya da Safiyya suji labari Amma Fatima da Boddo gasu nan dai gasu nan. Haka sauran ma. Kanwar Imam wadda ya tafi ya barta tana da shekara shida, yanzun Haka ta Kai shekaru Sha hudu me suna Anisa ta rugo parlon da suke ciki tana kwala Kiran Adda Safiyya, Safiyya ta Mike tana gyara zaman veil din ta tace

" Ya akai Anisa?"

Tana panting saboda gudun da tayi tace

" Adda! Hamma Imam ya dawo daga UK!"

Wani karamin ihu Safiyya ta saki tana fadin

" Da gaske Anisa? Oh Allah alhamdulillah!! Kin gan shi? Yana Ina?"

Ta fada tana kokarin fita, Anisa tayi saurin rike ta tana girgiza Mata Kai alamar kada ta fita ta Kuma tsaya ta saurare ta. Hakan tayi ta tsaya amma she's so excited and eager to see him.

" Ban gan shi ba Adda, naji Hamma mujahid na fadawa Innan su Boddo"

Ta sake sakin murmushi tana juyawa alamar fita, wannan karon ma Anisa ta sake rike ta tace

" Ke Adda Safiyya so kike wancan old hag din ya kashe ki? Kin manta ke amarya ce? I assure you Hamma da zarar yaji kece amaryar shi zai rugo wajen ki"

Wannan abun ya sake sanyaya zuciyar Safiyya ta koma ta zauna sede ta kasa nutsuwa, ta dinga murmushi upon murmushi idan ta tuna mutumin nata ya dawo bayan shekara da shekaru! Duk yadda Imam yaso ya zille ya koma hotel wajen zainab Abu ya gagara, Haka ya cigaba da Zama cikin cousins din shi da abokan su. Se wajen goma ya samu ganin Ummiey wato mahaifiyar shi, farin cikin ganin shi sosae ta kasa boyewa, murnar ganin shi sosae tayi. Se da ya shiga zai kwanta zuciyar shi nayi Masa nauyin rashin ganin zainab, rashin ji daga gare ta aka turo kofa, Bilal brother din shi ya shigo ya zauna Yana Masa sannu da zuwa, har lokacin Imam Bai ma San wacece amaryar ta shi ba, shi dai Yana kyautata zaton Rukayya ce.

" Hamma old hag yace gobe akwai meeting karfe Tara, ka huta before then!"

Ya gyada Kan shi daga Haka Bilal ya fita shi Kuma ya kwanta Yana planning yadda given shi zata kasance. Washegari Yana dawowa daga sallar asuba, yayi wanka karfe shida ya fita daga gidan bayan ya kulle dakin shi yadda kowa idan yazo zaiyi assuming baya nan. Taxi ya samu har hotel din, kamar yayi tsintuwa zuwa ciki Haka ya dinga ji, so yake kawai ya ganta yaga lafiya take, Yana knocking Babu jimawa tazo ta bude, tana ganin shi ta fada jikin shi tana farin cikin ganin shi. Suka zauna saman cushion din dake dakin, ya Fara binta da soothing touches Wanda yasa ta Fara melting a jikin shi. Bayan sun nutsu ya tambaye ta yadda Daren ta ya kasance, tace Masa missing din shi badly da kyar tayi bacci, yanzun Kuma se ta Fara tambayar shi yadda ya samu Ummiey da Baffa kamar yadda taji Yana Kiran sunan su. Se ya zauna suka Karya sannan ya Fara Mata bayanin tayi hakuri ta Kuma Kara hakuri he'll take her home soon, yanzun yazo ya samu anyi Masa aure ne! Waji irin dagowa tayi...

Ta_kwalam ce

Good morning lovelies!
[1/3, 20:28] Maman: 023

Mamaki kamar zai kashe ni a tsaye, nace

" Batuul kiji tsoron Allah! Kada abun duniya da zai Kare ya saka ki bata tarbiyyar da akai Miki a gidannan..."

Tayi saurin katse ni da fadin

" A'a tsaya Bintu, wallahi banyi wani abun ba. Kar ma zuciyar ki ta zarge ni, I only used the beauty of my face nothing more!"

Ta fada tana wani irin murmushi tare da shafa fuskar ta, na girgiza Kai nace

" Ki dai ji tsoron Allah!"

Daga Haka na fice zuwa kitchen Dan yin meat bread din da aka saka ni. Awa daya na kammalla sannan nayi packaging, se da na jira aka karba kafin na dauki zobo da pieces biyun da suka rage na wuce daki na Fara ci Ina tunanin maganganun Batuul, yanzun da gaske take zata iya rabuwa da Suleiman? Duk yadda yayi dawainiya da ita da Kuma shakuwa da sukai Amma zata iya Haka? Se naji kawai al'amuran Batuul ya Fara bani tsoro. Ina nan zaune Ina ci Ina Kuma karatu se gata ta sake shigowa, ta zauna bayan ta gutsiri Rabin meat bread din tace

" Dan Allah idan kin Yi ki dinga sammin!"

Ta kusa saka ni dariya, nace

" Ki saka order, kici ki barshi!"

Ta tabe Baki tace

" Matsalar business people kenan, you guys don't care about relation at all!"

Nayi Mata banza Ina cigaba da duba book di na, kafin na Kai ga dauka ta dauke ta cinye tana dariya. Nima se nayi murmushi nace

" Batuul!"

Ta kalle ni nonchalantly tace

" Bintu! Ya akai?"

Nace

" Zancen Suleiman ne, ba zakiyi reconsidering ba, ki tuna years of relation da kuka dauka ke da shi, to ma tsaya tukunna, ya Zaki Fara samun Kawu da wannan maganar?"

Tayi dariya tace

"Kudi da kike gani Bintu Babu ruwan su da wani years of relation, what matters is na samu abin da nake so. Na Dade da gane Suleiman ba class di na bane ba, zancen su Kawu da kike bani Zan same su ba su zasu same ni. Ke dai ki zaba idanu ki gani. Ni dinnan ta Honorable Kura ce da yardar ubangiji"

Nayi wani sneering nace

" A'a Honorable Zaki ba kura ba. Ke Kika sani"

Ina kwanciya Bayan na Jima Ina karatu sannan na kunna data, wani lokacin tsautsayi ke saka kayi wani abun. Ina kunnawa na tafi nayi uploading story akan washegari zanyi glazed pancake for breakfast me so yayi order. Har Zan kashe data din bansan me yasa ba se kawai na koma bangaren chat di na. Ina Fara scrolling se Naga wani message yayi popping, hannu na ya Kai Kan number, Ina shiga Naga image ne aka turon. Na bude na kurawa invitation card din da aka turo min. Abin da ya Fara daukar idanuna shi ne sunan Wanda zasuyi auren, wani irin mikewa nayi na zauna, na sake bude idanu na Dan na tabbatar sunan Samiha Suraj nake gani da Kuma sunan Bashir Garba Me yaki! Auren gaba daya sati biyu kawai ya rage, idanuna Suka ciko da kwalla Ina kallon sunan BashPrince00 da Samiha, so Haka sukai deciding, so a karshe dai aure zasuyi abin su, ikon Allah na sake ayyanawa a cikin zuciya ta. A take se Kuma naji kwallar da ta cika idanuna ta Fara sakkowa a hankali, na cigaba da sheshekar kuka a hankali Ina ayyana ni Kam akwai ranar da take zuwa take wucewa ba tare da hawaye ya fita a idanuna ba? Ko nace bazan Yi ba se wani abun ya gifta da zai saka naji kirji na yayi nauyi, Kuma the only solution is for me to cry! Duk yadda na dinga lallashin Kai Na se da na Jima Ina kuka kafin Kuma na Fara tuhumar Kai na dalilin Bata lokaci na Ina kuka dan kawai zasui aure? Kenan har yanzun Ina son BashPrince00 nake nufi Koko me? Se naji hawayen sun dauke daga idanuna, naji it's ok suyi auren su Nima watarana rabo na duk inda yake zai zo. Se na goge idanuna na kwanta Ina adduar Allah ya Kara min hakuri!
Chapter 23 · 0% Book details