← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 44

Sashe 30

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bance Mata komai ba kawai na janyo lottafi na dan nayi karatu, to dai Batuul ba shawara take nema ba, gwara na barta tayi abin da take so. Ina nan zaune se naji wayar ta na ringing da farko taki dauka se a Karo na biyu ta dauka. Na kalle ta ta Kara Bata fuska kamar a gaban shi take,

" Tohm!"

Daga Haka ta tashi ta Shiga toilet ta wanke fuskar ta, ta sake fitowa ta canja Kaya zuwa wata embroidered Abaya color baka, ta Ciro Addictive Ambergris daya daga cikin collection din SCENTMANIA. Turaren nan duniya ne, indai nice, cool and soft scent kake so ka nema SCENTMANIA. Ta fice Babu jimawa se gata ta dawo da wata katuwar leda a hannun ta, mamaki sosae ya Kama ni, ta zauna sannan ta dauki wayar ta ta Kira shi, Babu jimawa se ta Fara fadin

" Bribe ne wannan din?"

Bansan me yace Mata ba se Naga tayi dariya, a'a se na sake Baki Ina kallon matar da tuntuni take kuka. Bayan ta dauki wajen mintina ashirin tana waya sannan ta kashe ta dube Ni

" Kinga hakuri ya bani, Wai Bai San me ya hau Kan shi ba"

Na gyada Kai nace

" Batuul kenan!"

Ta Fara Ciro kayan Dake cikin ledar, wani zungureren roasted fish ta ciro, ta baje shi hade da juice ta Fara ce min

" Nasan Baki ci abinci ba, kizo muci"

Na girgiza Kai nace

" Thank you!"

Ta zauna taci abin ta sannan wannan ya wuce. Bamu sake haduwa da Dr Akram ba se da wani sabon satin ya kama, a class Muka hadu zuwa lokacin na Fara ramewa, wani.pills na samu nake Sha, ranar farko da na Sha ko gado na a durkushe nake sakkowa daga kan gado naje toilet, cikina kamar zai fita Dan ciwon da yake min, Amma zuwa dare se da naji jiki na ya Fara saki. Da nasha na biyu ya bani side effects din Amma Kuma Bai Kai ranar farko ba, a hankali Ina sha side effects din na tafiya shikenan se Kuma na Fara ramewa a hankali. Anan naga wata me yawan siyan cake waje na tana tallar wani herbal slimming tea, na saya ta Aiko min na tafasa nake sha, a hankali abunnan Yana bin jiki na Ina Kuma Dan ramewa. Bayan na Gama lecture di na na ranar ya rage se tashi kawai, na Ciro slice cake din da na taho da shi a jaka ta na cinye sannan na Sha ruwa, Babu jimawa se gashi ya shigo, a Karo na biyu ya karaso inda nake zaune fuskar shi da murmushi yace

" Fatima howwa u?"

Nace

" I'm fine sir!"

Ya gyada Kai sannan ya aje min meat pie da Schweppes, nayi saurin fadin

" Sir naci abinci!"

Yace

" Mhmm it's an add more!"

Daga Haka ya juya ya tafi, Alamin da Sadiq Suka juyo suna min dariya, se da yayi gyaran murya kafin dukka muka sake maida hankalin mu Kan shi. Cikin nutsuwa ya gama lecture din mu sannan ya tabbatar Mana akwai possiblity din zaiyi Mana test mu Zama cikin shiri. Yana gamawa ya dake yace

" Fatima ki same ni a office di na!"

Nayi saurin kallon shi sannan Kuma na kalle saura Yan class din mu da wasu ke murmushi, kamar nayi ihu Haka naji, Wai shi baya tsoron bakin mutane? Shi baya tunanin zaace ko wani abun ne tsakanin mu, shi baya wannan tunanin. Har ya tafi ban fara kokarin bin shi ba se da Alamin ya sake yimin magana kafin na tashi na tafi. A zaune na same shi wannan karon Yana cin danwake, har na juya Zan koma ya dawo dani ta hanyar Kiran sunana, na kalle shi yace

" Dawo ki zauna na Gama!"

Ya rufe kyakyawar warmer ya aje gefen table, magani ya ballo ya hada da bottled water ya Sha kafin yayi excusing din Kan shi zuwa toilet ya kuskure bakin shi sannan ya dawo ya zauna tare da ce min

" A Ina muka tsaya Fatima?"

Na danyi kasa da Kai na nace

"Na manta!"

"Ni ban manta ba"

Ya bani amsa Yana sake gyara zaman shi yace

" Me yasa kike son rage kiba, Zaki iya bani labari!"

Wani lokacin wata tambayar se ta dawo.maka da dukkan wasu past and painful memories, a lokaci daya dukkan rayuwa ta tayi flashing ta idanu na. Amma na kasa magana saboda Ina ganin idan na fada Masa zai ga iyayen na Basu da hanklai. Kafin nayi magana se naji yace

" Were you body shamed? Shi ne dalilin da yasa?"

Na gyada Kai na a hankali, idanu na suna cikowa da kwalla wadda kafin nayi kokarin maida ita har ta Fara zubo min a saman kuncin na, se yayi shiru Yana Jin Babu dadi cikin zuciyar shi, dama ya sani baiyi min magana ba, if at all yasan hakan zai Zama sanadin kuka na.

" I'm sorry Fatima, kiyi hakuri bansan zai saka ki kuka ba"

Tashi yayi ya bude backpack din shi ya Miko min handkerchiefs yace

" Share hawayen ki kinji! I'm so sorry Yi hakuri"

Kunsan wani lokacin idan ana baka hakuri kawai se ka Fara sakalci, Nima kawai se naji kamar Yana ce min I should open up to him. Cikin kuka nace

" Ba Wanda yake so na, kowa criticising di na yakeyi akan inada kiba, a gidan mu ba Wanda yake so na..."

Kuka yaci karfi na, yayi shiru Yana kallo na Wai Bai masan actual abin da ya faru ba kenan...

Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 032

Ta zauna tana Masa sannu da zuwa, ya zauna Yana amsawa. Tace

"Ya patient din naka? Ta tashi?"

Ya shafa kan shi yace

"She eventually regain consciousness, na Kai ta gida"

Safiyya ta gyada kai tace

"Abinci fa? Ko kaci?"

"A'a Ummaah! Daddy bai dawo ba?"

A lokacin tayi mishi bayanin Daddy wato Imam ya tafi gaida Ummiey, ta sanar Masa Ummiey har Dada ma na cigiyar shi. Yayi murmushi yace

" Ni fa laifi sukai min Ummaah, Wai naje gaida Ummiey na samu Dada na wajen ta, Nausaiban Uncle Ali taje wajen su kawai suka Fara ce min Wai sunyi min Mata!"

Safiyya tayi dariya tace

" To Banda abinka ai is high time kayi aure, you're turning thirty two in few days Akram, ya kamata zuwa yanzun ka Fara tunanin aure ko?"

Yayi murmushi yace

"Ummaah nace Miki lokaci ne fa, Ni na fada Miki gaskiya ba zanyi aure cikin gidannan ba beside waye zai aure ni na zame Masa burden Ummaah? Ki Bari a hankali Zan samu wadda zata karbe ni regardless of ciwon da ke jiki na"

Ya Dade da fada Mata hakan, dama ai Haka ne barewa ba zatayi gudu a jeji ba sannan ayi tunanin danta zaiyi rarrafe ba. Har yanzun a cikin gidan abin da ake yi kenan, mutane baifi uku Bayan Imam suka auro bare ba, yawancin ma Kuma auren mutuwa yake shiyasa da yawa Basu son aurar bare, Amma shi dai Akram ya kudiri niyyar shi na ba zai aura wata cousin ba, a waje zaije ya samo matar shi ya aura. Beside bashi da lafiya, kullum Safiyya tana Masa adduar ya samu wadda zata kula da shi, ta jure dukkan wata al'alar shi, amma idan ta duba se taga to wacece? Yanzun Mata are lazy kafin Kuma Azo ga extra burden.

" Allah ya kaimu, adduar mu ba zata Fadi ba. I'm sure daughter in law Dita tana wani wajen a boye!"

Yayi murmushi, Haka suke tamkar kawa da aboki Haka Akram yake da Safiyya, relationship din su is very healthy unlike na sauran matar uba da dan miji. Da kanta ta Mike ta kawo Masa abinci, Yana budewa ya saki murmushi tare da dago kai ya dubi uwar tashi yace

" Ummaah Allah ya saka Miki da aljanna!"

Ta amsa da Amin tana Zama inda ta tashi. Iman ta fito da spoon hannun ta, Wanda yasa Akram yace

" To zaa Fara parasitism kenan? Zo mu ci"

Tare suka ci dashishin da ya Yi washar ya Kuma samu wadataciyya Miya ta taushe, sosae Akram yaci Yana ta Mata santi kafin ya kammalla, tare da Iman suka kwashe komai, sallama yayi Mata akan zaije wajen mahaifin shi, a hankali suke tafiya shi da Iman, tana ta bashi labarin birthday din Anwar da akai school, ta Fara lissafa Masa abubuwan da Anty ta raba musu, Yana ta sauraren ta. Lokaci lokaci yana gaida uncles din shi da suke haduwa da Kuma wani lokacin cousins din shi. A Haka suka karasa bangaren Abba da Ummiey inda mahaifin shi da Kuma uncles din shi biyi ke nan. Suka gaisa suna tambayar shi aiki da Kuma jikin shi, ya Basu amsa da Yana lura da kyau. Daga Haka Imam ya mike yayi musu sallama Suka tafi gida. Yana zuwa yayiwa iyayen shi sallama ya wuce wani daki dake jikin na shi, machines ne Wanda suke a gym, daya ya hau bayan ya cire kayan shi ya rage daga shi se singlet da short, timer yayi setting na mintina talatin. Yana kammallawa ya sakko ya dauki ruwa ya.sha sannan ya wuce dakin shi yayi wanka, ya fito sanye da robe. Se da ya kammalla Sanya pyjamas kafin ya dakko wani Dan karamin bakin jaka, wata karamar na'ura ya Ciro ya zura Mata wani stick kafin ya dauki karamar allura yayi pricking Kan shi, Dan drop din jinin da ya fito ya samu ya saka jikin stick din dake jone jikin na'urar. Babu jimawa wasu figures Suka bayyana a jikin na'urar 6.8... ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida ya rufe ya dawo ya runtse idanun shi Dan yin baccin. It has been a long day actually with all Bintus' issues. Se ya Fara tuannin me yake damun ta, from the looks of gidan da ya kaita jiya Babu alamar rashin abinci to Amma me yake faruwa. Haka kawai se zuciyar shi take fada Masa he needs to know the girl ko zai iya gane matsalar ta!
Chapter 30 · 0% Book details