← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 44

Sashe 4

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bansan me yasa maimakon Baba ko Kuma Abba ko ka Daddy, da ywanacin ake Kiran iyaye mu a gidan mu Kawu muke cewa, Haka muka tashi muka hi sauran yayin mu na Kiran shi muma Kuma muka dauka. Asalin sunan mahaifi na Hamisu, mutum ne dogo da Kuma jiki, irin mutanen nan da ake Kira da giant, Kuma Baki ne sosae, Dan kuwa Bai bar gida ba. Labarin da na Baku na rashin son bakaken Mata yasa yake da nacin nema, tun da mahaifiyar shi tace Masa ai fararen Mata masu kyau tsada ne da su, shikenan ta birkita wannan bawan Allah, karatu yayi na primary anan cikin Hadejia, kafin da ya Gama ya taho minjibir yayi makarantar maza ta karamar secondary! Da ya kammalla se ya dawo nan tsohuwar makaranta me cike da tarihi wato Rumfa college da ke cikin birnin na Kano. Anan Yana zaune gidan wani kanin mahaifin shi Kawu Sabaru, daga can yake Hawa Keke yaje makaranta, idan aka tashi ya cire uniform ya kulle a Leda ya tafi kasuwa inda nan ne yake yaron shago cikin kasuwar kwari, idan yamma tayi Kuma ya tuko Keke ya dawo gida. Yana ta fama har Allah ya nufe shi da kammalla secondary School, kamar ba zai cigaba ba Amma uban shagon ya nuna masa muhimmanci da yake gani a tattare da karatun Boko, cikin saa da kullum yake fada, Yana Kuma alfahari da shi din me sa'a ne a rayuwar shi. Ya samu gurbin karatu nan cikin bayero University, dukda Haka Yana kasuwancin shi, Yana Kuma yin taro yadda Baku tunani, a kwana a tashi , karatun shi yayi nisa haka ma kasuwan cin shi, mahaifin shi ya aike Masa da sakon komawa gida Dan an zaba Masa Mata. Kunsan dai ya Riga da yayi alkawarin mace in dai baka ce to Bata da gurbi a cikin gidan shi, Bai Yi musu ba ya tafi Hadejia Dan ganin Mata, Yana zuwa ya tarar da Yar kanin baban shi ce Salamatu, shi yarinyar saboda bakin ta ko magana ba yayi Mata, kuji fa gwano baijin warin jikin shi, shi ma da bakin ne. Ya nunawa mahaifin shi rashin son auren Amma mahaifin shi yace Babu fashi, shikuwa ya tattara na shi ya nashi ya dawo Kano ya cigaba da sabgar shi, aka daura aure kamar yadda aka saka rana, Amma ango har amarya tayi wata guda Babu shi Babu dalilin shi, Haka mahaifin shi ya dakko Salamatu ya taho da ita Kano, ya aje Masa ita dakin shi na zaure Dake gidan Kawu Sabaru. Se dare ya dawo kamar kullum, da bredi na kullum da yake tahowa da shi da Kuma alawa saboda Yara. Yana zuwa ya shiga dakin shi Kamar yadda ya saba, ya cire Kaya ya fito zuwa wani shago Dake makwabtan su yayi wanka sannan ya dawo, se da ya saka Kaya sannan ya lura da dankwali an kulle Kaya da shi, ya saka kafa ya shura dankwalin se Kuma ya dauki biredi da sauran kayan shi yayi cikin gida, Jin sallamar shi yaran Suka taho da gudu, dukda ba kula su yake can sosae ba, Amma dai Yana Basu alawa, shi Kuma alkhairi Yana saka mutum ya Shiga ran Wanda yake bawa, shiyasa kayi kokarin ganin ka kyautatawa mutane.

Ya Mika musu ledar alawar su, sannan ya bawa babbar biredi Dan ta kaiwa mahaifiyar su, anan zaune yayi Ido hudu da Salamatu,  da taimakon aci balbal din Dake gaban ta wadda aka kunna Dan ta haska gidan, ya Bata fuska Yana ayyana wannan mayyar har nan ta biyo shi ko ko me? Suna gaisawa da Inna talatu matar Kawu Sabaru, se ga Kawu Sabarun ya shigo, Suka gaisa da Kawu Dake kokarin juyawa Amma Kawu Sabaru ya dakatar da shi, tabarma Salamatu ta shimfida musu Suka wanke hannu Suka ci tuwo tare, wannan cin tuwon tare implies alot, ya tabbatar akwai gagarumar magana a kasa Yana Kuma fata Bata danganci auren Salamatu ba, Dan kuwa ba zai aure ta ba, ba zai zauna da bakar mace marar wayewa irin ta ba. Idan Kuma suka matsa to gaskiya ba zai jure ba, zai bijire duk abin da zai faru ya faru, wannan shi ne  tunanin da yake yawo a cikin kwakwalwar Kawu. Bayan sun Gama cin tuwo an wanke hannu, Bayan Gama sude sude saboda Inna talatu ba dai girki ba, matar nan da ace a wannan zamanin take, to tabbas zata buge food content Creators da yawa!

Cikin lallami, da Kuma tsara kalamai Kawu Sabaru yayi wa Kawu bayanin halin da ake ciki, na an Riga da fa an daura Masa aure da Salamatu, shi ne dalilin dawowar ta nan, ya kada Baki da fadin Kuma Yana son yayi hakuri ya zauna da matar shi lafiya su samu zuri'a dayyiba. Kawu da yake ta auna kalaman cikin Kan shi, like for real shi akaiwa auren Dole? Ko Kuma bashi Hamisun ba? To su wanne digimi ne ya kaisu entrusting Yar su gare shi, bayan he clearly said it, baya so, baya son ta ba Kuma zai aure ta ba. To fa cikin Abu biyu Dole zaayi daya, ko dai ayi Abu cikin lumana ko Kuma hatsaniya ta biyo baya domin shi dai Bata da space cikin rayuwar shi!

" Kawu Sabaru, gaskiya maganar Allah bana son yarinyar can, bana kaunar ta ba Kuma Zan zauna da ita ba!"

Kawu yayi saroro Yana kallon shi da mamaki a fuskar shi yace

" To Hamisu waye yayi auren soyayya? Ai dukka Hadi akai Mana Kuma gashi mun manta cewa ba soyayya mukai ba! Ka da kake neman albarka..."

"Wannan fa ya wuce Kawu! Ni na fadawa malam (mahaifin shi) ni ba Zan aure ta ba, saboda ni matar da Zan aura ba irin wannan suffar nake so ba"

Mamaki ya Kara kama Kawu Sabaru, ai se ya Fara fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Amma wannan fadan Bai saka ya janye kalaman shi ba, Haka suka rabu baran baran, ya koma daki Yana ta pacing cikin tsukakkaen dakin Yana Kuma nemawa Kan shi mafita, a karshe se ji yayi an turo kofar an shigo, ya dago idanun shi Yana tunanin wanne isashen ne? Se gata a tsaye ta Sha lullubi Wanda ya Bata Masa Rai, maimakon Barin ta ta shigo se ya maida kofar ya barta a nan tsaye.

A takaice kowa baccin bacin Rai yayi, kowa jira yake safiya tayi ya dauki mataki. Asuba nayi ya hade kayan shi tas saboda yasan idan ya aiwatar da abin da yayi niyya to tabbas zaman shi gidan Kawu Sabaru yazo karshe,shi Kuma saboda gurin Zama ba zai cuci rayuwar shi ba. Ana idar da sallah yayiwa Tasha tsinke ya hau mota se Hadejia, shima Kawu Sabaru Yana idar da sallah wanka ya dawo yayi a gida sannan ya dauki hanya se Hadejia!

Ko da yaje gidan su ya wuce, ya samu mahaifin shi ya dawo daga su, wato kamun kifi saboda sanaar shi kenan, Bayan sun gaisa aka kawo Masa tuwon buski da miyar kuka, ya zauna yaci yayi hani'an kafin mahaifiyar shi ta Fara tambayar shi wajen su Inna talatu da Kuma amaryar ta shi? Lafiya kawai yace Mata sannan ya fice zuwa wajen baban shi, ya samu har Kawu Sabaru ya iso Kuma an Kira Kawu Mamman wato mahaifin Salamatu, dukka suna zaune suna sauraron abin da Kawu Sabaru yake fada musu. Ko dar baiji ba yaje ya zauna, malam ya Fara fada se Kawu Mamman ya dakatar da shi yace

" Hamisu baka son Salamatu ko?"

Ya gyada Kan shi, ba tare da yaji ounce of rashin dacewar abin da yayi ba

"Bana son ta Baba, ban shirya aure ba. Ku gafarce ni, bana son zumunci ya lalace, ba Kuma nasan Bata muku, ko Kuma na zalunce ta shiyasa nazo nace muku ni na sawwake Mata igiyar aure na daya dake kanta idan ta samu miji tayi aure"

Kun Yi subscribing top-notch season 3? To kada ku Bari NAZNEEN, BINTUN BATUUL da Kuma GEN NASIR ZAKI ya wuce ku. Wannan tafiyar daban take, labaran daban suke. N1300 for 3, N1000 for 2 and N500 for 1.
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Ayshatuuu

Top-notch season 3

006

Ni fa ban yadda ace Wai wannan matar ba tada kishi ba, kowacce mace tana da kishi, Kuma tana da nata salon yadda take bayyana shi. Dan namiji yace zaiyi aure ba Wai Yana nufin ya gaji da ke ba, ko ya tsane ki ko Kuma irin kin kasa ta wani bangaren, it's a call they answer, raayi ne Haka Kuma yiwa mace kishiya a nawa ganin ba laifi bane ba, Amma dai a dinga kokarin yin adalci da Kuma gane concept din polygamy! A gani na laifi da akw shi ne path din da ake bi wajen auren da Kuma bayan auren, yadda wasu mazan ke muzgunawa matan gidan ko su wofantar da su, wannan shi ne laifi, Kuma Ina ganin abin da yawancin mu Mata muke tsoro kenan, kishiya

Adda ta Kan ce tayi Dana sani tada hankali da dukkan abubuwan da tayi, idan da har tasan Mamaa ce kishiyar. Ni fa a gidan mu nake kasa banbance iyayen mu, su Adda suna da wani exceptional relationship tsakanin ta da Mamaa, shiyasa har zuciya ta bana ganin polygamy as a problem, rather wadan da suke cikin polygamy dinne masu matsala! Bari na fada muku Adda tayi balai, ta tada hankalin ta yadda Baku tunani, a ganinta wannan shi ne karshe, ta Yaya ma zaace Bata shekara biyar ba ayi Mata kishiya, akwai Rights din Kawu da ta daina saukewa, Wai ita tana fushi. A irin wannan lokacin, it's a crucial moment saboda aure zai iya mutuwa, idan namiji baiyi da gaske ba se kaga aure ya mutu.
Chapter 4 · 0% Book details