← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 44

Sashe 37

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowar Uncle Ali yasa tayi.masa sallama ta tafi, Akram na tsaye Yana jiran ta se gata ta fito Suka wuce. Washegari Friday, very early ya fito Dan zuwa office, slice of wheat bread kadai yaci da wani spread din su na masu condition irin na shi, Amma sede ajin na su babu kowa, se ya Kira Alamin ya tabbatar Masa ai ba su day class ne. Washegari ya gaji da wannan wasan Dan Haka kawai ya rufe idanu ya saka Sadiq ya tura Masa contact Dina. Ina tsaka da aiki a daki Dan zaman lafiya a gidan ya Dan wanzu har kawaye na sun tafi, nasan mun kusa Fara exams dole na dage da karatu. Unexpectedly se kawai Naga Kiran shi, bansan waye ba kamar yadda kuke tunani, Ina dagawa yace

" Fatima!"

Yana fada nasan shi ne saboda shi kadai ke Kira na da Fatima ba Bintu ba. Nayi saurin aje gum din hannu na nace

" Sir Ina wuni?"

Yayi murmushi yace

" I'm good fatima!"

Wai Kuma dukka se mukai shiru se shi ne yace

" Kina ji na?"

Nace Masa Ina Jin shi, ya gyara zaman shi yace

" Kawai Ina son naji yaushe zamu Gama session din mu? Ko you're busy!"

Nayi saurin ture kayan da nake hada delivery box da shi nace

" No Babu abinda nake sir! Mu cigaba"

Kunsan dai yawanci Wanda sukje zuwa therapy session Basu kaunar session din Amma ban dani, I was excited ma da zaa cigaba. Ya sake rike wayar a kunnen shi Yana gyara zaman shi saman couch yace

"Ina jinki"

Yau ko musu Babu nayi relaxing baya na a pillow na Fara bashi labari na tun daga abin da Zan iya tunawa har zuwa yanzun! Kunsan se banyi kuka ba, da alama dai zuciya ta ta kekeshe, nayi shiru Ina maida ajiyar zuciya me nauyin gaske nace

" This is all I went through sir! Ban sani ba ko inada laifin discriminating di na da akai a gidan mu, mutanen gari da suke criticizing dina Akan abin da bani da laifi"

Yace

" I'm sorry!..."

Kawai haka yake fada saboda gaba daya zuciyar shi wani irin yanayi yake ji da ba zai iya misalta shi ba...

Ta_kwalam
[1/3, 20:28] Maman: 38

Somewhere in Nigeria

Gloves din hannun shi yayi saurin cirewa tare da tashi daga Kan cadaver da yake examining, wayar shi ya dakko da take ringing a Karo na biyu, Yana dubawa yaga Babu number se de anyi hiding din caller ID din, ba tare da damuwa ba yayi swiping green ya dauka tare da karawa a kunnen shi Amma baiyi magana ba, daga dayan bangaren cikin harshen turanci Wanda kana Fara sauraro zaka San turancin second language, saboda yadda take fitar da kalaman zaka fahimci akwai wani yaren da ya riga yayi staining harshen ta.

"Sadik Garba?"

Ta tambaya a hankali, yayi murmushi dan a take ya fahimci wacece, wannan kusan shekaru uku rabon da ta Kira shi, Bata taba barin ID din ta a bude ba, so idan ba ita ta neme shi ba, Babu yadda zaayi ya neme ta.

"Ma'am kwana biyu!"

Tayi murmushin Jin har ya Gane ta tace

" Ina lafiya! Ya Akram yake? Ya jikin shi? Yayi aure? Ya Gama makaranta?"

Yayi murmushi Yana zama nesa da examination table din da cadaver yake Kai yace

" Akram Yana lafiya, Babu wani episode da ya samu a shekara biyu da Suka gabata. Ya samu aiki Yana lecturing a wata prestigious University!"

Wani farin ciki ya saukar Mata tace

" Baiyi aure ba?"

Ya girgiza Kai yace

" Har yanzun dai babu wannan maganar a kasa!"

Ta gyada Kai tace

" Nagode! Bank details din ka sune har yanzun?"

Ya gyada Kai, kafin yayi Mata sallama har ta kashe wayar!!!

***

"Fatima!"

Ya fada a tausashe, na Dan ja numfashi kadan nace

" Sir!"

"Yana cikin abin da mu Dan Adam mukai lacking, da farko se kin so kanki kafin wani ya soki, you've to accept yourself before others accept you! Fatima Mata nawa ne suka fiki kiba, Suka fiki baki Amma suna rayuwa cikin farin ciki? Kinsan me yasa? To saboda sun rufe kunnuwan su Kuma suna alfahari da yadda jikin su yake, kema da haka kikai bana tunanin abin da mutane suka fada zai dame ki. Shi Dan Adam da Kika gani ko ubangiji da ya hallice shi baya iya Masa, Dan Adam bawa ne marar godiya, baa iya masa komai se yayi magana. So you can never impress people just impress yourself kiga yadda mutane zasu manta da sunyi criticizing din ki!"

Maganganun shi sun shiga kunnuwa na, Kuma sunyi sinking cikin Kai na, Kuma Haka ne tabbas idan Kai baka so kanka ba, kayi alfahari da kanka ba to duk duniya Babu me yi maka hakan, for the world to recognize you, you have to accept yourself. To Amma ta Ina Zan Fara ganin Kai na a matsayin Nima na Isa?

" Sir it's hard!"

Yace

" Na sani Fatima, shi ne next abin da zamuyi. So yanzun Naga an kusa daura lunch, don't just stay in your room. Go and help out!"

Nayi murmushi Wanda I'm sure yaji sautin shi nace

" Sir nagode! Sir nagode!! Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, thank you so much sir, I'm very grateful ! Nagode..."

"A'a tun kafin session din ya Kare, kada ki damu anything for you. Just make sure you saved my contact kinji!"

"Right away sir!"

Na fada Ina Jin wani Abu a kirji na, da wani farin ciki me sakawa kaji kamar a gajumare kake... Bayan na kashe wayar se na Fara kokarin saving contact din nashi, Amma bana son saka sunan shi, nayi ta kawo sunaye cikin Kai na Amma a karshe se nayi Masa saving da *Noor* kunsan me yasa? Saboda a rayuwa ta Akram haske ne da ya haska tawa rayuwar , ya Kuma haska min hanyar da nake takawa.

A bangaren shi kamar wani Wawa Haka bakin shi ya kasa rufuwa, dukda tausayi na na gaske da yake ji Amma se yake Jin zuciyar shi is light like a feather, yake Jin kamar yayi ihu saboda murna Amma se yake kokarin suppressing hakan ta hanyar murmushi kawai. Sallamar Safiyya tasa yayi saurin aje wayar tare da mikewa har lokacin curve din da labbansa sukai saboda murmushi ya kasa gushewa, bayan ta aje tray din data shigo da shi ta zauna, shima ya zauna Yana gaishe ta, ta amsa tana fadin

" Menene labari, saboda fuskar ka ta nuna akwai abin da ake so a fada min!"

Yayi dariya yace

" Ummaah ya ake Gane idan ana son mutum?"

Ta dan bude idanun ta da kyau tana kallon shi, da farko mamakin tambayar tayi Amma a karshe adduar ta Allah yasa ya samu wata Yana son ta ne!

"Mhmmm! Ya danganta da me kake ji. Can you share with me?"

Ya gyara zaman shi, Dan Yana daukar Safiyya tamkar kawarshi ba mahaifiyar shi ba, saboda itama kamar aboki ta dauke shi ba dan ta ba.

" Ummaah Ina kin tausayin ta sosae da farko, ko na rabu da ita lokauta da dama se naji Ina son sanin me take Yi? Ko Kuma me yake faruwa da ita a wannan lokacin? Ummaah idan Ina magana da ita I feel the happiest a rayuwa ta and I cherish every moment da mukai magana da ita. Idan bata kula ni ba, Ummaah hankali na tashi yake. Kwana biyunnan I've checked har Google ko Zan ga da gaske son Fatima nake Yi"

Safiyya har lokacin Bata dai na murmushi ba, Dan ita din sarauniyar hakan ce Kuma hakan weapon din ta ne, tace

" Son ta kake, wannan shi ne feeling din soyayya Akram"

Se taga murmushin fuskar shi ya dauke, kamar tsoro ta gani saman fuskar shi Wanda ya Bata mamaki tace

" Are you scared? Why"

Yace cikin rauni

"Ummaah ta Yaya zata aure ni Bayan Ni bani da lafiya?"

Tace cikin kwantar da murya

" Kayi Mata bayani? Kace Mata kana da diabetes?"

Ya girgiza Kai yace

" I'm scared Ummaah! Kar tace ba zata iya daukar wannan burden din ba"

"Ba zata ce ba, Kai fa kace min she's very good,she has a pure heart ko? To kayi kokarin winning tata zuciyar. Ai nasan ba se na koya maka ba ko?"

Yayi murmushi a kunyace, Yana son Safiyya yadda take Kara karfafa Masa gwiwa. Gaba daya ranar Haka ya karasa ta cikin walwala da annashuwa, ji yake kamar ya tsinci hakori...

🎵🎶 _So idan ya Kai so, abin da baka zato kake yi_
_Baka gane haske balle duhu se ka sauka layi_
_Al'ajab na so ko da wanne lokaci ya kanyi sauyi_
_Bai da tausayi, Dan kuwa Bai barin gangar jiki cikin sauki_ 🎶

"Abbaa"

Safiyya ta Kira sunan Imam a hankali lokacin da ya Gama Shan tea din shi na kullum kafin ya kwanta, ya dago ya kalle ta Yana kokarin plugging system din shi jikin socket, ya juyo yace

" Akwai magana ne?"

Ta gyada Kai, hakan yasa ya koma ya zauna tare da Bata dukkan hankalin shi, tace

" Akram dazun munyi magana da shi, da alamar ya samu yarinyar da yake so..."

" Yar wacece?"

Tun da ya Fadi hakan ta fahimci yayi tunanin a nan community din su yake nufi, tayi murmushi tace

" Amma kasan barewa ba zatayi gudu Dan ta yayi rarrafe ba ko?"

"Me kike nufi"

"Eh Ina nufin outsider ya samu, Kuma nayi Masa alkawarin nu da Kai zamu Goya Masa baya dari bisa dari. We need cross breeding!"

Imam yayi murmushin cross breeding din da tace, yace

" Shi kenan, idan ya Baki details din yarinyar se na saka ai launching bincike akan ta ko?"

Se ta saki ajiyar zuciya tace

" Duk ba wannan ba, yaushe zamu fada masa shi din Yana da wata uwar bayan ni. Nasan yasan bani na haife shi ba, Amma Akram yayi min Kara da Bai taba nunawa yasan bani na haife shi ba. So Dan Allah Abba Ina son muyi Masa bayani, he owes her addua ko da Bata Raye"
Chapter 37 · 0% Book details