← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 44

Sashe 14

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina ganin yadda jikin ta yayi sanyi, se ta biyo ni bayan ta tattare kayan cikin Leda, se mamakin ta nake Baki bude, mamakin karfin halin ta da Kuma karshen rashin kunyar ta kawai nake gani, Amma Kuma har lokacin Ina ganin ba Haka bane ba.

"Samiha..."

Tayi saurin katse ni hade da fadin

" Kinga Bintu, nasan Zaki ce ko na yudare ki, ko Kuma na Miki snatching Amma Kinga ba Haka bane ba..."

"Menene Samiha? Ina kallon yadda kike mishi murmushi fa"

Ta saki wani murmushin da ya sake Kona min zuciya tace

"He chose me Bintu, a gaban ki yace ni ce type din shi ba ke ba, Kinga idan akwai me laifi Bashir ne bani ba. Ni kawai dama na samu Kuma na bi, so I'm not at fault!'

"Dukka friendship din da mukai karya ne kenan? Samiha dama Haka zakiyi min, kinsan yadda nake son shi ko?"

Se kawai ta girgiza Kai tace

" Don't push yourself hard Bintu, kije ki aura daidai dake!"

Wannan maganar ita ce tafi duka na a kaf abin da Samiha ta fada min, na juya a hankali na koma daki na lalubo waya ta na Fara Kiran shi, se da na Kira sau biyu ana uku sannan ya dauka,

"Kaje gida lafiya?"

Shi ne abin da na Fara tambayar shi, haushi Kuma na Fara ji bayan maganar ta fita daga Baki na. To Amma ya zanyi? Son shi nake Kuma bana tunanin akwai abin da zai canja wannan son, a hauka na fa!

"Naje lafiya Bintu, kiyi hakuri abin da ya faru, I know I did a mistake da ban tambaye ki picture din ki ba, amma kiyi hakuri I can't continue with you!"

"Ka Manta kace min fuskata doesn't matter, what matters is kyakyawar zuciyar da nake da ita, so it was all a lie..."

"Ba Karya bane ba Bintu, I loved you wholeheartedly!..."

"Then me kake Yi yanzun?"

Yayi shiru ya kasa ce min komai se kawai na saki wayar ta fadi akan terrazzo flooring din dake wajen, nasan ta fashe, waya ta C2 ce da kawu ya siya min, na tafi na dakko katon Dutse tun karfi na na fasa wayar tare da taune sim din, meye ya rage? Meye Kuma amfanin wayar? Dama Dan shi nazo da ita, to it's all over then what's the essence? Ina nan tsaye Ina rike da kirji na dake zafi na hango Samiha ta fito da waya a kunnen ta, yadda kuka najr na shake ta Haka nake ji, Amma se kawai na juya zuwa daki. A wannan Daren kwana nayi banyi bacci ba, ga shi ni daya ce cikin dakin, wani irin dare ne na bakin ciki a gaba dayan rayuwa ta, bana fata wani ya dandana abin da na dandana a wannan Daren. Se komai na rayuwa ta ya Fara dawo min, tun daga Kan yadda Yan gidan mu suka ta tsangwamar ta Akan kiba ta, da yadda kowa ma idan na fita yake kallo na kamar wadda nayi laifi, se naga to ai bani da amfani, meye amfanin rayuwa ta gaba daya? Idan na cigaba da numfashi Haka Zan ta kullar bakin ciki, Dan Haka na mike zuwa locker ta na bude Dan lokacin shida na safe, Ina bude locker se ga kwalbar Dettol, a hankali dukda wasi wasi da nake Yi Amma na dauka Ina bude murfin...a Raina Fadi nake

" Bari na mutu ko Zan huta da wannan rayuwar!!!"

Har yanzun Wai bakiyi subscribing tafiyar top-notch season 3 ba? Kinsan kuwa irin fascinating stories din da Muka zo dasu? Wannan karon fa ba TSINTUWA bace ba, ba Kuma ASHRAF bane ba balle SANIN GAIBU!

Magana ake ta GEN NASIR ZAKI, NAZNEEN da BINTUN BATUUL. N1300 kacal jama'a
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Top-notch season 3

Ayshatuuu

014

*Kina da kiba? Ko ke gajeriya ce? Ke siririya ce? Doguwa ce ko Kuma ke siririya ce? Are you being criticized saboda hallitar ki? To tsaya kiji wannan halittar, wannan kamanin uniqueness naki ne Wanda Allah ya Baki kyauta! Don't ever look down on yourself, it's your pride, don't body shame yourself*

Shi ya biya min kudin sake registering jamb, zuwa yamma na shirya tare da saka Kaya na na fita, Ina zuwa aka ce min na makara sede na dawo washegari, Haka na dawo Babu yadda Zan yi Haka nan na dawo gida Rai na Babu dadi, washe gari da wuri na fita, kunsan mu a gidan mu muna da a bit of freedom, zaka iya fita ko baka tambaya ba, wannan shi ne kuskure na farko da iyaye ke Yi, Bai kamata ace yaro Yana da so much freedom ba, hakan zai Bata Masa tarbiyya sosae da sosae.

Ko da naje wajen nayi generating remita da komai na biya, sannan na dawo da taimakon su a cafe din na cike komai nayi finger prints, Suka bani wasu books da zasu fito a English part. Ina kammalla na fito Ina kokarin tarar napep Dan komawa gida, wasu samari dake tsaye bakin titi, suna ta Hira, tun da na taho suke kallo na, kunsan Ni bana fita idan ba dole ba, bana kuma Shiga cikin mutane, ko yanzun da Zan fito Babu yadda Zan Yi shi yasa na fito. Ina tahowa daya daga cikin su yace

" Kaga wata tana tahowa, kalli wata uwar kiba!"

Har Wanda ma ba dasu yake ba dukka Suka juyo suna kallo na, a take na Fara Jin wani irin yanayi, kamar kasa ta tsage na shige, ko Kuma na ruga a guje na buya Amma Babu halin hakan tun da na riga da na taho.

"Yanzun fa se tace ita budurwa ce, Ina salis shi ne me son masu kiba"

Ina tunanin wannan shi ne salis din yace

" Kaiiii! Barta dai yau waye zai aura wannan abun, ruguzaza!"

Kunsan wani lokacin kana ji Amma se kaki ji, ka gani kaki gani. Akwai wani human instinct da mutum yake da shi, ability mutum ya saurari abin da yayi niyya. Haka nan na blocking kunnuwa na daga sauraran munanan kalaman su. Bayan na koma gida na tsaya a gaban madubi, Ina kallon Kai na, ta Ina Zan Fara rage wannan kibar? Ta Ina Zan Fara gyara wannan fuskar tawa? Me yasa nake muzanta cikin mutane. Kawai s na Fara kuka a gaban mudubin, nasan Ina da kiba, idan ka kalle ni dukka kiba ce amma to ya zanyi? Ta Ina Zan Fara?

Rashin Sanin yadda zanyi yasa kawai na hakura na cigaba da muamula ta da BashPrince00. Ana Haka Muka koma makaranta mukai jamb, Kuma cikin hukuncin Allah se gani da over 200 score. Nayi murna na Kuma godewa Allah babu iyaka. A Haka dai Muka Fara waec Wanda yasa Muka Fara zaman extension. Wani dare mun Yi chatting da BashPrince00 yayi min albishir din zuwa ya ganni da weekend. Murna da na dinga Yi na kasa tsayawa har safiya tayi na bawa Samiha labari me dadi, a Daren na wuce dakin su na samu tana kwance tana waya, na zauna gefen ta Ina sakin murmushi Wanda tana gani tasan it's something to do with BashPrince00, Dan tasan shi kadai ke sani irin wannan farin cikin.

"Bani labari! Me ya faru?"

Cikin murna da zakwadi nace

" He's coming on Saturday!"

Na fada Ina jujjuya Kai na cikin farin ciki, tayi murmushi tace

" Finally wata zata ga habiebie dinta"

Nace

" Wallahi! I'm so excited Amma Kuma tsoro nke ji"

Na fada har tsoron Yana bayyana a fuskata. Ta Kara gyara zaman ta tace

" Tsoron me kike ji? Why are you afraid?"

Nace

"Mhmmm! Idan yace ban Yi Masa ba fa? Idan yace nayi kiba da yawa fa?"

Tayi murmushi tace

" Ba zai ce ba, ai ke yake so ba wai jikin ki ba, Kuma ya yadda Yana son ki irrespective of kamar ki ko jikin ki. Kullum ina fada Miki BinGin you've a good heart, duk Wanda ya aure ki yayi nasara, your soul is beautiful kumma wallahi fuskar ki Bata da Muni, jikin ki baiyi Muni ba, kullum Ina fada Miki cherish what you have, shi wannan jikin da wannan fuskar kyauta ce Allah ya Baki. Kiyi alfahari da jikin ki, feel proud about it ki daina sunkuyar da Kan ki, kiba ba laifi bace ba!"

Ina ma ace kowa yana tunanin da Samiha take, inama ace kowa mind din shi irin nata ne, Ina ma kowa idea din shi da view din shi akan kiba irin na Samiha ne. Kilan da ire ire na bamu ji rayuwa tayi Mana zafi ba. Har wajen daya Kuna ta shirye shirye da ita, a Karo na farko naji confidence a cikin rayuwa ta, naji cewar Nima mace ce Kuma I can stand out gaban kowa. Muna ta shiru har Saturday tayi wadda ta kasance ranar visiting, dama nace dasu Adda ba se sun zo ba duk wahala ne, Dan su akwai kokarin zuwa visiting, sun dauke shi kamar wani Abu daban. Nayi wanka wajen karfe goma, na shirya cikin goggen house wears di na, na shafa powder na saka khol tare da saka lip balm a lebe na, wannan Shirin da nayi is once in my life, bana saka powder saboda Ina ganin powder daban fuskata daban. Balle Azo zancen su foundation ko wani concealer, Tun ranar dana taba saka foundation zamu je biki Hadejia, na saka skirt da Riga na yafa veil irin yadda suke yafawa, Ina fitowa Zahra ta kalle ni ta tuntsure da dariya, dariyar ta ta janyo hankalin Adawiyya da tazo Dan mu tafi tare, itama ta Fara kyakyatawa

" Wai Bintu waya ce Miki kiyi wannan kwalliyar? Kin taba ganin mutum yasa foundation ba irin skin tone din shi ba"

Zuhriyya da ta gama waya lokacin tace

" Ku bar ta dai ai, ita Abu ba kadan ba kiga wani yafen mayafi da tayi!"
Chapter 14 · 0% Book details