Sashe 2
Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana karasowa inda nake kwance, Wanda suke kusa dani a zaune, already sun baibaye ni, Yana zuwa Babu hesitation kawai ya taba fuskata da hannuwa na, gumin ya daina se sanyi da jiki na yayi kamar mataciyya, flashlight din wayar shi yasa ya haska kwayar idanu na, ganin ta yi dilating, wato ta Kara budewa ya saki ajiyar zuciya, tare da kallon sauran Yan class yace
" Who's the class president?"
Alamin ya daga hannun shi, cikin sauri ya wulla Masa key din motar shi ya fada Masa model din ta sannan yace
" Idan ka bude ta, a backseat akwai wata bakar jaka, in 30 seconds nake so ka kawo min"
A guje ya fita, Ema ya bi bayan shi, Basu Sha wahala ba se gashi Ema ya dawo da Jakar shi Kuma Alamin ya tsaya locking motar, wata na'ura Yar karama ya Ciro, ya zura wani strip a ciki, sannan yasa allura ya caka hannu na, a take jini ya bayyana, ya disa a strip din sannan ya jira har na'urar tayi reading, kowa se kallon shi yake in amazement, kadan ne Suka fahimci abin da yake yi, Wanda ko ni da idanu na biyu bana tunanin Zan gane me akeyi.
" 1.8?!"
Ya fada bayan numbers din sun watso a jikin screen din na'urar, fadar da yayi kamar me tambaya kamar me mamaki, suna tsaye ya saka min ruwa Wanda kafin 50mls su Shiga jiki na, na Fara kokarin bude idanu na, tare da kokarin tashi na zauna amma ya dakatar dani ta hanyar fadin
" Be calming down! Ki Kara hutawa!"
Ya fada Yana mikewa tare da komawa gaban podium, Wanda hakan ya tilasta ma sauran colleagues di na komawa wajen su. Cikin kwarewa da iya koyarwa ya cigaba da exploring din mu cikin course din, yana bayani Yana rubutawa akan farin allon Dake gaban shi, Sanin jiki na ba shi da kwarin da Zan iya rubutu se kawai na kunna recorder din waya ta dan ta nadar min bayanai. Bayan kamar awa ruwan da yake Shiga jiki na ya kare, kafin nayi Masa magana yazo ya cire min, Bai Kara minti na talatin ba ya Mana sallama ya fice!
" Bintu azumi kike Yi?"
Alamin ya tambaye ni, na girgiza Kai na nace
" Ko daya! Abinci ne ban ci ba"
Ya Bata Rai tare da tambayar
" Me yasa? Me Zaki ci?"
Nayi murmushi Ina gyara Zama na nace
" Kawai bana Jin cin komai ne!"
Yayi shiru Yana kallo na na Dan lokaci, Wanda yasa na takura nace
" Alamin!"
Yayi murmushi tare da mikewa ya fita, se ya zamana ni daya kawai na rage a cikin ajin. Nayi shiru deep in thought Ina ayyana dalilin halin da na Shiga dazun, ni dai a rayuwa ta ban taba Suma ba, ban taba fita a hayyaci na but what happened? Se Kuma na Zama curious akan lecturer da ya fita, waye shi? Is he a Doctor and an architect a lokaci daya? Kai hakan ba Mai yiwuwa bane ba...
Shigowar Alamin tasa nayi snapping daga tunanin da nake, in da ya tashi nan ya koma ya zauna tare da aje ledar hannun shi a gaba na,
" Nasan abinci ne Baki ci ba, Haka Dr Akram yace, Wai glucose din jikin ki ne yayi dropping!"
Na kwalalo manyan idanu na waje nace
" Likita ne? Amma me yasa yake koyar da mu?"
Yayi dariya Yana bude min ledar da ya kawo, alala ce se coke me sanyi
"Ko daya, kawai dai yasan abunne, PhD yake yanzun shiyasa Kika ji Dr Akram!'
Na gyada Kai tare da Yi Masa godiya, ya tashi ya tafi Dan bari na naci abinci, na bude Coke din na Kai Baki na Ina ayyana to yaushe ne Zan rage kibar, gashi Ina son Fara slimming Kuma Haka kawai na Fara suma.
A gajiye na fito daga faculty din mu, ni daya kamar kullum, na duba screen din wayata, biyar ta wuce sosae hakan yasa na hanzarta Fara tafiya Dan wucewa gida. Waya ta ta Fara ringing, na Dan dakata a gefen hanya, na dauka kiran
" Maman Anum Ina wuni?"
Daga dayan barin tace
" Lafiya Lau Bintu, kin tashi a school?"
Nasan wani aikin zata saka ni, nace
" Eh yanzun nake fitowa!"
"Yawwa, kinaji ki biya school din su Anum ki dakko su, ki wuce gida da su. Zan biyo na dauke su!"
Na Kara Jin wata gajiya ta sakko min Amma Babu yadda Zan Yi nace
" To!"
Ban jira abin da zata ce min ba kawai na kashe wayar, Babu yadda zanyi Haka na tari me napep ya Kai ni school din yaran, kusan su kadai suka rage baa dauke su ba, suna gani na Ahlam yace
" Ina Mama? Me yasa Kika zo?'
Ko kula shi banyi ba, nayi signing sannan na dube su nace
" Baku iya gaisuwa ba ko?"
Anum ta gaishe ni Amma Ahlam se Bata fuska yake, na tafi da su gida, Muna Shiga suka wuce wajen Mamaa ni Kuma na wuce daki na. Ban Kara saka su a idanu na na se da naji muryar Maman su a parlor, na fito Ina sanye da hijab, tana zaune da su Mamaa har da Adda ma, yaran duk sun baibaye ta, daga shigar Dake jikin ta ya tabbatar min biki taje, na zauna na gaishe ta Amma maimakon ta amsa se ta Fara fadin
" Dan Allah Bintu yaran nan kiga ko Kaya baa canja musu ba, haba Bintu ke kuwa!"
Na kallo yaran sannan na kalle ta Amma bance uffan ba, maimakon tayi min godiya Akan wahalar dakko su day nayi, shi ne tazo take korafi, to Haka kusan dukka Yan gidan mu suke, in dai aikin wahala ne to Ni zasu saka, Amma babu godiya da Kuma zarar an Dan kuskure shikenan se korafi.
Adda da se lokacin tayi magana tace
" Suleiman zai zo anjima ki shirya!'
Na kalle ta Ina marairaice fuska nace
" Ayya Adda wallahi na gaji, banyi karatu ba yau dukka, Kuma na karba order shawarma. Beside Ni gaskiya bana son shi"
Maman Anum ta dube ni tace
" Ban gane Baki son shi ba, ke har option ne dake dama?"
Se na kalle ta da rashin fahimtar abin da take fada, nace
" Kowa ai Yana da option din ya kawo Wanda yake so, ni me yasa ake denying min wannan right din?"
"Tun da kike waye ya taba zuwa gidannan da sunan Yana son ki?..."
Kafin ta karasa kawai se na Mike Dan komawa daki, bansan meye amfanin Adda ba Dake wajen, na rasa gane dalilin da yasa iyayen mu ke kasa depending din mu irin wannan. Ko Dana koma daki se naji na Kara tsanar Kai na da rayuwa ta, na duba mudubi Wanda a kullum nakan kalli Kai na kamar sau goma Naga ta inda Zan Fara rage wannan fat din Dake jiki na, kilan shi ne dalilin da yasa kowa baya so na, shi yasa kowa yake kallo na kamar wata kasakantaciyya.
Har karfe biyu na dare idanu na Basu runtsa ba, Ina zaune saman gado na wayata a hannu na Ina duba online methods na rage kiba, da farko Naga akwai dieting, akwai pills akwai Kuma tea, na kudiri aniyar da gaske wannan karon ko zam mutu se na rame, no matter what!
Na zata abun me sauki ne, na zata idan na rame na Zama Yar caras Zan tsira daga bakin mutane, Ashe ko Mai kayi ba zaka taba tsira daga bakin mutane ba, ba zaka taba burge su ba Kuma ba zasu fasa magana ba!
To be continued...
Top-notch season 3! Kun Yi subscribing kuwa? Ko har yanzun? To ku tuntube mu ta wannan number 09063467258
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_
Top-notch season 3
Ayshatuuu
002
Na Jima akan gadon Ina Jin amsa kuwwar Kira na da golf da abokin shi yayi, me yasa mutane suke min haka? Why am I being criticized akan abin da bani da power Akan shi?
Shigowar Batuul yasa na dawo daga tunanin da nake, ta zauna gefe na tana bi na da kallo, Batuul kyakyawa ce, kamar ta daya da Adda akasin ni da zakuyi mistaken dina for Yar riko.
"Bintu ya kikai da Suleiman?"
Ta tambaya tana bani dukkan attention din ta, na kalle ta da kyau amma bance Mata komai ba,
" Matsala ta Dake kenan, Ina Miki magana kiyi min banza!"
"Ki Kira shi ki tambaye shi Mana!"
Na fada Ina kokarin janyo handouts dita ta intro to landscape design, tana ganin Haka tayi saurin dauke shi saboda tafi kusa da bedside table din akai na, haushi ya Kama ni Akan Wanda already nake ji
" Ai nasan da shi nake tambayar ki, Kinga Bintu kowa na kokari akan ki, duk abin da ake yi Dan ke akeyi..."
Na daga Mata hannu Ina fadin
" Batuul Dan Allah ki tafi, ki rabu da ni, ki kyale ni"
Ina fadin Haka na warci handout din da ke hannun ta na bude na Fara karantawa, wani Abu Dani inada determination, idan na dage akan Abu mussamman karatu, to zaku ga nasara ta same ni cikin hukuncin Allah! Asali bani da kokari ko kadan, I'm always last a ajin mu, saboda yadda suke min akan rashin kokarin hakan yasa na dage na Kuma daura damara, se gashi nayi succeeding, dukda hakan Bai saka anyi acknowledging di na da kyau ba.
Ba Wanda ya sake bi ta Kai na, se bayan maghrib, na idar da sallah na wuce kitchen Dan zuba abinci, rabo na da na ci tun breakfast din safe, anan mukai kicibis da Adda, ban masan ta dawo ba. Na gaishe ta Ina fadin
" Adda sannu da zuwa!"
"Yawwa Bintu, tun dazun kina Ina?"
Na gyara tsayuwa ta Ina karbar yoghurt din hannun ta nace
" Ina daki!"
Aikuwa se ta Fara sababi
" Ke kam kullum kina daki? Baki da gurin Zama se daki? Wai ke wacce irin yarinya ce?"
Nayi shiru Ina tunanin to menene laifi na anan? Yawo ake so na tafi ko mene?
" Karatu nake Adda! Kiyi hakuri"