← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya rungume ta sosae cikin jikin shi wani irin guilt Yana addabar zuciyar shi, dama Haka ake barin? Shi yayi tunanin silently cikin zai fita Babu wani ciwo, Amma me yasa zainab din shi ke wannan irin ciwon hakan? Tsoron kada fa ta mutu yasa ya koma daki ya canja kaya, itama ya samo Mata wasu kayan sannan suka tafi asibiti, cikin gaggawa aka karbe ta a gynae, bayan hoto da akai Mata aka tabbatar da cewar ciki ya lalace, Dan da yawa ma ya fita, suka fito bayan sun daura Mata ruwa hade da Mata allura wadda zata easing Mata pains din da take ji. Imam na zaune a waiting area kamar yadda aka umarce shi da ya zauna ya jira, Yana ganin fitowar mutumin ya Mike tare da nufar shi Yana tambayar yadda jikin ta yake yanzun, se ya tabbatar Masa Babu yadda zasuyi su saving cikin sedd ya saka hannu idan ya yadda ayi Mata wankin mahaifa. Cikin sauri yace

" Will she be ok? Kana ganin Babu complications da zai biyo baya?"

Gaba daya Yana cikin tarin da na sani da guilt, da yaji shawarar Murad ya batta tun da ya tabbatar Masa duk inda ta Kai wata uku zata daina at most ta Kai wata biyar. Me yasa tausayin ta ta rinjaye shi har ya kara saka ta cikin pains haka?

" Complications din kadan ne wani lokacin ma babu gaba daya, just sign the consent form, muyi mu Gama"

Haka kuwan yayi seda yayi signing sannan ya shiga inda har lokacin zainab bata daina murkususu ba, yaje ya zauna ya ruko hannun ta, idanun shi sun kada sunyi jawur saboda tsananin tashin hankali da kaduwar da yake ciki.

" I'm sorry solace! I've caused you a lot of pains!"

Ta cije bakin ta cikin azabar ciwo, da azabar ciwon zuciya na fitar yaron da ta kwallafawa Rai akai, tace

" Chum I'm sorry, I failed to protect our child!"

Duk mazantaka irin ta Imam se gani yayi hawaye kawai suna sauka Masa daga kuncin shi, me yasa yayi Haka? Me yasa ya raba ta da abin da kullum yasan se tayi zancen shi, se yake Jin kunyar hada idanun shi da nata.

A ranar akai komai, Wanda Bayan an Gama Mata wankin marar baccin da Bata samu tayi ba ya dauke ta ba tare da ta shirya ba. Shima se lokacin ya samu ya runtsa, a hankali ta Fara dawowa daidai duk da kullum se tayi kuka tare da bashi hakurin bata kula Masa da yaron sa ba, duk lokacin da tayi hakan se yaji Babu dadi cikin zuciyar shi, se yaji kamar bai cika masoyin ta na gaske ba, a Haka yayi deciding fada Mata gaskiya, aikuwa tayi ta kuka, tayi fushi da shi Wanda ya zamana shi ne na farko a zaman su, dukka sun wahala kafin ban Baki da Kuma shishigi da yake Mata yasa ta hakura!

***

Fast forward, na cigaba da rayuwa ta, yadda na dukufa da istigfar da Kuma yin abubuwan da zasu saka na dauna yawan tunani yasa na daina kawo suicidal thoughts cikin zuciya ta, duk lokacin da na tuna ma ai na taba attempting kashe Kai na se na ji kunyar Allah nake ji, gani nake na kasance butulu akan tarin ni'imomin da yayi min.

A gidan mu duka sun shiga hankalin su, tun daga kan iyayena har siblings di na ma. Mamaa wuta ta bude musu sosae, akwai ranar da bana mantawa na karba order mocktail na wasu masu bridal shower, Wanda Suka turo zai karba musu ko kadan bana Jin shi, Dan Haka na fito da 500 di ta Dan a siyo min airtime na Kira shi tunda lokacin event din ya kusa, ban samu ko matazu me Mana wanki ba, kawai se na wuce dakin Mamaa na samu sani a zaune Yana kallo, Ina Shiga ana Gama haska series din, na dube shi na marairaice fuska nace

" Dan Allah Yaya airtime zaka karbo min Dan Allah, kaga maghrib yayi bazan iya fita ba!"

Yayi kamar bai jini ba, na sake narke murya nace

" Kaji Yaya"

Yayi tsaki Yana karbar kudin yace

" Uban me zakiyi da Kati da Daren nan? Kede nasan ba saurayi gare ki ba, yau yadda kike dinnan kamar wata giwa ai sede sugar daddy!"

Wannan abun kawai Mamaa taji, aikuwa ta rufe shi da fada kamar zata Kai Masa hannu,

" Baka da hankali zaka fada Mata Haka, idan sugar daddy ne ma Ina ruwan ka, Kai kayi kanka da zaka tanka halittar wani? Wawa kawai!"

Se Kuma ta dawo Kai na tana tambayar me ya hada ni da shi in the first place, nace

" Kawai tsokana ce Mamaa, ba se kinyi fada ba. Yaya Dan Allah siyo min Mana suna jira na"

Ya wullo min dari biyar din Bayan ya maka min harara ya fice, Ina ganin lokacin da bakin shi ya motsa yace

"Shegiya kurbusu kawai!"

Naji wani Abu ya Dakar min zuciya ta, Amma ban kula shi ba kamar yadda kuka sani, se ma Zama da nayi na karba wayar Mamaa na Fara Kiran mutumin, aikuwa ya dauka na bashi hakuri sannan na bashi address din.

Wannan tsayawa da Mamaa tayi min, yayi min dadi cikin rayuwa ta ya Kuma bani karfin gwiwar yin Hira da ita, na Kan fada Mata labarin fitar da nayi idan har na fita, hakan ya rage min yawan kadaicewar da nake Yi, Amma har yanzun ban daina kin shiga mutane ba, ban Kuma daina jin yadda zanyi na rage kibar jiki na ba. Ana Haka aka Fara bada admission, cikin hukuncin Allah na fito cikin Wanda Suka samu gurbin karatu cikin BUK, Architecture din da na cike shi din aka bani, farin ciki ranar kowa a gida se da ya fahimci hakan, naje na fadawa Adda bayan ta dawo daga office, tayi murmushi tace

" Bintu kin tabbatar Zaki iya kuwa? Kinga University da secondary ba daya bane ba. Nasan Dan kin Dan samu luck kin ci exams shiyasa kike ganin kamar architecture din Wasa ne bko?"

Adda ba zata daina muzanta ni Akan da ban kasance me kokari ba, Amma ni dai nasan yanzun kowanne course aka bani bana tunanin Zan Fadi, Dan kuwa I'm determined sosae da sosae! Duk jiki na yayi sanyi, saboda akwai abin da nayi lacking a rayuwa ta, toshe kunne na daga abin da mutane ke fada, ko Kuma kada na bar maganar su ta dame ni tunda mutane ba a iya musu, Amma bana iya hakan ko nayi niyyar hakan se na gagara, shiyasa Abu kadan zaa fada se ya tayar min da hanklai na, yaci ace zuwa yanzun na sike na Kuma Dake Amma ko kadan bana iya hakan.

Kawu ya bani duk kudin da ake bukata na Yi registration da komai, da farko nace Ni hostel Zan zauna Amma Kuma se na fasa tuna cewar yanzun hostel din akwai mutane da dama a cikin shi, Kuma zaa din ga criticizing di na anyhow Wanda ba Zan iya jurewa ba, ba Kuma Zan iya bada amsa ba, se kawai na yadda na bari akan na dinga day, dukda Nisan Dake tsakanin mu. Na Fara karatu cikin hukuncin Allah, da farko it was hard to adjust Amma dana Yi wata daya se na Fara daidaita yanayi na. Bana iya fitowa daga aji duk lokacin da Naga mutane sun yawaita, bana shiga harkar kowa saboda gani nake kowa kallo na yake Yi Kuma babu Wanda zai so yin kawa dani. Ko da nazo da wuri to can baya nake zama Abu na, kullum fuska ta dauke da mask, sannan kayan jiki na ma kadai Kara min kiba suke. Idan Babu kowa a class to Zan saka earpiece kunne na Dan kada ma naji wani Abu da zai Bata min Rai na. Ranar Ina zaune Babu kowa cikin aji, Ina nufin lecturer, se mu kadai suna ta hayaniya, nayi shiru Ina rufe idanu na cikin tunanin duniya, se naji an taba ni, nayi firgigit na bude idanuna, wata Mata ce zatayi wajen shekaru ashirin da biyar zuwa sama, ta zauna kusa dani tana fadin

" Sannu baiwar Allah!"

Nace

"Yawwa!"

Se tace min

"Ina kike Kai Babyn ki raino kuwa?"

Se naji wani banbarakwai wani namiji da suna...nace

" Bani da Baby, banyi aure ba"

Kunsan wasu ba suda hankali ko kadan, instead ta tashi ta tafi se cewa tayi

" Ke din? Tabdi me Kika tsaya Yi har yanzun bakiyi aure ba?"

Nayi Mata banza ban Bata amsa ba, maimakon ta tafi se ta dauki ID card dina na school Dake makale jikin lanyard, a jiki akwai date of birth, a take tayi wani exclamation

" Ke din ce shekarar ki Sha shida? Tabdi kina da girman jiki wannan ai we can mistaken you for someone of fourty years!!!"

Kunsan menene? gaba daya idan kuka duba harshe bana tunanin anatomically akwai inda Kashi ya tokare shi, shi din tsoka ce amma Kuma tafi mashi kaifi, harshe masifa ne saboda shi yake magana, akwai lokutan da yawa da connection din da harshe ke dashi da kwakwalwa yakan tsinke, harshe ya ta fadan abin da Bai kamata ba. Kunga wannan abin da ta fada min, Wai nayi Kama da Yar shekara arbain se naji gaba daya zaman ajin ya gundure ni, tana ta surutu na Mike tare da daukar jaka ta na fita, Ina tafe Ina ayyana how old am I looking? Shiyasa Ashe idan naje submitting Abu se Naga ana cemin Hajiya? Hawaye ya Shiga sakko min, ta Yaya ma zaa hada budurwa Yar shekara Sha shida da shekara arbain? Wannan cin mutunci bashi da na biyu. Na karasa gida na cigaba da tsayuwa gaban mirror din dakin mu, na kalla fuskata, bani da kibar fuska in fact hallitar fuska ta irin ta Yara ce, idan ka dauke Baki da kurajen ta bana tunanin akwai wani abun assha a fuskar, na duba jiki na, a take na Fara kuka Ina ganin nayi kiba da yawa, a ranar se Naga kibar tafi ta kouaushe fitowa ma...

Ta_kwalam ce

BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI is not free! Contact the writers to make payment.
[1/3, 20:28] Maman: 022
Chapter 20 · 0% Book details