← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 44

Sashe 10

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwanakin da suka biyo baya har yaranta masu aure ta Kira akan su zo su roki kawu ya fasa maganar, Yaya Auwal yayi ta Mata dariya Wai dama Haka take Sona Bai sani ba, Ni kuwa se shiri na nake a hankali ni da Mamaa. Adda a karshe ta hakura ganin Babu Wanda yake Jin abin da take ki, ita dama mutum ce me so yaranta, dannewa take saboda Mamaa, Kuma yadda Mamaa ke wahala da mu ko ita Bata Yi rabin hakan ba. Kafin na tafi Adda da kanta ta kaini katsina, muka kwana nayi musu sallama, kowa na ya yimin fadan nayi karatu banda wasa ban da kuma abokan banza, daga nan se gidan su Mamaa Muka wuni sannan Muka wuce Hadejia muka kwana. Bayan mun dawo yasa Yaya Auwal ya kaini gidan Yaya Fatima da Fadima, Adawiyya da Zuhriyya.

A fateful Monday, shi ne ranar da na bar Kano na tafi Niger, Mamaa da kawu da Batuul da sajida sukai min rakiya, ban masan ko murna nake ba ko kuma akasin hakan, na dai San kafin na dawo Yan gidan mu sun manta da ni tunda dama can ba Wai suna so na bane ba a tunani na kenan! Se da aka Gama komai na tafi hostel kafin suka tafi, tun da Muka shiga makarantar aka Fara checking Kaya na ko akwai contrabands Batuul ta Fara kuka, ai da na Fara Jan  akwati na se ta biyo ni ta rungume ni tana kuka, Amma naji wai I made a bad decision ko daya banji ba, in fact ji nake Dan Allah su tafi su barni!

Ina shiga hostel aka raka ni daki na, aka nuna min gado na, room captain tace

" Menene sunan ki?"

Cikin turanci nace

" Fatima Bintu Ginsau! From jigawa"

Tayi min murmushi tare da sake min barka da zuwa, se naji Dadi har cikin zuciya ta, kunsan ance shimfidar fuska tafi ta tabarma. Da Kan ta ta nuna min inda Zan jera kaya na da komai, tace nayi sauri nan da 30 minutes sauran student zasu dawo daga games, itama zata wuce wajen su. Na Mata godiya ta tafi na gyara komai nayi wanka na saka sabon house wears di na sannan na zauna akan gadon da na dame da sabon bedspread,ba jimawa na Fara Jin hayaniya alamar sun dawo. Dakin mu mu biyar ne, biyu ajin mu daya, biyu SS2 suke se room captain da take SS3. Babu laifi dukkan su sunyi min magana tare da min barka da zuwa. Washegari na Fara zuwa class, Kuma a ranar na Fara period, ga bani da pad tun da shine karon farko da na Fara period din, rashin Sanin yadda zanyi yasa na tafi wajen Senior Aisha, tana zaune a class na same ta, ta dago tare da min murmushi, na mayar mata a hankali se ta tambaye ni ko akwai wani Abu? Nayi shiru kafin can na kakaro courage na fada Mata, da sauri ta Mike tace na biyo ta, mukaje clinic ta karbo min da kanta ta gwada min yadda Zan saka kafin na tafi.

Zama na a school din Bai canja min halaye na ba, I was still Bintu da kowa ya sani marar son shiga mutane da Kuma hayaniya, wadda take tsoron wanne kallo mutane suke mata, to still Haka nake. A ajin mu Babu me tsokana ta Wai ko nayi kiba ko Kuma nayi Baki, saboda na samu Wanda Suka fini kiba da tsayi, suka fi ni Muni so Babu ma Wanda yake maida hankali Kai na, hakan yayi min dadi Amma Kuma dukda Haka bana iya sakin jiki a cikin mutane. A bangaren karatu naci da nake yasa Kai na ya Fara budewa, na Fara fahimtar abin da ake yi har na Fara ganewa, idan aka zo prep bana hira karatu kawai nake, saboda Haka Yan class din mu suke cemin Bintu nerd! Amma abun da zai Baku mamaki ko a class ake tambaya wallahi ba Zan bada amsa ba, I don't want anyone to notice my existence, gani nake da zarar anyi noticing di na kowa zai Fara aibata min jiki na Yana body shaming di na. Duk ranar kuwa da aka takira se nayi magana a class to kilan se nayi kuka, I lack the confidence da zanyi magana a cikin mutane!

Wata na daya a school, visiting day tazo, dukka Yan dakin mu Bata shiri suna ta buga waya gida suna fadar abin da suke so akawo musu Amma ban dani, Ni ranar visiting din ma bayan nayi wanka se na kwanta Akan gado as though bana expecting zuwan kowa, Ina nan kwance se room captain ta saka a Kira ni, na tashi na fita, ai se na hango Batuul tsaye, mamaki ya Kama ni na ganin su, a hankali na cigaba da tafiya Ina Jin wani Dadi cikin zuciya ta marar misaltuwa ashe nayi missing din su. Tana gani na ta taho da gudu ta rungume ni, Ina murmushi na rungume ta, se na zauna kowa se tambaya ta yake ya school? Dukda ba dukkan su Suka zo ba, Adda da Mamaa da sajida se Batuul da zuhra, Suma anan suka kwana yau Suka zo. Na tambayi Kawu da sauran. Sajida tace

" Bintu kiba Kika kara, ke yanzun makaranta yafi gida kenan!"

Ban ce Mata komai ba, Amma a Rai na gani nake to ba dole nayi kiba ba hankali na a kwance Babu me takura min ko me body shaming di na! Haka ranar ta Kare min cikin farin ciki, da zasu tafi Adda ta Jani gefe tana tambaya ta ko akwai wani damuwa? Na girgiza Kai nace

" Babu komai! I'm happy living here"

Ta gyada Kai tana murmushi tace

" Naji Dadi! You've improved a lot!"

Daga Haka Suka tafi akan zasu sake kwana se washegari su wuce Kano, ni Kam Haka na cigaba da rayuwa ta cikin makaranta har akai hutun farko!

Subscribe for top-notch season 3, @ N1300 only and have access to our beautiful and fascinating stories!

[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Top-notch season 3

Ayshatuuu

011

Haka na cigaba da rayuwa ta, dukda tayi afuwa Amma dai ba kamar yadda kowa yake rayuwa ba, akwai tabon da idan akai ma rayuwan ka to idan ba Kai da gaske ba wannan abun zai ta hunting rayuwar ka har abada! Hutun farko da na koma kano, precisely ma dai satin farko kowa ji yake da ni kamar wani lallaba ni ake, to saboda ban Saba ba, se nake kallon abun odd na kasa sakin jiki na da kowa a gidan, na cigaba da Zama na daki.

Bayan na kammalla session di na na farko, ma sake dawowa hutu, anan na cewa Kawu Ina son naje na koya snacks

" Me yasa? Me zakiyi da shi? Ba akwai kayan girki ba ki koya a gida Mana!"

Na Dan Yi shiru Ina tunanin yadda Zan tsara Masa words din not to sound some how!

" Kawu Ina son na dinga yin snacks din siyarwa ne, shiyasa!

Ya girgiza Kai yace

" Ke Bintu me yasa kin Faye kawo bidi'a cikin al'amuran ki! Karatu zakiyi ko kuwa snacks Zaki dinga siyarwa?"

Nayi shiru Dan bansan me zance ba, se kawai nace

" Kayi hakuri kawu my mistake!"

Yayi tsaki Yana canja channel yace

" Ehhh ai gashi kullum shiyasa ba Zaki daina kiba ba, saboda son ci shiyasa idea Saida snacks ya zo Miki Rai!"

Wani Abu ya sake zuwa min wuya na, na juya na fita mukai kicibis da Batuul zata shigo, tace

" Kawu na parlor?"

Kafin na Bata amsa tayi saurin fadin

" Zanje nace Ina son naje koyon mota, Suleiman can be my couch!"

Na gyada Kai ba tare da nace Mata uffan ba, Amma a Rai na , na tabbatar dole zai barta, aikuwa Bai kunya ta ni ba, zuwa yamma se gata ta ci kwalliyya da key din motar kawu a hannun ta, na dube ta lokacin da nake Zane akan plain sheet din Dake gaba na, nace

" Ya yadda?"

Tayi murmushi tana wulwula key din tace

" Har wani yaji ma, ya yadda nake fada Miki!"

Na gyada Kai na Ina Jin wani kunci cikin zuciyata, is not like ta Kai shekara goma Sha takwas, is not like ni bare ce a gidannan? Then me yasa ake treating di na equally? Ni ba bakin ciki nake ma Batuul ba Amma Dan me yasa ake yin hakan? Menene dalilin wannan partiality din? Na kwanta na Fara kuka wani irin bakin ciki da nake ji, naji na tsani rayuwa ta, na tsani komai, kowa baya so na. Akwai wani feeling na hopelessness, helplessness da Kuma worthlessness, to wadannan abubuwan guda uku su nayi taji, Haka zuciya ta ta dinga yimin wani irin zafi, na dinga Jin kunci. Har hutu ya Kare baa sake maganar ba, se ana gobe zan koma school naje dakin Mamaa Ina sake crosschecking abubuwan da aka siyo min, na karasa dubawa sannan na fada Mata abin da nake son a Kara min tace

" To Bintu! Kawun ki yace Wai kwanaki kin ce kina son kiyi joining classes na snacks?"

Na tabe Baki nace

" Ai maganar ya wuce!"

Ta kalle ni tace

" Ke kinsan matsalar ki? Zuciya, baka zuciya da abin da baka da shi"

Cikin kosawa da maganar nace

" To Mamaa me zance? Komai na tambaya a gidannan baa yarda , kamar baa so na, kamar nayi laifi..."

" Bintu!!!"

Ta fada cikin karaji, kamar maganar batai Mata Dadi ba, Amma yau daya dai Ina son na fada abin da ke cikin zuciya ta, Ina son naji how it feels when one voice out

"Mamaa Dan Ina da kiba ne ko Kuma Dan ni baka ce"

"Zan mareki Bintu idan na sake Jin maganar ki? Waye yace Miki baa son ki? Waye ya takura Miki a gidannan?"

Nima se nayi shiru, bance komai ba, a fusace tace na fitar Mata a dakin ta kafin na Sha Mari, Haka kuwan na tashi na fice, ko awa baayi ba se ga Adda a dakin mu, I'm sure Mamaa ta fada Mata abin da nace me shiyasa tazo. Bayan ta zauna tace min
Chapter 10 · 0% Book details