← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 44

Sashe 13

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ki zaba abin da Kika San Kan ki zai iya dauka, kinsan bana son failure a gida na"

Na gyada Masa Kai sannan nace

" Na saka architecture?"

Yayi dariya yace

" Waye zai iya architecture Bintu? Amma ba ke ba ko?"

Na Dan Bata fuska nace

" Zan iya Kawu!"

Ya gyada Kai tare da fadin

" Then carry on'

Na fita zuwa dakin Yaya Auwal na fada Masa architecture zai cika min, da Kuma makarantar da nake so, ya danyi dariya yace

" Bintu kin San menene architecture kuwa? Ke din ce Zaki iya wani architecture? To Ni Adda cewa tayi na saka Miki education na biology Kuma na Riga har na coke"

Na dube shi wani Abu ya kawo min wuya nace

" Biology education Kuma? Ni me yasa ba zaa ji raayi na ba? Haba Yaya"

Ya shige ya barni a wajen, na koma daki kawai na Fara kuka, nayi me isata sannan na wanke fuska ta na karbo wayar Mamaa nayi dialing number BashPrince00 Wanda na Riga na haddace a Kai na. Ina magana yace

"Princess me ya same ki? Kuka kikai?'

Na gyada Kai na nace Ina Kara sakin wani kukan, ai se ya rikice gaba daya ya Fara tambaya ta abinnda ya faru, aikuwa Ina kuka na fada Masa duk abin da ya faru, se da nayi shiru yace

" Are you sure zai iya architecture din?"

Na gyada Kai na kamar Yana gaba na nace

" I'm determined!"

Se yace

" To Ni Zan turo Miki kudi kije ki sake registration a nearby jamb office!"

Nayi shiru Ina tunanin Anya kuwa na karba kudin shi? Ai Bai kamata ba, se na girgiza Kai na nace

"A'a ka bar shi, I can't accept it!"

"Saboda kin Raina ko? Me yasa kike min Haka ne Bintu? Baki dauke ni yadda na dauke ki ba ko? Kinsan yadda nake son ki kuwa? Ina Jin kamar akan ki I can move the mountain for you and I can melt the snow for you!"

A take fuska ta ta cika da wani annuri me kayatarwa, bansan menene love language din ku ba, Amma nawa love language din is "words of affirmation" Ina son mutum constantly ya din ga tuna min Yana fadin how much I mean to him, yadda yake ji na cikin zuciyar shi, tamkar kuwa Bashir ya sani ko fahimta yayi he always does yadda nake so!!!

Ta_kwalam ce

BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI rubutu ne na kudi, Wanda N1300 kawai ta ishe ka subscribing...
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Top-notch season 3

015...Last free page

Ayshatuuu

*Kece me kallon mutane kice musu sun Yi kiba ko? Kece me kallon su kice ke Kinga ranar da kikai? Kun San illar bakin ku kuwa? Kunsan me maganar ki take jawowa?*

"I finally got to see my BinGin"

Ya fada Yana sake matsawa gefen da Samiha take, yayin da ko second glance Bai bani ba balle na saka ran zaiyi min magana. Wani irin Abu naji ya zamo min wuya na ya tsaya min tamkar an samo katon dutse an saka a gurin. Nayi shiru Ina kallon Samiha dake murmushi from ear to ear, na kalle shi ya lumshe idanun shi duk lokacin da wannan jijiyar ta goshin ta ta bayyana, there and then naji, I've lost this battle, wannan ba fadan da zanyi nasara bane ba, Amma se zuciya ta ke cemin

" Bintu tafiya zakiyi? Ina Zaki je Baki fada Masa kece ba?"

Se na tsaya saboda har lokacin Samiha taki tace ita ce BinGin, ta Kuma taki denying hakan, na cigaba da kallon yadda suke ma juna killer smile Kai ka rantse da Allah kace dama can sun San juna, kamar Zan Yi hakuri Naga gudun ruwan su, Amma a yau se hakuri na ya kare, na gagara yin hakan, Babu shiri nace Masa

" Habiebie na!"

Se ya juyo da sauri, I'm sure ya Gane murnar da Kuma salon da nake amfani da shi duk lokacin da Zan Kira shi da hakan, se Kuma ta juya ya kalla Samiha da murmushin fuskar ta ya Fara daukewa, ya kalle ni wani irin kallo na kada kice kece BinGin, na gyada Kai na nace

" Nice Bintu Ginsau wato BinGin"

"Kece?! How?"

Ya fada cikin wata murya me wani irin amo, nayi shiru na rasa me zance masa, shima se yayi shiru yayun da nakan ga Yana stealing glance din Samiha wadda tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ko kadan ban taba kawowa Samiha zata iya yin abin da tayi min ba, ko da Wasa ban taba kawowa hakan ba. A hankali yace

" I'm sorry Bintu but..."

Se yayi shiru ya kasa karasawa, Kun taba Jin bugun zuciyar ku ya karu har Kuna tunanin Anya wannan zuciyar tawa ba kokarin balls kirji na take ta fito ba? To Haka naji, I was so scared da zuciya ta ta kasa controlling bugun da take, nayi kokarin rike kirjina Wai duk kokari na, na kada zuciya ta ta fito

" Bansan Haka kike ba, kiyi hakuri but you're not my type, bana son Mata masu *KIBA* "

Ya fada idanun shi na Kan Samiha da lokaci daya murmushi ya Kara bayyana akan kumatun ta da fuskar ta. Na kalle shi sosae, na Kara kallon shi a Karo na biyu kafin Kuma na samu brain Dita ta Gama processing maganar da yayi min. Se na fahimci Yana nufin ni Bintu by type din shi bace ba, type din shi Samiha ce, beside baya ma son mace me kiba. Ai ina Gama tantance hakan ban jira wata magana ba, na juya na Fara wulla kafata, a wannan lokacin wallahi na manta cewar visiting akeyi, ko kadan na manta Wai hall din a cike yake da mutane, idanu na ba abinda suke gani, idan kuka dauke memory cells Dake taimakawa kowanne Dan Adam wajen tuna abin da ya Riga da ya sani, to bana tunanin Zan iya Kai kaina hostel. Na manta Wai bana son mutane, na manta wai bana sakewa idan mutane na guri, all that matters shi ne na kadaice. Ina zuwa hostel na Fara cire kayan jiki na, se da na cire tas na bar towel Dake daure a kirji na sannan na zumbula hijab na fita, Ina zuwa waje na samu drum ana Kone kone, a take na zuba dukkan kayan a ciki sannan na dawo, ba Wai Ina cikin hayyaci na ba ne ba, a lokacin I've completely lost my sense, bana cikin hayyaci na ko kadan. Ina zuwa toilet na tsaya gaban katon mirror Dake corridor kafin ka Shiga cikin toilet, nayi ta kallon Kai na, Ina juya Ina kallon tun daga fuskata down to my feet, Ina dadewa ban ga Muni na ba, Amma a wannan lokacin se Naga duk duniya Babu mummuna, Babu wadda batai dacen figure ba iri n, gani nake Babu wani Dan Adam da yafi Ni Bintu kiba a duniya, na wuce toilet na zauna saman toilet seat na Fara wani irin kuka Wanda har yau bana son na tuna wannan ranar

" Shike nan? Ya Kare? Shike nan har an gama? Yanzun da gaske na barwa Samiha BashPrince00 kenan?"

Kai a cikin zuciya ta nace Samiha ba zata taba yimin hakan ba, ba zata taba son abin da nake so ba...lol! I was too innocent, I was too softhearted, I was too kind-hearted also! Ban kawo ko wildest dreams dina Samiha zata iya son habiebie ba. To Amma se na ayyana ya akai har yanzun Bata biyo ni ba, kenan itama ta yadda ta Kuma karbe shi a matsayin saurayi

To dai na Jima Ina kuka, kukan da yasa hanci na Fara zuba, kunne na ya toshe kamar kurma, sannan Kai na yayi wani irin nauyi kamr idan na tashi Zan Fadi. Ban dai na kuka ba se da naji hawaye ya daina zuba daga idanu na kafin na sakarwa Kai na ruwa na wajen minti na ashirin kafin na Mike zuwa daki, Ina zuwa na Fara karkarwa saboda sanyi da ke ratsa jiki na, hakora na suka Fara karkarwa kamar an saka ni cikin kankara. Haka na kudundune cikin blanket Ina wani irin karkarwar sanyi, ku tuna I was only sixteen years old, Kuma dama duk rayuwa ta na kasance bakin ciki kawai nake kunsa, Samiha da BashPrince00 su ne mutanen farko da na Fara samun solace wajen su, se gashi Ashe su ne zasuyi betraying di na, Kuna ganin kuwa Zan iya sake trusting mutane easily? Ai Abu ne me wuya.

Ina nan kwance bansan har lokacin da na Kai a kwance ba, rufin asiri na period nake shiyasa har lokaci yayi nisa bansan karfe nawa bane ba. Ina nan a kwance inata kuka Ina Kuma karkarwar zazzabi. Se da hidaya room mate di ta ta shigo sannan ta ganni a Haka, cikin tashin hankali ta nufe ni tana tambaya ta abin da ya faru, Amma ganin halin da nake ciki kawai se taje ta Kira matron din hostel din mu, Suka dawo tare, sannan Suka taimaka min na saka Kaya suka kaini sickbay, ban ma dai San abin da ya faru ba na samu bacci me nauyin gaske ya tafi dani. Bani na farka ba se yamma can sannan akai discharging di na na dawo hostel Amma ko duriyar Samiha Babu a wannan clinic din har na tashi. Mamaki sosae nake yadda ta iya karkade idanun ta, but can kasan Rai na Ina Bata benefit of doubt, Ina ganin kamar abin da nake gani ba hakan bane ba, a Haka na karasa hostel Amma dakin su na Fara zuwa, na same ta da Yan dakin su sun baje Kaya suna kalla, it's down on me cewar kayan da ya kawo min ne. Da sallama na shiga Wanda yasa ta Mike tana kallo na tace

" Ance Baki da lafiya?"

Ban Bata wannan amsar ba nace

" Ina son magana da ke please, can you step out?"
Chapter 13 · 0% Book details