Sashe 29
Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gyada Kan ta tare da tura Anisa taje taga yadda suke, sede tana zuwa.suna kokarin fitowa saboda ciwon Mara da Kuma bleeding da Safiyya ta Fara tun dawowar su. Da sauri ta koma ta sanar da Ummiey, Ummiey hankalin ta ya tashi tace tayi maza taje ta fadawa yakumbo halima wadda ta kasance kanwa ga mahaifin su Imam, cikin sauri ta sanar Mata aikuwa ta zaro mayafi ta same su har sun Shiga mota, tare suka tafi Bayan an tafi sanarwa Dadan Safiyya abin da yake faruwa. Suna zuwa asibiti aka tabbatar tana da ciki Kuma ya lalace, akai Mata wankin ciki Suka dawo washegari. Yan dubiya da masu tsegumi Haka suka ta zuwa, yayun da Imam ya zauna tsayin daka kula da Safiyya duk kuwa yadda yake cikin damuwa me yawan gaske.
Bayan sati da maganar basu Kara haduwa da Alhaji Gidado ba, maganar ma cikin community din tasu ta lafa, da daddare suna zaune sun Gama cin abinci, kowannen su yayi shiru Yana tunanin zainab, Amma kowa ya kasa furtawa Dan uwan shi Dan gani suke zasuyi hurting feelings din juna musamman shi Imam din. Sallamar mahaifin shi da yaji a kofar parlon yasa shi mikewa da sauri ya nufi wajen, aikuwa Abba ne da Kuma baffan Safiyya, suka shigo suka zauna, a lokacin Safiyya ta fito da mayafi, ta tsugunna ta gaishe su sannan ta kawo musu ruwa.
" Imamu me ya faru?"
Shi ne tambayar da baffan Safiyya ya fara Yi masa, aikuwa a take Safiyya ta fara kuka, Imam ya dube ta da kulawa yace
"Kiyi shiru kiyi hakuri"
Imam cikin kwantar da Kai ya Fara bayani yace
" Nasan nayi laifi Abba, nayi aure Babu Wanda ya sani ..."
A hankali ya Fara Basu labari komai da ya faru har karshe, Bayan ya Gama baffan Safiyya yace
" Me yasa baka fada Mana ba? Kana ganin muna Jin dadin abin da mahaifin mu yakeyi? Bamu Jin Dadi amma mu yaran shi ne ba yadda zamuyi, we want one of you to challenge him. You should have informed daya daga cikin mu da Haka Bai faru ba"
Imam yayi shiru me faruwa ai ta faru, Ina zai San iyayen shi zasu goye Bayan shi.
"Bamu San inda ya kaita ba, Kuma baice Mana komai ba"
Abba yace
" Ya maida ta Qatar, Ina ce baka sake ta ba?"
Ya gyada kai, se Suka ce ya Basu lokaci. Haka suka cigaba da rayuwa kamar Imam ba zai Kai ba saboda kullum dare idan ya tashi sallah se yaji kewar zainab a cikin jikin shi, kullum faking yake Amma rashin zainab, tunanin halin da take ciki na saka zuciyar shi cikin kunci. Safiyya tayi kokari dukda wani lokacin tna Jin zafin zainab tun da kishi gaskiya ne Amma Kuma tana kokarin danne shi. A hankali shekara tazo ta wuce Babu wani labari Haka shima Alhaji Gidado baice komai ba, sede duk kokarin barin kasar da Imam yake Yi ya gagara saboda strings da Alhajin yayi pulling. Safiyya Bata sake samun ciki ba har shekara bakwai tazo ta wuce.
A wannan shekarar Kuma Alhaji Dake da sauran karfin shi ya saka Imam a gaba akan su tafi Qatar dakko yaron shi!
Somewhere in Qatar
Da yammaci jirgin da ya dakko ta ya Isa kasar tata, kuka har ta gaji da yin shi musamman idan ta tuna yanayin da ta bar shi a ciki, ta kalla ko Ina ko a mafarki batai tunanin zata dawo kwana kusa ba,. Se gashi ta dawo ba tare da ta fahimta ba. Gidan jadda ta wuce wadda zuwan zainab din ya daga Mata hankali Amma ganin ta kamar hankalin ta baa kwance yake ba se kawai ta kyale ta, se da ta saka tayi wanka ta kawo Mata abinci Wanda tana cin shi ya dawo ta barta ta huta. Se Bayan kwana biyu zuciyar ta ya danyi sanyi kafin ta sanar ma jaddar abin da ya faru a Nigeria, ba karamin gudunmawa ta bawa daidaituwar zainab ba, wadda Suka fahimci ciki ne da ita. Ana ta raino har ta haifi Dan ta namiji ta kuma saka mishi Akram Bayan dogon deliberation. Kullum idan ta kalle shi mahaifin shi take gani a tare da shi, tana Kuma kewar Imam da Safiyya, lokuta da dama Haka zata shuga daki ko cikin dare tayi kuka ta godewa Allah, tayi tunanin wanne halin suke ciki Bayan tafiyar ta. A Haka shekaru sukai ta tafiya, Babu means din da zatai communicating da shi.
Kullum jiran ta inda Imam zai zo take amma Babu Imam Babu dalilin shi, har Akram yayi shekara uku, a shakarar jadda ta rasu, zainab ta rasa kowa se ita se Akram, she's strong even for the sake of Akram. Se Bayan shekara bakwai, Akram ya Fara girma se ga Imam out of nowhere yazo gurin ta. Ku kaddara irin farin cikin da zuciyar ta zata kasance a ciki!
Refer to page 1
Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 033
Bayan na fito daga office din na tsaya can nesa da gurin, na Fara tuhumar Kai na akan dalilin da zai saka na bude Masa ciki na, menene tsakanin mu? Yaushe ma na san shi da har Zan zauna Ina amsa tambayar shi kamar Wanda yayi bewitching dina irin dinnan! Se Kuma wata zuciyar tace ke kuwa Kika San shi tunda kuwa he saved your life ba sau daya ba, duk da bai san ke din wacece ba, gashi yayi kokarin Sanin matsalar ki Dan nema Miki magani. Se na tuna lokacin da nayi attempting suicide a Niger, I remembered Doctor din ya fadawa iyaye na akan lallai lallai su kaini wajen therapist, Amma kalla sun Kai ni? Bayan na dawo ma baa sake tuna maganar ba Tasha ruwa. Kuma tsangwamar da suke yimin ba dainawa sukai ba. Dan har yanzun zancen auren Suleiman bai gama mutuwa ba Dan ko shekaran jiya se da Adda tayi min maganar Shi, shi ba Kira na yake ba ba komai ba Amma sede yace musu yana ta Kira na naki dauka, na kasa gane abin da gayen yake nufi Dani.
Ban sake komawa class saboda nasan we've closed for the day, na Gama dukkan lecture din da nake da shi a timetable. Gida na wuce kamar yadda na saba, na Shiga dakin Mamaa na sanar mata dawowa ta sannan na wuce dakin mu Bayan na tabbatar Adda Bata dawo ba. Ina zuwa na tarar da dakin a kulle which is odd, Ni nasan bama kulle daki no matter what, kitchen na Shiga na dauki ruwa sannan na tambayi Alawiyya ko tasan Wanda ya kulle dakin. Se tace min ai Batuul ce, tun dazun ta dawo Kuma ta rufe Kan ta a ciki. Se da na shanye ruwan na yadda sachet kafin na wuce dakin, na Fara knocking a hankali, na kusa minti na biyar a tsaye kafin tazo ta bude min kofar. Idanun ta sunyi jawur sannan sun tashi, ko baa fada ba kasan kuka tayi ta godewa Allah. Na Shiga ciki na Fara cire kayana sannan na wuce toilet nayi wanka, anan na Fara kallon ciki na, I can swear Naga yayi kasa ba kamar ko yaushe ba. Tabbas slimming pills dinnan da lemun tsami suna aiki. Har karamar rawa nayi a toilet din kafin na fito, har lokacin Batuul na kwance akan gado tayi rub da ciki se sheshekar kuka take yi, se da na Gama saka kayana sannan na dawo na zauna a gefen gado na yadda Ina iya kallon ta, se Kuma na mike na rufo dakin hade da saka lock a kofar sannan na dawo na sake Zama nace
" Batuul me ya same ki? Me ya faru?"
Ina ga dama neman Wanda zata fadawa take Yi, Dan kuwa Ina Mata magana tayi saurin tashi ta zauna, se da na kwalalo idanu da naga yadda fuskar ta tayi, tayi jawur ga swollen eye na alamar ta dade tana kuka, hancin ta Kan shi diga yake mura har ta Kama ta, na duba kasan daki yadda ya baci da used tissue paper, alamar ta kusa bata roll daya saboda fatar hanci. Rungume ni tayi ta sake fashewa da kuka, a'a se na saki Baki Ina mamakin ruwan da ta sake ballowa, saboda a gaskiya tarbiyya dai Batuul tayi lacking, an sakar Mata da yawa, iyayen ta suna kallo tana abubuwa Amma sun kasa Hana ta. Ni na raaa ma Ina suka saka gaba, idan kudi ne ai Babu laifi muma muna da daidai rufin asiri to me yasa suka barta take hakan
"Batuul me ya faru? Fada min"
Saki na tayi tana kukam tace
" Honorable ne!"
Na saki Baki Dan Ni ban ma gane waye honorable din ba. Kamar ta fahimci abin da nake tunani se tace
" Wanda Zan aura fa! Could you imagine Bintu wai hotel ya kaini Kuma Wai he wants to have..."
Se ta kasa fada min sauran maganar, ni Kuma se yayi Popping Kai na, ance hotel anzo Kuma ance have, ai karshen magana sex ake nufi. Ban wani kidimu ba saboda nasan mutane ba kowa ke tsoron Allah ba, yadda ya dinga Mata ruwan kudi abun zai Baku mamaki amma ba kowa ke hakan saboda Allah ba, wasu suna yi Dan Allah saboda son da suke wa mutum yayinda wasu su Kan yi Dan wani manufar su. I dunno tun ranar da na fara ganin shi, wani dare da yazo zance, irin kallon da yake Mata kawai naji ban yadda da shi ba. To Amma wa Zan cewa hakan Nima da ba yancin kaina na samu ba.
" Me kike tunanin Yi yanzun?"
"Ni bansani ba Bintu, bansan ya zanyi.ba!"
Nace
" Ki fadawa Kawu kawai!"
A take kukam ya dauke tace
" Kawu kuma? Idan na fada musu ai zasu ce a fasa auren."
" To ke meye damuwar ki Dan kin rabu da shi. Hakan Bai Isa gaya Miki jikin ki yake so ba?"
Na fada Ina gyara Zama na, ta girgiza Kai tace
" Ba zan fada ba, kema Dan Allah kada ki fadawa kowa Dan Allah."