← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 44

Sashe 19

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan ihun da take yasa Batuul shigowa da sauri da take sanye cikin jeans da customized rigar su ta graduation, idan ka kalla Batuul zaka rantse ba Yar musulmai bace ba saboda shigar da tayi, ta dame jikin ta, an Sha fixed hair da lashes, ga uban artificial nail da akai polishing din shi aka Kuma je extra miles aka jera stones akai. Wani bingilin veil ne ta yafa Wanda ko kirjin ta Bai rufe ba, Ashe fada sukai kaca kaca ita da Suleiman Akan wannan shigar da tayi, tayi fushi ta sauka daga motar ta shiga napep ya kawo ta gida, tazo dan ta kawo karar shi wajen Mamaa Kuma se me Mana aiki ta sanar Mata ai Mamaa na dakin mu shi ne ta shigo. Juyawa tayi da sauri ta Kira Adda, Kawu dake tsaye window yaga gudun da Batuul ke yi, shima Babu shiri ya zura jallabiyya ya fito, suna zuwa Suka samu Mamaa na daure min hannu na, se kuka nake yayin da ko uffan Bata Kara ce min ba. Adda tana ganin wannan abun kawai ta Fara kuka, se da ta gama daure min hannun kafin ta dubi Batuul Dake tsaye tace

" Ki zauna da ita kafin mu gama magana"

A sanyaye Batuul ta gyada kai, yayin da Mamaa tayi waje, da kawu da Adda Suka bi bayanta, se da suka zauna parlon kawu sannan Mamaa ta dube su dukkan su hanklain su a tashe yake tace

" Me yake faruwa da Bintu? Ko kunsan Reza ta dauka ta yanki kanta? Inda ban zo ba bansan wanne irin yanka zatai yiwa kanta ba"

Kawu ya dafe Kan shi Yana ambaton sunan Allah! Wannan wacce irin siririyar masifa ce ta kunno Kai gidan shi

" Ban sani ba, ban Kuma San me suka fada muku daga makarantar su Bintu ba, Amma koma menene yanzun Bintu tana bukatar a saka Mata idanu, ba a barta ita kadai ba, na fahimci kamar dukkan ku Kuna cikin damuwa, to Amma damuwa zata bayar da sahihin maslaha? Bana tunani..."

"Ina ga Zan aika ta wajen Fadima a sokoto!"

Adda ta fada tana Jin wani irin rashin Dadi cikin zuciyar ta. Kawu ya girgiza Kai yace

" A'a Asiya, gwara ta zauna anan akan mu tura ta wani gurin taje ta zame musu burden.."

"Gwara ta zauna nan, Ni Zan kula da ita, Zan Yi magana da ita, idan tana bukatar likita se muje"

Adda ta dinga Yi Mata godiya kafin Mamaa ta Mike Dan komawa daki ta ganni, Ina zaune na kurawa pillow na idanu, Amma a zahiri ban masan a wacce duniyar nake ba, Batuul tayi jugum se kallo na take, ta Kuma rasa abin da zata ce min, Wanda hakan yayi min dadi Dan bana son hayaniya ko kadan. Haka ta shigo ta same mu, muryar Batuul da ke amsa maganar Mamaa yasa na dawo hayyaci na, na Dan kalle ta, itama sashen nawa take kallo, idanuna da fuskata sun rame kana kallo na kasan akwai abin da yake damu na, ko dai rashin lafiya ko wani abun.

" Tashi muje Bintu!"

Babu musu na mike a sanyaye na bi bayanta, har cikin bedroom Muka je, ta nuna min gefen gadon ta akan na zauna Babu musu na zauna, ta fita se can ta dawo da abinci ta aje min tare da kura min idanu da ya saka ni Babu yadda Zan yi na dauki spoon na Kai Baki na, wani irin daci naji rice din tana Yi, Amma kallon da take min yasa na cigaba da taunawa Ina Jin rashin Dadi a Baki na, se da naci da Dan yawa har naji Dadi a ciki na kafin na Sha ruwa Mamaa ta Fara yimin magana cikin tausashen murya.

"Bintu kinsan hukuncin Wanda ya kashe Kan shi kuwa?"

Ta fada tana ruko hannaye na cikin nata, ganin ba zanyi magana ba tace

" Idan Kika mutu a Haka to kin mutu kafira, duk sallar da kikai, duk azumin da kikai, duk dokar Allah da Kika bi ta tashi a banza. Yaushe Bintu? Yaushe zakiyi wannan danyen hukuncin. Duk abin da rayuwa ta yi ai karki manta Allah Yana tare dake"

Har lokacin ban ce komai ba, tasan maganar ta Bata shige ni ba, hakan yasa ta kyale ni. Wajen yamma ta shirya tace Nima na shirya mu fita, se lokacin nace

" Ina son Zama a gida"

Tace

" Eh ba jimawa zamuyi ba!"

Haka na shirya muka fita, Babu inda Muka je se zagaya unguwa, a hankali naji abin da yake cikin zuciya ta Yana Dan raguwa musamman da Banga wani yayi min wani irin kallon kalla wannan katuwar! Muna Shiga gida ana Kiran maghrib, tare mukai sallah tace na daga hannu na roki Allah gafara Dan tana da tabbacin Allah fushi yake Dani, wannan abin da ta fada se kawai na Fara kuka Jin wannan abun, dama abin da take so kawai taga nayi kenan. Kilan idan nayi kuka akwai tendency nayi magana, magana ta kuwa zai rage min radadi cikin zuciya ta!

A kalla se da Muka dauki sati tare da Mamaa, kullum tana Kan yimin nasiha da nuna min babban laifi na aikata, Adda kullum se ta shigo ta ganni, Haka kawu ma, wannan dan abin da nayi se yasa na samu attention daga gurin iyaye na, na manta da jin wani yace min wai nayi kiba ko wani abu. Hankali na se ya Fara kwamciya har zuciya ta sanyaya na Fara Jin loved and belong!

Sai da akai sati sannan da safe bayan mun kammalla breakfast ta Fara tambaya ta

" Bintu bani labari, fada min me yasa Kika Sha Dettol a school?"

Nayi shiru Ina kokarin battling da zuciya ta Akan na fada ko kada na fada a karshe na bude Baki na, na Fara fada mata

"Mamaa bakwa so na, Babu Wanda yake so na a cikin gidannan, kowa blaming di na yake saboda Ina da kiba Mamaa, Amma Kun manta ai ba laifi na bane ba, Nima da an bani zabi bazan Zama me kiba ba...."

Tayi shiru Allah kadai yasan yadda zuciyar ta take wani irin tafasa, tamkar zata fito Haka take ji, ko itama ta tuna watarana da na taba tambayar ta me yasa basa so na, Amma amsar da ta bani ba me Dadi bace ba

" Laifi na ne Mamaa? Shiyasa Naga rayuwa ta Bata da amfani naga gwara na kashe Kai na kowa ya huta, kunga Kuma ba zaku damu da ganin mummuna a gidan ku ba!"

Wannan karon rungume ni tayi, hakan yasa na Fara kuka ita Kuma tayi shiru Amma dai Bata ce komai ba. A washegari da Kuma nasihun da take Yi min yasa na Fara neman gafarar ubangiji, Ni kaina se naji kunyar Kai na nake, balle Allah, na tabbatar Allah yayi fushi Dani . Na dage Babu dare Babu Rana na dukufa neman gafarar shi, yadda nake rokon Allah se zuciya ta ke washewa, nake Jin kamar ni din wata sabuwar halitta ce. Na Fara mantawa da wani BashPrince00 da Samiha, dukda wani lokacin se naji I'm crazily missing him, Amma idan na tuna abinda sukai min se naji babu wani Abu da ya rage da Zan zauna Ina neman shi. Cikin iyayen nawa su uku kowa kokarin kyautata min yake. Wasu lokutan har Adda idan zata je office se ta tafi Dani dukda ba son hakan nake Yi ba Dan kunsan bana son shiga cikin mutane. Shikuma kawu se ya sake biya min naje na sake advance cake training, to wannan yafi komai yimin Dadi. I got to understand how much flour means to me, I find solace duk lokacin da na Fara kwabi. Cikin hukuncin Allah na Fara karbuwa hadi da naci da nake. Ina yin cake na sako su meat pie da wasu cikin assorted snacks!

Ta_kwalam ce

BINTUN BATUUL, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI is not free!
[1/3, 20:28] Maman: 021

Peacefully zainab tayi bacci har wajen tsakiyar dare se wajen uku na daren sannan ta Fara Jin kamar ana mintsinin ta cikin marar ta, cikin rashin Jin dadi ta Yi juyi tare da Kara stretching kafarta, Amma a hankali se ciwon ya tashi daga mintsini ya koma ciwo sosae, Wanda Babu shiri zainab ta bude idanun ta tangararau, anan ta tabbatar da cewar ciwon da gaske ne. Ta tashi ta zauna a daddafe, taree da kallon gefen ta inda Imam ke baccin shi hankalin shi a kwance, Dan kada motsin ta ya tashe shi se ta Mike zuwa can living room ta Fara safa da marwa, wani lokacin ta durkushe a wajen ta saki siririyar Kara, ciwo yayi ta gaba, har tazo ta kasa ko da daga kafafun ta, gaba dayan su are numb. A hankali taji kamar Abu Yana sauka daga jiikin ta, tana Kai hannun ta Kan wandon sleeping wear din Dake jikin ta se taji danshi, ta saka hannun ta ta shafo kasan a take taji ruwa, ai kawai ta saki wata Kara Dan.tasan definitely jini ne. A gigice Imam ya hantsilo daga gadon, har Yana a dungure ya kunna fitilar bedroom din, sede Babu kowa hakan ya tabbatar Masa tana linving room, cikin hanzari ya nufo in da take durkushe tana kuka Kuma ta damke marar ta. Yayi saurin karasawaya tsugunna gaban ta Yana fadin

" Solace! Me ya faru?"

Ta Fara kuka a hankali tana fadin

"Chum Mara ta, I'm bleeding, I'm losing my baby!"
Chapter 19 · 0% Book details