← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 44

Sashe 3

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fada Ina Ciro Mata tumbler daga inda ake adana su, ta amsa ba tace min komai ba tayi ficewar ta. Ban koma ta kanta ba na zuba abinci dai dai yadda zai ishe ni cikin plate, Amma kafin na dakko spoon town crier gidan, wato Batula Fatima Hamisu Ginsau ta Fara kwala min Kira

"Bintu Fatima Hamisu Ginsau!"

Na aje plate din hannu na Ina kokarin fitowa, Alawiyya me Mana aiki ta shigo tana fadin

"Wani yazo karbar cake a waje uwar daki na!"

Tana daya daga cikin Wanda ban hada komai da su na jini ba, Amma suna mutunta ni.

" Wayyo na manta, Kuma tun dazun ya Kira ni! Bari na Baki Dan Allah ki Mika Masa!"

Ta amsa ni da to, ni Kuma na wuce nayi packaging eight inches fondant cake, se da ta fita kafin na tafi Kiran da ake yimin. A parlon Adda na same su dukka, na gaishe su sannan na zauna bayan Mamaa tace min na zauna

" Ya kukai da Suleiman?"

Kuma Kan ku nasan Kun gaji da karanta sunan Suleiman dinnan, balle ni Kuma da ake tambaya, for God sake magana Bata karewa a gidan nan ko menene?

" Wanne tambaya kike Mata haka Mamaa? Bayan shi Suleiman ya riga da ya fada Mana abin da tayi Masa!"

Adda ta fada kamar zata Kai min duka, na sunkuyar da Kai na, Ina ayyana ko wanne irin sharri yayi min a wajen su? Allah masani

" Duk abin da ake yi ba Dan ke akeyi ba, ba kokari ake aga yadda kuka tashi tare da Batuul ba tayi aure ta barki ba, shi ne Zaki musu rashin arzikin naki ko?"

Nanma bance uffan ba, hakan ya Kara hasala ta, ta cigaba da yimin fada kamar zata ari baki, se da ta gama sannan nace

" Adda, Mamaa kuyi hakuri. Bana son shi, saboda Bai dace ace tsohon saurayin Batuul ni Kuma na koma Kan shi ba."

" Ke Zaki ce ga abin da ya dace, idan an barki wa zai ce Yana son ki, fuska fal kuraje da munin ki a gurin, ke ba jiki me kyau ba!!"

Wani irin dagowa nayi unconsciously, na tsira Mata idanuna da Suka kada lokaci daya sukai ja, wani irin Abu nake ji cikin zuciya ta Yana taso min, a hankali naji trickle din hawaye akan kunci na, kawai se Naga ta cije bakin ta, alamar subul da baka tayi, but who even cares? Mamaa tayi shiru tare da sunkuyar da kanta,

" Na tafi?"

Na fada in between sobs, Kai kawai ta gyada min, na Mike na wuce daki na, na fada Kan gado, na Fara tambayar Kai na

" Menene laifi na? Me yasa ake criticizing di na akan abin da bani da iko akai? Menene kyau? Menene Muni? Ko dai akwai wata alfarma da kyawawa daa Kuma farare masu kyan jiki da suke samu, yayin da muke rasawa?"

Na Jima a kwance Ina tunani kafin Kuma nayi sallar ishai na koma Kan karatu. Washegari na tashi kamar mayunwa ciya, Amma saboda wani Abu da na darsawa zuciya ta cewar ni fa se nayi slimming ko da Zan dai na cin abinci ne gaba daya, ban nema abinci ba nayi wanka na shirya cikin atamfa zani da Riga, na dakko hijab na saka sannan na dauki jaka ta na fita dakin kawu! Yana zaune Yana sauraren radio freedom nayi sallama, ya amsa Yana Dan adjusting volume din radio, muka gaisa yace

" Se makaranta?"

Na amsa da eh, yayi min addua kamar kullum sannan na tafi wajen Adda, ta gama shirin tafiya office, tun abun jiya da ya faru bamu sake haduwa ba, dukda ba karon farko da ta Fadi hakan ba, wani lokacin you can mistaken her for ruko na takeyi!

"Adda Ina kwana?"

" Lafiya Lau Bintu? How was your night?"

Na amsa da alhamdulillah, sannan na juya Zan fita se tace min

" Jira na sauke ki a makaranta"

Kamar zanyi musu se Kuma nace Mata to Amma Bari na gaida Mamaa, na wuce dakin ta tana zaune tana karatun qurani, gani na yasa ta rufe tare da min murmushi tace

" Bintu an shirya?"

Na zauna sannan na amsa ta, na gaishe ta ta amsa tayi min adduar kullum kafin tace

" Nasan Suleiman Karya yake abin da ya fada, ki rabu da shi, kina zaune Allah zai kawo Miki naki mijin"

Hakan da ta fada se ya dada min Rai na, naji sanyi cikin zuciya ta, har bansan nayi murmushi ba, daidai shigowar Adda, suka gaisa da Mamaa sannan sukai sallama na mike na bi bayanta, se da tayi warming motar sannan Muka tafi, da farko tafiyar shiru Babu wanda yake magana cikin mu, se can ta Dan rage volume din speakers din motar,

" Bintu akwai abin da yake damun ki?"

Na Dan kalle ta kafin na girgiza Kai na bance komai ba,

" Kinsan bana son shiru ko? Idan nayi magana Nafi son ki min magana"

Nayi saurin bata hakuri Dan Adda na da temper, nace

" Ba komai Adda!"

" Then me yasa Baki sakin jiki da kowa a gida? Kin maida kanki kamar wata bare"

To me Zan ce mata? bayan su Suka maida ni hakan, su suka Fara nuna min kamar I doesn't belong to them, dole na janye jiki na. Jin nayi shiru se Bata Kara cewa komai ba, se da ta sauke ni gaban faculty sannan ta ciro kudi cikin Jakarta ta miko min, na girgiza Kai na nace

" Kawu ya bani kudi"

" Na kawu daban nawa daban, karba joor!"

Haka na saka hannu na karba, tayi murmushi mukai sallama, a hankali na sauka zuwa class dina mu, kamar kullum Ina cikin biyar din farko da suke zuwa da wuri. Na samu seat na zauna na dakko waya ta Ina sake duba timetable din ranar saboda semester Bata Jima da farawa ba, ban Gama haddace yadda schedules din suke ba!

A hankali ya aje pen din hannun shi bayan ya duba agogon dake hannun shi, karfe takwas saura mintina goma, yasan Yana da class dole ya bar aikin dake gaban shi, wannan ne karon farko da zai Shiga ajin, hakan ya faru saboda sati biyu baya gari, ya dauka suit din Shi ya daura saman sky blue long sleeve din rigar shi, Ya dauki takardun shi sannan ya fita, mintina biyar Suka kawo shi class din mu, Yana shigowa ya tsaya Kan podium tare da gyara zaman glasses idanun shi, dukkan mu muka bada hankali Dan fahimtar abin da zai koyar.

" I'm Akram Imam, I'll be guiding you on design process in Architecture!"

Dukka Muka bada hankali, cikin turanci yake magana, Amma Haka kurum se nake Jim kamar a nesa nake Jin muryar ta shi, idan na dago na kalle shi se na ga Yana yin dishi dishi, na runtse idanu na Ina ayyana abin da yake faruwa da ni all of a sudden, se kawai na daina ji gaba daya, idanuna Suka Fara daukewa duk yadda nake kokarin bude su, wani irin yanayi ne me wuyar na fada muku, gumu ya jika ni sharkaf, kwace ruwa aka zuba min. Inata battling da idanu na, Naga alamar sakkowar shi Yana tahowa, na Fara kokarin composing Kai na Amma Abu yaci tura....

BINTUN BATUUL ba kyauta bane ba, na kudi. Tafiyar ba Ni kadai bace ba, tafiyar top-notch ce a Karo na uku, wannan karon Aziza tana tafe da GENERAL NASEER ZAKI, yayin da Anty Ramla ta kawo muku NAZNEEN duk akan N1500 kacal. Ki biyo mu ki Sha labari
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_

004

Ayshatuuu

Top-notch season 3

Da farko dai sunana Bintu, a gidan mu na Zama tamkar wata shadow ce, wato idan nace shadow Ina nufin Inuwa, shi ne dalilin da Kai tsaye baa Kira na Bintu, sede ace BINTUN BATUUL. Da farko ban gane hakan ba se daga baya da nayi wayo na gane dalilin Kira na da hakan.

Kamar yadda kuka sani, a kasar mu ta gado, wato kasar Nigeria mu nada arewaci da Kuma kudancin kasar, mu din Yan arewa ne Kuma arewar ma north west, wato arewa maso yamma. Da bana gane wannan intersection din se a hankali na Fara fahimtar yadda suke da Kuma me suke nufi. A jahar jigawa akwai wani daddaden gari me tarin tarihi, wanda ake tunanin suna daya daga cikin Hausa bakwai, wannan gari masarauta ce cikin daya daga cikin masarautu biyar da suke a garin na jigawa. Wannan garin kuwa shi ne Hadejia ginsau birnin Doki. 

Kamar yadda kowanne gari zaka ga Allah ya hallitta musu irin mutane, yaren su da Kuma abincin su, ways of living, norms din su day values din su, to Suma a Hadejia suna da wannan! Na farko dai idan ka fiye Baki a jigawa we consider you Bahadeje (No offense, this is the reality) Yan garin bakake ne, saboda suna da asali da barebari, Amma Kuma akwai farare tunda ana samun auratayya tana hada su day wasu! Akwai Kuma miyar kuka, ban sani ba ko sune founders din miyar kuka, Amma mu a jigawa kirarin da ake ma kuka is always "Bahadejiya kin fi giya tsiya" Wai kuka fa ake cewa Haka, gaskiya justice for miyar kuka....lol

Suna da ruwa,  shiyasa suke da kifi, garin Hadejia akwai kifi akwai Kuma ruwa, I remembered duk shekara Kawu zai ce ya tafi Yi musu jaje, either flooding ko Kuma garin is about to flood. Haka dai maganar take. Mahaifi na Dan asalin Hadejia na, tun daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, tun mahaifi na Yana karami Allah yayi Masa son fararen mata, hajja tana yawan fada Mana ko bakuwa akai in dai Fara ce, to ko an aike shi sai saa zai je, da ya Fara girma kuwa kusan duk wadda ya gani Fara se yasan yadda yayi yayi Mata magana, se Kuma yasan yadda yayi ta kula shi ya Fara zuwa gidan su. Wannan shi ne mahaifi na!!
Chapter 3 · 0% Book details