← Book details Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 44

Sashe 11

Bintun Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" So boarding din da kikaje fitsara da tsaurin idanu kuka koyo kenan?"

Nayi saurin fadin

" Kiyi hakuri Adda!"

Se tayi shiru, nasan fada tazo tayi Amma wannan hakurin da na Bata se yasa tayi shiru tana kallon na Ina karasa saka ironed house wears di na. Can kafin ta fita tace

" Har yanzun kina son cooking classes din?"

Na gyada Kai na a hankali, daga Haka ta Mike ta tafi na tare da ta sake magana ba, washegari very early Muka wuce makaranta, bana mantawa a wannan term din na Fara yin kawa, sunan ta Samiha, Samiha yar katsina ce, kyakyawa ce sosae, gata fara Dan wani lokacin se tana magana ka dinga ganin jijiyoyin ta koraye na fitowa. Mutum ce me ibada, me kirki me Kuma ilimin addini. Zaman mu da ita is a form of symbiotic relation, Ina couching din ta abubuwan da akai class ita kuma tana koya min Qur'an da yadda ake gyara ibada. A hankali na Fara Jin dadin kawancen mu da ita, na fara amfanuwa da ita, duk da tana yawan complain din bana sakin jiki sosae da ita but to me shi ne Abu na karshe da Zan iya Yi!

Da akai hutu maimakon na tafi Kano kamar yadda aka Saba, se na tafi Lagos gidan sajida, Wai Bata da lafiya laulayin ciki take, Haka naje na same ta duk ta firgice ta fita a hayyacin ta. Wannan zaman da nayi anan nayi joining classes din, naci da nake da shi yasa nayi wani irin succeeding, aka bani certificate na tafi, a Haka na koma school nan ma bayan anyi hutun na koma gidan ta na cigaba da Zama da ita. Zaman shiru yasa na bude Facebook da wayar ta, nake ganin yadda duniya ke ciki da Kuma gaisawa da mutane. Samiha ta bude min 2go da username dina BinGin wato Bintu Ginsau. Wannan lokacin na daya daga cikin lokaci da nayi farin ciki a rayuwa ta na gaske, Amma se Bai daure ba, Dan Haka se Kuma rayuwar ta sake kwabewa!

Na manta ko 2go shi ma friend request ake turawa, ban dai San yadda nayi coming across wannan gayen ba, nasan dai kawai mun Fara

" Hello" da Kuma "hi" shi ne abin da muka fara exchanging ni da shi, daga baya bacci ya Fara dauka ta, ban manta ba na saka ta a away saboda saboda star di ta ta bar Novice zuwa step na gaba, Wanda nasan ba professional bane ba Amma na manta wanne ne yanzun.

Ko da safe Ina tashi bayan nayi shara da su gayaran gida ma sajida, na hadawa Yaya Saif breakfast, ya fito Muka gaisa Yana ta yimin godiyar dawainiya sannan yaci ya fita, Bayan ya fita n samu sajida a dakin shi tana kwance nace Mata

" Sajida me Zaki ci yau?"

Ta jiya tana kallo na tace

" Alala!"

Na bude Ido nace

" Da safennan?"

Ta tashi ta zauna tace

" Ke Baki San meye ciki ba"

Nayi murmushi na fita zuwa kitchen, na wanke wake, na hada markade na bawa yaron da ke Zama a compound din su Yana matsayin errand boy, na bashi ya Kai yadawo. Cikin lokaci kalilan na kammalla wannan alalar nayi serving din ta sannan na tafi nayi wanka, lokacin da na fito na zauna Kan gado wani Dadi naji cikin zuciya ta saboda gajiyar da nayi. Kullum Haka nake fama wani lokacin idan na gaji se naji kawai Ina ma a koma makaranta. Bayan na Gama shiryawa na dakko wayar Ina logging cikin 2go di na, anan na tarar da messages da yawa har da na BashPrince00 na share ba tare da nayi kokarin dubawa ba, se can da ya sake turo min magana kafin na bude Dan ganin content din messages din

BashPrince00: hello
BashPrince00: are you there
BashPrince00: have you slept off?
BashPrince00: I guess kin Yi bacci, goodnight then and I wish you the sweetest of dreams!

Wannan su ne sakon shi na dare, se na samu Kai na da Sakin murmushi tare da sake rike wayar a hannu na, kamar wadda zaa zo a kwace ta, na maida hankali wajen karanta na safen

BashPrince00: hello princess! Ina fata kin tashi yanzun?
BashPrince00: haba Mana kiyi min reply naji Dadi!

Whoa! Na furta Ina Jin wani irin waves of happiness Yana radiating cikin zuciya ta, awnnnn har princess yace min ya Kira ni da shi, na fada ina Jin kamar nayi winning medal a rayuwa ta. Na Jima da wayar a hannu na Ina tunanin me zance Masa? Se can nace

BinGin: I slept off ne Amma na tashi alhamdulillah!

Tuni se ga reply din shi

BashPrince00: that's a relief princess! Ya Kika tashi? Kinci abinci

Ni Bintu Naga ta Kai na, ai kamar wata wawiya na Shiga girgiza Kai kamar kadangaruwa nayi replying back da

BinGin: a'a tukunna dai

BashPrince00: ki hanzar ta kici kada ki bar Kan ki da yunwa bazan hi dadin hakan ba!

OMG!

BINTUN BATUUL na kudi ne, a daure ayi subscribing N1300 a samu damar accessing NAZNEEN, Gen Nasir Zaki da wannan labarin na Bintu⊂((・▽・))⊃
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Ayshatuuu

Top-notch season 3

012

A hankali ya karasa in da take tsaye, Amma ko da ya tsaya, tamkar ba naughty Imam ba se dukkan wasu kalamai da suke bakin shi Suka kafe, wata irin nutsuwa out of nowhere ta shige shi, kada ma da ta juyo yaga yadda fuskar ta tayi jawur, hawaye ya wanke Mata fuskar se yaji shima kamar ya fashe da kukan, wannan din ba halayen shi bane ba, in fact Bai ma taba jin Wai ya kalla wata mace yaji wani Abu game da ita ba, but who the hell is this girl?

"I'm so sorry! I'm sorry please my Dear!"

Ya fada muryar shi a tausashe, Jakar ta da ta Riga da ta Fadi a kasa ya tsugunna ya dakko Mata, tare da ma Charles signal din matsowa da motar, se da ya bude Mata owner's corner ya saka Mata Jakar a ciki kafin kuma, ya karaso ya Fara fada Mata tazo su sauke ta gida, Amma mirsisi Zainab taki yadda, se da kyar sannan ta Shiga ciki, yayin da Charles yake Jin kamar yayi bindiga saboda haushi, wanne Abu ne Imam ke Yi haka, se wani rokar yarinya yake kamar wani Wanda knots din Kan shi ya kunce!

Gefen ta ya zauna, tare da bawa Charles umarnin Fara tukawa, cikin kunci Charles yace

"Boss what are you doing?"

"Me ye damuwar ka?"

Ya tambaya yana talle Masa keyar shi, Zainab ta dauke Kai tare da murmushi a hankali, ita kawai dariya yake bata, tun da suka taho bayan ya tambaye ta address din ta fada masa wani close by off campus hostel ne. Kafin su karasa ta dubi Imam tare da fadin

" Zan sauka anan, thank you for the lift!"

Ya girgiza Kai yace

" Ai se na Kai ki har hostel, be comfortable!"

Ya fada Yana sakar Mata wani tattausan murmushi, ba tare da ta mayar masa martani ba ta dauke Kan ta, but yunwa take ji, so take taci abinci kamar ba gobe Amma Kuma ba zata iya fada Masa ba, se da suka Isa gaban hostel din sannan ya dube ta lokacin da take kokarin bude kofar da already aka saka ta a central lock. Yace

" Dan Allah just wait a few second please"

Daga Haka ya five ta Dan ja karamin tsaki saboda gajiyar da tayi, Kuma ta kasa fita, Bayan wajen mintina goma se ga shi ya dawo da leda, like a gentleman ya bude Mata motar, ta fito sannan ya Mika Mata ledar yace

" Ban San menene favorite din ki ba, but I was able to buy my favorite for you!"

Kamar ba zata amsa ba, Kuma se ta tuna abin da Mr Fahad yake yawan fada mata, kada ta rinka maida hannun kyauta baya, hakan halayen shedanu ne. Ta saka hannun ta ta amsa tare da fadin

" Shukhran jazeelan!"

Kada ku manta Zainab fa balarabiya ce, so karku Sha mamakin wata Rana kuji Imam ma ya Fara larabci...lol

A wannan Daren Imam ya saka wani Dan Qatar, Murad wan da shi ma daya daga cikin yaran shi ne ko nace abokan shi, shi ne yayi bincike ya Kuma bashi feedback Akan Zainab, hatta da timetable din ta na lecture a hannun Imam ya kwana! Abu ne da Bai taba Yi ba, yasan baya Jin magana ko kadan hasalima dalilin da yasa aka Aiko shi kasar waje. Ya kwanta yayi.shiru a lokaci daya picture din Zainab ya cigaba da haskuwa cikin idanun shi, ya lumshe idanun shi tare da sakin murmushi wnda zaiyi melting zuciyar Wanda akai wa. Sede Yana son tafiyar da komai a hankali kada ya zake...

                                ***

Cikin kankanin lokaci wata shakuwa ta Fara Shiga tsakani na da BashPrince00 babu wani abu da na sani bayan username din shi, Amma yadda yake nan da ni da yadda ya damu da ni yasa zuciya ta ta Fara fada Masa Nima. Akwai lokacin da attention kake bukata, akwai lokacin da matsalar is just for someone to care about you, yadda na koma cikin walwala da farin ciki se na fahimci kawai abin da nake bukata ba Wai ace ni kyakyawa bace ba, Ashe dai attention nake bukata, I need wajen da Zan samu solace!

Tun sajida Bata fahimta ba, har ta fahimci yadda nake yawaita murmushi, yadda nake sakin fuska Wanda da can ba Hali na bane ba ko kadan, hasalima kunsan nafi son Zama a daki. Duk da har yanzun Ina zaman daki amma dai akwai sauyi cikin rayuwata!

"Bintu wai nikam soyayya Kika Fara ne? Naga kina ta murmushi kamar wawuya"

Na Dan kalle ta Ina murmushi da duk kokarin da nake na maida shi na kasa, se tayi dariya tace

"Inyeeee! Yan soyayya. Ai shikenan Bintu, muna tunanin zakuyi karatu Amma ke da Batuul kun dage da soyayya! Ita Suleiman na can ya firgita Mata lissafi!'

Na Kara murmushi nace

" Ni fa bance Miki ba, karatu zanyi, ni da nake son Zama Architect!"

Ta zaro idanu tare da fadin

" To fa da wanne Kan zakiyi architecture din?"
Chapter 11 · 0% Book details