← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 34

Sashe 9

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Allah ya kyauta" ya fad'a sannan ya kalli gefen Mu'azzam "Ibrahim kaima baka kyauta ba meyasa ka d'auki hukunci a hannunka baka bari anzo nan ba?.." Wlh ni yayi min dai-dai" cewar Hajja...

"Ayi hak'uri Abba za'a kiyaye" Mu'azzam din ya fad'a...

Ring din da wayar Abba tayi ne ya dakatar da shi, Amsa wa yayi tare da cewa "shigo ciki Umar gamu nan parlor na" daga haka ya datse kiran...

Sallama Farook yayi a Parlon ido Samha ta zuba masa cike da begen sa kwana d'aya tal da basa tare taji matuk'ar kewarsa, saidai kasan ranta tsoro ne fal dan batasan ainihin dalilin zuwansa ba, gaisawa yayi dasu Abba a girmame tare dasu Momy, har Ammi da kuma Hajja sannan ya bawa Mu'azzam hannu sukayi musabaha, guri ya samu ya zauna gefen Mu'azzam din...

"Yawwa Umar dama so nake nasan ainihin dalilin da ya saka naga Samha a gida, muna jinka" cikin kwanciyar hankali ya shiga warware musu irin zaman da sukeyi da ita na tsawon shekara d'aya da watanni, ba girki kullum yana cikin take away, ga rashin mutunci da take yiwa 'yan uwansa, ga yawo kamar taci kare sannan ya karashe da cewa "wlh Abba yanzu haka Mami na cewa tayi nazo kawai na sallame ta na bata takardar ta, nayi bata Hak'uri amma abin tura tace lallai ko zata dawo dole sai ta gyara halinta shiyasa na yanke shawarar barinta gida na tsawon wata d'aya ko zata gyara sannan ta koyi girki dan tace bata iya bane dan haka wannan dama ce a gareta ta gyara, dan Allah kuyi hak'uri inna bata muku" girgiza kai Abba yayi ya dad'e da sanin Hak'uri irin na Farook ko tsayar gida da take kullum abin magana ne dan tafi kowa zuwa gida ko Nusaiba da Aymana da yake kanninta ne kuma gidansu ne gidan surukansu basa yawan zuwa kamar ta, kai har Samihar ma, idan yayi magana Uwar ta tace daga makaranta ne take d'an biyowa dama yasan wannan lokacin na zuwa sauran laifukan kuma duk Uwarta ce ta ja mata tun ba yau ba yasha nuna mata ta koyawa yaranta Tarbiya mai kyau da kuma girki da tsabta dan ba dole mazajensu suyi tolerating abinda yayi tolerating ba duk da shima hak'uri kawai yake, ganin Zulaiha na zaune lafia da nata mijin haka Nusaiba ba tarbiya d'aya ba su sun koya inda ya dace basu saka girman kai ba, sabanin ita data biyewa uwar ta yau ga ranar k'in dillanci....

"Babu komai Umar ai kamayi mana hallaci mun gode kuma ina baka tabbacin za'a gyara inshaa Allah" gyaran Murya Mu'azzam yayi "Abba nima irin matsala kenan da Samiha, ita abin nata har da iskanci dan har haihuwa bata so planning take ba tare da sanina ba saidai na gano ta..." Zaro ido tayi ta fara rantse-rantsen k'arya, tsawa daddy ya daka mata wacce ta tilasta mata nutsuwa "wato rashin kunyar taki har takai haka mijinki kike karyata anan, kenan kece mara kunyar ba Uwata da kuka lak'abawa"murmushin takaici ya saki tare da fito da pill din daga Aljihunsa ya mik'awa Abba.

"Gashi a dak'inta na same su, saman mirror ta manta" kara zaro ido tayi tare da cewa da k'arfi..

"Wlh bani kad'ai ke sha ba hadda samha tare muke sha, ita ta bani shawara" Samha dake mak'ure gefe d'aya tana kuka, hukuncin Farook yayi mata tsauri da yawa, gashi ko kallon inda take bai ba tun da ya taho, kara volume kukanta tayi..

Shi kuma Farook a zabure ya d'ago jin me Samiha ke fad'a tare da Nuna Samha da hannu baki na rawa.....

_Ash, feeling sick😤🤢, kuyi manage dan ma nayi alkawarin yine yasa nayi, Ku kara hak'uri dani my fans yanayi ne #love you All😍😘#_
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*Kada ka dogara da mutane da sosai, saboda ko inuwarka takan barka kai kadai, ka maida komai naga gurin mai duka (Allah) zai Isar maka akan komai👌🏻*

Duniya Makaranta✍🏼

*page* 3⃣8⃣

______"Dama har ha'intata kike Rukayya(Samha)?" Farook yace cikin tashin hankalin yana kallonta, girgiza kai ta shiga yi hankalinta a tashe matuk'a dan bata tab'a tsammanin wannan abun zai fito fili ba, ta kasa cewa komai sai hawaye dake bin kuncin ta "nagode sosai wannan ne ya k'ara tabbatar min bakya ra'ayin zama dani tun da har kike k'yamatar hada jini dani" juyawa yayi gurin Abba da idanunsa jajir tsabar B'acin rai "Abba zan wuce na barku lafia" ya fad'a tare da bawa Mu'azzam hannu sannan ya wuce....

Dak'yar Abban ya iya Amsa masa, ransa ya matuk'ar b'aci "wannan shine sakamakon da zakuyi mana ko? Ashe ba'ason haihuwa ne aka haifeku? Mahaifiyarki karatun ta jingine gaba d'aya dan kawai kula daku, amma ku karatun ne ya hanaku Ku haihu ko?..."

"Kabar Shegu Mamuda! Matsiyata tirr daku, kun hana kanku haihuwa ita mai yin itama kun mana asara, Allah ya isa kawai ya rage tsakanina daku..."

"Haba Inna ya zakice haka kika sani itama wacce aka yiwa laifin ko batason ni'imar da Allah yayi mata" Ammi ta karb'e ta, harara Hajja ta watsa mata "waike waya sako dake anan?" Gum Ammin da bakinta Dady ya karb'e "nasan Uwata kam bazata aikata Hali irin na wadannan shashashun ba, amma ba laifinku bane duk na uwayen ku" Momy wacce jikinta yayi ta kasa cewa komai dan itama batasan da zancen ba koda wasa bata tab'a ce mata tayi planning ba da har maganar haihuwa tana mata wasu lokuta, itama Umma yi tayi kamar batasan zancen ba, duk suka nuna basu man sunayi ba, aiko fad'a suka sha sosai gurin su Abba da Dady, su Momy ba bakin tarewa....

Sannan Abba yace tun da zaman gida suka zaba gashinan sai suyi tayi, in sun so su gyara halinsu in sun so suci gaba duniya ce ta ishi kowa Riga da zane har kallabi idan kanaso, itama Hajja kamar ta ari baci ta zage su tatas su da iyayen nasu, bamai damar tare ko yayi wani yunk'uri uwar masu gida ce...

Daga karshe tace zata wuce da Aymana Gwarzo dan ta bata kyakkyawar kulawa dan Fatima bata sonta ga 'yan tsurku gefe (cewa dasu Momy) Abba yace wannan saidai a tambayi mijinta har zata fara jinini a tunanin ta zai hana ne.....

Yace su sauka lafia, yanayin yadda yayi maganar alaman ko a kwalar rigarsa, satar kallon sa Aymanan ta take tayi saidai ko kusa bata ga ya damu ba, da gaske kenan ya dena son nata, tab'e Baki itama tayi alaman tafi nono fari.....

***************

Har ya kama handle d'in motarsa Hajja ta zabga mishi kira har da gudunta "kaga Ibrahima dan tsaya mana" juyowa yayi tare da cewa "ya akayi matar" fuskarsa a sake, itama sake da fuska tace "Gwarzo nakeso ka kaimu idan an fito masallaci" dan Jim yayi ita kuma ta kafe da ido "yau wai?" Ya jefa mata tambaya...

"Ban gane azancin yau ba, kaga in ba zakaje ka fad'an banson iyayi" ta fad'a tana fikifiki da idanu "Sorry maida wuk'ar, Ku zama cikin shiri yanzu zan dawo" daga haka ya juya ya shige motarsa tare da ficewa "dan Iska zanyi maganinka ai" tace tare da komawa ciki tana mitar duk halinsu d'aya 'ya'yansu Zainab da Suwaiba sunyi bak'in gado...

Momy kasa zama tayi saikai da komo take a dak'in, Samha na mak'ure kan sofa tana kuka "kin rufe min baki anan ko sai na make ki ne, kamar nina aikeki kiyi abinda kikayi, bayan ko shawara dani bakiyi ba, ke dan Allah tun da kike dani kin tab'a ganin nayi planning? Ko kuma ita Zulaiha kinga tayi planning d'in kuma kina gani duk tana cikin karatun ta haifi Hanif da Husna, kuma ta gama karatun ta lafia ba tare da matsala ba, ka kuma ga 'ya'yanta a hannunta? Amma ke bansan waya baki wannan rub'abbiyar shawara ba" share hawayen idonta tayi "Momy kiyi hak'uri ni kaina ji nake dama banbi shawarar Samiha ba(nifa na rasa gane Wanda ya ba wani shawara a cikinsu? kufa Fans??) itace tace muyi planning kada mu samu matsala a karatun mu, shiyasa na yadda amma yanzu na gane kuskure na gashi Faruuk yayi fushi sosai Momy kila bazai yafemin ba" ta karashe fad'a cikin kuka....

Daga kafad'a Momy tayi duk da deep down tausayin 'yar ne a ranta dan Allah yasan cikin 'ya'yanta tafijin Mu'azzam da Samha a ranta sosai ko don sunfi kama da Abban su ne oho!

"Ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, ke banda rashin zuciya ma irin taki har yanzu son Faruuk din kike duk da rashin mutunci da tujarar da ya gama yi mana dazu kuma suma su Alhaji suka goya masa baya, cewa fa yayi baki iya komai ba a matsayin ki na mace ai karshen cin fuska kenan, me zakiyi da shi ki bari kawai ya kawo miki takardar ki, kije ki auri wanda yaji zai iya sonki a yadda kike yo dama banda son da kika nace akansa ai kowa yasan ke ba ajinsa bace yaje can ya k'arata .."

"Aa Momy wlh inason Faruuk shine dai2 dani, Momy ina matuk'ar k'aunarsa pls Momy ki dena min fatan rabuwa da Faruuk bazan iya rayuwa ba idan bada shi ba" ta katse uwar tare da k'ara volume d'in kukanta, ware ido uwar tayi tare da tab'e baki "lallai kuwa aiki ya sameki saiki yi himma" tace tare da bar mata dak'in gaba d'aya....

"Hajja ce da kanta taje ta d'auko mata trolley kayanta dama komai na ciki, yana dawowa suka d'auki hanya bayan sunyi sallama da mutanen gida, tunda suka d'auki hanya ba mai magana tun Hajja na yi ita d'aya ba mai tanka ta har taja bakinta tayi shiru itama, ba abinda ke tashi cikin motar sai karatun Qur'an, itakam Aymana hadda dan guntun baccinta.....
Chapter 9 · 0% Book details