Sashe 3
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ba a haka ba 'yar galadima, aje a sako hijab, nasan me nakeyi" kallon Samiha tayi da bata da abin sawa a rayuwar ta fiye da gyale bata tab'a ganinta da hijab ba, sai ita da bata cika saka gyalen ba yau ma kawai sha'awar kwalliya tayi "ok saboda kada a ganni ace matarka ce kwaila ko shiyasa kake so na saka hijab ko? na d'anyi girma a ciki, to cool zan saka ba hijab kad'ai ba har nik'ab zan saka dan na boye fuskar itama kada aga kwaila" tana kai nan ta juya kawai....
Dafe kai yayi a rayuwa Aymana na tsananin bashi ciwon kai, kullum sai tana abu kamar bata ganewa kuma ya sani tana sane da komai takeji "Ashe haka take?" Ya fad'a a fili..
Zunbulelen hijab irin na islamiya ta zubo da kuma hadda nik'ab d'in da ta fad'a, abin yayi masa dad'i sosai dan hankalinsa yafi kwanciya a haka, jan motar kawai yayi ba tare da kowa yayi magana ba, wani k'aton Mall ya kaisu ya basu damar zab'en me suke da buk'ata.....
Shi kuwa yaje gurin kayan da yake da buk'atar rabawa mutane na azumi..
Ido ya zuba mata kayan da yaga ta jibgo shaddodi atamfofi zuwa less kamar mai shirin fara d'an business, yi tayi kamar bata ganshi ba ta fuske tare da d'auke kai gefe, ATM card nasa ya basu suka cire kud'in su tare da had'a musu aka kai musu booth.....
"Ke zoki kwashe kayanki anan gabana" yace mata bayan gate man ya gama shigo musu Da kayan ciki, Samiha ta kwashi nata, ita kuma ta mik'e zata bar Parlon...
"Ai naka ne" ta masa mishi bayan ta juyo, kallon kin ma rena ni yayi mata "kamar ya?"
Dawowa tayi ta zauna a k'asa tare da fara bud'e kayan "kayan da zaka kaiwa su Abba ne da su Momy da sauran mutan gidan na sallah" nan ta shiga nuna masa na kowa har da yaran gidan gaba d'aya, har ta kammala baiji ta kira kanta ba..
"Hmm to ai su Abba suna da kud'i basu buk'atar irin wad'annan" ya fad'a fuskarsa d'auke da fara'a dan ba k'aramin mamaki ta bashi ba "haka dai ka fad'a ka fara kai musu idan basu amsa ba tukun kace hakan" na Hajja ta d'auka
"Pls kaje dani mukai wa Hajja tare?" Kallon ta kawai yake "to kefa ina baki?" Ya tambaye ta..
Murmushi tayi for d first time "ni ai inada su da yawa wad'anda bamma d'inka ba sun isheni" tashi tayi tare da shigewa part d'in ta...
Yatsun sa ya nutsa cikin sumar sa tare da shafo ta yana murmushi idonsa kur a k'ofar part d'in nata da ta shige.....
*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*An karb'o daga Baban musa (R.A) yace Manzon Allah (S.A.W) yace Mad'aukakin sarki yana yiwa Azzalumai talala idan ya kamasu bamai kwatar su a hannunsa.*
Husnul Muslim👌🏻
*Page* 3⃣2⃣
______Yadda yaga farinciki a fuskar Abba game da kyautar tasa gareshi, haka ma Dady dasu Momy kowa ya nuna farincikinsa har yaran sai tsalleh murna suke, albarka kam ya shata kamar me cikin fara'a Abba yace "lallai Ibrahim aure ya saka ka k'ara hankali sosai, to Allah yayi albarka kuma ya Baku masu jinkan Ku" Ameen ya fad'a cikin farinciki yana jin wata k'ima da girman Aymana a ransa mai cakud'e da Zazzafar k'aunarta, yana mamakin kaifin basira irin tata, shifa rena shekarunta yake sosai ganinsa banda shirme ba abinda ta sani, koda yake ba mamaki Idan akayi la'akari da 'yar Ammi ce, Ammi renon Hajja da Malam Sa'eed dole duk abinda zata rena ya zamo mai cikakken tarbiya da hangen nesa, murmushi kawai yake yanzu ya k'ara tabbatar da duk shirmen da shiriritar da take masa wato tana sane tana yi kawai kamar yadda ya d'auketa....
Ta baya ya rungumota tare da d'ora kansa akan kafad'arta yana aika mata wasu sihirtatten sak'anni da idanuwan sa ta mirror d'in, k'asa tayi da idanuwan ta, dan bata iya jure kallonsa "Thank you so much Bilkisa ta" d'ago ido tayi tare da kallonsa alaman tambaya..
Kashe mata ido yayi "yap yau nasha Albarka akan ki, Allah yayi miki albarka my Habibty ya bani yara kyawawa masu tarbiya daga gareki kamar ki" ya karashe yana murmushi, bata tanka shi ba saima tura baki gaba tayi da son ta mik'e tsaye, saketa yayi ta mik'en yana binta da kallo, sip ta bud'e ta ciro kayan da zaka saka, toilet ta shige abinta...
Kishingid'e ta same shi kan sofa idonsa a lumshe, samun kanta tayi da zuba mishi ido tana k'are masa kallo, sanye yake da kaftan na wani tattasan yadi ash colour ya kafa hular damanga yad'an turata baya, iya halitta Allah yayi anan ba dai cikar halitta ba Ya Mu'azzam duk gidansu ba mai kyawunsa ta sani, yana wani irin kyau mai d'aukar hankali bata cika ganin laifin Samiha ba wasu lokuta akan haukar da take akan sonsa tasan ya isa yama wuce hakan ma, shiyasa ma har yau ta kasa yadda da kalmar son da yake faman gaya mata, to ta ya ma za'ayi ya sota? Duk da zuciyar ta tana gaya mata gaskiya ne, amma ta kasa aminta da hakan....
"Kodai cinye ni zaki yine 'yan mata wannan kallo haka?" Ya katse mata tunani, still idonsa a lumshe suke, bai kuma motsa ba kaman ma bashi yayi maganar ba, saurin d'auke kanta tayi tare da fara takawa da niyyan Barin d'akin, saurin tashi zaune yayi tare da rik'o hannun ta d'aya, tsayawa tayi ba tare data juyo ba..
"Tafiya zakiyi ki barni a d'akin bayan ban gama kallon kwalliyar taki ba, so nake naga ko zan iya cinye ki, tunda ke kin kasa cinyeni" shiru tayi masa.
"Sakeni girki zanyi" tace a hankali "wow wannan matar tawa akwai ado wannan duk kwalliyar girkin ce? Bari nazo muyi tare ko" yace tare da mik'ewa, a tare suka fito yana rike da Hannun nata, Samiha dake zaune a parlon wani mugun kishi ne ya turnik'e ta ganin su a haka da tayi, D'auke kanta tayi, ji take kamar taje ta rufesu da duka gaba d'ayan su, murmushi ya saki ganin yanayin ta tare da sake ma Aymana hannunta, dama takura ta yayi shigewarta kitchen tayi shi kuma ya nufi inda Mihar tashi...
Cikin sauri-sauri take kwab'a fulawar tata, dan wake kawai take sha'awa ci, ita kanta mamakin irin kwad'aye kwad'ayen nan daya taso mata yanzu take, kusan kullum a 'yan kwanakin sai tayi abin kwad'ayi a kitchen d'in tana ci tana girkin, kuma hakan bazai hanata ci sosai ba idan ta kammala girkin, tadai zama a cici har tsakiyar dare tashi take taci, aiko tayi wata 'yar lukuta da ita, ga haske na musamman data kara da kyau, ga shegen bacci dan saidai in bata kishingid'a ba nan take sai bacci....
Sanda ya shigo kitchen d'in tuni ta kammala d'an wakenta da yaji dafaffen kwai da kayan lambu, yasha yaji sai d'aukar ido yake, ta Dora tukunyar girkin tare da zama kan kujera ta d'ora plate din a table tana ci kamar ta had'a da plate d'in, zuba mata ido yayi yana wani nazari a kanta, kafin ya karasawa shigowa gaba d'aya...
"Iyye wane irin abincin rowa kika samu kika lab'e anan kina cinye kayanki ke d'aya" ya fada tare da jan d'ayar kujerar dake facing d'inta yana kare mata kallo, banza tayi masa kamar yadda ta saba, wanda tuni ya saba da shirun nata dama can dai bamai yawan magana bace ya sani kamar shi saidai wannan ya had'a da wata hanya ta horasa daga cikin hanyoyin horon nasa da take da, hannu ya saka a tare suka cinye shi tsaf ba tare data ce masa komai ba, sannan taci gaba da Aikinta yana tayata kamar yadda ya saba yana ci gaba da janta da surutu da tsokana, ya fahimci har rashin kunyar yanzu ta rage sosai, kuma in yayi abin dariya takan murmusa ko da ba zata amsa ba....
Washe gari sukaje Gwarzo inda Hajja kai mata nata kayan dama ita ya saba siya mata, Samiha Allah kiyaye tayi musu Dan tace ba inda zata, dan Sam basa shiri da Hajjar, dan Hajja ba ruwanta da iskanci kowa kwaba ma magana take muddin taga take-taken mutum, shiyasa Sam basa shan inuwa d'aya da Samiha da Samha..
Tayi murna sosai da ganin su sai nan nan take dasu, tana k'ara godewa Allah daya cika musu burin su, sai bin Aymana da kallo take duk inda tayi tana murmushi, nan suka wunin mata sai marece dake ya na Hutu ne.
Kamar kar su dawo taji taso ya barta inda Hajjar ta kwana biyu, saidai Hajjar ma bata aminta da hakan ba, dole ta hakura ta biyosa tana kumbure- kumbure har Hajjar fushi take da ita.....
************
Tana zaune A main Parlour tana kallon peace TV, daga shi har Samihar duk sun fita, tun safe take jinta gata nan duk bata kwarin jiki, a daddafe ta samu tayi musu jalop d'in macroni, haka kawai taji tana sha'awar zama a Parlon, tana kallo har bacci ya sureta dake banzanta ne...
Samha da Samiha ne suka shigo gidan a tare, ganinta kawai sukayi kwance tana sharar bacci, zaro ido Samha tayi tare tab'e baki tana jifan ta da mugun kallo kamar tasan tana yi kafin takai duban ta ga Samihar wacce itama yanayin ta ya canja tana bin Aymanan da kallon tsana..
"Yanzu ke Sami haka kika zubawa shegiyar yarinyar nan ido a gidan nan ta samu sake haka, kiga wani fresh da tayi irin tana hutawar nan ke gakinan jiya i yau"
Tab'e baki tayi "Hmm baki San azabar bak'incikin da nake kunsa ba ai, duk yaya Mu'azzam me, ya barta ta rena shi ta reni ni, duk abinda take gidan nan baya bari mata komai kamar mai tsoron ta nima ya hanani tab'a ta wai kuruciya"
"Kutt! Wannan ce da kuruciya, kedai kice kawai an kai yaya na inda aka kai Abba ni nasan wannan iskancin ba banxa ba dora ta akayi akai, shiyasa kika ga yaya ya kasa komai amma ba haka ba me zaiyi da wannan abar" Samhar tace ranta a bace.