← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 34

Sashe 4

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nikam Allah bazan d'aga mata kafa ba da nice, bari kiga dama ina k'ule da ita, yayan nanan?"

Samiha da dama so take ta tunzura Samhar suci uban Aymanan kota rage hassafi "baya nan fa dan kinga ai bamu samu motar ba"

"Good" tace tare da zuwa fridge da sauri ta d'auko gorar ruwa masu shegen sanyi, tazo ta tsaya kan Aymanan tare da bud'e su ta fara kwara mata su a kai...

A firgice ta mik'e cikin tsananin kad'uwa tana zare ido, kafin ta gama dawowa hayyacinta tass taji saukar mari, rike gurin tayi idonta tar kan Samhar, bata tsaya Neman ba'asi ba itama ta sauke mata nata marin, tare da bin ta da kalar kallon da take mata "da nayi maki me? Aina gaya miki Aunty Samha jiya d'in ta wuce ba yau bace.." Bata rufe baki ba itama Samiha ta sauke mata nata Marin...

Cikin k'arfin hali itama ta juya ta sauke mata nata "bazan t'aba yadda wata k'atuwar mata ta zuban tafi a banza ban rama ba, ko waye ita"..

"OK yanzu ko jikinki zai gaya miki dan uwarki, badai mu kika Mara ba" Samha ta fad'a tare da yowa kanta ta fara kai mata duka tana Tarewa, itama Samihar kanta tayo suka taru kanta su duka...

Duk da tayi iya k'ok'arin ta gurin ramawa saidai sarkin yawa yafi sarkin k'arfi aiko tuni suka ci k'arfinta dama gata yau din ta tashi sai a hankali, tuni suka kaita k'asa..

Samihar na kan ruwan cikinta ta mummuk'ar ta, itama Samhar yi take duk wani haushi da takaicin ta da sukeji suke son sauketa tun tana iya ihu har ta dena, su kuma jibgar ta suke kamar ba gobe....

Tun kafin ya kammala parking yake jiyo kamar ihu cikin gidan, aiko bai kammala parking d'in ya fito a guje tare dayi cikin gidan ...

"What nonsense..." Kasa isuwa yayi hango Samihar da yayi kan Aymana ga Samha gefe suna jibgarta, suma cak suka tsaya tare da fara zare ido suna kallonsa a gigice kowacce ta kasa motsi..

Da gudun ya iso gurin tare da tura Samihar da k'arfi, sannan ya d'ago Aymanan zuwa jikinsa wacce tuni ta some Sam bata numfashi, kallonsa ne ya sauka kan k'afafun ta jini ne kebin su har ya fara b'ata tiles d'in "jini!" Yace da k'arfi.

Suma sai lokacin dubansu yakai a gun, kara zaro ido sukayi banda mazari ba abinda jikinsu yake sun had'e guri d'aya kamar munafukai...

K'ara rikicewa yayi a rud'e ya sungumeta gaba d'aya, kamar ya d'auki baby, idanuwansu sun kad'e sunyi jajir kansa har wani jaja yayi ransa duk a dagule, cike da tsana da tsananin b'acin rai ya kalle su...

"Kisa! Kisa kuka yi? Wallahi duk yarinyar mutane ta mutu you will pay for" gama fad'a ya fice da ita a hannu yana kwalla was gate man kira da shima yaga rashin amfaninsa a ga reshi, saidai yanzu bai da lokacin wannan...

Shima duk ya gama rikecewa motar yace ya bud'e masa baya ya sakata sannan ya zagaya da sauri ya shige...

Da gudu gate man din yaje ya wangale masa gate, ya fita a guje kamar iska.......

😢😣 _Wayyo my Aymana_ 😢

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*An karb'o daga Jabirin (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) yace misalin sallolin Farilla guda biyar da mukeyi a yini, kamar misalin koraman ruwan tafki ce take gudana a bakin kofar kowannen mu, yake wanke jikinsa a kullum sau biyar a rana(yana nufin yadda mukejin dad'in jikin mu Idan mukayi yawaita wanka muna wanke daud'a to kamar Haka sallar ke wanke mana zunuban mu! Allah ya bamu ikon kiyaye ta👏🏻)*

Husnul muslim👌🏻

*Page* 3⃣3⃣

_____kasa daurewa ya isa Malam Aminu kano yayi ganin yadda take bleeding sosai gashi har yanzu ba numfashi a tare da ita, ga hankalinsa da baya jikinsa driving yake kawai amma ba wata nutsuwa a tare dashi, wata private clinic na kan babban titin unguwar tasu ya shiga da ita, aiko a gaggauce aka kawo gadon d'aukar marasa lafiya aka d'auketa, Emergency aka shiga da ita ganin ta in critical condition, bin gadon yayi hannunsa cikin nata yana shafawa, shidai fatan bai wuce ta dawo hayyacinta ba duk a rid'e yake ya kasa yin tunanin komai...

Yanayin da yayi musu magana dashi da yadda ya figi motar ba girma, ba karamin kad'uwa ya sakasu ba, sun San yana da zafi sannan akwai tsare gira saidai wannan yanayin nasa na yau ya sha banban koma suce basu tab'a riskar sa a irin yanayin ba...

Sosai jikin Samha ya sanyaya lallai sun tabka ta'asar da basu san iya abinda zai biyo baya ba, tun anan ta fara data sanin biyo Samihar da tayi ba tare da ko mijin ta yasan ta fito ba "bleeding? Mean for?" Ba Momy ta gaya mata ta hana Yayanta shiga shirgin ba, kuma tasan yadda yake tsananin yi mata biyayya amma tabbas wannan jinin ba shakka na zubar ciki ne alamar yana kulata tunda ga sakama ko b'aro-b'aro....

Ciki ta koma a guje tare da d'auko kayanta ko mayafin a tafe take yafashi, rik'eta gam Samiha tayi tare da yi mata wani irin kallo wanda yafi kama Dana maraici, itama jikinta yayi sanyi lakwas dan batasan makomarta ba "kina nufin tafiya zakiyi ki barni anan?" Figze hannunta tayi tare da watsa mata harara "to da na zauna ya sameni kike nufi, au ke zama zakiyi kenan?"bata wani jira cewarta ba ta wuceta cikin sauri, itama ciki ta koma da gudu tare da tallabo veil d'inta cikin sauri ba zata yadda ta zauna ya dawo ya sameta ya nemi kasheta, gara yaje gida komai ta fanjama fanjam..

Saidai me suna zuwa bakin gate mai gadin yace bai san zancen ba dan yallab'ai yace kar ya bari kowa ta fita a cikinsu kuma kar a shigo, bala'i da hauka suka fara gwada masa dake dama ya kulle kuma mak'ullin na hannunsa yasa ya sharesu dan k'arshe ma ya shige d'akinsa ya rufo k'ofarsa ya barsu nan suna ruwan ashar d'in su, shidai umurnin oga kawai ya ke bi kodon ya wanke laifin da yayi masa, dan tabbas yaji hayaniya a ciki saidai sanin dokar sa tayi masa iyaka daga gate sai gate, yasa baije ba laifinsa kuma da bai kirasa kuma wannan Sam baizo kansa ba..

Daga karshe ganin tabbas da gaske ba barinsu fita zaiyi ba ya saka su dole komawa ciki hankali a tashe dan sun San tabbas yau kashin su ya gama bushewa saidai har cikin ran Samihar taji dad'in zubewar tsinannen cikin da sam basu San da zamansa ba, tabbas wannan al'amarin yayi mata dad'i duk da ranta fal fargabar makomarta...

Samha kam safa da marwa ta shiga yi a parlon dan abubuwan sun had'e mata da yawa itafa ba ma da niyyan zama tazo ba dan 'yan kwanakin sun fara samun matsala da mijinta k'orafin ta cika yawo ga rashin girki ya gaji da yin take away, rashin iya tsabtace gida duk da kuwa tana da maid kuma tana yi amma dake Neman rigima yake yace sai ita zatayi da kanta yaushe zata iya, ga dokar fita daya kafa mata ba tare da izninsa ba, har ya tabbatar mata ta sake zai d'au tsattsauran mataki akanta, gashi tana so ta koma gida kada a dawo ya samu bata nan an hanata, dabarar kiran Momy ce ta fad'o mata...

Nan take ta shiga labarta mata duk abinda ya faru, a zabure Momy ta mik'e "What! Kika ce ciki fa? Waima ubanwa yayi mata cikin dan badai my Son ba" Momy ta fad'a kausashe cikin tashin hankalin da ya dirar mata a yanzu a ba zata "ciki fa kuma yadda ya nuna damuwar sa da yadda ya fita hayyacin sa ya nuna ya damu da ita yana sonta, nidai ba wannan ba Momy yanzu ya za'ayi na fita da matsala fa"

"Karki damu yanzun nan zan turo mudi ya d'aukeki aini kin biyani dota, ki kwantar da hankalinki ba abinda zaiyi muku, shi kuma dan ubansa zai zo ya sameni, kice ma Samiha itama ta biyoki kuzo tare"

"Hum ni ai ba wani biyowa da zanyi ta nan gida zan wuce dan na gaya miki da Matsala" amsa mata tayi sannan ta katse wayar...

Safa da marwa kawai Momy keyi tama rasa bakin magana wato ita Mu'azzam zai ninke a baibai ita zai renawa hankali, da ba dan su Samha ba kenan da saidai ta wayi gari taga abinda tafi tsanar faruwar ya faru wato had'uwar jini tsakaninta da Fatima "bazai tab'a yuyuwa ba!" Tace a fili da k'arfi "wannan karon dole nayi abinda banyi ba a baya koda haka na nufin Barkewar rashin jituwa tsakanina da Alhaji, dole na raba wannan tsinannen aure dake shirin hargitsa ni, dole nayi magantu fiye da baya, tabbas Mu'azzam zai fuskanci matsancin fushina ni..ni yakeson had'awa jini da Fatima tabbas ya d'auko magana" haka tayi ta tambatun ta cikin tsananin b'acin rai...

************

"Sir!"

Da sauri ya juyo tare da kallon nurse d'in da rinannun idanuwansa da kallo d'aya zai tabbatar maka yana cikin matsananciyar damuwa, tunda aka shiga da ita ya kasa zama sai ka da komo yake yana kallon k'ofar ransa fal tausayin ta cike da damuwa Mara adadi...

"Yes! Yawwa ya ake ciki ta farfad'o?"

Ya tambaya a same time, cikin tausayawa da sanyi irin na wasu ma'aikatan jinya Idan zasu gaya maka bad story about ur patient(bak'in labari game da majinya cinka) "sorry 2 say kun rasa babyn ta samu miscarriage, and tana buk'atar jini yanzu saboda jinin da ta rasa sosai" kasancewar end of week ne hospital d'in ba Dr sai nurses....
Chapter 4 · 0% Book details