Sashe 32
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai me kenan? Mu'azzam kai da baka iya d'aukar jarirai ba, taya zaka d'aukar wannan mai kama da lomar tuwo d'aya, bata da kwari fa" haka yake cewa idan akayi sabuwar haihuwa baya d'auka wai basu da kwari karyewa zasuyi in ya d'auka, shi kanshi yana mamakin yadda yakejin zai iya d'aukar baby'n duk da k'ank'ar tanta, zuciyarsa ta kara shiga rud'u fa, to wai mema sukeyi anan da sassafen nan?, sannan ina Hajja da Aymanah? Abinda yasan bazai yuyu bane wai Aymanansa ce ta haihu ba tare daya sani ba....
'Yar dariya yayi tare da Sosa kansa "au na manta ne Momy, Ina Hajja ne, Hajja ta?" Ya mik'e yana kwala mata kira, har ya d'aga labulen bedroom d'in Hajja Ammi tayi Sallama "ina uwar rakad'in take, 'yar cibi da ita sai muryar kamar wata babba" tace tana dora flask d'in da ta shigo dashi a dinning...
Dawowa yayi Falon yana gaida Ammin "Aa Mu'azzam kaine da safiyar nan?" Kafin ya Amsa sai Nusee na kwad'o sallama...
"Wayyo ina kike Besty, Kin sauke kin huta kin barmu da aiki, Besty, ina babyn tamu..." Saurin had'e yawo tayi tare da Adana sauran kalaman ta, ganin Ashe duk iyayen su na falon, hadda Yayansu, yadda ta shigo da shirme duk tsananin farincikin new baby ne ya isheta...
"Ke! Meye haka Baki ga yadda kike bane? Wata bestyn ce ta haihu ba dai Aymanah ba?"
Shiru tayi tana Muzurai yayin da su Momy suka saki dariya, ganin yadda ya k'asa gaba ya k'asa baya duk ya rud'e shima...
"Yo da wazai haifi wannan 'yar cibin bayan kai, gashi dai sai muga ta kushen girman 'ya'yan wasu, gata nan dai ba'a ko ganinta da kyau" Momy ta fad'a tana mik'awa Nusee ita...
Sororo ya tsaya, baisan lokacin da yace "Maman Arif da gaske Aymanah ce ta haifo wannan mai kyan?" Murmushi kawai Ammi tayi, sai Umma ce tace...
"Itace dai, amma ina kyau anan Ibrahim Abu sai kace bakwaine 'yar cas da ita da murya"
"Alhamdulillah bini'imatihi tatimus salihat! Allah nagode maka daka azurtani da wannan 'yar, Allah kayi mata albarka da sauran yaran musulmi baki d'aya" yace cike da farinciki, tare zuwa gaban Nusee ya karb'i yar dake motsa d'an tsut d'in bakinta mai kama da nasa, alaman tanaso ta tashi, k'ank'ameta sosai yayi a jikinsa yama k'asa zama sai kallon ta yake kamar ya fyato ta a hanci tsabar kamar da suke da ita, kyau kam ai ba'a magana rashin girman dai ne kam dakyar tafi 'yar seven months...
"Oh! Mu'azzam samu guri ka zauna mana" Umma ta fad'a tana dariyarsa..
Ammi kam ficewa tayi tana murmushi.
"Kafa gama fitsarewa dan nan, to ai gashi ka kora Fatima, muma bari mu tashi tun da uban 'ya yazo, ba sauran kara" Momy tace..
Zama yayi "wlh Momy abin ne a bazata jiya fa har 12 munyi waya da ita, wai ma yaushe ne ta haihu, gida ko asibiti? Kuma shine aka k'i gayamin Momy?"
"Aa lale da iroro Angon k'arni, anzo an isko haihuwa bagata tan" Hajja ta katse sa wacce ta fito daga bedroom...
Sallama Momy da Umma sukayi wa Hajja ba tare data amsa tambayarsa, tun da Hajja ta iso magana ta k'are "Hajja Bari naje na kawowa Aymanah, abinci ganan ruwan zafi ta sha tea kafin nazo"
Bai jira jin me Hajjar zatace ba ya shige bedroom d'in, dan ya tabbatar tana ciki...
Tana tsaye gaban mirror tana goge kanta da k'aramin towel, babba na d'aure a kirjinta, takowa yayi, ya zagaye ta da hannayensa tare da d'ora kansa a kafad'arta, Murmushi ta sakar masa...
Hararan wasa ya jefa mata "ni ba ruwana dake ai Habibty, ki haihun ba tare dana sani ba? Wai ya ma akayi haka ashe haihuwar sauki gareta har haka?" Ya karasa cike da tsokana yana dage gira...
"Hmm lallai ma Yaya ai haihuwa duka sunanta haihuwa, amma gaskiya wani yafi wani samun sauki, dan ni kaga jiya har bacci nayi bayan kammala wayar mu, sai fa guraren 3 dare ne haihuwar tazo kuma kafin asuba na haihu, amma fa da wahala Allah, tab lallai dole a gaida su Momy wai" murmushi ya saki tare da janta jefen gado suka zauna ya amshi towel d'in yana ci gaba da goge mata kan...
"Hakane gaskiya Babynah ai kinsha fama, haihuwa is not easy dole ma mu jinjina wa iyayenmu sannan mu girmama ku matayen mu, Allah yayi miki albarka ya faranta miki kamar yadda kika farantamin, Allah ya raya mana ita akan sunnah, yayi mata albarka yasa Hafiza ce kamar Bilkisata" murmushi ta saki ta amsa da ameen cike da kunya...
"Wankan tafashasshen ruwa kikayi ne?" Da uhm ta amsa masa...
"Kai lallai matar nan tawa ba k'aramar jaruma bace bakya tsoron ruwan zafi, ke fa badai karfin hali ba akwai jarumta, sai ki shirya muje hospital nasan ma dole sai Dr tayi fad'a tun da tasha maimaita kar na barki ki haihu gida"
"Kaji ka Yaya ai dole na nayi Jarumta ina tare da jarumi, kuma ma Hajja ai ba zata tab'a d'agamin k'afa ba, kofa lokacin da na samu miscarriage dinnan sanda ta hadani da ruwan zafi hmm Hajja kam ai ba dama"
Murmushi yayi "ai yafi gara ki gasu duk yafi sauran kame-kamen nan na shan tab, yanzu dai bari muje hospital d'in muji me Dr zatace"
"Hhhhhh Dr Ayshan fa tazo tun dazun ta yi duk abinda ya dace ta wuce, ai da ita aka gyara babyn, taso ta kiraka ta gaya maka Su Momy sukace kar ta kira bazata za'a maka"
Bud'e baki yayi "wato nidai kawai aka kwara nine last na sanin haihuwar 'yata gaskiya kun zolaye ni, amma shikenan akwai next time" dariya ta saki....
"Sorry my Yaya my Ibrahim khaleel nah ni d'aya"
"Um ba wani keda cute dai, anya cutie na ba zata kwace maki ni ba, kinfa iya haihuwa tawan, matsalar d'aya ce kin haifota 'yar fit, anya ma wannan cikin ba saura wai?" Ya karasa yana danna cikin, 'yar kara ta saki...
"Kai Yaya da zafi fa, miki ne fa?" Rungumota yayi yana dariya "oh so sorry baby sannu ko" kafin tace wani abun suka jiyo 'yar na cayyara ihu muryan zai....
"Hmm wannan cute d'in taka ko, inaga ba zamu shirya ba, ta cika kuka iyakanta 5 hours a Duniya amma kukan ta ta mana yakai na awa 2, ga idonan kwai dasu"
"Kaman naki ko? Nifa tun yanzu kar ma a fara takurawa cutie tam, dan bazan yadda, wama ya sani watakil ko abincinta ba'a bata ba" ya fice domin karb'o babyn, murmushi tayi tare da tashi ta shiga shiryawa......
A falo kuwa sai yinta sukeyi shida Hajja tace ya zo ya wuce ya basu gu d'an ba wani zaman jego da zai yi musu, yace yaji amma dai ta barshi ya kara tukun, amsar babyn yayi da Hajja tace ya sadata da uwarta ai tayi zuriya ma(hoho su Hajja anyi kama kunne)...
***********
"Baby zo ki taimaka mana dan Allah yunwa mukeji" yace bayan ya sakawa babyn lips d'insa aiko ta kama da k'arfi ta hau tsota, zama tayi bayan ta gama zura gown d'inta ya Dora mata ita akan cinya yana kallon su cike da sha'awa...
"Kai! Wash, wallahi da zafi" tace jin yadda babyn ta cafki maman ba sassauci, aiko sai yarfar da hannu take cike da shagwab'a...
"Oh! Baby kaddai cutie zakima kuka kuma bayan kin gama yiwa Abbinta"
"Hmmm Yaya bakaji bane da zafi Allah" daf da ita ya zauna yana shafa kanta "sorry Habibty daure dai da sannu zaki saba" kasa daurewa tayi "nikam Yaya wai ina kasan harkar haihuwa har haka" murmushi ya saki....
"Nifa lauya ne baby, ba sashen da bamu sani ba, bare ma ko dan ke ai dole na koya"
"Uhum lallai Yaya!
" yawaa wane suna kikeso a saka mata?"
"Umm sunan Momy Yaya"
"Niko kinga da Sunan Maman arif naso a saka"
"To Yaya ai ba damuwa basai a bari next time d'in kamar yadda kace asa sunan Ammin ba" sosai ta Kara burgeshi wato yarinyar tasan kanta tana da kawaici da hangen nesa, amsan babyn yayi bayan ta gama feeding d'inta yayi mata huduba da sunan Momy wato *Zainab*
"Nikam wai duk girman cikin nan ita kuwa 'yar fit"
"Hmm haka Dr tace wai rashin girman nada nasaba da miscarriage d'inta nayi" jinjina kai yayi...
"Haka ne Allah ne ma kawai yayi sai tazo Duniya Allah ya inganta mana ita akan tafarkin gaskiya" ameen ya ta amsa, a tare suka yi Karin duk abinda tace tare dashi, Hajja da Momy sai tsiya suke masa Umma da Ammi na karesa, sai 12 yabar gidan saboda mutane da suka fara zuwa 'yan barka...
Murna kamar mi a gun Momy da taji takwara aka mata, musamman da taji Aymanah ce da kanta ta, lallai yarinyar ta cika 'yar halak sosai ta kara samun fili a zuciyar ta kimarta ta karu I donta..
Abba ma yayi farinciki jin an saka masa sunan uwar gida sarautar mata, Ammi da Umma ma ba bakin ciki, Ammi hadda tukuicin an mayar mata da sunan Auntynta..
Tuni 'yan uwa na nesa dana kusa aka fara garzayowa gidan kullum cike yake taf da jama'a su Nusee, kam kullum ana nan dasu ake zaman jego, Mu'azzam ma kullum yana nan duk irin korar da Hajja keyi masa, yana mak'ale sai yawan mutane ke tilasta masa tafiya...
Kulawa kam ba'a magana mai jego da baby ta ko'ina samunta suke niko har nake ga ta musu yawa, lallai 'yar dangi sai dangi, kayan barka kam kamar hauka ta ko'ina zuwar musu sukeyi, Abba, Dady, Momy, Umma, Ammi, Hafiz, Adnan, Zulaiha, Samha, Samiha, Nusee, Amira, Uncle salman da Amaryar sa Fauziya kowa yayi rawar gani...
Abba mota sukutun kirar Vibe mai kyau irin ta mata kalar light brown, gida kam mashaa Allah ya dinki mutanen Gwarzo, bauchi da sauran 'yan gari duk an garzayo, biki akayi na 'yan gata....