← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 34

Sashe 18

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bayanta ya lallab'o tare da rungumo ta ganin yadda ta matuk'ar lulawa a duniyar soyayya wato dai sakonnin sa sunyi tasiri, k'ara shigewa jikinsa tayi tana shakar k'amshin san nan mai nutsar da ita a k'auna....

"All dis for me My khaleel?" Ta tambayesa idonta a lumshe bayan yayi turning nata suna fuskantar juna, bai amsa mata ba, face sunkuyowa da yayi yayi kissing wuyarta tare da zagaye ta da hannayensa...

"Sunyi miki kyau?" Ya rad'a mata a kunne lokacin da ya iso nan gun, bata iya amsawa da bakinta ba sai kai data girgiza alaman eh, saboda salon nasa ya sakata zama so weak...

Murmushi mai sauti yayi tare da cewa "anything is for you Habibty, ur my world, my everything.."

"..I..love....you so much Hayatiy" ta fad'a can cikin mak'oshi dakyar..

Kara rungumeta sosai yayi shi kadai yasa ya yakeji idan ta furta masa Kalmar so, sama ya dagata tare da fara takawa...

"Yaya?" Tace cikin rauni tana kallon k'ofar part d'in Samiha, kallo d'aya yayi ma part d'in ya d'auke kansa, baice da ita komai ba ya fara taka step da ita, itama shiru tayi tare da k'ara kankamesa ido lumshe......

Mashaa Allah ta fad'a a ranta lokacin da ta tsinci kanta tsakiyar falon sa, sanyin Ac da daddad'an k'amshi suka bugi hancinta a lokaci d'aya, lumshe ido tayi a hankali kafin ta bud'e su, shine first time data shigo part d'insa tsawon zamanta gidan yo ina zata shiga dama can da ana 'yar tsama...

Komai na parlon lemon green and milk ne, ko'ina neat sai k'amshi yake zubawa baza idanu tana kallon dukiyar da ya narka sai kace d'akin wata sabuwar amarya, but nashi very unique ne dama Yayan nata na daban ne, wadannan tafka tafkan enlargement d'in nasa data gani a dakinsa na family house nasu, su ta sake gani anan dama tana matukar son fotunan, aiko gabansu taje ta zuba musu ido ko kiftawa bata yi.....

Bataji zuwansa kusa da ita ba sai da ya tab'a ta "tau inkin gama kallon sai mu shiga ciki 'yar Gwarzo" kunya ce ta kamata tayi saurin rufe idonta tana murmushi "kaima naga d'an Gwarzon ne ai"

Murmushi ya saki yadda tayi maganar a shagwabe da yanayin yadda ta tura bakin gaba "eh naji amma ba kamar keba ta Hajja takwaralle inji Hajja" yace da sigar tsokana...

"Nidai Allah Yaya uhum.hum..hum" tana diddire k'afa, Aymanah rigima ya fad'a a ransa tare da rungumeta yana mata magana kasa-kasa, wadda duk kwakwa ta an hanani jiyota, a haka ya jata zuwa bedroom d'insa, shima dai ba k'arya ya tsaru ta ko'ina yasha adon Sky blue and white.....

Mamaki ne ya kamata data samu tafkeken enlargement nata a d'akin, ko'ina ya samu foton har yayi enlargement d'insa oho!

"Kina mamaki ne" ya jeho mata tambayar....

Ido kawai ta zuba mishi "tare akayi min su da wad'anda kika gani a falo, zaro ido waje tayi cike da sabon mamaki zatayi magana ya katseta dan bai shirya answering question nata yanzu ba.....

"Ki Adana question naki, Ba a wannan lokacin ba, yanzu lokaci na kara'in many things, kinga yanzu dai taso muje muyi sallar mafi daraja da kikasa muka rasa" yace tare da kashe mata ido d'aya, saurin yi k'asa da idanuwanta tayi sai lokacin tsoro ya fara ziyartar zuciyarta ta kuma tuna daga ita fa sai shine a gidan, oh yau an ba kura fida sai yadda ta kasance da ita kuma...

Ganin taki koda motsi ne bare niyyan tashi ya saka shi takowa da kansa ya dagawa, toilet ya kaita, sukayi alwala tare, katuwar darduma ya shinfid'a musu ya shige gaba ya jasu sallar, addu'o'i sosai ya kwararo musu da yaren larabci zuwa turanci, da Hausa duk ya had'a, bayan ya dafa kanta kamar yadda sunnah ta tanadar...

Tankwashe kafa yayi sannan ya kalleta sosai kafin yayi magana "Bilkisu" ya kirata da asalin sunanta..

D'ago ido tayi ta kallesa na tare da amsawa da na'am, tare da maida kanta kasa ganin yadda yaci serious tasan muhimmiyar magana ce zaiyi...

"Allah ya sani wannan ranar tana daga cikin manyan ranaku a rayuwa ta, ina cikin farinciki sosai, da Allah ya daidaita mana kan Zuri'ar mu, sannan ya daidaita tsakanin mu dole mu godewa Allah da wannan dimbin alfarmar da yayi mana" nisawa yayi "Bilkisu, nasan kinsan aure yafi karfin ayi wasa dashi, wata daraja ce da baiwa da Allah madaukakin sarki yiwa bayinsa, sai mu godewa Allah daya sako mu a cikin jerin ma'aurata" kara nutsuwa tayi sosai tana sauraronsa...

"Bilkisu banyi alkawarin a kullum zamu kasance cikin farinciki ba, bance ba zamu sab'a Dan kinsan hausawa na cewa zo mu zauna so mu sab'a! Amma ni Ibrahim nayi miki alkawarin rikeki da amana, zanyi miki adalci a zaman mu, banyi alkawarin bazan kara aure ba, dan kamawa hakan keyi saidai inaso ki sani bani da burin k'ara auren wata mace daban bayan ke, zan kula dake da jiki da aljihuna zan killace ki anan tsawon rayuwata" ya nuna saitin zuciyarsa "bazan tab'a barinki ki sha wuya ko ki shiga damuwa ba ta dalili, zan tsaya miki na kare dukkanin hakkokin ki da suka rataya a wuyana, sannan ina mana fatan auren mu mai dorewa ne har mutuwa" ya karasa fad'a yayi yana murmushi tare da kallon fuskarta, can ciki ta amsa da Ameen, still kanta a k'asa...

"Game da Samiha kuma, abar mutaya ta da murna ce, Dan ta samu kubuta daga babbar sabo, wannan wata dama ce Allah ya kara bata muna fatar ya zama silar shiriya a gareta, addu'a ya kamata ki tayata da Allah ya zaba mata mafiyi alkhairi damuwa ba zata canja komai ba, kinji!" Kai ta gyada masa kawai tana jin tausayin Samihar da gaske tare da yi mata Addu'a dan tafi kowa sanin yadda take k'aunar Mu'azzam.....

"Nikam wannan salihancin da kika aro kika yafa yanzu ban gane ma'anarsa ba" yace yana janyo ta jikinsa, zamewa ta fara yi tanaso ta tashi ta gudu part din ta, dan har yanzu bata manta first night din su, bare yadda taga wannan rawar kan nan nasa ai tasan zata gayawa mutanen Gwarzo(ai kila hadda na Bauchi🤪)

"Yaya bari inji inyi wanka, wanka nakeson yi" sarai ya gane wayonta, kara riketa yayi tare da rad'a mata a kunne "karki damu yanzu zamu tare idan muka gama cin kazar amarcin tamu" ware ido waje tayi tana fadin ta koshi ita kam, dariya ya shiga yi mata tare janyo ledar da ya shigo da ita, kaji ne dakwale sai turiri suke sun sha kayan alatu, fresh milk, exotic and hollandia.....

Da tsokana da wayau da dabara ya samu ta yadda sukaci kazar sannan sukayi wanka a taren kamar yadda ya fad'a, duk yadda take alkunya tana kaucewa sanda Mu'azzam yayi ya tabbatar da ta saki dashi Dan yaci burin raya wannan daren ya kafa shi cikin darare masu daraja garesu......

A wannan daren masoyan sunyi kukan farinciki, taga tsantsar k'auna Mara algus, wacce bata taba tunanin samu a gun wani ba bare tsadadde, nagartaccen namiji kamar Mu'azzam, ta k'ara tabbatar da ba wata a zuciyar mijin nata face ita, wannan dare ya kasance dare mafi daraja da kafa tabbatar ciyar k'auna a zuciyar Ma'aurata......

*********

Bacci take sosai Hani'an Wanda ke nuni da tana enjoying baccin nata sosai, yafi minti 10 zaune a gefenta yana aikin kallonta, sai yayi kamar ya janye blanket din da take cukuikuye a ciki, sai kuma ya fasa....

Wrist din hannunsa ya kalla sannan ya sake kallonta yana murmushi "hmm Sleeping beauty" sannan ya fara shafa fuskarta a hankali...

Cikin baccin taji alamun ana tab'a ta, turo baki tayi tare kwaba fuska, murmushi ya kara Saki yadda tayi kamar wata baby doll, sunkuyowa yayi ya manna lips dinsa akan nata yana tsotsa....

Bud'e idanuwa ta fara yi a hankali har ta ware su gaba d'aya, inda ta tabbatar ba mafarki take ba shidin ne a zahiri, saurin lumshe ido tayi tana murmushi, dariya ya fara yi mata yana Jan faratan kafarta bayan ya yaye mata bargon...

"Marhaba biki habibty, barka da farkawa ma heart" kara jan bargo tayi tana rufewa duk jikinta har kanta, kara janyewa yayi....

"Common Raguwar matata baccin ya isa haka kada yunwa ta kama min ke"

Saurin mikewa zaune tayi tare da kallon agogon da ke manne a bango da kallo zaro ido tayi ganin har goma da rabi, sannan ta maida kallonta gareshi tana kwaba fuska kamar zatayi kuka......

*nafa zama lazy sai hakuri fans😅*

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*🌐DUNIYA MAKARANTA​​🌐*

*_Idan mugu ya hadu da na kwarai nan take asirinsa yake tonuwa. In da wahala take shi ne idan mugu da mugu suka hadu, wanne ne ya fi Mugunta! Idan na kwarai guda high suka hadu wanne ne ya fi alheri?_*👌🏻

*Page* 4⃣7⃣

_____"Oh! Babe kinfa koyi rigima, me akayi maki kuma yanzun daga tashin ki?" Yace yana kama hannunta ya mik'ar da ita tsaye yana kallon cikin idonta...

Tura baki tayi tare wal da ido wanda ya kusa sumar da shi, baisan time dinta ya rungumeta ba, fadi yake a ransa dis gal wanna drive me! go gaga...

"To ba kai bane ka wani barina inata bacci har wannan lokacin gashi ko break fast ban maka ba, har 10 after" tace cike da shagwaba tana turasa a hankali daga jikinta, tasan halinta sarai zai iya canja salon kai tsaye...

"Naga ko yanzun da ban tada ke ba, ba tashin zakiyi ba, Oh ni Ibrahim tawa ta sameni na had'u da lazy women" bara baki tayi tana kukan shagwaba tare da bubbuga kafafu tana dukan k'irjinsa, matse ta gam yayi a k'irjinsa ko motsin kirki ya hanata tayi sai dariya yake mata, ita kuma sai mutsu-mutsu take tana ci gaba da kukan shagwaba "Allah ni ba Lazy bace Yaya, duk jarumtata kake kirana lazy, ko ka manta nifa kwaila ce..." Duk cikin kukan shagwaba take maganar....

Daina dariyar yayi amma fuskarsa a yalwace da murmushi, cikin shaukin k'aunar ta ya d'ora lips dinsa forehead nata tare da sauke mata kiss, idanuwansa a lumshe yace cikin sanyin murya..
Chapter 18 · 0% Book details