Sashe 17
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin zafin rai da bacin rai Hafiz ya taso ya kama hannun mahaifiyar tata dake ta sambatu ba wanda ya tanka ta, sai kara barar musu da sauran kimar takeyi, yana janta tana turjewa dakyar ya samu ya fita da ita daga Falon, waje yayi da ita tare da jefata a mota ya kulle...
Shima ya zagaya da sauri zuwa mazaunin driver, ganin yadda take ta buga masa glass kamar ta fashe masa shi ko zafin hannayenta da take bugawa bataji, hauka dai tuburan, hawaye sosai ke sauka daga idanunsa uwa mace.....
"Haba Umma! wane irin laifi mukayi miki da zakiyi mana irin wannan hukuncin, Umma meye duniya? Me kika nema kika rasa a rayuwa, nagartaccen miji, Allah yayi ni'ima ta samun 'ya'ya, wasu na nan ba mijin ba 'ya'yan wasu da mijin ba yara, wasu da yaran ba mijin, meyasa? Meyasa Umma? Irin godiyar da zaki yiwa ubangijin ki kenan, ta hanyar butulce masa ta hanyar shirka...."
"Kai! Dan ubanka zaka bud'e ni na fita na koma gun mijina ko sai na maka baki" ta fad'a da karaji, alaman bata maji me yake fad'a ba...
Murmushi ya saki mai ciwo " Miji fa Umma? Miji kikace? Bayan kin zubar da wannan damar kin yanke wannan igiyar mai daraja da kanki, kin yanke ma Samiha tata itama" bai saurari zagin da take dura masa ba akan ya sauketa yaja motar tare da ficewa tsiyace daga gidan, duk sambatun da take masa da zaginsa bai saurare ta sanda ya jingina da ita gidan su, inda dama a hannun Yayanta ne take dan iyayen su sun dad'e da rasuwa, yana kaiwa nan sai ga kiran Abba dake tambayar sa ina yake, ina yakai Unman tasu, nan ya shaida masa gashi ya kawo ta gida, duk da Abba baiso hakan ba amma yana ganin wannan shine last solution a garesu, Allah ya kyauta kawai ya fad'a...
************
Bayanin kai suwaiba gida da Hafiz yayi Abba yayi musu, sannan yace za'a barta gida na zuwa lokacin da zata fahimci kurakuran ta tayi nadama ta gaskiya sai a dawo da ita, Hajja ta amsa da hakan yayi, Dady kam cewa yayi shikam gaskiya ya gama zama da ita, Abba yace wannan kam labari ne ko don darajar yaranta za'ayi mata uzuri muddin ta gane kuskuren ta, a haka taron ya watse zucuyoyin su cike da abubuwa nadan-daban na Al'ajabi mamaki, nadama da tsoron Allah...
Karo na farko a tarihin Zuri'ar, yau ga Momy da Ammi, Zulaiha, Samiha, Samha, Nusaiba da Aymanah a kitchen tare suna girki cike da k'aunar juna, sosai Momy da Samiha, da Samha suke tambayar abinda basu fahimta ba, cike da farinciki sukayi girkin cikin k'aunar juna, musamman yadda Ammi ta dake gurin kawar ma Samiha da Samha damuwar su, kuma tace a sasanta zasu zauna su ringa shiga kitchen a tare da koyon sauran abubuwan da suka shafi gyaran gida da dabarun zaman gidan aure....
Inda Momy tace itama baza'a ware ta ba, kullum zata ringa zuwa ayi da ita, Hajja dake Falon tare da sauran yaran Su Munira, Munir, Adeel, Fadil, Fadila, Sageer, Sageera, Arif, sai kara godewa Allah take da ya ara mata rayuwa taga wannan ranar da take tsumaye a rayuwar ta, sai murmushi take tana kallon yadda yaran keta rahar su, dama Allah yasa kananun basu d'auki mummunar ak'ida ba.......
Haka suka wuni a wannan ranar a tare aka ci abinci tare sai raha da annushuwa suke kamar ba abinda ya tab'a faruwa a baya, wannan rana tayi tasiri a rayuwar su, sun kafa ta a cikin kundin tarihin su, sun sakata a ranar farin cikin wannan Zuri'ar, a yau sun kara dunkulewa sun zama *Zuri'a d'aya* sannan kuma *Rikicin cikin gida* ya kare inshaa Allah, sai zaman lafia mai dorewa...
******
Yana isa bakin matsakaicin gidan, wanda kana gani kasan ba babba gida bane saidai a kirasa gidan mai rufin asiri kawai, waya ya zaro ya kira kawun nasa, akayi sa'a kuma yana gida, a soro suka tsaya yayi masa bayanin komai, sosai ya cika da mamaki dan shi dai yasan ya tsaya sosai a kanta, amma tunawa halin ta na son fafa da nuna isa, dan bazai manta ba, yasha samun case nata akan karyar da take a school akan yar wani da wata ce ansha tsure ta, sannan kuma d'anta ne ya gaya mishi kuma yasan duk rintsi baxai yi karya wa mahaifiyarsa ba, jinjina kai yayi tare da fadin Allah ya sawwaka, sannan suka isa motar.....
Umurnin ta fito su shiga ci Yayan nata ya bata, fitowa tayi ba musu dan har gobe tana shakkar Yayan nata, yace ta shiga ciki, kamar tayi ihu taji saidai ba yadda ta iya dolenta taja kafafunta zuwa ciki, tana jimamin yadda zata Zauna gidan tare da matansa har uku da yara sunkai ashirin...
Sallama Hafiz yayi masa ya wuce akan sai ya sake dawo wa, gidansa ya wuce direct ya kulle kansa a daki yayi kukan bacinciki kai kace wata macece, sai bayan isha ya isa family house nasu dan daukar Nusee shima dan kada a zargi wani abu daban ne, kiranta yayi yace ta same shi a waje...
Saida ta tsorata da ganin yanayin sa, cikin rawar baki ta kama hannunsa "Ya....Yaya...Hafiz kuka kayi?" Ji yayi kamar ta tunzurasa shima ya runtse hannunsa a nata tare da Dora kansa a kafad'arta kamar jariri sai saukar Hawayensa taji kafin yace....
"Nusaiba dole ne na koka! Nusaiba banyi dacen Mahaifiya ba, meyasa na kasance d'anta Nusaiba meyasa...!?" Saurin zare hannunta tayi ta rufe masa baki tare da dora dayan a kayinsa tana shafa Sumarsa...
"Aa my heart karka ce haka, kada ka bari bacin rai yasa kayi sabo wannan kaddara ce, taka kalar kaddara ce, kayi hak'uri da hukuncin Allah, ta sanadin haka sai kaga ka dace, ka daure ka saka Umma a addu'a ita uwa ce koya take kyautata mata ya zama dole....
Haka tayi ta rarrashinsa da daddadan kalamai, har saida ya samu nutsuwar zuciya, rungume ta yayi tsam a jikinsa yana mai jin sanyi a ransa, lallai mace ta gari rahama ce(dama Annabin rahama yace duniya wani dan jin dadine, mafi jin dadin ta, wanda ya dace da mace ta gari👌🏻, mata mu daure mu kasance ababen alfaharin mazajen mu ba fitina a garesu ba, mu zame musu fitila mai haske ba duhu, ba mu taimaka musu gurin kara dankon zumunci tsakanin su da iyayen su ba nesanta su dasu ba, mu fa tuna muma iyayen wasu mazan ne wata rana).
Mu'azzam kuwa yana barin gidan tunda aka kammala taron sai 9 ya dawo d'aukar Aymanah, cewa tayi ya barta na yau d'aya ta kwana gida yadda take farinciki gata cikin dangi anata raha, nan fa Hajja da Ammi hadda Aunty Zulaiha suka korata, Momy nata mitar su kyale mata 'yarta, sosai Samiha tayi kokari gurin danne zuciyarta dake bijiro mata da abu, ta bisu da murmushi yake, bayan wucewar su ta dauki hankalin mutane daya tafi wani gurin, ta shige bedroom ta dirza kukanta.....
Sai wani kunbure-kunbure take masa mota ita a dole ya hanata kwana, shareta yayi kamar ma baisan me takeyi ba sai murmushi yake tare da mayar da hankalin sa kan driving NASA..
Tun a harabar gidan daya ke tar kamar lantarki ta ga canji, kamar ma har pentin gidan an canja, ga wani ado da akayiwa gaban gidan yana fitar kalolin wutace masu ban sha'awa an zagaye su da furanni masu kyawun launi....
Ba tsammani taji an sama da ita, sai lokacin ta dawo daga duniyar shagala data tafi, yar kara ta saki, tare da kankame sa...
"Bayan kince ba zaki biyoni ba, meye na wani bud'e ido kina kallar min kayana" ya rada mata yana fuskewa..
Murmushi ta saki tare da yi masa unexpected light kiss a lips, tare da kasa kankamesa "sorry My Khaleel, ai gani na taho ko, gaskiya yayi kyau sosai"
Murmushi ya saki tare da yi mata peak a goshi, a haka suka karasa kofar falon yana d'auke da ita, da kafa ya tura kofar suka shiga...
"Wow! Wow!! Hayatiy it's so beautiful!" Ta fad'a tare daci gaba da kallon falon................
_💃🏻💃🏻💃🏻its is a time, love time!😘😍 oya one corner my fans👯🏻♀👯🏻♀🤪 #Team Muz'Aymah💋#_
*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*_🕌 its Anoder Friday again, may Allah(S.W.T) upon his Rahman and mercy on we, may d bless of dis day be wit us ahead🤲🏻. JUMU'AT MUBARAK🕌_*
_Masoyan 😘Muz'Aymah😘 a duk Inda kuke to Muz'Aymah na miko gaisuwa 'yar inyass, khairy b-b, zuzu, ummu annur, mom zee, Maman Nana and rest Allah kuna da yawa duk na gaida Ku kyauta, kuyi farinciki wannan shafin naku ne all, ina sonku billahi ilallahi👌🏻_
*Page* 4⃣6⃣
_______dire ta yayi tare da fad'in "ouch! Yarinyar nan kinja kaya fa, kinjiki kuwa?"
Dukan wasa takai masa a k'irji, tana tura baki gaba, cikin shagwaba "Allah nidai Aa yaya ba wani kaya dana ja" tana doddoka kafafu, wani laushi da taji a pootmat din k'ofar yasa takai ganinta kasan, wani irin lallausan welcoming mat ne shimfid'e a gurin, anyi rubutu jikinsa boldly *welcome back home Habibty Aymah* yanayin yadda akayi rubutun da adon da ke jikinsu ba karamin tafiya da ita yayi ba, sai murmushi take tama kasa cewa komai, a hankali ta taka zuwa tsakiyar falon tana ci gaba da kallon balloon d'in da ke lilo ta ko'ina masu shape din heart kala-kala kowane d'auke da haruffa masu bayyana tsantsar k'auna gun Wanda akayi domin sa....
Rungume hannuwa a k'irji yayi tare da zuba mata ido, itakam sai tsalle da juyi take a falon sossai sakon da yake so ya isar gunta ya samu gun zama daram a zuciyarta, gun wasu manya manyan wall stickers taje tana shafawa da aka manna a bangon falon suma dai d'auke suke da kalaman soyayya zuwa gareta, sosai abubuwan suka shagatal da ita, sai mamaki take wai duk akanta Ya Mu'azzam yayi abubuwan, Ashe haka yake mata k'auna bata sani ba...