← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 34

Sashe 19

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aini matata tafi karfin kwaila, ta zarce mata dubu, matata full option ce, zinariya kasaitacciya, ishasshiya a cikin mata, matata Bilkisu mai gadon zinari Queen of ma world" sosai kalamansa suka sanyaya mata rai kuma daga ji tasan ba karya daga zuciyarsa suke, murmushi ta saki har yana jiyo sautinsa...

"Hey you! Ji ta sakani sai zuba nike oh wannan rigimammiyar kwailar nan tawa ta koyamin zuba" ya sake fad'a bayan ya saketa tare da rungume hannayensa a kirji yana kallon murmushin nata bai ban sha'awa...

"Uhum! Wannan d'an gayen mijin nawa badai yanga ba, ka iya basarwa da tsare gida, but yanzu na gama ganoka tsab! I love ur style angon Aymah kwailah!" Tace dashi bayan ta fara takawa zuwa gabansa tana zagayesa tare da wani watsa yatsu tana jujjuya kwayoyin idanuwanta yanayin yadda take juya bakinta da lips nata duk na daban ne cike da salon cin nasara, aiko tayi nasarar wargaza duk wata nutsuwar sa, sakin baki yayi yana kallon ta kamar wani soko....

Murmushin gefen baki ta saki tare da kamo kwalar rigarsa da hakoranta kamar zata cijesa sannan ta d'anyi tsalle ta bugi habarsa alaman ya kama bakin, kashe masa ido d'aya tayi tare da d'aga masa gira tana murmushin iya shege sannan ta doshi kofar fita daga dakin.....

Yayi sakwanni daskare a gurin tsabar mamaki, tsakanin daren jiya zuwa yau ta shayar dashi mamaki da salo-salonta na d'aukar hankali, Tabb lallai d'an hakin da ka rena...shike tsole maka ido...

Murmushi ya saki tare da nutsa yatsunsa cikin kwantacciyar sumar kansa ya shafo, taku d'aya zuwa biyu ya rikito ta zuwa jikinsa abinka da dogon mutum, kyakkyawan masauki yayi mata a jikinsa tare watss mata narkakkun idanuwansa "I love ur style too" taji ya fad'a yana kallon ta ba tare daya d'auke idanunsa, lumshe ido tayi dan idanuwansa ba karamin nakasa mata zuciya yake ba.....

"Yaya pls zanje na had'a mana kari?" Tace sanyaye still idanuwanta a lumshe, sama kawai taji anyi da ita kafin tayi kyakkyawan junkuri har ya d'auki hanyar toilet da ita "Aa pls yaya break d'in fa" hannu ya mata a baki yace "shitt no more talk" shirun tayi tana tuttura baki, tura kofar yayi ya shiga da ita tana tsaye ya had'a mata ruwan wanka bisa umurnin karta yarda ta matsa a gun daya bata, zuwa yayi zai sabule rigar baccin tayi saurin rik'ewa tana fad'in "nidai zanyi da kaina Dan Allah" harara ya jefa mata "oganki kikewa musu..."

"Sorry amma dan Allah ka barni nayi Yaya time is going pls" tace cikin muryar rarrashi, murmushi ya saki tare da lakuce mata guntun hancinta "ga tsiwa sai tsoro! Farar kura kawai" murmushi ta saki "agreed Sir!" Ta fad'a tana turasa....

"Love you, am waiting" yace shima d'auke da smiling tare da mata blowing kiss tsakanin yatsunsa sannan ya ja mata k'ofar...

Sip nasa ya bud'e ya fito mata da kayan da zata saka a gefen da ya jera mata kayanta ciki, pencil jean white ya fito mata dashi tare da top navy colour my white vest ciki, undies din ma duka white ne, ya feshe mata da turare ya d'ora kan bed tare da ficewa daga dakin...

Murmushi ta saki bayan ta fito ganin kayan da ya fitar mata, wato dai yana son English wear din da take sakawa, cikin sauri tayi shafe-shafenta da fente-fententa bakin yayi rad'au da maroon lips stick, ear ring silver simple ta saka, tare da jera manyan necklaces na bits black and maroon, high hill ta manna kafar ta.....

_Wow fans Ku kissama Aymanan Ku_😘👌🏻

Karar takun takalman ta ne daga stars ya sanar dashi isowarta "fatabarakallahu akhsanul khalikeen" ya furta a fili tare da zuba mata idanu da wannan murmushin nata ta iso gurinsa tare da tsugunawa ta d'ora tafukan hannayenta kan cinyarsa "my bae yaka ganni" tace tare da mik'ewa tana juyi a gabansa, sosai ya shagala da kallo zubin halitta da Allahu yayi a gurin, cikin da zakuwa da zafin nama ya fizgota ta fad'o jikinsa, zaro ido tayi baki a sake saboda unexpected ne ya zo mata "1+1" ya fad'a yana dariya tare da rufe mata bakin...

Kunya ce ta ka mata ta boye fuskarta a k'irjinsa tana d'an bubbugawa k'irjin nasa "nidai banaso yaya is OK ur d winner bari naje na samar mana koda ruwan zafi ne, musha tea am hunger" tayi yunk'urin tashi...

Maidata yayi "harkin karaya kuma jarumata? it ok bama wannan ba, muna da break fast since 9 aka kawo, Momy da Ammi sunce ki huta shiga kitchen for a while kawai ki kula da....." Ya kashe mata ido...

Hannu tasa ta rufe ido, k'ara dukansa a k'irjin tayi tana hararansa "Ash!!wash!! Yace yana kama gefen k'irjin satin zuciyarsa..

D'an rud'ewa tayi " Menene?" Kama hannunta yayi ya dora a nasan dake kan zuciyarsa, yana ciccize lebe kamar gaske "ba kece ba, bayan kin cikata da kaunarki tunbul kuma kike dukanta salon kisa ta fashe ko?" Murmushi tayi wadda ya bayyana jerarrun fararen hakoranta yanayin yadda yayi maganar kamar yadda take masa da shagwaba....

"C'om yaya banason kana zama da yunwa, muje nidai cikina is empty" taja hannunsa "yes ma'am" haka suka jera a tare suka isa dining din, break fast suka gudanar mai cike da salon k'auna...(❤Allah yabar soyayya sannan ya had'a kowa da masoyinsa na gaskiya🤲🏻)

***********

Daren ranar Samiha sosai ta raya sa da Sallah da karatun Qur'an, istigfar, godiya ga Allah, tana kuka tana nuna kaskancinta da tsantsar nadamar ta zuwa ga mahaliccinta, Wanda ya kasance shine karo na farko data taba yin tsayuwar dare, yo sallar farillah ma sai tayi mata suger, rungume al-qur'an sosai a k'irjinta tana zubar da hawaye ba zata iya tuna when ta d'auki Qur'an ta karanta ba, lallai tayi sake da yawa saidai tana godewa Allah, ba baiyi mata talala ba ya ankarar da ita cikin lokaci, sosai takejin son Ammi a cikin ranta dan itace ta bata wannan shawarar lokacin da ta sameta a dakin tana kuka, lallai Qur'an waraka ne dan sosai wasu kashi na damuwar ta sun tafi, ta kuma yadda ta d'auki kaddarar rasa ya Mu'azzam, duk da sai a hankali zata saba da hakan amma ta d'au alkawarin yaki da zuciyarta iya iyawarta, ta kuma sanya Ummanta a addu'a Allah ya sakata cikin masu rabon shiriya, kamar yadda suka samu sum.....(zunubin mu koda ya tokare sama Allah S.W.T zaizo mana da gafara cikin duniya, muddin mukayi tuba mai kyau _taubatan nasuhaa_ kofar tuba kullum a bude take mu tuba zuwa ga Allah tun bamuje gargara ba)

B'angaren Umma kam zamu iya cewa kusan haukacewa kawai, tama rasa mai ke mata dad'i ga wani karamin daki da aka bata ba komai a ciki daga 'er katifa sai fanka, dake gudu kamar tsohuwar mota....

Hankalinta bai gama tashi ba, sai da dare yayi aka turo mata wasu yaran gidan da tuwo miyar kuka, kallo d'aya tayi musu zuciyarta ta fara tashi, kin ci tayi, Dan tasan ko kaisa bakinta ba zata iyayi ba, gidanta ta tuna sai abinda ranta yakeso zata saka maid su dafa mata, ba ruwanta da iskan fanka Ac ce a ko'ina, ba zata tuna when sauro ya cije ta ba, tama manta da akwai sauro duniya, yau kuwa gata gashi sai bata yake dan maganin sauron da aka saka baida wani amfani gunta bai tare komai ba.....

Kafin taga safe tayi wata biji biji da ita ga damuwar zuciya gata jiki, duk sauro ya lalata mata farar fatar da da cizo, ga yunwar cikinta da kad'ai ta gama isarta dan rabonta da abinci tun safiyar jiya.....

Tun kan gari ya gama wayewa ta suri jakarta ta saki jiki ta sulale daga gidan, saida tayi tafiya mai Dan nisa sannan ta samu isa titi zuwa lokacin gari ya gama wayewa, napep ta tara tace ya kaita gurin cin abincin na kusa, hakan kuwa akayi, Allah ya sota tana da kudi a jakar har 10k sai lokacin taji 'er nutsuwa, haka tahau kan abincin kamar wata kamun yunwa sanda ta kammala ta samu nutsuwa sannan hankalinta ya dawo jikinta "boka mai da nisa" ta fad'a ranta a bace, biyan kudin abincin tayi sannan ta fita ta sake ta tari wani napep d'in........

Shiga tayi tare da yi masa kwatancen inda zai kaita........

_Sauka lafia customer mai gobe da nisa🤣_

*Sorry fans, kuyi hakuri dani dai, na shiga busy ne, wlh na matsu na kammla nima tashi sai yi nice yaci karewa😕😫* love you all😍🤗

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*A duk lokacin da shedan ya had'u da iyalansa ba abinda ke saka su farinciki kamar Abu uku:- musulmin da ya kashe d'an uwansa musulmi, mijin da ya saki matar sa, mai rowa dan gudun talauci👌🏻*

Duniya makaranta✍🏼🌍

*Page* 4⃣8⃣

______tafe take kamar ta kifa d'akyar ta samu haye tutsetsen dutsen duk zuwan da take bata taba jin wuyar haurawa ba kamar yau ba, da nisha da zufa da komai ta isa gurin bukkar, wani wari taji yana tashi tun daga bakin bukkar, toshe hanci tayi tare da kutsa kai ciki.....

Zaro ido gaba daya waje tayi tare da d'ora hannuwa akai, tana ihu, jikinta kyarma yake awa mazari, cike da tashin hankali take kallon gangar jikin bokan nata dake yashe a kasa, ciki yayi suntun ya kumbure alaman ya dad'e da mutuwa kenan, wannan warin da take jiyowa daga waje Ashe shine, da sauri ta fice daga bukkar har tana cin tuntub'e, kuka take sosai hadda majina sai sharewa take da mayafinta, bakinta banda kalaman tsinuwa wa bokan ba abinda ke fita dama tazo ne ta yi masa tujara akan cin amanar da yayi mata na lalata mata 'ya daganan sai ta canja wani sabon boka amma ganin bokan a mace wulakance ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, jikinsa yayi sanyi sosai da sha'anin biyar bokaye.....
Chapter 19 · 0% Book details