← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 34

Sashe 29

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawowar Umma bai saka Samiha barin part din Ammi ba tana nan daram anan ake shirye-shiryen komai dan ita kam jin Ammin take na sosai a ranta kamar mahaifiya take jinta..

Tun da aka shigo satin auren shirye-shirye ya kara kacamewa tuni gidan ya fara karbar baki ta ko'ina kai kace auren fari ne, ba kunya ranar aure saiga matan Yayan Umma saidai kam jikinsu a sanyaye sanin tsiyar da suka shuka mata, ga mamakinsu sai sukaga ta karbe su ba tare data nuna musu komai ba cikin faram-faram sai hidima da take dasu, basu San tasun tayi darasi ba yadda takeji a yanzu komin girman cutarwar mutum a kanta ba zata iya tsayawa tayi ramako ba, adai yadda rayuwa ta bata darasi kuma successfully Allah ya kara dawo mata da ni'imar meya rage mata bayan godiya washi da wadannan ni'imomin musamman cire daga duhu zuwa haske......

*************

Sanye take cikin doguwar rigar material d'in da sukayi akon yinin biki dashi ash mai manyan touches din red, hakan ya bata damar amfani da red Kashmir veil da flat shoes and purse suma duk red, sosai tayi kyau abinta ga cikinta daya zauna das ya kara mata kyau, tasha make up da d'auri head, wanda tayiwa amarya ce ta musu suma....

Dube-dube take ko zataga yaro a harabar gidan ta aikesa, fizgarta taji anyi da k'arfi, cike da tsoro ta bare baki tana shirin zunduma ihu, saurin rufe mata baki yayi da hannun "dalla malama yi mana shiru, waye zai zo har cikin gida ya saceki, farar kura kawai" sauke ajiyar heart tayi tare kallonsa yadda ya yake wani yamutsa fuska saima yaso bata dariya, murmushi kawai ta samu zarafin yi.....

Yayi mata kyau cikin Ash d'in giznarsa wacce tasha aikin sama wanda ya k'ara fitar da cikar haibarsa hannun na clips ne inda yayi amfani da wani had'adden clips mai chain, bakar hular tangaran ya murza saman lallausar sumar sa, ba karya yayi ba hasada, hannunta kawai yaja zuwa dakin sa na gidan...

"Ke ko?" Ya fad'a bayan ya zaunar da ita kan seat, ya watsa mata harara, tasan laifinta bai wuce yadda da tayi ta kwana gidan ba, dake basu gama ayyukan su ba jiya duka gidan suka kwana dan basu suka gama ba sai around 2am na Daren jiyan...

Tun da taga ta tura masa morning text da ta kira duka ya kyaleta tasan ya shaka dama ko jiyan sanda Momy ta korasa ya yadda ya wuce....

Kwantar da kanta kan cinyarsa tayi tana wasa da button din gaban rigarsa cikin karyar da murya da neman sulhu take magana "pls kayi hakuri mana I know am wrong u but don't mean to hurt you" k'ara dauke kansa sama yayi "uhm" kawai ya furta...

Murmushi ta saki tare da zageye shi da hannayen ta, saman mak'ogoronsa ta Dora hannunta ta mintsilesa aiko da sauri ya sauke kam yana dariyar dole "kedai kin shigesu da fitina Allah, bayan kin kwareni kin Nisan tani da baby nah na tsawon rana" yace yana Jan mata kunne...

'Yar kara tayi "kaiko gwanin iya k'eta ba, yo naga auren ex d'inka ne ba gwara nayi participate sosai ba" zaro ido yayi.

"Lalalala! Dama ashe kin matsu ta tafi kina tsoron na dawo da abata" dariya tayi sosai "lallai ma Yaya kaiko anya kodai kishi kakeyi anya ma wannan fushin bashi da nasaba da auren ma?"

"Oho! Wai ma wace gulmar ce ta fito dake daga gidan, kodai missing din mijinki kikeyi 'yan mata" yace tare da daga mata gira yana kashe mata idonu" d'an duka takai masa tana murmushi..

"Yo idan ma hakane laifi nayi, tun da mijin nawa ya kasance gwanin ado da jan hankali Wanda kesa dole ayi kewarka idan akayi nisa dakai"

Murmushi ya saki tabbas kalamanta sun karbu, sun isa kamar yadda ya dace a birnin zuciyar sa, amma sai ya basar "uhum sannu tsari master, ana missing din nawa ne aka nisance ni, kinga bama wannan ba, in har zai yuyu kizomin da ex dina yanzu" dariya ta saki...

"Shaukin ne ya motsa, karfa ka manta saura awanni dai" tace tare da mik'ewa domin cika umurninsa, tasan waye mijin nata sosai dan haka ko d'ar bataji a ranta ba...

Rike mata hannu yayi tare da zuba mata narkakkun idanuwansa masu nakasata, saurin d'auke nata idon tayi saboda tsaro "a bari na gaisa da babynah tukun madam, kada zafin yamin yawa" ya fad'a k'asa-k'asa kamar mai rad'a, ganin bata motsa bane ya sanya shi mik'ewa tsaye shima ya taka gun ta....

Sunkuyawa yayi dai-dai cikin ya dora bakinsa tare kissing nasa, sannan ya saka hannayensa yana shafar cikin a hankali, sosai yakejin nishad'i yadda yakejin movement na babyn a hankali, zagaye hannayensa yayi a waist nata tare da sauke mata peak a forehead "habibty babynah yayi break" da kai ta amsa "sure?"

"Yes Habib rouh"

"Gud gal" yace "in tafi?" Ta fad'a a hankali dan tasan halinsa sarai karamin aikinsa ne ya baro mata aiki yanzu, shiru yayi kamar ba zai amsa ba, komawa yayi ya zauna kan seat tare da jingina bayan saman kujerar ido a lumshe "yeap jeki"....

Bayan 'yan mintuna sai gata ta dawo tare da Samihar wanda take mamakin kiran Ya Mu'azzam din dan idan bata manta ba tun rabuwar sa har zuwa yau iyakacin gaisuwa ke hadasu shima idan yazo gidan sun had'u.....

Kyautar 100k yayi mata tare da set na jewelry na gold, sannan ya Dora da guntuwar nasiha tare da mata fatan Alkhairi, tsantsar farinciki ta riske shi a wannan ranar ashe Ya Mu'azzam bai tsaneta ba kamar yadda take tunani, godiya sosai tayi masa tare da kara cewa Aymanah ta tayata godiya, Sam ran Aymanah bai sosu da abinda yayi ba saima burgeta da ya kara yi, cikin gida ma sai farinciki suke tayata Umma kam ta rasa bakin magana tabbas Allah na sonsu da rahamar sa.....

Amarya dai a ranar ta tare gidan mijinta dake Kaduna bayan tasha fatar alkhairi daga masoya da 'yan uwa..

*A week later....*

" Habib Rouh! Pls ka barni naje, Allah yaya jikina yamin nauyi, kuma kaga Dr take ina ringa exercise" a marairaice take maganar uwa tayi kuka, ido ya zuba mata Sam bayason fitar a ransa saidai ta riga ta nace gashi kuma ya riga yayi latti...

"Kinga Habibty ki zagaye cikin gidan nan mana ai is OK for you, kibar zancen fitar..."

"Yaya Mana, kaga fa tun da nike a unguwar nan ban taba fita koda gate d'innan da kafana ba fa saidai a mota kullum nidai yaya uhum!"

Dafe kansa yayi, ta Riga ta iya fitina in ta motsa mata ba dama bare yanzu har cikin na kara mata ita, ga fushin banza data iya Abu kad'an sai ta haye "is OK, ki bari idan na dawo zamu fita tare mu zagaye unguwar!"

"Uh um! Nidai nafiso yanzu da sanyin safiyar nan, Allah ba dadewa zan ba, kuma ai tare da Sabira zamu fita ta rakani"

"Oh! Shikenan kije but pls take care of ur self and unborn for me pls"

"I'll yaya inshaa Allah, Allah ya tsaremin kai a dawo lafiya" ameen ya amsa tare da wucewa da Sauri, itama ciki ta koma cikin farinciki ta d'auko hijab da wayarta da purse, ta kira Sabira suka fita..

Sosai yanayin yake fizgarta tana jin dadin sansayar iskar safiyar, kallon unguwar take daki-daki da kyau Ashe dai ba laifi unguwar Nada kyau, hango mai siyar da agwaluma tayi, nan take yawu ya tsinke, yana d'an nisa dasu bata tsaya wata-wata ba, ta fitar da kudi a purse tare da nuna wa sabira shi akan ta siyo mata ita kuma ta samu wani d'an dutse a gurin ta zauna...

Game ta fara yi da wayarta hankali kwance kafin sabirar ta dawo su wuce, jin nauyi a kanta alamar an tsaya mata yasa tayi saurin D'agowa...

Zaro ido tayi k'irjinta uwa ya fito waje ganin gardawan da ke gabanta su uku kowanne fuska a murtuk'e ba rahama...

Kafin tayi wani yunk'uri, d'aya daga cikin yayi saurin shaka mata wani farin kyalle a hanci, nan da nan ta zube a hannunsa a sume...

Kinkimar ta sukayi suka saka a motarsu tare da barin unguwar da gudun tsiya...............

_🤦🏼‍♀😰 Wayyo silly Aymanah kosu wanene oho! Kome ta musu?, Abu dai kamar ana targeting ta🤔?_

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌎 *Duniya Makaranta* 🌎

_idan muka rasa kudi mukan ji ciwo mu samu damuwa a ranmu, a kullum mukan rasa kwanakin mu na Duniya amma bamajin komai ko a jikin mu, hmmm kudi abokin tafiya👌🏻_

*Page* 5⃣7⃣

______Koda Sabira ta dawo wayam ta samu gun da tabar auntyn nata ba koma, gudu tayi sosai har karshe layin bata ba mai kama da ita, tunanin ko gida na koma ya sanyata rankaya wa gidan...

Tana haki ta isa gate, da sauri gate man din ya taso ya cimma ta ganin ta a firgice kuma ita d'aya ba matar gidan, tambayan ta ya shiga yi ina Hajia, k'ara firgicewa tayi tace tare da gayamai abinda ya faru, shima nan take hankalinsa ya tashi, wayarsa ya koma da sauri ya dauko tare da dannawa uban gidan nasa kira.....

Mu'azzam dake zaune a office d'insa, tun da yazo ya kasa yin komai haka kawai yake jin yanayin ba dad'i Sam baida kuzari, wayarsa ya zaro da niyyan kiran Aymanah yaji ta koma gida duk da yasan dole ma ta koma tun da tace ba dad'ewa zatayi ba, kusan sau uku yana gwada no ta ana gayamai tana a kashe, kuma duka rayukan ta, mamaki ne ya kamasa yasan tana da full charge kuma rufe waya ba dabi'arta bane, kafin yayi wani dogon nazari sai ka kira ya shigoshi ganin gate man ne ya saka shi hanzarin d'auka dan yasan da wata a kasa....

"What!" Ya fad'a da k'arfi, tare da yasar da wayar a k'asa, zubewa yayi akan seat tare da dafe kansa da dake wani juya masa "what's mean ba'aga Aymanah ba, meke shirin faruwa ne?" Da sauri ya mike cikin zafin nama kamar wadda akayi allura keys kawai ya zara ya fice da sauri...
Chapter 29 · 0% Book details