← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 34

Sashe 30

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ya isa gidan kuka sosai ya samu Sabira nayi, tsawa ya daka mata "ya akayi ta bata amma ke gaki anan?" Ya fad'a a tsawace, aiko tuni jikinta yad'au bari, cikin inna-inna ta gayamai yadda akayi tare da nuna masa agwalumar da canjin....

"Innalillahi wa'inna ilairraji'un" ya fad'a cike da tashin hankali "kuma ko alamar ta baki gani ba da kika dawo?" Kanta ta shiga juya masa kamar kad'angaruwa......

Bai sake bi takan su ba, ya sake figar motar ya fice tsiyace, direct police station ya zarce yakai report, duk tunaninsa ya gama tushewa to me zaisa a sace masa mata me yayi da zafi haka, me tayi itama da za'a saceta ba tare da an duba yanayin ta ba, rashin sanin madafa da abinyi ya saka shi zarcewa gida direct dan su san halin da ake ciki....

Sosai hankulan su suka tashi matuk'a, anyi Sa'a Dady na gida Abba ne dai bayanan, cikin tashin hankali Dady yace "kinga Suwaiba idan da hannunki a cikin b'atan yarinyar nan, tukan abin yayi nisa ki gaya mana" tuni hawaye suka wanke mata fuska illar mugun hali kenan, ko ka bari ba lallai tambarin ya tafi ba, dana sani na sosai take da rayuwar bayanta gashi har yanzu mijinta bai gama yarda da ita ba.....

"Haba Yaya taya zakace haka, Ummu sageer ba zata aikata haka ba, adai bincika gidajen 'yan uwa tukun ko can taje kila" cewar Ammi duk da hankalin ta a tashe yake matuk'a da batar 'yar tata wacce take da tabbacin ba inda zataje a halin da take ciki, jikinta na gaya mata saceta akayi amma bata zargin Umma dan d'an zaman da sukayi na dawowar ta, ta fuskanci tayi tubar gaske...

Hajja kuka take bil hakki "Kabiru ku kira Mamuda kuje ku binciko marainiyar Allah nan, Suwaiba ba zata aikata haka, dan Allah kuje Ku nemota"

"Dadyn Samiha wlh babu hannuna a ciki ka yadda dani" sai kuma ta bashi tausayi ganin yadda take kuka "kiyi Hakuri Ummu sageer ki dena kukan mun sani ba zaki aikata ba, bara na kira Alhaji yanzu yasan me ake ciki" cewar Momy....

"Nifa na fara zargin akaina ne aka saceta zai zamo cikin mutanen da nayi shari'a akan su ne" sai lokacin mu'azzam yayi magana bayan ya dad'e yana nazari akan abun...

"Idan kuwa haka ne gara ayi reporting case dinnan wa police, sannan kuma abi kididdigin wayarta yadda abin zai so da sauki" cewar Momy..

"Haka ne bari muje kafin yayan ya iso"

"Dady na riga nakai report d'in tuni ai" dafa kafad'arsa Dady yayi yana bubbugawa ..

"Relax my son be a man, kada ka damu za'a ganta inshaa Allah, cikin koshin lafiya"

Sai lokacin hawayen da yakeson yi suka samu damar sauka "Dady meyasa zata biya bashin laifina? Me tayi musu? Meyasa ba zasu yimin ba nida nayi musu?"

"Take it easy, kaji zo muje" bin bayansa da kallo su Momy sukayi sosai ya basu tausayi yadda ya koma wani iri kamar ba sadaukin jarumi Ibrahim mu'azzam bane....

**********

Da salati a bakinta ta farka tare da bin dak'in da take kwance da kallo, sannu a hankali kwakwalwar ta, ta tariyo mata abunda ya faru, da sauri ta mike cikin tashin hankali, zuciyarta na burgawa da sauri Wanda ya haddasa wa dan cikinta juyawa da k'arfi, hannayenta ta saka ta tallabe cikin, tana hawaye tare da Dana sanin bijirewa maganar mijinta, tana tunanin dalilin sato ta a kawo ta anan...

Jin an turo k'ofar ne ya sakata kallon k'ofar da sauri, daya daga cikin mutane ukun nan ne masu mummunar kama ya shigo "ke!" Ya daka mata tsawa wadda ta kara firgitata ita da d'an cikinta..

"Biyoni muje" kawai ya fad'a ya juya, kamar ba zata ba kuma sai ta tuna ko bataje ba kaita za'ayi gara ta rufawa kanta asiri taje da k'afarta, jiki a sabule tabi ta k'ofar da ya fice.....

Wani Alhaji ta samu hakimce yasha babbar Riga a shigar kam kaga kamilallen mutum, yana zaune kan seat ya dora kafa daya kan daya yana girgizawa, umurnin ta tsaya a gabansa suka bata a tsawace wannan karon hadda mata biyu a cikin su, saidai daga ganinsu ire-irensu ne...

Binta yayi da Kallo daga sama har k'asa, sannan yayi wata mayaudariyar dariya "Mrs Barr Ibrahim Mu'azzam Gwargo!" Ya fad'a yana tab'e baki..

Itadai sai hawaye take tana kwaroro addu'a duk wacce ta sawwaka ta kuma zo mata a baki, tana mamakin yadda ya kama sunan ta, kenan akan Yaya Mu'azzam aka satota kenan, kome zasuyi mata, ita dai gata ga Allah..

Kamar yasan tunanin da take kenan "DAT gud, Ibrahim ya kusa zama Abba kenan, kina son d'an cikinki kuwa?" Ya jefa mata tambaya a bazata, da kai kawai ta samu zarafin amsa masa...

"Hahahaha! Nima kinga inason d'ana Amma Ibrahim ya nace saida ya rabani dashi, kada ki tsorata da yawa fa, nima iya d'an nasa zan Ciro na rabasa dashi kamar yadda ya rabani da nawa shikenan vice versa" ya sake fad'a hankali kwance yana dariyar k'eta...

Zaro ido tayi tare da Kara rumgume cikinta sosai, jikinta na rawa hawayenta sun dad'a karuwa, zubewa tayi akan guiwowinta "dan Allah kayi Hakuri Baba ka yafe mana karka rabani da d'ana bashi da laifi baima san sanda akayi maka laifi ba, na rokeka karka rabani da cikin nan" tana kuka sosai tana rokonsa, shi kuma kamar zuga shi take yanajin tana masa goge ne, Wai ya yafe ma Ibrahim....

"Ke! Rufemin bakinki! Kinsan lokacin da na d'auka ina jiran wannan ranar d'aukar fansa, kinsan abinda na batar akan irin wannan ranar? Nonsense! Ke kuzo Ku shige ciki da ita ku fafemin cikinta Ku ciromin d'an Ibrahim yanzu na ganshi a gabana" ya fad'a cikin k'araji fuskarnan ba rahama kamar bai taba dariya ba....

Kuka sosai take tana tirjewa su kuma suna janta da karfi tare da daka mata tsawa, har su ka shige dakin da ita cike da rashin tausayi.....

"Abba nan ne direction d'in" Adnan ya Fad'a lokacin da suka iso kusa wani kangon gida, babba ne sosai, daga nan sukayi parking motocin su, mota uku biyu na 'yan sanda d'aya tasu ce Abba, Dady, Mu'azzam, Adnan da Hafiz...

Cikin dabara da taku suke bin directing d'in, har suka isa wani b'angare da suke jiyo alamun mutane...

"Wayyo! Wayyo Allah na, wayyo Abba na, Ya Mu'azzam pls, innalillahi wa'inna ilairraji'un, shikenan sun kasheni!"............

_fans ba jan aji ko jan ra'ayi bane kamar yadda wasunku ke tunani, yanayi ne dai ya canja ayimin uzuri👌🏻 😘😍 heart you All_

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌎 *Duniya Makaranta* 🌎

_Babu mugun Abu kamar bashi, yakan tozarta mutum da rana, da dare kuma ya hana masa bacci, ya Rahman ka rabamu da bashi👏🏻 Ameen.👌🏻_

*Page* 5⃣8⃣

________jiyo ihunta ne ya basu tabbacin tana ciki, Mu'azzam dake tafe kamar kazar da kwai ya fashewa a cikin yini d'aya tal ya fita kamanninsa ya dawo wani kala ba kace babban barrister nan ne mai cike da kwanji da kwarjini ba, Wanda sam barazanar kowa bata tsoratar wa, namijin duniyar nan mai sanya mazaje su gudu, amma yau d'aya duk ba wad'annan siffofin a tare dashi saboda Aymanah itace weak point nashi, akanta kawai yake susucewa ya rasa sanin karan kansa bare waninsa "Dady wlh muryar ta ce, Aymanah ce Abba muje da sauri Dan Allah ranka ya dad'e kada su illata ta" ya fad'a da karaji yana kokarin bance k'ofar, cikin sauri Dady ya rik'osa cike da tausayin sa..

Girgiza masa kai yayi alaman ya dena ya bubbuga bayansa, Su Adnan cike da tausayi suke kallon sa, Wai Ya Mu'azzam ne ya susuce haka lallai so ma wani Abu ne daban, shima Abba ido kawai ya zuba mishi, ogan police d'in ya daga masa hannu tare da yin k'asa da murya "yi hakuri komai yazo karshe, kayi a hankali kar komai ya lalace ba abinda zai faru da ita okey!" Shikam sai yaji kamar zugashi sukeyi ga tsantsar fargaba da tausayin Aymanah yadda take ihu da karaji gwanin tausayi sannan ace ya tsaya idan wani Abu ya sameta bazai taba yafewa kansa ba....

D'aya daga cikin police d'in dake mak'ale jikin k'ofar ne ya jinjina babbar yatsar sa alamar sauran su zama cikin shiri....

B'angaren Su Alhaji mai dala kuwa jiyo karar Aymanan na yawa ne yace daya daga cikin ukun ya dibo menene yake gudawa, da sauri ya dawo tare da sanar dashi aita hanasu yin aikinsu ne ta d'auki makamai itace ke barazana sannan ita ke ihu, cike da fushi yace suje su danneta shi d'an kawai yake da bukata....

Sam basu ji shigowar mutane ba saukar kan bindiga kawai sukaji a kwakwalen kawunan su, Wanda ya tilasta musu dakatar da abinda suke yi, cikin zare ido da mamaki yadda aka gano gun da yake cikin sauki duk tsananin tanadin da yayi, kamar ogan nasu yasan me yake tunani yace "sakenka daya ne daka yadda kuka shigo da wayarta, haha so next time saika kiyaye kuskure komai k'ank'antarsa saboda tsaro" yace cike da gatsali tare da tura k'eyarsa, suma sauran aka tasa su gaba...

K'ara fashewa da kuka tayi cike da jigata ta fad'a jikin Mu'azzam, sosai ya k'ank'ame ta cike da tauaayin Kansu, sai lokacin ya samu sukunin zubar da hawaye wato wani sa'in ma kuka samun damace, yama k'asa cewa komai sai bubbuga mata baya yake a hankali, zameta yayi daga jikinsa ya kafa hannunta suka k'arasa gurin su Abba...

Kallon ta su Abba keyi cike da tausayi yadda tayi biji-biji da ita ba takalmi bare d'ankwali gashin kan yayi wani yamutsewa kace sabon kamun hauka sai sauke ajiyar zuciya take, nan Suka shiga rarrashin ta kafin police d'in su gama kwashe su Alhaji da yan daban sa, a mota, Abba ya bisu suka wuce station su kuma su shiga motar su suka wuce....

************
Chapter 30 · 0% Book details