← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 34

Sashe 20

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan azahar ta isa gidan Yayan nata a jigaye wuji-wuji da ita, a tsaye ta samesa tare da matansa tsakiyar gidan kirco-kirco Neman duniya sunyi mata sun rasa inda ta Shiga, gashi Hafiz ya kawo mata kayanta dazu ya tabbatar musu bataje gidan su ba, wannan ne ya kara tayar ma yayan nata hankali kaddai guduwa tayi wani gun, dan tun jiya ya fahimci a hargitse take, tsoronsa d'aya kar taje ta sakeyin abinda ba shine ba, ko kuma wurin haukanta taje ta fada mugun hannu, Wanda baya fata duk Girman laifinta har gobe ita 'yar uwarsa ce, bazai so ta cutu ba ko yaya ne, wannan ne yasa ya tayar da hankalinsa ya kuma tayar ma matansa nasu...

Kallon tuhuma ya bita dashi tare da watsa mata mugun, Wanda ya saka 'ya'yan cikinta yamutsawa tare da hadiye yawu "ina kikaje tun safe Suwaiba!?" Ya tambaye ta a tsaurare tare da tsare ta da ido.....

Kame-kame ta fara tare da fad'in "um...uhm..dama...naje gidan wata k'awata ne shine na biya kasuwa na sayo wannan" ta nuna masa net din da ta siyo tare da gaya masa d'akyar ta iya bacci jiya........

Wani kallon ban aminta dake ba ya bita dashi "wallahi tun wuri gara kisan me ke miki ciwo Suwaiba, kedai ba yarinya bace gara ki maida hankalinki ki Dena biyewa rud'in duniya, ba abinda wanin Allah zai amfana miki dashi sai bata, ki kula dakyau duniya ce gidan banza ki nutsu kiyi tunani da kyau" yana kai nan ya buga rigarsa bayan ya gaya mata sako nan daki da Hafiz ya kawo mata na kayanta....

Jiki a sanyaye ta shige dakin, yayin da matan suka tabe baki tare da binta da harara wata hadda mata tsuki, gefen kafitar ta zauna tana mamakin matan yayan nata kamar basu ne 'yan korenta ba musamman lokacin bikinsu Samiha dasu akayi komai sai wani bin da suke kamar jela anan gidan suka kwana kuma sune ta sanya gaba akan komai suka wawushi kaya suka wuce amma wai yau itace abar wulakantawar su, lallai sun cika 'yan halak..

Janye damuwar su gefe tayi tare da duba kayan da Hafiz din ya kawo mata, trolley har biyu shake da kayanta sai kenan tazo zama ne, ga Dadyn su ko ta kanta bai bi kota kira baya dagawa me kenan, aiko muddin ta kara sati a gidannan bone ya cita, amma Meye mafita a gareta, ya za'a yi ta samu Dady ya fara sauraronta, yanzu ina ma zata samu wani bokan, idan ma ta samu ina kudin suke na kai masa?? "Lallai dole na nemo mafita dan burina bazai tafi a banza ba...." Ta fad'a a fili.......

************

"Kasan me Yaya?" Aymanah ta fad'a tana duban cikin idonsa, zaune yake kan three seat, tayi filo da cinyarsa, tana kallon series din da ake haskawa a Mbc Bollywood, na Madhubala, inda bata fahimta ba shike fassara mata dake da larabci suke gabatar da shi, wasa yake da gashin kanta daya barbazu a cinyar tasa dan ya kunce mata ribbon da ta kama shi dashi yace yafi masa kyau a hakan, shima maida kallonsa gareta yayi "aa sai kin fad'a" ya amsa mata....

"Nifa har yanzu mamaki nike Allah Yaya"

"Game dame fa?" Ya tambayeta..

"I can't believe Yaya ka Dade kana k'aunata amma ban sani ba, waima tsaya tukun tun yaushe ka fara??"

Murmushi yayi kawai, saida ta fara tura masa baki dan sannan yace "oh kinfa koya rigima baby to me kikeso nace ne?"

Kara turo bakin tayi "oho ni kama barshi na fasa saurara tunda sai ka ja min rai" d'agota yayi sannan ya rungumeta sosai a jikinsa....

"Nima bazance ga ranar da na fara kaunarki ba, abinda kawai zan iya cewa shine, na rayu da k'aunarki ne a raina ne, watakil ma tun ranar da na fara ganinki ne" tun da ya fara maganar tayi lakwas a jikinsa tana kallon yadda dan ficicin bakinsa ke motsawa wato abin daga jininsa dan yadda yake yamutsa fuska idan yana magana kamar baya har yau hakane bata canja xane ba, Wanda bai fahimci halinsa bane sai d'auka yanga yake masa ko kyamatar sa yake...

"Uhum yaushe kenan kake nufi? Wai ranar da ka hantare ni a gidan Hajja?"

Girgiza mata kai yayi alaman Aa "tun ranar da aka fara turamin fotonki kina jinjira nake nufi" zaro ido gaba d'aya tayi, dariya yayi tare da hure mata idon...

"Ragemin wannan na mujiyan naki masu firgita ni a kullum" ya kara sa yana kashe mata ido daya, itama dariyar tayi tare da kara kankamesa, wani irin sonsa ne ke huda duk wata gaba ta jikinta yana ratsawa...

" I can't believe Yaya....." Uhum nima a lokacin ban gane k'aunarki nike ba gaskiya na d'auka kawai dan kin kasance 'yar Uncle Hashim ce da aunty Fatima, but time going on na fahimci k'aunar ce dai nake miki kuma irin ta aure, hmmm bakisan how much I hurt b'cos of you ba, karfi da yaji naso na yaki ce ki a raina a lokacin, dan a ganina karshen kunya kenan wai ke nakeso Sorry to say kwaila dake, dan watakil da auren k'auye nayi zan haifi kamarki" ya karasa yana mata dariya, itama dariyar takeyi saidai tana dukan k'irjinsa a shagwabe..

"Kinsan ma tashin hankalin lokacin kin riga kinyi nisa a tsorona, kin ma san meyasa kika fara tsorona??"

"Ka dauka zan manta ne tsawa kake min kana kamar zaka dokeni" dariya yayi "clever gal, amma kin manta kece kin cika rashin ji da kukan banza a lokacin, ga Hajja na Neman sangartaki shiyasa nake maki hakan amma bawai rashin so ba kin gane" jinjina kai tayi alaman gamsuwa..

"Sannan lokacin da na gane sonki nake da gaske, rashin fad'ar shi ne alkhairi a gareni duk da nasan I so much burn inside, amma nasn Dana fad'eta a lokacin da rikicin cikin gidanda ake a lokacin ya zarce tunani kinsan komai dai ga kuma samiha da ake ta turamin a lokacin...."

"Ake tura maka ko kake sonta dai" ta katse shi...

Murmushi ya Saki "Aymah Habibty kenan! Ban taba k'aunar wata 'ya mace ba bayan ke"

"U mean har aunty Samiha?" Jinjina mata kai yayi "to Amma ai kai da kanka ka amince da aurenta?"

"Saboda kinyi rejecting d'ina ba" kara zuba mishi ido tayi tana son gasgata zancensa..

"Nasan ba zaki fahimci komai ba a time din, tunaninki kawai na cika tsanani musamman a kanki sai kika d'auka tsana ce kawai, but da kin kula a lokacin nafi miki tsawa ne musamman idan na ganki da Hafiz ko Adnan dan a tunani na waninsu zai iya cusa mini soyayyarsa musamman yadda naga kuna da shakuwa a tsakanin Ku, hmm I can't explain everything but a sanadin ki ne na ke dadewa ban dawo kasar ba dan banso amin maganar aure saboda ke nike jira duk da cewa bansan taya auren mu zai kasance ba, dan ban taba sanin wasiyya uncle ba idan ba ranar da aka fad'eta a gaban kowa ba" jinjina kai tayi.....

Wannan shine son maso wani kenan Samiha na jiransa shiko ita yake jira ba tare data sani ba, to ai har gara Samiha yasan da ita...

"Hmmm I can't explain my feeling lokacin da kika ce ba zaki aureni ba, naji matukar zafi a raina sosai shiyasa na amince da auren Samiha kai tsaye ba tare da dogon tunani ba, don bansan kalar zafin da mutum keji ba idan Wanda yake k'auna yayi rejecting nasa ba sai time din shiyasa na kasa yiwa Samiha abinda kika yimin duk da ba ko kwayar sonta a raina, saidai kar taji zafi a ranta kamar yadda naji kuma inajin nauyin Dady musamman yadda ya nace saidai inna amince....."

"Niko sai wauta ta debe ni na dubi kwayar idon Abba nace ban amince da aurenka ba saboda butulci na" ta katsesa tana jin zafin abinda ta aikata "c'om babe aina miki uzuri daga baya tunda Nina ja komai da kaina, kuma ai iya gaskiyarki kika fad'a ko?"

Zatayi magana bell door ya katseta, kallonsa tayi tare da tashi daga jikinta, wrist din hannunsa ya kalla 1:30pm..

"Kinga ma it almost time 4 salat, bari na duba waye zan wuce masjeed daga can...

Narai- narai tayi da ido kamar zatayi kuka " Hayatiy to ci gaban labarin fa" murmushi ya saki tare da peaking forehead nata "ya miki dadi ne?"

"Sosai I really enjoy"

"Bari na dawo to muci gaba, kinga anata danna bell door din" jinjina masa kai tayi tare blowing masa light kiss a lips...

Nusaiba da Amira ya samu a kofar gaisawa sukayi sannan ya fice, sauke numfashi Nusee tayi "Yaya ho, an gama shanya mu anacan ana love shine ake wani tsare mana gira" dariya Amira tayi "to ya son ranki so kike ya mana wasa kamar besty? Ko kina masa abinda take masa ne?"

Saurin baki tayi tana dariya tare jan hannu Amira akan su shiga tana fad'in "rufamin asiri wannan saidai ita nidai barni da ya Hafiz dina"..

Jiyo muryar su da tayi ne ya saka ta daka tsalle tayo kansu "me! Lallai yau gidannan da manyan mutane a cikinsa" tana dariya tare da kama hannayen su...

Hararar wasa Nusee ta sakar mata "uhum so love manya! Bayan an gama shanyamu ko" dukan wasa takai mata tau 'yar magana zaki fara ko, naga dai love dinnan kowa nasha da nasa habibin bayan ma kun koramin shi"

"Aa beyi zafi ba mu tafiyar mu ki dawo da kayanki" cewar Amira itama cike da tsokana, dariya sukayi a tare sannan suka isa cikin falon, suna ma juna tsiya...

Basu zauna anan ba suka wuce part d'in ta don gabatar da Sallah, Wanda tun jiya da ta dawo sai yanzu ta leka amma ga mamakinta sai ta samesa tsaf sai kamshi ke tashi ko'ina a gyare...

Murmushi ta saki tasan aikin gogon nata ne yasa aka gyara, sosai taji ta kara tsunduma a koramar sonsa........

*Marraha home of peace, na gaida Ku kyauta ana tare iya wuya en uwa😍😘*

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
Chapter 20 · 0% Book details