← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 34

Sashe 27

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wata innocent gal ce from a poor house, yaron gidan da take aiki yai mata fyade, the wicked guy haka ya mayar da ita karuwar gida Amfani da ita, bayan ya tsorata da duk ta bari wani ya sani saiya harbeta, a haka ta samu ciki in a very young age 12years, shine fa ya d'auketa ya kaita wata private clinic akan a zubar da cikin a garin yaya akaje aka samu matsala jini ya b'alle mata, tunda aka gaya masa ya shura takalmansa ya gudu, inda Allah ya kawo mata sauki, ta ari wayar wata nurse a asibitin ta kira Abbanta ta gayamai halin da ake ciki har asibitin, koda suka zo ta gama fita hayyacinta...

Hankali tashe baban yaje can gidan aikin nata ya sheda musu amma kememe uban yace badai d'ansa ba saidai wani can daban haka ya zazzagesa yaci masa mutunci, in takaice maka dai yanzu hukumar 'yancin mata ce suka saka case din kotu, jiya bayan wucewar ka akazo aka sameni da case din, har asibitin nike wlh Barr saida na kokama yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, na girgiza kuma da case din, yaron d'an gidan Mai Dala ne, duk wata shaida sun boyeta Brr, case din yafi karfina shine nazo gareka nasan zaka iya assisting dina"

Sosai labarin ya daka Mu'azzam matuka "zan taimaka Barr Zayyad, muje na ga yarinyar da iyayenta....."

Baisan sadda kwalla ta zubo masa ba bayan yaga yarinyar da halin jin jikin da take sannan yaji cikakken labari daga iyayenta, Dan ita kam dakyar take magana yadai tabbatar da yaron ne ya aikata mata daga gareta, saidai ta ina zai fara yasan waye Mai Dala a garin da karfin power sa, saidai ya lashi takobin yin case din, Dan ganin yarinyar yake kamar 'yarsa ko k'anwarsa wadanda idan hakan ya faru dasu sai inda karfinsa ya kare....

Sosai yau ta zage ta gyara part din nasa hadda wanke masa inner wears, sannan ta sauko k'asa da taimakon Sabira ta had'a daddad'an girkinta favorite nasa tayi masa semo and egusi da kuma zobo da jinja duk dan ta Burgesa, saida ta tabbatar komai yayi yadda ya kamata sannan taje ta tsala wanka na d'aukar magana..

Sosai ta had'e cikin wata dakakkiyar Shadda brown gown ce tasha aikin sama, make up, sosai tayi kamar mai shirin zuwa biki bayan ta kafe d'auri...

Ta damu sosai ganin had 4 after bai dawo ba wanda iya dad'ewar sa, 3 ga ko kiran da text da yake mata bako daya yau...

Ta kikkira yana ring be daga ba, jugum ta zauna tana tunanin ba lafiya kam...

Can zuwa 5 ya dawo tun daga yanayin fuskarsa ta fuskanci da damuwa, duk da kokarin boyewa da yakeyi "wow princess wannan kyau haka ina zaki kaini?"yace bayan ta tarbesa tare da yi mata sannu da zuwa...

" Yaya muje kayi wanka ka gaji da yawa" sosai tafiyar da shi tare da taimaka masa yayi wanka tare da cin abinci, bayan sun kammala ya d'an huta tazo ta sameshi yana zaune yayi nisa cikin tunani Wanda a zahiri nazarin case d'in nan ne kawai yakeyi....

"Yaya!" Ya kirashi bayan ta kama hannunsa, ido ta zuba masa bayan ya d'ago ya kalleta..

"Meke damunka ne?"

"Sorry baby yau ba kira bare text ko?" Sai lokacin ya d'auko wayarsa wacce ya sakata a silent run lokacin da sukaje clinic din nan....

"Ashe ma har kirana kikayi kin gani ko a silence take ban gani ba"

"Yaya menene?" Ta kara fad'a cike da damuwa...

Dago hannunta yayi ya sumbata "kada ki saka Damuwa dayawa fa kinsan conditions naki wani Case ne kawai ya tasomin" dama tayi tunanin haka yana mugun saka kan shi damuwa indai yana da case ta kula da haka tun ba yau ba...

"Yaya na menene hala?"

"Uh um! Nasan halinki da tausayi zaki iya saka damuwa kema a ranki, banason wani Abu ya sameki ko baby nah kimin Addu'ar nasara kawai"

"Pls yaya ka gayamin ba abinda zai faru..."

Rungume ta yayi yana dora hannunsa a cikin ta "barin duba lafiyar babyn Abinsa nayi missing nasa"...........

So yakeya share zancen ta fahimci haka " Yaya Mana" ta sake fad'a tana narke masa......

_love you my fans😍💋_

*Siddiqa CE*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌎 *Duniya Makaranta* 🌎

_Idan Allah ya daukaka ka duniya da masoyanka zasu san matsayinka, idan ka shiga jarrabawa lokacin ne zakasan asalin masoyan ka._👌🏻

*Page* 5⃣5⃣

_________washe gari su Uncle Salman suka zo kamar yadda suka yi musu alk'awari, wuni cur suka musu sai bayan asr suka wuce, sosai wani irin sabo da shakuwa suka shiga tsakanin Fauziya da Aymanah kace wasu kawaye da suka taso tare, sai tsakanar juna suke suna ta areren su, shima Mu'azzam tun yana dari-dari da cin magani saida ya sake yadda Uncle Salman ya keta jansa da hira gasu Adnan da Hafiz suma sunzo dake basu samu haduwa ba jiya, dole ya sake shima akayi dashi, saidai duk da haka yana yi yana basarwa da yamutsa fuska Wanda dama his nature ne shima Salman d'in ya fahimci hakan....

Exchange contact sukayi tare da tabbatar da zasu ci gaba da zumunci dan an riga an zama d'aya, Fauziya na tabbatar da Aymanah data haihu ta sanar musu tun suna hospital dan suzo cin remgem da wuri, dariya tayi ta tabbatar mata aiko itace zata fara gayawa ko, haka suka rabu cike da nishad'i.....

Dakika da koma sakan, sakanni sun koma awa, awanni sun juye sun zama kwanaki, kwanaki sun koma watanni, watanni haka rayuwa ke nausawa da dad'i ba dad'i farinciki sab'aninsa is all about life...

Zuwa yanzu Samiha ta gama iddar ta, in ka ganta a yanzu kai da kanka kasan ba waccen Samihar bace ta dawo wata Sayyada, bata missing zuwa islamiyya duk da tana kan karatun ta ne, duk ta tattare gyalulukan ta ta kyautar ta mayar da hijabai ta dawo decent sosai so cool, tuni manewa sun fara kawo mata hari tun daga Samari zuwa Zawarawa, ganin haka ne Abba da Dady sukace ta tsaya ta nutsu ta zabi wanda ya kwanta mata a rayuwa ta yadda da halayyarsa ta tsayar sai su kuma suyi bincike yadda ya kamata, su Momy ta shawarta inda Ammi tace ta farayin istikhara duk wanda ranta ya nutsu dashi shine mafi alkhairi agareta.....

Shawarar Ammi tabi tayi istikhara, cikin ikon Allah taji ta samu nutsuwa da wani Sudais dan abokin Dadyn ta ne, yayi aure saidai matar ta rasu gurin haihuwa, dake dama a shirye yake cikin k'ank'anin lokaci komai ya kankama.....

**************

"Yanzu Kabiru haka zakayi ta zama ba mata? Ka maida matarka kace sam kuma kak'i ka sake wani auren Anya Kabiru rayuwa zatayi haka, kada ka manta fa kune kad'ai kai da d'an uwanka kuka ragemin ba Mahaifinku ba d'an uwanku u'um?" Hajja tace da Dady, cikin sigar rarrashi da nasiha...

"Nima abinda nake ta magana kenan Inna yayi hakuri ya mayar da matarsa kodan darajar zuri'ar da ke tsakanin su, ga auren 'yarta za'ayi bata da masaniya, ka rabu da ita kuma ka rabata da yaranta, kar kaga sun d'auke idonsu suna bin duk abinda kakeso ka d'auka basa sonta, komin munin halinta suna k'aunar ta kuma basu da sama da ita, kuma na tabbatar zuwa yanzu itama ta gama gane kuskuren ta, ka d'aure ka bata wata damar Ku sake zama" Abba ya dora akan zancen Hajja.

Jinjina kai yayi Suwaiba tayi musu abubuwa fa a rayuwa "Inna, yaya bawai naki ta taku ba, amma kada Ku manta wacece Suwaiba ba wanda batayiwa tab'o a cikin mu ba, bata tsoron Allah bata da imani..."

"Haba Kabiru ya kake magana kamar haka, kamar ka manta kaddara?" Hajja ta fad'a a d'an tsawace....

"Kanina kada ka manta ko ubangijin mu muna masa laifi ya yafe mana bare d'an Adam, kai da kanka kace Yayanta ya tabbatar maka da canjawar ta, ka daure ka bata damar nan kayi mata uziri ajizanci ne irin na d'an Adam" Abba ya fad'a bayan ya dafa kafad'arsa da sigar rarrashi...

"Shikenan zan dawo da ita inshaa Allah, Allah ya shige mana gaba" a tare suka amsa da Ameen, kana sukaci gaba da tattaunarwar da sukeyi game da auren Samiha..

Cikin gida kuwa shiri sosai sukeyi game da bikin, sosai Samiha ke ganin gata gurin Momy da Ammi har hajja ba'a barta a baya ba, tuni ta d'auki sheki dama ba Samiha akwai kyau a fuska jikin ne dai a bushe shima ba laifi ta cicciko da taji tsumi d'an gaske abinda ta rasa a auren ta na fari....

Su Aymanah ma ba'a bar su a baya ba, suma suna nasu shirin duk da kaffa-kaffa da Mu'azzam keyi da ita Saboda Babyn sa, amma tsabar rigima kullum tana hanyar gida suna tsare-tsarensu, dasu nusee hadda Kawalliyar Amarsu Samhar Farooq, d'an cikin Aymanah da ya shiga watanni bakwai ya fito das, sosai yayi mata kyau, har Mu'azzam ke tsokanar ta wasu lokutan wai kamar kar ta haihu tafi kyau da ciki, duk ya gaya mata haka cewa take kace haka man tun da bakai ke d'auke dashi ba, dariya yakeyi mata yace yo meye marabin dambe da fad'a bayan duk keda cikin d'aukeku nake bari ma kiga...

Nan yake d'auketa yayi ta zagaye da ita suna dariya, zallar k'auna take gani daga gareshi tasan itakam ta gama dacen duniya saidai fatar dacewa a kiyama kawai....(Allah yasa mudace )

_Ina labarin Umma wai.........?_
Chapter 27 · 0% Book details