← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 34

Sashe 26

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amaryar Uncle salman mai suna Fauziya tana tsakiyar su sai fira ake nan Aymanah ta shige cikin su bayan sun gaisa da Amaryar Uncle din da Aunty Samiha su Amira kam tsiya suka shiga yiwa juna, nan da nan Suka saba Da Fauziya dake ita kai waye ce ta saki jiki sai fira ake ..

Sai cewa take "gaske da Yaya ya kasa mantawa da Aymanah Ashe Aymanan wanke hannu ka taba ne chanchadi" dariya sukayi a tare "Shiyasa ai ta kama yaya yadda takeso" cewar Nusee, harara ta watsa mata "talle kewa Audi gori aike da Amira zan gayawa haka malama" dariya suka karayi sannan tace...

"Ke kuma matar Uncle ai kin ma fini had'uwa Allah" dake itama kyakkyawace ba laifi "kika ce ba, amma kema kinsan gaskiya ai" nan sukaci gaba da shan firar su suna kyakyatawa abinsu cike da nishad'i...

Samiha kam ganin firar tasu ce yasa ta zame jikinta da sunan zata shiryawa Abba abun bud'a baki Dan tuni firar tasu ta koma daki yadda zasu fi sakewa...

Sai bayan isha suka wuce gida cike da farinciki, Su Salman sukayi musu alkawarin Zuwar musu gobe kafin su wuce, suma suka wuce gidan da suka sauka na wasu causing Nasu...

"So much thank you My khaleel" tace bayan ta Dora d'ayan hannunta akan nasa wanda baya driving dashi...

"Are you happy?"

"Bohot kusshi pyaa(farinciki sosai masoyina)"

Murmushi ya saki "lallai matar Khaleel yau Indiyanci akeji...."

_Sorry fans aci gaba da hakuri dai👏🏻🤝🏼😍_

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌍 *Duniya Makaranta*🌍

_Masoya sirri suke suna daga nesa juna, mafad'ata hargowa suke suna kusa da juna, kusancin zuciya shine mai muhimman ci bana gangar jiki ba_👌🏻

😍😘 *Masoya masu bibiyata ta waya ta message, through chat domin sanin lafiya ta saboda shiru da suka ji, nagode sosai da sosai da nuna kulawa, kuma na yaba muku matuka, Ku sani nima maryam Abdul kuna raina abubuwa ne kawai suka sha kaina, amma inshaa Allah, zanyi iya kokarina har na kammala muku Zuri'a daya lafia, Allah yabar zumunci🤝🏼, one love dearies😍😍😍💋*

*Page* 5⃣2⃣

__________kulawa ta sosan gaske take samu daga gurin Mu'azzam, komai ya hanata yi indai yana gida komai shike mata, sai idan ya fita ne take d'an wasu kananun ayyuka duk da ya hanata yin komai yace kome takeson ayi mata ta saka Sabira, dake yarinyar Sam bata da kyuya ga kama jiki, kuma tasan makamar aiki, duk da kankantar ta Dan ba zata wuce 12years ba sa'ar su Munira ce, bata sha wahalar amfani da kayan birni ba dake ta san su a gidan Hajja saidai wasu wasu ta bata sani ba, suma da an nuna mata take ganewa, sosai take gyara ko'ina k'al, part d'in ogan ne dai bata shiga, shike gyarawa da kansa Dan ya hana Aymanah tayi masa...

Yau ma kamar kullum, tsaye yake gaban mirror around 8am, perfumes yake fesawa cikin sauri da alama dai sauri yake, kama hannunsa yaji anyi Wanda ke rike da perfume d'in....

"Morning Habibty" yace yama mata murmushi tare da jan ta ya rungume ta da kyau sannan yayi pecking forehead nata, yana kokarin k'arbar turaren a hannunta....

Lumshe ido tayi jin saukar peck din tare da ware idon a same time, tana kallonsa, baki ta d'an zunburo gaba "shine baka tasheni na tayaka shiryawa ba" tace tana ci gaba da kallonsa sosai yayi mata kyau a suit d'in takan kasa tantance a wadanne kaya yafi yin kyau tsakanin suit, kaftan, kananun kaya, ta bar abin kawar akan daga halittar sa ne kowanne shiga yayi karbarsa take....

"Sorry Habibty kin manta da kina on bed rest ne, kina bukatar Hutu, nima ba dan fitar ta zamo ta dole ba, ai da ba inda zanje na barki keda my unborn"

"Duk da haka My khaleel, kuma fa ni qlau nake jina yanzu dama fa na sati take gashi har ina shirin yin 2 week, kaki ka barni nayi komai, Allah ni na gaji da bed rest dinnan yaya Dan Allah ka barni yau na motsa jinina nayi maka girki da gyaran dakinka?" Cike da shagwaba take maganar tana bata fuska.

Shafa fuskarta yayi "Baby rigima, ki bari ki kara hutawa pls, banason abinda zai taba min lafiyarki data baby nah"

"Yaya pls ka barni Allah naji sauki, kuma na maka alk'awarin na fara naji bazan iya yi zan daina, pls Yaya ka barni na motsa jinina shima karin lafiya ne" cikin sanyi da taushin murya take maganar wata kalar tausayi, murmushi ya saki tare da lakuce mata hanci..

"Habibty badai wayo da dadin baki ba, naji kiyi din tun da zaki iya but kika ji ba dai2 ba ki barshi kawai kinji" girgiza masa kai tayi sannan ta kara fesa masa turaren tare da gyara masa Jan tie din wuyansa...

"Kayi kyau sosai my Khaleel, um nifa ji nake kamar ma karka fita a haka a kalle mun kai!" Dariya sosai maganar ta ta karshe ta saka shi, musamman yadda tayi maganar da kishin nan..

"Uhm ai ke bakya tsoron kishiya keda kike kuka lokacin da ake kwashe kayan kishiya tsabar soyayyar ki da kishiya, ai ki bari kawai ayi replaced extra part din can" lokacin da Abba ya turo a kwaso kayan Samiha shine tai ta kuka wai kada a kwashe shine yake tuna mata.......

Dire-diren kafafu ta fara tana dukansa a kirji tare da kukan sakarci Wanda babu hawaye fadi take "Allah ni yaya, Allah ni banason irin haka, ai dan tana Aunty Samiha ce shiyasa nayi kukan amma ni gaskiya ka dena min zancen kawo wata ko kuma Allah na koma gidan mu" dariya sosai yake mata tare da riketa gam ganin yadda take daga tsalle kar ta jima kanta da babyn su ciwo...

"Rufamin asiri karki kwanto min kura baby! Sorry Habibty, nima da wasa nake miki kin sani ai, ba wata saike kika je gida yanzu kika barni ai matsala za'a samu"

"Aiko tafiya zanyi in baka dena ba" kneeling yayi dai-dai waist nata......

"Na dena ai, barin gaisa da sweet unborn na wuce na kusa makara ana jirana" fara kal din best din da ke jikinta ya daga yana shafan Dan cikin nata da ya fito kadan Wanda ba lallai a gane ba in ba ta saka best ba ko body hug, shafawa ya shiga yi cike da shaukin son babyn, yanajin yadda yake motsawa a hankali, kafin yakai bakinsa ya manna masa kiss mai kyau, kallonsa take tana murmushi tare da kara godewa Allah daya azurtata da nagartaccen miji mai matukar kulawa, cikin ganin damarsa ba tare kaifinta ko dabara ba, hannayenta ta tsoma cikin lallausar Sumar kansa tana shafawa a hankali tana murmushi...

Dagowa yayi ya kalleta " uh um baby bari karki janyo min rigima yanzu" tasan kwanan zancen, murmushi ta saki tare da zare hannayenta ta rungume su a k'irji, tana fadin na "dena" murmushi mai sauti ya saki bayan ya mike "raguwa" ya fada yana d'aukar brief case d'insa, hannunsa ta d'ora kan nasa, kallon yadai yayi mata, narke idanuwa tayi "break fast fa"

"Don't mind dear, nasha tea and chips since, kema ga naki can" ya nuna mata mini center table din da ke gefen fridge "ki cinye gaba daya pls kafin ki fara aikin kinji"

Girgiza masa kai tayi "kai da kanka kayi?" Noodling head nasa yayi alaman eh "meyasa baka saka Sabira ba, she's good in cooking dear"

"I'm good too" ya takaita zancen tare da fara tafiya, tasan halinsa sarai bayason komai na yar aiki in ba dole ba, yarinyar da dak'yar yake amsa gaisuwarta yaushe zai iya sakata aiki "muje na raka ka to" tace bayan ta cimmasa tana karbar jakar...

"Kiyi zamanki baby kada ki wahala da yawa hawan nan da sauka" nidai zan iya Yaya sai kayi ta sani cewa na dena komai kana ragemin lada"

"Its OK! Muje" ya fad'a bayan ya zagaye mata kugu da hannayensa, yana murmushi itama murmushin ta saki, a haka suka sauko, ganin Sabira a falon kasan tana mopping ya saka ta zare jikinta daga nasa, ba musu ya saketa dama haka take batason yarinyar tana ganinsu manne da juna saboda kula da tarbiya...

Gaida su tayi da lafiya kawai ya amsa yayi gaba fuska d'aure bakya ce shine ya sauko yana murmushi ba, cikin sakin fuska ta amsa mata tare da tambayanta lafiyarta.....

Amsar brief case din yayi tare da pecking nata dake yarinyar bata hangosu "take care baby! I love you!"

"Love you too Hubbi rouh, Allah dawomin dakai lafia, Allah ya taimaka ya bada sa'a, pls yaya ka kiyaye halal da haram saboda ka gina mu da halal yadda zamu dace gobe kiyama saboda duk dadin duniya lahira ta fita"

Hannunta ya runtse cikin nata yana fad'ada murmushinsa shiya tabbatar ya gama dace da matar aure ya samu jindadin duniya saidai yayi fatar samu a lahira "inshaa Allah zan kiyaye Bilkisa nagode" itama murmushin jindadin samun sassaukan miji kamarsa tayi "ba godiya tsakanin mu yaya it my responsiblity! Take care" saurin juyawa tayi ta koma ciki Dan tasan taci gaba da tsayuwa gabansa ba tafiya zai ba gashi ya gama makara..

Shafo kansa yayi yana murmushi tare da bin bayanta da kallo, yadda take yawo cikin bujen wandonta irin na indiyawan nan mai fadi sosai.....

**********

A corridor da zai sada shi da office d'insa, yaci karo da Barr. Zayyad, musabaha sukayi sannan suka gaisa, kallonsa Mu'azzam yayi da kyau "Barr Zayyad whats going on ne! Na ganka wani iri, jiya bana jinka da kyau da kayimin waya menene?"

"Hmmm! Is a big issue Barr, mu shiga ciki nayi maka bayani" ba musu yayi gaba tare da bud'e office din...

"Yes! Ina jinka Barr" ya fad'a bayan yayi mazauni kan kujerar office dinsa, shima Zayyad d'in ya zauna a gun wacce guest suke zama suna fuskanta juna...

Fuskarsa kalar tausayi da bacin rai yace "is a case about raping" shima tuni fuskarsa ta sauya dawowar kasar nan zuwa yanzu yaga cases kala-kala amma majority akan raping ne ko child abuse, wannan wace musiba ce tayi yawa a cikin wannan al'ummar tamu....

"Ehem inajinka"
Chapter 26 · 0% Book details