← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 34

Sashe 23

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gwanda da kika ce as ur think, danni tun da na fara sonki zuciyata ta kulle na kasa kallon kowacce mace a matsayin mace sai ke, and ur preety too, u have good manner, and educated gal too, so why do you think am not going to love you?"

"Yaya ur such unique dat hardly to find, I can't believe you love a silly gul like me!"

"Hmmm Bilkisa kina manta cewa shi so ba ruwansa da isa ko matsayi, ko cancanta ba, bama wannan ba, bani da bambanci dake ta ko'ina mudin *Zuria d'aya* asalin mu d'aya idan har baki goranta min tarbiya dana tsotsa daga Ammin ki ai ni bai kamata naji wai na fiki ba, ban taba Dana sanin soyayyarki ba, kuma bazan taba yi ba har abada, fatana shine mu rayu cikin Aminci tare da zuria dayyiba wadanda nake fata zuki kalar tarbiyarki"

"Ameen" ta fad'a tana sunne kai....

Kashe mata ido daya yayi tare da daga mata gira, yayi kokarin zira harshensa cikin NATA......

*Siddiqa CE*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌍 *DUNIYA MAKARANTA* 🌍

_Sau daya damuwarka takan sanya wasu dariya, yi kokari kada dariyar ka ta kasance damuwa akan kowa_👌🏻

*Page* 5⃣3⃣

_________"OK zan gaya miki but kada ki yadda naga hawayen ki, kika yadda naka kukan ki I will punish you okay!" Girgiza masa kai tayi tare da fad'in "Eh Yaya".....

" Well! Case ne na cutar wa is about rape and child abuse" zumbur ta mike zaune tare marairaice fuska "Yaya Wacece haka wayyo meya faru"...

" U see har kin fara ko, aiki take gidan wani mai kud'i shine yaron gidan yayi amfani da wannan damar ya lalata musu 'ya......" Bata labarin yayi complete har zuwansa gurin su can hospital din.....

"Wayyo Yaya an cutar da ita, pls ka amshi case d'in Yaya don Allah ka kwatar mata hakkinta" hawaye kam sun gama wanke mata fuska, ita tama manta da an hanata hawayen, ga kwalliya rad'au a fuska amma hawaye sun bata, harara ya watsa mata "good gara da kikayi kukan, bari kiga" d'agata yayi cak, ya nufi upstairs, sai lokacin ta tuna da laifinta...

"Wayyo Yaya yi hakuri kaima kasan dole zan koka wannan labarin mai dukan zuciya haka? Pls kayi hakuri my Yaya my Khaleel, my Hayatiy"

Murmushi ya saki "daga baya kenan 'yan mata amma yanzu kam dole ki karbi punishment naki yarinya" kwaba fuska tayi tana dukan masa kirji a shagwab'e "Allah Yaya wayo dai kawai"

Tura k'ofar yayi da kafarsa yana 'yar dariya "koma meye dai" ya fad'a tare da tura k'ofar saura kadan ya murzan hannu a k'ofar wai na dakata anan( _yaufa Muz'Aymah sun dakatar dani daga kyaure_😔🤧)

***************

Duk yadda ya d'auki case din ya wuce tunanin sa, yanzu ne yake k'ara tabbatar da Shu'umanci irin na Masu kud'i, duk wata kafa da ya kamata ya samu gamsasshiyar sheda sun toshe ta, Mai Dalar da kansa ya same shi har gida akan ya janye don ya samu labarin case d'in hannunsa yake, ya riga yasan Zayyad bazai iya ba kasancewar sa bai dad'e da fara aiki ba so kuma case irin wannan yana bukatar gogewa da sanin makamar aiki...

Makudan kudade ya bashi akan ya janye, baiyi mamaki ba don wannan ba shine karo na farko a gareshi ba, sosai ya gaya masa magana son ransa sannan ya tabbatar mai case yanzu ya fara kuma da yardar Allah sune masu nasara, cike da bacin rai Alhajin ya yabar gidansa tare da tabbatar mai ya tsammacesa...

D'auki ba dad'i aka shiga yi, sosai ya ya shiga busy a Dan tsakanin, na matukar sosai Aymanah ke k'arfafa masa dan har asibitin da aka maida yarinyar saida ya kaita ta dubota, ta samu sauki ba laifi duk da jikin da saura, waccen clinic din tuni Mai dala ya saye su sun canja komai, hakan yasa hukumar 'yancin Mata ta canja mata wani asibiti itace daukar da nauyin kulawa da ita, kotu sau biyu ana zama ana dage k'arar saboda rashin gamsassun shedu da basu samu ba, wanda zai tabbatar yaron ne ya aikata mata hakan saidai duk yadda Alhaji Mai dala yaso ayi watsi da karar bai yuyu ba saboda wasu shujjuji da Ya Mu'azzam ya kafa wadanda dole a basu uziri akan su a jira su, su kawo shedun su....

Barazana ta ko'ina samun ta yake daga mai dalan saidai wannan bai hanashi gudanar da duk abinda ya kamata ba akan case din, ba, musamman yadda yake samu kwarin guiwa daga iyayensa da Yan uwansa uwa uba matarsa Sahibarsa, na sosai yake kokarin samar mata lokacinta a cikin wannan yanayin..saboda sauke nauyinta...

Yau ne akayi zama na karshe Wanda dak'yar ya samu aka daga k'arar wannan karon har yarinyar anzo da ita da yake ta samu sauki sosai, gabatar da ita akayi tayi bayani da bakinta duk abinda ya faru, lauya mai kare yaron yayi mata tambayoyi ta amsa mishi, sannan aka gabatar da yaron, hankali kwance Mu'azzam ya taho inda yake yana sanye da wannan rigar da hular na lauyoyi Wanda ba karamin kara fitar masa tsantsar kyawu, kwarjini da haiba sukayi ba...

"Ko kasan wancen yarinyar?" Ya tambaye sa yana nuna masa ita, kallon ta yayi sannan ya mayar da kallon sa ga Mu'azzam din..

"Eh 'yar aikin gidan mu ce" murmushi ya saki sannan yace "meye alakar ka da ita?"

"Ni..ni meye alakata da ita ko, ni banda wani alaka da ita face dai nasan tana aiki a gidan mu" ya fad'a cikin dakewa duk da yadda muryarsa ke rawa, ga rashin gaskiya muraratan ya bayyana akan fuskarsa..

Murmushi ya kara yi mai sauti "Abbas kenan! Wato baka da alaka da ita amma ka kaita asibiti domin a zubar mata da ciki?"..

" objection my lord, wannan ai salon rikita masa tunani ne bai kamata mai tambaya yayi ma Wanda ake tuhuma irin wannan tambayar ba, taya zai ce ya kaita a zubar mata da ciki bayan baida wata alaka da ita"..

"Barrister Ibrahim ka kiyaye" amsawa yayi cikin girmama wa kafin ya nemi a bashi damar gabatar da shaidarsa, aka bashi....

Wasu papers ya fitar ya nunawa yaron "Abbas zaka iya gane wannan sa hannun waye?"

Wata irin zabura yaron yayi ganin takardun da ya rubuta sunansa da sa hannunsa, lokacin da ya kaita asibitin, bai ko bud'e baki ba yaji ya kara cewa "ko zaka iya gane wannan muryar?" A matukar rud'e yake jiyo muryarsa da yayi rad'au a cikin mp3 lokacin da yake bayanin yanaso a cire mata ciki ne matarsa ce saidai tayi k'ankanta da renon ciki da haihuwa....

Murmushi ya saki "malam Abbas Sidi mai Dala, me zaka iya cewa ko har yanzu baka da alakar komai da Zakiyya?"

"To..to..to...Dan Allah kuyi hakuri Sharrin shedan ne" yace a matukar rud'e ba tare da yasan me yake fad'a ba, zufa keto masa tace ta ko'ina, Alhaji Mai Dala dake zaune kamar mutum mutumi ransa a matukar jagule, shikam lawyer da ke kare Abbas d'in soke kansa kan bench din gabansu yayi...

Tattara mp da takardun Mu'azzam yayi ya mik'awa muhti shi kuma ya bawa alkali..

Bayan dogon lokaci da alkalin ya d'auka yana nazarin evidence din da kuma kalaman Abbas din rubuce-rubuce yayi sannan ya D'ago "Abbas sidi mai dala ka amshi laifinka ko har yanzu kana da ja?"

"Na..na.aminta ranka ya d'ade, wlh Nina aikata da kaina, amma dan Allah a yafemin sharrin shedan ne" tun da ya amsa laifin da bakinsa Alkalin ya mayar da hankalin sa ga rubuce-rubucensa...

"Bayan dogon zama da wasa da sharia da wannan mai laifin yayi mana, samun gamsassun hujjoji da tabbatar wa daga bakin mai laifi, wannan kotu mai daraja ta dubi girman laifinsa da bata lokacin mu da akayi an yanke masa hukunci dai-dai laifinsa a musulunce na bulala 80 na laifin aikata zina yana saurayi sai laifin kashe rayuwa wato cikin da aka zubar da kuka laifin tursasa karamar yarinya saboda zalinci an yanke masa shekara 15 a mak'argama, tare da horo mai tsanani da kuma tarar naira million 2, na jinyar da akayi ma wacce aka cutar" alkalin yace sannan yaci gaba da cewa..

"Sai asibitin da ta bada shedun karya akan wannan shari'ar kotu ta cita tarar million 1 na bayar da shedun zurr da boye gaskiya da tayi" buga hatimi yayi yana kammala bayaninsa....

Hawaye ne kwance a idon iyayen yarinyar tare da murmushin farinciki, ihu yaron keyi yana kiran sunan Dadyn sa lokacin da yan sanda sukazo wucewa dashi, shima uban idanunsa jajur kamar gauta ya kasa koda motsawa....

"Mun gode, mun gode sosai barrister Allah ya kara girma ya tsareka da tsarewarsa Allah ya shirya maka Zuria" sosai yaji dadin Addu'ar "Ameen Ameen nima nagode baba, Allah ya tsare na gaba"

"Nagode madallah Yaya, Allah ya saka da alkhairi" yarinyar ta fad'a, murmushi yayi mata "Ba komai Zakiyya hakkina ne na karbo miki 'yancinki, Allah ya baki rayuwa mai inganci nan gaba" godiya sosai suka kara yi masa sannan ya wuce....

"Am back Habibty!" Ya fad'a da d'an saurinta tazo tare da shigewa hannayensa daya ware mata "Sannu da dawowa Habib rouh! Ya case din? Ya kuka kare duk da fuskarka ta shedamin mune masu nasara"

Murmushi ya karayi tare da kara matseta a jikinsa yana shakar daddad'an kamshin ta "hakane baby Allah ya Dora gaskiya akan karya ya tubi raunin bayinsa ya sassauta mana komai munyi nasara we are d winner"

"Alhamdulillah bini'imatihi tatimmusalihat! Yaya nayi matukar murna muje kayi fresh up kaci abinci"

"Uh um baby na gaji da yawa yau ke zakiyim komai"

Murmushi tayi tare da kama hannunsa cikin nata "ur wish my command my Husby, yanda kace" zagaye hannayenta a kugunta yayi ya rad'a mata magana a kunne...

Zaro ido tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta "Allah nidai ba ruwana yaya"

"Chab!! Nikam da ruwana baby muje mana......""""

😔ouch wlh kwanakin nan sai a slow aci gaba da hakuri dai #One love😘😍#

*Siddiqa CE*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌍 *DUNIYA MAKARANTA* 🌍
Chapter 23 · 0% Book details