Sashe 16
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba abinda zance da Ubangiji sarkin sarakuna sai dimbin godiya a gareshi daya nuna mana wannan ranar, babu bukatar nayi muku dogon bayani komai a idonku ya wakana, ina fatar wannan ya zama izna a gareku, Ku d'auki darasi daga gareshi, inaso dukannin mu, mu d'auki wannan a matsayin kaddara, kada kowa ya d'orawa kowa laifi mu d'auke shi a cikin wata kaddara ta rayuwar mu, wannan kadai ya ishemu darasi a rayuwa, sannan inaso kowa ya tsarkake zuciyarsa ya fitar da duk wani kulli dake ransa, mu mu'amalanci juna da zuciya d'aya duk rintsi kada mu cutar koda an cutar damu, inshaa Allah komai tsawon zamani Gaskiya zatayi halinta, gaskiya d'aya kuma a killum itace kan gaba koda an kayar da ita zata taso ta kayar Ku rike wannan" sannan ya nisa ya kira sunan Dady..
"Kayi hakuri Kabeer na sani da zafi kuma da ciwo amma inaso ka d'auki wannan a matsayin kaddara a rayuwarka, kada wannan yasa kace zaka k'ullaci Suwaiba kayi hak'uri ka yafe mata, sannan ka nemar mata shiriyar ubangiji, tana tare da sharrin zuciya da kuma kaidin hassada, kada ka manta duk rintsi an Riga an zama d'aya tun da an had'a zuri'a da ita, ita uwar 'ya'yanka ce, bawai nace kada kayi mata hukunci bane aa, inaso dai kada ka yadda ka dauki mataki a cikin fushi, ka bari ka nutsu ka dawo hayyacin ka tukun, kayi hak'uri"
Hafiz da Samiha ya kira "kuyi hak'uri yarana kada wannan ya zamo kalubale ga rayuwarku sannan kada kuce zaku tsani mahaifiyarku akan wannan aa, addu'a ya kamata kuyi mata, sannan kada Ku itace mahaifiyarku Baku da sama da ita kome ta zama koya take dole Ku kyautata mata, kuyi hak'uri Ku saka wannan a cikin kaddarar rayuwar ku, sannan ke Samiha, ina fatar kin dau darasi daga yau ina fatar kin yasar da bak'ar akidar da kika taso a ciki inaso duka ki watsar da komai ki d'auki daidaitacciyar hanya"
Cikin shesshekar kuka tace "na gane Abba, wlh na gane kuma daga yau zan canja daga Banza ballagazar Samihar da kuka sani zuwa nagaratacciyar Samiha"
"Alhamdulillah naji dad'i sosai da hakan, Allah ya kara hade kan wannan family, ya barmu a matsayin *Zuria d'aya* tsintsiya d'aya cike da aminci" duk aka amsa da Ameen...
"Sannan ina so naja muku kunne, bana so naji ko naga wani nuna wariya ko gorantawa a tsakaninku duk nan d'aya ba banbanci Ku rike wannan a ranku" ya fad'i hakane Dan kar ko cikin bacin rai wani ya goranta wani Musamman su Samiha a goranta musu akan laifin mahaifiyar su...
Itama Hajja nata nasihar tayi sannan Momy ta d'ora Ammi ta saka albarka...
"Zo nan gareni 'yata Aymana zo gareni 'yata" cewar momy, cike da kunya Aymanah taje gurin ta, ta durkusa tare da sunkuyar da kai, dagota Momy tayi zuwa jikinta...
"Yata zaki iya yafewa irin wannan uwar kamata data watsar da 'yarta akan son rai, zaki yafemin 'yata Aymanah, ki soni ko kad'an ne duk da ban dasa son ba tun farko?" Rike mata Hannaye tayi sosai, tana hawayen farinciki...
"Aa Momy don Allah karki ce haka, wlh ina k'aunarki tun farko, kuma ni ban rikeki a raina ba ko kad'an kullum kallon uwa nake miki, naji komai daga Ammi kin nunan k'auna momy" jinjina kai Momy tayi tana tunanin Fatima wace irin baiwar Allah ce mai matukar kyan zuciya haka? Share mata hawayen tayi sannan tace "nagode 'yata..." Saurin katseta "Aa momy nice zan miki"....
Suma Samha, Samiha yafiyar Ammi da Aymanah suka nema duk aka yayyafe kai tsaye...
"Tau zaku iya tafiya, Allah yayi muku albarka baki d'aya" shima Dady albarkar ya sanya musu, har zasu tashi Abba ya dakatar dasu..
"Ibrahim!" Ya kira Mu'azzam, amsawa yayi cikin girmamwa "ka manta da komai past is past, ka dauki matayenka Ku wuce gida, a bar komai daya wuce a gina sabuwar rayuwa" sanin halinsa na kafiya ya saka shi yimai magana, amsawa yayi amma har cikin ransa baya da niyyar maida Samiha Dan ta fice masa arai gaba daya...
Kuka Samiha ta saki cike da kunar rai, nan fa hankalin kowa ya d'aga, sai tambayar ta ake meya faru, ko batason komawa ne, kasa cewa komai tayi sai dan neman kuka da take sharba, ran dady ne ya baci ganin yadda kowa ya rud'e a kanta gashi tak'i magana, tsawa ya daka mata yake ko ta fad'i meke ranta kota fice ta basu guri, Dan a ganin sa renin wayo ne shi Mu'azzam din bai ce bazai maida ita ba sai itace zata kawo iskanci...
"Haba Kabeer a bita sannu mana, zo nan 'yata ki gayamin meya faru?" cewa Abba..
Dakyar ta iya bud'e baki tace "Abba...au...aure. Aure ya kare tsakanina da ya Mu'azzam!" Tare da sakin wani kuka mai cin rai..
A zabure suna rige rigen tambayar dalilinta, ciki kuwa hadda Mu'azzam din da Aymanah....
"Abba zina nayi...zina na aikata da aurensa?" Nan ta warware musu abubuwan da suka shiga tsakaninta da boka wanda ko uwar da ta kaita gun sa bata sani....
Sallallami Hajja da momy suka shiga yi, yayin da su Dady ke furta innalillahi wa'innah ilaihirrajiun, Hafiz runtse ido yayi ransa na suya, yayin da Mu'azzam ya dafe kansa dake sara masa, Ammi sarkin tausayi tuni hawaye suka wanke mata fuska dasu Aymanah, Nusaiba, Samha har Zulaiha bare uwa uba ita Samihar dake kuka da duka karfin ta....
A zubure Dady ya mik'e tare da ficewa daga falon, Abba na kiransa amma ina saidai ko waiwaye baiyi, Umma ya isko daki tana jera kayanta a cikin akwati da alama tafiya zatayi, baiyi wata wata ba, ya danko wuyarta, sosai tayi yunkurin kwatar kanta saidai Sam bata samu wannan damar ba sai mutsu, mutsu take, ko magana ta kasa yi tsabar tsakar da tasha, saida ya tabbatar ta jigata sannan ya jefata kan sofa ya nuna da yatsa..
"Burinki ya cika Suwaiba kinyi nasarar kashewa 'yarki aure, kema kije na sakeki, sannan ki sani kin cutar dani kin cutar da 'ya'yanki musamman Samiha, wannan ne so ki kaita da kanki gurin boka ya lalata min 'ya?"
"Lalatawa!" Ta fada da karfi, tana dafe k'irji..
Kallon banza ya watsa mata tare da buga babbar rigarsa ya fice rai a matukar bace...
Hannu ta d'ora akai tare da kurma ihu "Wayyo mai gobe da nisa ka cuceni, Samihar tawa ka lalata min, Allah tsine maka tsinanne ya tsinewa saninka da nayi a rayuwa........."
🤷🏼♀ _kaikayi koma kan mashekiya_
*Siddiqa CE*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*Page* 4⃣5⃣
_______"Abba don Allah kayi wani abu, kada ka bari auren Aunty Samiha da Yaya ya lalace, Hajja kina kallo haka Zai faru, don Allah kuyi wani Abu Aunty tana son Yaya sosai komai da tayi akan son sa ne dan Allah Ku taimaka" Aymanah ke fad'a cikin kuka da tashin hankali kamar itace akace aurenta ya k'are....
Mamaki ne sosai ya kama mutanen cikin falon ganin yadda Aymanah ta hakikan ce iya gaskiyarta tana rokon su Abba, ciki har ta ita Samihan kanta, sai kallon mamaki take mata, tana tunanin iya Saninta iya zamanta da ita bata tab'a yi mata abun alkhairi ba, kullum burinta ya Kare ne a ya zatayi ta k'untata ita da Mamanta mata kamar yadda ta tashi taga Ummanta nayi kuma take sakata amma wai a yau itace ke bakinciki da bakincikinta take damuwa da damuwarta, lallai rayuwar Ammi da iyalanta abar koyo ce, sune nagartattu, rayuwar su abar burgewa da sha'awa ce sune masu koyi da karantarwar manzon Allah S.A.W na sowa dan uwansu abinda suke sowa kawunan su, na alkhairi, duk da cewa kishiyarta ce ita, amaimakon tayi farinciki miji ya zama nata ita kad'ai, lallai tana da kawun zuciya na sosai(dama Samihar ba jahila bace Kawai dai son rai ne mai kaiwa ga halaka) Allah kiyaye mu da son zuciya wanda yake kasancewa Bacinta.....
Murmushi Abba "Ummina wannan ba hukuncin mu bane, kamar yadda nasan ke ba jahila bace, dan haka duka mu d'auki wannan a matsayin kaddara, wacce take rubutacciya tun farko, muyi hakuri gaba d'aya mu rungumi kaddarar mu"
Kamata Momy tayi tana rarrashin ta, Hajja tace "wannan haka yake, kaddara ta riga fata, kuma wannan kukan kurciya ne, wanda sai mai hankali kan gane, Allah yasa wannan ya zamu izna gareta damu gaba d'aya...."
Ameen suka amsa, Dady ne ya shigo da sallama amma fuskar tamau ba sassauci, tuni yaran suka sha jinin jikinsu, Abba, Hajja, Momy, Ammi, da kallo suka bishi cike da fargabar meya aikata "Kabiru! Kaddai wani abu kaje kayi mata cikin fushi" cewar Hajja "ni nasan dan uwana bazai yi abinda bai kamata ba, meka aikata Kabir?" Kafin ya iya bud'a baki yace wani abu....
Saiga Umma ta fad'o a falon kamar wata sabon kamun hauka, a hargitse a ramutse, bako Sallama kamar wacce aka ingizo "wallahi karya ne Kabir, Allah karya ne baka isa ka sakeni ba, wlh kayi kad'an aurena dakai auren zobe ne, wlh kayi kad'an mutu ka rab'a takalmin kaza, ba inda zani ina nan saika mayar dani d'akina" haka ta ringa sambatu kamar wata zararriya sai zare idanu take, ganin abin zai zama hauka kuma duk da Abba baiso haka ba da Dady ya saketa cikin fushi, duk da a wannan gabar sakin shi kad'ai ya rage a matsayin maslaha a tsakanin su, watakil ya zama darasi a gareta...
"Suwaiba ki dena wannan shirmen ki samu gu ki zauna muyi magana a...."
"Ba zaman da zanyi, kuma ba ruwanka ban sako ka a ciki ba" tayi saurin katse Abban cikin haukarta da ta kamu da ita na wucin gadi...
Zabura Dady cike da haushi, wannan wane irin abin kunya ne a gaban yara "ka gani ko yaya? Kina kallo ko Inna?" Rikesa Dady yayi yana girgiza masa kai da shafa hannunsa, zama ya dawo yayi yana huci, ita kuma sai sakin maganganu take na rashin kan gado, sudai sauran mutane sai kallon ikon Allah suke yaranta kuwa bakin ciki kamar ya kar su..