Sashe 11
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Daga inda ka aikemu sallamamme, wlh Hafiz ka kiyayi ranar da zan juyo kanka zakasan baka da wayau" daga haka taja hannun Samiha sukayi ciki suka barshi anan tsaye, dafe kansa yayi Umma na bashi ciwon kai a rayuwa Sam baya k'aunar Hallayarta gashi tana so ta kashewa Samihar aure tunda ta koya mata komai ta iya, yasha zaunar da ita yayi mata fad'a da nasiha akan ta dena miyagun halayen da take musamman ma da tayi aure yana jin zafi sosai a ransa game da ita da mahaifiyarsu gashi ba halin yace ya gaya musu gaskiya Abu ya zama dan zane shiyasa da yayi aure ya d'auke k'aramar k'anwar su Sageera ya mayar inda yake da sunan yana so ta zauna tare dashi amma a ransa ya d'oketa ne kawai kada itama halayen uwar suyi tasiri a kanta kamar yadda sukayi akan Samiha..
Gashi 'yan kwanakin nan ta matsanta masa akan Nusaiba tace ya zama sallamamme bawan mace ko kishin 'yar uwarsa bayayi yadda d'an uwan Nusaibar ke gasata amma shi ya koma a gindinta ya tare sai abinda tace ko laifin ta baya fad'a shiko har ga Allah baida matsala da Nusaiba dan ta na nutsuwa da sanin ya kamata ko sab'ani ne suka samu suke sasanta kansu tana matuk'ar kokari wajen kula dashi da Sageera gaba daya Sam bata nuna masa wani banzan hali ba, kuma ai su duka *Zuri'a d'aya* asali daya to meye na wani bambanta wa a tsakaninsu, kuma ma ai duk abinda Mu'azzam keyi akan gaskiyarsa yake, sune basu da gaskiya kuma sun kasa yadda bare su nemi hanyar sulhu.....
B'angaren Momy kam abubuwa sun gama dame mata sosai ga matsalar Samha gata Mu'azzam abubuwa su had'e mata goma da ashirin, ga Samhar kullum cikin kuka duk ta fita hayyacin ta, dole ta dawo rarrashinta da bata baki, Mu'azzam kam ta kasa gane inda ya dosa duk da daurewa kawai take tana share shi da d'auke masa a kai a tunanin ta hakan zai sa ya dawo yayi abinda takeso, bangaren Abba ma ba dama ya bawa iska ajiyarsu, har kunyar Suwaiba takeji idan tana ganin Samiha a gidan duk da cewa laifi sukayi, shiyasa ma ta kasa samun ta suyi magana tsayayya, duk da dai cikin ranta baso take ba, Fatima kam gani take tafi kowa farinciki da abinda da ya faru da 'ya'yansu, amma take wani munafurki, maganinta zatayi daga ita har 'yar tata da Uwar mijin tasu gaba d'aya....
Mu'azzam ma b'angarensa a jigace yake abubuwa sun taru a kansa, sunyi masa over ga hukuncin shariya wa Aymanah daya d'aukarwa kansa, Wanda yake ganin shine best solution a gareshi duk da gangar jiki da Ruhi sun jigatu, ga shariyar da Momy ke masa duk akan Samiha shikam yarinyar ta gama sire masa akai gaba d'aya ko zaici gaba da zama da ita to sai ya tabbatar ta gyara halayyar ta....
Shiru-shiru har sati ba Mu'azzam ba labarin sa a Gwarzo, zuwa yanzu Aymana ta gama yaddar ma kanta son Yayan nata ne ke d'awainiya da ita, saidai it too late to cry, tun da yanzu bata gabansa ya barta kamar yadda ya fad'a ta kuma san yana magana ne da iya gaskiyar sa, lallai tawa kanta bak'ar dabara yanzu ya tayi dan son bada wasa yake yawo a jininta ba, duk tsayuwar motar da taji saita ringa tunanin shine saidai taga Su Abba kosu ya Adnan ko kuma mutanen Bauchi, kullum cikin tunani take wani sa'in hadda kwallarta saidai tana kiyaye idanun Hajja...
Abinda bata sani ba Hajjar ta dad'e da sanin halin da take ciki tadai yi mata banza ne taga iya gudun ruwanta tun da boko take mata, tadai dage da tsimata da gyarata da irin tasu dabarar ta tsofaffi........
Hajiya Samiha an zama 'yar hannu manyan customan bokaye kenan, haka ta cika satin ta tana zuwa wani katon kawai yana morar ta son ransa, fitarsu kullum yasa Dady yin magana akan yawon tace gurin koyon girki suke zuwa tun da ance sai sun iya girki za'a zauna dasu cikin gatse tayi masa maganar saboda yadda ya Saki baki akaci musu mutunci a taron, amsawa yayi da cewa yadai fi musu badan kanta kodon 'yarta, wucewa tayi tana Murmushin keta "zakuci gidanku ne Ku duka dan har kai saina kara jaddada rikon ka dan naga ka samu sassauci".....
Sati na cika Boka mai gobe da nisa ya bawa Samiha wani tandun kwalli yace ta shafa shi ta tabbatar sunyi ido biyu da Mu'azzam at any cost daga nan taja linzaminsa har ya kusanceta dariya ya sheke da ita sannan yace " badai shi ba saidai wani zata juya shi fiye da yadda ake juya waina" sannan ya basu wasu layu, yace ta binne cikin gidansu can tsakiyar dare to ta gama da duk wani mai magana ta rufe bakin kowa, a ranar sun dawo gida cike da farinciki Mara misaltuwa....
Washe gari suka shirya zasu fara gudanar da aikinsu wanka ta d'auka na fitar hankali ta rambad'a kwallinta sannan ta kirasa a waya, duk da yayi mamakin ganin kiranta dan shi rabonsa da ita tun ranar da akayi taron, da kamar bazai daga ba sai kuma yaga rashin dacewar haka, tun da har yanzu a matsayin matarsa take.....
Lankwashe murya tayi cike da kad'ayi tace masa dan Allah tana so ta ganshi da akwai maganar da takeso suyi mai muhimmanci, yanda tayi wani sanyi tana rokonsa sai ta bashi tausayi hakan yasa yace ta same shi a dak'in sa nada yana gidan......
Dan wasu lokuta a gidan yake zuwa yayi zamansa idan ya tashi daga office Ammi kawai ta sani dake ita ke bashi abinci, koda ta kirashi yana kan sallaya ya gama sallah yana karatun alqur-an mai girma....
Tsalle ta dama tare da fad'in "yes!" Da k'arfi taje ta labartawa uwarta yadda sukayi, itama cike da murna tace tayi sauri taje ta kuma tabbatar tayi komai yadda ya dace.........
Da sauri ta fice tana fad'in "kamar kina Zaune Ummana"........
😭😭😭 _Allah ka tsare bayinka da sharrin shihiri_
*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*_Idan kana sallar dare kada ka rena masu bacci, akwai da yawa 'yan aljannah wadanda an fisu Aiki, da tsarkin zuciya suke kere mutane, mu tsarkake zukatan mu.👌🏻_*
Duniya Makaranta✍🏼
*Page* 4⃣0⃣
_______banke k'ofar tayi bako sallama ta fad'a, tana fad'in "Where r u my heart beat? I really missing u Yaya" cikin wata irin muryar mai cike da kissa da shagwab'a dan tasan yana son Shagwab'ar....
Ci gaba da karatunsa yayi saidai zuciyarsa sai wani mugun harbawa take da sauri-sauri, ga fad'uwar gaba na musamman da taji lokacin da ta shigo, hakan yaji kawai bai yadda da ita ba, saida yakai inda yake buk'atar tsayawa sannan ya rufe Qur'anin tare da rungumesa a k'irjinsa yana kwararo addu'o'i, sosai yaji nutsuwa ta saukar masa ( 'yan uwa sihiri gaskiya ne saidai yana tasiri ne da izinin Allah, kamar yadda addu'a ta kasance takobin mumini, nasan wasu zasuce ta yaya duk akayi ma su Mu'azzam sihiri baya kamasu, bayan ya tab'a kama mafificin mafifita sayyidina rasulillah, to abinda nakeso ku fahimta sihirin da akayi Manzon mu ya kuma kamasa wata aya ce Allah ya saukar mana kuma ya buga misali akan mafi soyuwa agare shi domin ya tabbatar mana da sihiri gaskiya bawai dan sun isa ko sun kai suyi masa sihirin ba sai dan kafa aya agaremu Al'ummar sa, saidai ku sani kamar yadda sihiri yake gaskiya haka ma Addu'a gaskiya ce kuma takobin Mumini kuma duk wanda ya riketa a rayuwar sa yafi karfin mutum bare aljan, koda kuwa anyi nasarar galaba akansa tabbas zai karye ba da dad'ewa ba muddin ya rike addu'a Allah ya bamu ikon riko da addu'a ya tsare mana imanin mu da mutuncin mu, ya kare mu da sharrin masu sharri da hasadar masu hasada ameen).
"Haba dear nah, bayan kace nazo shine ka wani shanya ni anan, pls kayi hak'uri ka dena fushin wlh bazan k'ara ba...."
"Enough..ni bana fushi dake, kece kika shigo bako sallama kamar ba musulma ba, kuma ai isko ina karatu ko?"
"Afuwan Yaya mantawa nayi" tace tare da komawa tayi sallama, amsawa yayi ba tare daya d'ago ba, zuwa tayi dab dashi ta zaune tare da kamo hannunsa ta saka cikin nata sai bin shi da kallo tace tana wani murmushi "Yaya!" Ta kirashi cikin wata irin murya...
"Ina jinki meke tafe dake wata irin magana ce?"
"Haba yaya ko kallona fa bakayi ba alaman har yanzu fushi kake dani.." Ta sake fad'a cikin kirsa da jan hankali.....
*****************
Yau kam ta kai mak'ura gurin dauriya, yanzu ta gama tabbatar wa kanta son yayan nata ya jima tare da ita, sai yanzu take gasgata maganganun Nusee da take cewa wlh tana son yayanta dashi kansa da yake cewa tana sonsa tadai kasa ganewa ne, saboda son hukunta shi akan laifinsa da ta saka a gaba...
Tabbas yanzu ta gama gasgatawa gashi shi ya manta da ita ko waya bai tab'a yi mata ba, bare yazo har kiransa tayi bai daga ba, kanta ya d'au zafi dama Ashe haka so yake da zafi? Ashe kenan ba son Uncle Salman tayi ba a baya, girmama shi kawai take yanzu ne tasan ainihin meye so, gashi kuma da zafin ta fara, Ashe haka Ya Mu'azzam d'in ta ke azabtuwa a lokutan baya lallai bata kyauta masa ba..
Wayar ta d'auka tare sake danna masa kira, inda tuni ya tashi daga Mugu zuwa my Khaleel saidai har ta tsinke bai d'aga ba, fashewa tayi da kuka tare da cillar da wayar, kusa kanta tayi cikin filo taci gaba da rera kukanta....
Hajja dake jikin labulen d'akin tun dazu tana kallon wainar da take toyawa, shigowa d'akin tayi tana salallami tana tafa hannu "me zan gani 'yar nan me aka miki kike kuka da farar safiyar nan" ta gaji da b'oyewa Hajja, muddin bata fad'i damuwar ta tana iya kamuwa da ciwo, fad'awa jikin Hajjar tayi tare daci gaba da rera kukanta...
"Oh ni Balkisu diyar Mamman! Kinga 'yar marainiyar Allah dena kukan nan idan baso kike na kama maki ba, ki gayamin menene?"