Sashe 28
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma duniya ta gama juya mata baya, dama ance idan kaga duniya bata baka kashi ba ka dena farinciki watakila tana gurin debo tsumagiyoyin ne, dama hausawa na cewa tafi bagaruwa iya jima, aiko ta jefe da Umma, Sosai zaman gidan Yayanta yayi mata matukar zafi, jinta take wane tana saman kaya, duk daukar kai jiji dakai da tak'ama ta nemesu ta rasa, Hajia Suwaiba mai wasa da nerori yau itace nera Biyar ke bata Sha'awa, tayi kuka tayi nadama mara iyaka, kullum saita roki yayan ta dan Allah yaje ya nema mata gafarar Dady take ya taimaka ya mayar da ita wlh ta gane kuskurenta a nema mata gafarar Abba dasu Ammi, dan Allah ya mayar da ita gurin yaranta, kullum maganar ta kenan, zaman daki kuwa wane matar takaba, tuni ta siyar da trolleys din ta da wasu daga cikin suturun ta ta cinye kud'in a cikinta, idan ka ganta ba zaka shede ta yadda ta jeme ta lalace tayi baki....
Tsakanin ta da matan gidan saidai harara da kallon banza, ga yaransu Sam basa jin maganar ta, sun gama renata, tayi laushi sosai kai ba kace Suwaiba ce mai bakin taurin rai da Zuciya ba, ta gane duniya ce ke rud'ar ta, kullum cikin kukan nadama da istigfari take, imana Dady zai barta taje gidan ta nemi yafiyar su....
Yau ma guraren karfe 3:00pm tana zaune kan darduma tana jan carbi tun da tayi zuhr bata tashi ba, sallamar yayanta ta jiyo bakin k'ofa hakan yasa ta amsa cikin sauri dan ta d'auka yazo yayi mata d'an ihsanin da ya saba yi mata ne idan ya dawo daga kasuwa na bada 200h ko 500h wani sa'in "bismillah Yaya shigo" ta amsa mishi...
Dogarewa da kulkin k'ofar yayi tare da d'aga labulen yana hangota, sannu da dawowa tayi mishi bayan ya amsa yace "baki ne dake suna soro kiyi maza ki kimtsa" yana gama fad'a bai jira amsarta ba ya sauke labulen tare da wicewa..
"Bak'i?" Ta maimaita yafi sau uku, kafin ta yunk'ura ta tashi, cike da tunanin su waye kodai manema ta fara samu ne, inko hakane zatayi auren dan rufin asirin ta, dan zuwa yanzu ta gama cire tsammanin Dady zai waiwaye ta, hawayen tausayin kanta da kanta suka wanke mata fuska wato son zuciya bacinta bata ga 'ya'ya bare miji.....
Turus taci burki take da tsayawa tana zaro ido waje, mamakin ganin Dady har da Abba ya gama cikata, saida yayanta yace ta karaso sannan ta iya d'aga kafafun da sukayi mata nauyi zubewa tayi gabansu tana kwasar gaisuwa kamar mai Neman gafara, mamaki ne ya ishe su na farko ganin yadda ta koma na biyu kuma ganin yadda take zuba musu gaisuwa kamar ba itace tayi musu tujara ba...
Amsawa sukayi sannan ta samu gefe ta labe kanta kasa, zuciyarta sai harbawa take dan batasan takamammen me sukazo dashi ba....
Abba yayi gyaran murya "Malam Mu'azu kamar yadda na gaya maka ba wani dogon zancen zamuyi ba, nazo nemawa kanina kara auren Suwaiba ne a karo na biyu" zabura Suwaiba tayi kawai sai ganinta gaban Abba sukayi "Yaya Aurena fa kace? Kara bani wata damar zakuyi kenan? Zaku sake barina a cikin zuri'ar Ku kenan? Wace irin kyakkyawar zuciya ne daku? Zuciyar yafiya da rangwame, nagode nagode yaya, dan Allah Yaya kafemin kayimin gafara wallahi na tuba na gane kuskurena kuma nayi alk'awarin komawa cikin Zuri'ar ku da zuciya d'aya, na canja wlh na canja daga Suwaiba mara imani da son zuciya zuwa Suwaiba ta gari..."
Dakatar da ita Abba yayi da Hannu kafin yace "komai ya wuce Suwaiba, Allah ya shige mana gaba" Dady kam komai k'in cewa yayi duk da tausayin ta yad'an darsu a ransa saboda ko ba komai sone ya hadasu kuma hadda zuri'a, basarwa kawai yayi dan ya auna hankalinta kota shiryu da gaske ne ko algus ne...
Nan kuma Abba ya sheda musu auren Samiha da za'ayi wata mai zuwa sannan yace zasu dawo wani sati sai a mayar da auren su Umma, taso ace yau dinnan aka mayar saidai ba yadda ta iya dole ta hakura har wani satin kada aga zalamarta amma anata son ran taso a d'aura yanzu kawai su wuce tare( 🤣 wuya ba dad'i, waya gaya miki gombe gabas take)..
20k Abba ya dire mata yace ko zatayi wani abin, dan da ganinta kaga mabukaciya aiko hannu na rawa ta amsa tana kwarara godiya uwa marokiya, ya bawa yayanta 10k, da zasu wuce ko sai kallon Dady take ji take kamar taje ta rumgume shi ta gayamai how much she missed him, gashi har zai tafi ya hanata jin koda muryarsa ne.....
Lokacin Abba ya gayawa su Momy dawowar Umma, sosai tashin hankali ya bayyana a tare da Momy har saida ta furta "dawowa kuma Alhaji" jinjina mata kai yayi "tabbas dawowa saidai ina muku albishirin zata dawo ne da kyakkyawar niyya" Fatan alkhairi sukayi kawai, yaran ta ma sunyi farinciki da jin zata dawo tun da koma meye itace dai uwa mahaifiya a garesu, saidai basu nuna a fili ba gudun kada marikan su, su d'auka ko sun rena da k'ok'arin su ne, barin ma Samiha da suka yiwa komai....
Kamar yadda sukayi alkawari sati na zagayowa suka d'auko kawun su daga Gwarzo, dama yasan da zancen, itama Nasu kawun yazo nan take aka mayar da auren bayan Abba ya biya sadaki, ana gama d'aura auren Amarsu ta tattaro 'yan Tsummo karanta bako 'yan rakiya ta biyo zugar angwaye😆 ba laifi tad'an washe ta rage ramar da bakin kad'an nace 20k Abba sunyi taimako...
Matan yayyin ta, ma sai ranar auren mai gidan ya sanar dasu, aiko lokacin da tazo musu sallama jikinsu sanyi qlau yayi sun san kalar rashin mutuncin da sukayi mata bazai fad'u ba, dan sun d'auka ba zata koma gidan ba, itadai ko ta Kansu bata bi sai murmushin ta na farinciki da takeyi, murmushin da ya kara nutsar dasu kogin kunya..
Suna isa gate kafin gate man ya bud'e musu ta saki sassayar ajiyar zuciya tare da yin hamdala wa ubangiji daya azurtata da wannan ranar...
Mamaki ne ya kamasu ganin yadda aka gyara harabar gidan Ashe walima ce suka shirya musu, wadda Hajja ce tayi Jagorancin ta, duk yaran gidan sun hallara inka cire Zulaiha da bata gari....
Umma na fitowa tayi arba dasu kowa cikin shiga ta Alfarma, kallon kanta tayi da kayan jikinta sanyi jikinta yayi sosai lallai bata kyauta ma kanta ba, sai taga ma duk sun sake sun kara wani kyau na musamman...
Ruu sukayo kanta suna murmushi tare da yi mata barka da zuwa, kunya ce ta lullub'eta sosai ta kasa motsawa sai kasa da tayi da kanta...
Zube gwiwowinta kasa tayi tare da kama kafafun Hajja "Inna dan Allah kiyi hakuri ki yafemin..." Saurin dakatar ita hajja tayi tare da mikar da ita suka rungume juna "karki ce komai Suwaiba Allah ya yafe mana baki daya" hawaye sosai kebin kuncinta "Ameem nagode Hajja" kallon Momy tayi "aunty Zainab..."
"Aa Suwaiba komai ya wuce Allah ya yafe mana baki daya"
Cikin rauni ta kalli Ammi "Fatima dan Allah..." Saurin rufe mata baki tayi "komai ya wuce Aunty Suwaiba wannan kaddarar rayuwar mu haka, Allah ya kara mana hadin kai da fahimtar juna"
Momy ta karasa da "ya kuma Kore shed'an da son zuciya a tsakanin mu" Ameen suka Amsa a tare har yaran...
_My friends sai kun kara hakuri dani, abubuwa ne suka min caa wlh shiyasa, amma Ku sani kuna raina😍😍😘_
*Siddiqa CE*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
🌎 *Duniya Makaranta* 🌎
_Aboki zama biyu ne a rayuwa, wanda zaka karu dashi da wanda zai karu dakai, na ukunsu banza ne, ka/ki gujeshi_👌🏻
*Page* 5⃣6⃣
________Hannu ta sanya ta jawo Aymanah zuwa jikinta "kiyi hakuri kiyafe min ba dan halina ba domin Allah 'yata" jinjina kai tayi "komai ya wuce Umma, Alhamdulillah da Allah ya nuna mana wannan ranar mai albarka" gefen hannunta tasa tare da goge kwallar da ta zo mata, tana murmushin takaici da jin kunyar abubuwan da ta aikata a baya "Haba keko Umman Sageer ki dena irin haka mana, kada fa ki manta ranar ki ce yau kefa Amarya ce" Ammi ta fad'a da sigar tsokana dan da kawar mata da wasu kaso na halin da take ciki, dariya sukayi a tare har hajja, sauran yaran mata suma sukayi murmushi, duk yadda Umma taso ta sake ta kasa gani take kamar har yanzu suna kallon ta da abin da ya faru a baya ne...
Sai daf da magrib aka kammala kwarya-kwaryar Walimar, daganan suka wuce cikin gida aka gabatar da salloli, dama tun rana su Nusee suka gyara part din na Umma, Aymanah ma da ita akayi saidai bayan ciwon baki ba abinda ta aikata musu dan su Aunty Samha sun ce ba wani aiki da zatayi tanaji da kanta, Nusee tace wariyar launin fata dai tun da suma jin suke da kawunan su, bayan gwalo da tsokana data sako su gaba dashi, su kuma sai mita suke......
Bayan isha Su Momy suka raka Umma part din ta bayan Su Mu'azzam, Adnan, Hafiz sun shigo wucewa da matayen su, nan ma dai rokon yafiyar su Umma tayi suma sukace bygone by bygone, farincikin Hafiz kam ayau ya kasa boyuwa sai Murmushi yake yau shima Mahaifiyarsa ta dawo turbar gaskiya.....
Duk yadda Dady yaso basarwa saida Umma ta shawo kansa da lallashi da rokon gafara da kwantar da kai, sannan ya sauko ya kuma yafeta daga baya kuma labari yasha banbam Ashe dai gyatumi yayi missing din gyatuma shima nan aka shige duniyar k'auna (oh 🤭 tsofai-tsofai su gwaggo🤪)....
Zaman lafiya na sosai wanda ahalin basu tab'a tunanin samu bane ke wanzuwa a gidan, kowacce a cikinsu ta tsarkake zuciyarta tana zama billahi ilallahi, sosai farinciki ya wadatu da annushawa a cikin gidan, wanda sai a yanzu suma suka fahimci Ashe wancen zaman rikicin cikin gidan da sukayi a baya ba Ammi kadai ya cutar ba har su, Ashe dai gaskiyar hausawa da ke cewa zaman lafiya yafi zama d'an sarki....